A HALF FULL LIFE
NETHERLANDS, AMSTERDAM.
Ɗakin taron ya yi shiru.
Ba irin shurun da yake sa mutum jin rashin natsuwa ba, A’a, irin shurun da yake faruwa idan kowa yana jiran tsammani, ko jiran bayani.
A ƙarshen dogon glass table din, Zayd ne a zaune, wani qasaitaccen saurayi me kimanin shekaru 42, kallo zaka yimishi ka sauke idonka saboda irin kwarjini da haiba da ke lullube da fuskar shi, Laptop ɗinsa dake gabansa kuma reports ne daban-daban suke bayyane a kan screen ɗin. Kusan mintuna ashirin kenan yana sauraron kowa ba tare da ya katse su ba.
Zayd mutum ne me tsantsar nutsuwa sosae, saboda haka Ba ya buƙatar ɗaga murya domin mutane su girmama shi, Ba ya buƙatar ya tunatar da kowa cewa shine CEO, Kasancewarsa a cikin ɗakin kadae ya isa yasa kowa yasha jinin jikin shi. shekaru da dama Zayd ya dauka yana gida sunan sa dana kamfanin sa, Shi ne ya kafa Meridian Axis Group, wani babban kamfani da ke Netherlands, a cikin garin Amsterdam, wanda suke harkokin logistics, technology, gine-gine da filaye, se kuma international trading.
Ya fara kamfanin ne da ƙaramin office da ma’aikata kaɗan, cikin ikon Allah da jajircewa, da kuma dagiya akan burinshi, kamfanin ya bunƙasa sosai, har ya samu ofisoshi a ƙasashe uku tare da dubban ma’aikata
Zayd ya gina komai from scratch yasa qarfinsa, kudinsa, lokaci da kuma tunanin sa. Tun farko ya zaɓi ya nisanta kansa da kasuwancin mahaifinsu saboda gina nashi buri shiyasa ya bar gida, Yayin da dan uwansa ya zauna a Najeriya, ya fara jan ragamar kasuwancin mahaifinsu tun sanda mahaifin nasu ya fara tsufa har kawo ynzu da be raye.
Yana son ya gina kansa da sunan sa ba tareda dogaro da mahaifinsu ba.
“The numbers don’t make sense.”
Muryarsa ta katse shirun ɗakin.
Financial Director ɗin ya ɗago kai.
“Sir?”
Zayd ya juya laptop ɗin kaɗan zuwa gare shi.
“You projected a twelve percent increase in operating costs for the next quarter. Explain it.”
Mutumin ya gyara zamansa.
“Sir, the increase is mainly due to..”
“I know what it’s due to.”
Muryar Zayd ta katse shi cikin natsuwa.
“I’m asking why you approved it.”
Mutumin ya yi shiru na ɗan lokaci.
Babu wanda ya motsa a cikin ɗakin.
Zayd ya kalle shi na wasu seconds kafin ya jingina da kujerarsa.
“We don’t spend money simply because we have it.”
Ya maida kallon sa ga dukansu sannan yaci gaba
“Every decision we make has a consequence. If you want this company to grow, you have to start thinking beyond this quarter.”
“Yes, sir.”
Zayd ya ɗaga kai.
“Reduce the unnecessary expenditure. Review the contracts again. I want the revised report on my desk by Thursday morning.”
“Yes, sir.”
Ya juya ga wata ma’aikaciyar da ke zaune a ɗaya gefen teburin ya kalleta kadan ya kauda kae
“And the Lagos expansion?”
Matar ta gyara zamanta.
“The permits are almost complete, sir. We’re expecting final approval next week.”
“Almost isn’t complete.”
Matar ta yi shiru.
“Yes, sir.”
“Don’t tell me what you’re expecting. Tell me what you know.”
Ta haɗiye yawu.
“We will have the approval by Monday.”
Zayd ya ɗaga kai.
“Good. Then I’ll expect confirmation on Monday.”
Ya rufe file ɗin da ke gabansa.
“That’s all.”
Kowa ya fara tattara takardunsa.
Amma kafin su fita, Zayd ya sake magana.
“One more thing.”
Kowa ya tsaya.
Zayd ya kalle su.
“I heard that some members of the junior team have been working until two or three in the morning.”
Babu wanda ya amsa.
“That’s not dedication.”
Fuskarsa ta ɗan tsananta.
“That’s poor management.”
Wasu daga cikin mutanen suka kalli juna.
“If a department can’t finish its work during reasonable working hours, find the problem. Don’t solve it by exhausting the people working under you.”
Ya kalli shugaban sashen kai tsaye.
“Your people are not machines.”
“Understood, sir.”
“Good.”
A wannan karon, kowa ya fita da tunanin gyaran da aka musu tareda neman hanyar gyarawa, mataimakinsa be fita ba se gyara zama da yayi sannan yace
“Sir.”
Zayd ya ɗauki wayarsa.
“Yes?”
“Your mother called again.”
Hannun Zayd ya tsaya.
“When?”
“About twenty minutes ago.”
Zayd ya sauke numfashi a hankali.
“And you’re just telling me now?.”
“Sorry sir”
“You can go.”
“Yes, sir.”
Ɗakin ya sake yin shiru.
Zayd ya tafi wajen glass wall din office din da zaka iya hango babban birnin iya ganin ka, Amsterdam na shimfiɗe a gabansa, Dogayen gine-gine, Motoci suna tafiya, Mutane suna ta harkokinsu, Kowa yana harkar gaban sa, Ya daga waya ya kira mamansa
“Assalamu alaikum, Mammi .”
Muryar Mammi ta shigo cikin sauri.
“Wa alaikum salam. Yanzu ka tuna kana da uwa kenan?”
Zayd ya lumshe ido na ɗan lokaci.
“Mammi..”
“Kar ka ce Mammi ka yimin daadin bakin da ka saba. Kullum aiki, aiki, aiki. Har ka manta da gida.”
“Ban manta gida ba.”
“To yaushe za ka dawo?”
Zayd ya kalli babban birnin da ke gabansa.
“Ba da jimawa ba.”
“Ba da jimawa ba?”
Ya kusa jin yadda Mammi ke kaɗa kai.
“Shekaru nawa kake ta faɗin haka?”
Zayd ya yi ɗan murmushi.
“Zan dawo.”
“Zan dawo kawai? Zayd, kullum haka kake cewa.”
Ya yi shiru.
Sai Mammi ta sauya sautin muryarta.
“Zayd…”
“Na’am, Mammi.”
“Allah ya nuna mini ranar auranka, idan kayi aure ko bakaso dole matarka ta rinqa jawoka kuna zuwa gida.”
Zayd ya yi shiru.
Mammi ta ci gaba.
“Shekara arba’in da biyu fa. Har yanzu kana nan kai kaɗai. Kana ganin ni ba na son in ga ka yi aure ne ko banason ganin jikoki na?”
Zayd ya jingina da glass din
“Mammi, aure ba aikin gaggawa ba ne.”
“Ba gaugawa nike maka ba, Kai ne ka mayar da shi kamar bazaka taba yi ba ai.”
Zayd ya yi murmushi.
“Insha Allah.”
“Insha Allah me?”
“Insha Allah zan yi aure.”
Muryar Mammi ta canza nan take.
“Yaushe?”
Zayd ya yi murmushi a hankali yache
“Mammi…”
“Ni dai ina son in ga wannan ranar kafin Allah Ya kira ni.”
Murmushin da ke fuskar Zayd ya ɓace.
“Kada ki ce haka, Mammi”
“To ka bani dalilin da zan daina cewa.”
Zayd bai amsa ba.
Mammi ta sauke ajiyar zuciya.
“Ka kula da kanka.”
“Zan kula in shaa Allah”
“Ka ci abinci.”
“Zan ci yanzu”
“Kada ka kwana a office.”
Zayd ya kalli laptop ɗin da yake kan teburin.
“Zan yi ƙoƙari in shaa Allah”
“Ba ƙoƙari nake so ba. Alkawari nake so.”
A karo na farko cikin kwanaki masu yawa, Zayd ya yi murmushi
“Na yi alkawari.”
“To shikenan. Allah ya tsare ka.”
“Amin. Ke ma mammi na”
Ta kashe wayar
Zayd ya ajiye wayar a kan teburin.
Na wasu seconds, ya tsaya yana kallonta.
Mammi na ɗaya daga cikin mutanen da suke iya sa shi ya manta cewa shi babban CEO ne mai shekara arba’in da biyu.
A gabanta, shi ɗanta ne kawai.
Babban ɗanta.
Wanda take yawan damuwa da shi.
Wanda take yi wa addu’a.
Wanda har yanzu take jiran ranar da zai shigo gida da amarya.
Zayd yana matuƙar son familyn shi, kawai shi irin mutanen nan ne da basu iya bayyanar da abnda ke cikin ran su ba
’Yan uwansa sun san haka shiyasa basu damu ba, Suna girmama shi sosai kuma Suna ƙaunarsa.
Amma kuma suna jin tsoronsa, Musamman idan ya fusata. Qaninsa shine akasin sa gabadaya, ya bambanta dashi sosai, shi ne wanda kowa ke gudu zuwa wurinsa in suna neman qwarin gwiwa, Shi yasan kowa a family, kuma kowa yasan shi very friendly kuma kullun cikin murmushi, Shi ne wanda yake iya zama suyi da dariya da Mammi sosai, Shi ne wanda ya san abin da yan uwa suke buƙata, shine wanda yasan kowa na son shi a family
Tun lokacin da mahaifinsu ya fara tsufa, harkokin kasuwancin kamfanin suka fara mishi nauyi , shi ya ɗauki nauyin gudanar da harkokin kasuwancin.
Yana ƙoƙari sosai, Kuma ya yi nasaran kawo ci gaban kasuwacin mahaifin nasu, Mutane da dama sun amince da shi, har suna muamala irinta mahaifinsu dashi. Yan uwansu suna girmama shi, musamman da shine dan gida kuma shi aka sani, Hatta tsofaffin abokan kasuwancin mahaifinsu suna yaba masa saboda kokari da kwazon da yake akan kasuwancin, Zayd ya san da haka shi yasa ke alfahari da ƙanensa sosae.
Yana nan tsaye shuru yanata tunani, shi yaushe yaga lokacin soyayya balle a kai ga zanchen aure? Anya shi kam zeyi aure ma kuwa? Gabadaya kallon shirme da bata lokaci yake yima soyayya, yana cikin tunani Wayarsa ta sake yin ƙara, wannan karon, kanensa ne, kamar yasan tunanin shi yake, fuskarsa ta qara sakewa sannan ya daga
“Hello.”
A Chan bangaren yache
“Hy big brother!”
Zayd ya ɗan yi murmushi.
“Me kake so?”
“Me yasa sai inason wani abu sannan zan kira ka?”
“Saboda yawanci haka kake.”
Fahad ya yi dariya.
“Wallahi ka karanche ni tsab.”
Zayd ya girgiza kai.
“Me ke faruwa?”
“Babu komai. Ina so ne kawai in ji muryarka.”
“Toh Ka ji ai, se anjima”
“Bro, ka daina haka manah Mutum ya kira yana son hira, kai kuma sai ka rinqa amsa magana kamar ana interview.”
Zayd ya yi murmushi.
“Kana da wani abun fadi ne?”
“Eh.”
“Na sani.”
Fahad ya sake yin dariya.
“Akwai wani biki da za mu je yau gamu hanyar airport, sokoto zamuje.”
“Bikin wa?”
“Na Safiyya”
Zayd ya ɗan yi shiru.
Sunan bai tuna masa da komai ba.
“Safiya wace?”
“Safiya ’yar mama Rukayya da ke sokoto, Ka manta?”
“Ban santa ba ma”
“Ai ko dai bazaka santa ba. Kullum kana can Amsterdam, anyi arziki baka manta da ita mama Ruqaiya din ba”
Zayd ya kalli agogon da ke ɗakin.
“To se kun dawo.”
“Fahad.”
“Na’am?”
“Ka kula da Mammi.”
shiru ya gitta tsakanin su.
Sai muryar shi ta yi laushi.
“Inshaa Allah.”
“Nagode.”
Daga nan Zayd ya sake ɗaukar laptop ɗinsa.
Yana qoqarin ya daidaita Hankalinsa ya koma kan aikinsa,amma ya fara tunanin wai ko dai yayi auren ne kawai kamar yadda mammi take buqata? Yasan in ba yi yayi ba bazata dena damuwa da maganar ba, in dai ba haka ba toh shi besan ranar da ze fara soyayya ba balle yayi aure. Ya dade zaune yana tunani daga qarshe dai ya kira secretary dinshi, ya dauki kayan shi suka fito daga conference room din, “sir are we going to your office?” Secretary din ya tambaya “No I’m going home” ya amsa, secretary din ya kalleshi da Dan mamaki saboda yasan ogan nashi be tashi aiki kullun se dare, da sauri da sauri ya dauki waya yayi magana da driver yache ya fito da mota Mr. Zayd Rahman is leaving. Koda suka isa kofar already driver na waje, bude mishi kawai akayi ya shiga ya zauna aka rufe suka kama hanyar gidan shi, sun dauki kamar 30 mins suna tafiya sannan suka shigo unguwar apollobuurt, suka dauki hanyar apollolaan street suka tsaya a gate din house no 17, security ya danna wani abu gate din ya zuge suka shiga ciki, zaid be jira an bude mishi qofar ba shi ya bude ya fito ya nufi hanyar main parlor ya danna wani abu se qofar tayi scanning face din shi ta bude, yana shiga ya wuche upstairs, driver dinshi kuma da ya shigo da jakar laptop da files se ya shiga wani daki a nan qasa, alamar study office ne yadda abubuwan karatu da rubutu da computers suke a dakin, ya ajiye su kan table din ya fito ya tafi, gidan me girman gaske ne kuma upstairs daki daya ne kawai (master bedroom) se a qasa akwai daki uku, da study dinshi da private gym dinshi wanda ke cike da qarafuna daban daban na motsa jiki, se kuma underground da ya maida kamar private home cinema, wurin kamar parlor ne saboda qatuwar tv din da ke maqale full a bangon dakin, se qatuwar sofa da ake iya converting dinta a maida ita gado wanda ke cike da pillows ash color, se kuma quilts masu laushi sosai da ke a nade a jere daga gefe daya suma ash color, komi na gidan zaid white and ash color ne
Zaid kuwa sadda ya hau sama wanka yayi sannan ya sauko qasa sanye da bathrobe fara, sadda yake saukowa kallo daya zaka mishi kaga cikakken namiji me ji da karfi, fari ne amma ba irin tas dinnan ba, yanada tsayi da cikar halitta, direct ya shiga kitchen ya bude fridge ya dauko wani canned ice coffee ya dawo parlor ya zauna ya chigaba da tunani.
Sai dai a daidai wannan lokacin kaddararsa ko kuma ince kaddarar su ta kirasu, kaddarar da bata san nisa, girma ko shekaru ba, kaddarar da take wani yanki daban, wata duniyar daban, kaddara ce da bata san kudi ba, ko wata daukaka ballantana kasuwancin da aka dade ana ginawa, kaddarace da zata tono sirrukan da aka binne shekara da shekaru!
Qaddarar Maryam!
Join our WhatsApp group
Follow this link to join my WhatsApp group: ***