WAY TO SOKOTO
Washegari, da safe Fahad ya kai mammi airport zata wuche Abuja shi kuma ya dawo cikin gari ya qarasa abubuwan da zeyi a sokoto branch na Northern Crest Holdings sannan next day shima ya wuche Abujan
Daya daga cikin drivers dinshi suka dauko shi daga airport zuwa gida, yana isowa yayi wasu yan aikace aikace da system dinshi sannan ya kimtsa yayi wanka ya fito ya shiga part din Mammi.
Mammi na zaune tana riqe da wayarta da alama wani abun take kallo, yayi sallama ya shiga
“Mammi.”
“Naam yaron mammi, ka iso lfya?
“Lfya alhamdulillah hope kin huce gajiyar biki?”
“na huta tun jiya saura kai daka dawo yau ka samu ka huta”
Fahad yayi smiling ya zauna a kujerar da ke kusa da ita.
Ya ɗan yi shiru kafin ya ce,
“Mammi maganar yarinyar da kika ga na kai gida a sokoto ranar da na dauko ki daga gawon nama.”
Mammi ta ɗago kai, da tunanin ko Fahad yache yanaso Yayi aure ai zata yimishi tunda Zayd dai ga alama be tashi ba
“Eh kayi min maganar ta tun wurin bikin ai kafin na ganta, kache zaka yimin magana game da ita, lfya?”
“Sunan ta maryam”
Mammi ta ɗan kalle shi.
“Maryam?”
“Eh, maryam”
“Toh ya akayi akwai wani abu ne? Tun wurin event kache zaka nuna min wata yarinya, se gashi ka dauko ni da ita a mota?”
Fahad ya yi murmushi.
“Ina ganin za ta dace da Zayd.”
Mammi ta ajiye wayarta ta kalleshi dakyau
“Shi ya baka kwangilar nema masa mata ne?”
Fahad ya yi dariya.
“Aa mammi naga dae kin fi kowa son ya yi aure”
“Hakane kam, Ni fa tun da dadewa nake cewa ya yi aure. Shi ne kawai yake ganin kamar na takura shi.”
“Halin zayd kenan ai.”
Mammi ta girgiza kai.
“Wallahi wani lokacin nakan rasa abin da zan yi da shi. Shekarunsa arba’in da biyu amma har yanzu babu abnda yasha kan shi se aiki, inata yimishi addua Allah yasa ba aljana ta aure shi ba don kwata kwata ko zancen mata bayaso”
Fahad yayi daria harda riqe ciki
“Ba wata aljana mammi, miskilanci ne kawae irin nashi shiyasa nace gwara a samo mishi matar kawai, kuma ina ganin Maryam za ta dace da shi.”
Mammi ta qura mai ido
“Me ya sa kake tunanin haka? Ka lura da wani abu game da ita ne?”
Fahad ya ɗan yi tunani.
“Tana da nutsuwa. Tana da tarbiyya. Kuma bata cika surutu ba, kinsan shi beson damuwa toh inaga zata iya jure zama dashi don itama batada hayaniya, sanda aka kira yan matan amarya wurin bikin Safiyya zamanta tayi seda wata taje ta jawo ta, kuma da tazo ta tsaya tanata jin kunya ta kasa rawa. Inaga Ki kira mama Ruqaiya kisa ayi bincike game da gidan su tunda kawar safiyya din che”
Ya ɗan yi shiru sannan ya ƙara,
“Ina ganin za ta iya jure halinsa, saboda naga nutsuwa da tarbiya sosae a tare ita”
Mammi tayi dariya
“Fahad Kai ma ka san halin ɗan’uwanka kenan”
“Fiye da kowa ma mammi” ya fadi yana murmushi
Mammi ta yi murmushi.
“Yarinyar yar gidan waye?”
“Na tambayi Safiyya tache sunanta maryam Bashir me salati che”
murmushin da ke fuskar Mammi ya ɗan ragu .
Ta yi shiru.
Ta maimaita “Bashir me salati?”
Fahad ya kalle ta.
“Mammi, kada kiyi wani tunani daban akan mahaifinta, Safiyya tache qawarta nada kirki sosai kuma suna tunanin abnda ake zargi gameda babansu ba gaskiya bane, kuma ni a ganina ko gaskiya ne ai halin babanta daban itama halinta daban, anyway kisa ayi bincike don ki tabbatar”
Shiru mammi tayi tana nazari
“Okay zan kira hajiya Ruqayya inji”
Ta bashi amsa a taqaice
Fahad bai kara che mata komi ba yayi shuru ya maida hankalin shi a tv
Bayan ɗan lokaci, Mammi ta sake tambaya
“Ka ce dai za ta dace da Zayd?”
“Gaskiya haka Nike tunani”
Mammi ta ɗan yi murmushi
“Ai inaga it’s hightime yazo gida mu ganshi, se in tura shi yaje sokoto, kaga se su hadu”
Fahad ya yi dariya.
“Ki fara tambaya if he is less busy within the month.”
“In tambaye shi? Ai idan aka bar shi, sai dai ya auri aikinshi”
Fahad ya sake yin dariya sosae
“Wallahi kuwa mammi”
Mammi ta ɗaga wayarta.
“Bari in kira shi.”
“Yaushe?”
“Yanzu manah”
Fahad ya kalle ta yana murmushi.
“Allah ya taimaki hajiya mammi”
Netherlands
Zayd yana office dinshi zaune kan kujera, Laptop ɗinsa a bude yana kallon Wasu reports da aka turo, hannun shi kuma wata takarda ce yana duba ta yana duba system din gaban shi, ya tattara duk natsuwar shi kan abunda yake, wayar shi dake gefen table din ta yi haske alamar kira saboda ya sakata a silent mode.
Ya kalli screen ɗin sannan ya dauka
“Assalamu alaikum, Mammi na”
“Wa alaikum salam, Zayd ya kake?”
daga jin muryarta yasan akwai magana
“Alhamdulillah, Me ya faru mammi?”
“Babu komai.”
Zayd ya ɗan yi shiru.
“Mammi…PLEASE MINENE?”
Ta yi shiru na ɗan lokaci sannan cikin serious murya ta fara magana
“Ina so kazo gida”
Zayd ya jingina da kujerarsa ya furzar da iska kadan sannnan yace
“Yaushe?”
“Ba da jimawa ba.”
“Me ya faru?”
“Babu abin da ya faru.”
“To me ya sa mammi?”
Mammi ta yi shiru.
Sai Chan ta ansa
“Ina son ka zo ka ganmu muma mu ganka”
Zayd ya kalli agogon da ke kan tebur.
“Mammi, ina da meetings and stuffs to do”
“Na sani.”
“Kuma ina da abubuwan da zan kammala.”
“Na sani.”
“To me ya sa kike son in dawo yanzu? in akwai wata matsala ne don Allah ki gaya min”
Mammi ta ɗan yi murmushi kadan sannan ta ansa
“Zayd, inason ganin ka kazo gida kawae”
Ya sauke ajiyar zuciya, duk abnda mammi tache dole yayi shi
“Toh in shaa Allah”
Ta sauke ajiyar zuciya sannan cikin Muryarta me daɗi ta fara yimishi addua
“Allah yayi maka albarka”
Zayd ya yi murmushi kaɗan.
“Ameen mammi Amma ba zan daɗe ba.”
“Ba matsala.”
Ta yi shiru na ɗan lokaci.
“Idan kazo akwai wata magana da nake so mu tattauna.”
Zayd ya ɗan sauya fuska kamar tana ganin shi don yasan kwanan zanchen
“Wace magana?”
“Aure.”
Zayd ya rufe idanunsa.
“Mammi…”
Ta yi dariya.
“Ka dai dawo tukuna.”
Ta katse kiran
Zayd ya ajiye wayar a hankali, yana tunanin maganar mammi, wannan karon kuma ya ze samu ya zame akan maganar da ya riga yasan qarshen ta duk baze wuce Aure ba, dan Kullum sukayi magana seta nanata mishi, amma wannan kiran yafi gaban tuni, yayi sensing decision, kuma da desperation cikin muryar ta, Ya kalli laptop ɗinsa sannan ya ci gaba da aikin sa sedae ya kasa samun cikakkiyar nutsuwa, yanata tunanin yadda ze kauche wa zanchen mammi idan ya tafi. Shi fah abnda yasa yaqi zaman Nigeria kenan, saboda bayason takura, yasan inda yana nan da ynzu ko cikin yan uwa ko abukkan mammi zaa samu wainda zasuyita zuga mammi ayi mishi auren hadi, shi a rayuwar shi bayason unnecessary drama shiyasa be tsaya Nigeria da business dinshi ba, Nigerians sunada too much drama ba kamar turawa da larabawa ba, babanshi ma da yake tsohon businessman ai seda anka samu wata drama da wani alh Bashir me salati a kampanin shi kuma dai abin beyi daadi ba, shi duk gudun ire iren abubuwan nan yasa shi gudu yabar Nigeria
Bayan mammi ta qare waya da zaid se ta nemo yar uwar ta Hajiya Ruqaiya ta danna mata kira, sun gaisa sun dan taba firar yan uwa daga nan mammi tayi mata bayanin dalilin kiran,
“akwai wata maryam da fahad ya nuna min lokacin bikin safiya yache qawar safiya che” “wata yar fara kyakkyawa haka?” Hajiya Ruqaiya ta tambaya
mammi tayi dariya “ai ba kyau ba hali, yache min wai zata dache da zaid saboda ya lura tanada natsuwa kuma batada hayaniya”
hajiya Ruqaiya ta amsa “Tabbas in dai maryam che duk abnda ya fadi game da ita hakane, ko zaman hour daya kikayi da Maryam zaki gane natsuwar ta, qawar Safiyya che sosai course daya suke a makaranta”
mammi ta sauke numfashi “fahad yache min diyar gidan margayi Bashir me salati che, kuma kinsan irin abunda ya faru tsakanin shi da kampanin margayi baban su zaid.”
Hajiya ruqaiya ta dan dafe qirji kamar mammin na gabanta “ke don Allah ki bari, wai babanta ne wannan Bashir me salati din? Nidai kawai nasan sunanta maryam Bashir. Kada ki damu yar uwa nidai tsakani da Allah na tabbatar da tarbiyyar maryam saboda na ma saba da mamarta, amma zan yima Alhaji magana yasa ayi muna bincike game da family din, duk yadda ake ciki zakiji ni”
Daga nan sukayi sallama
Da dare hajiya Ruqaiya ya samu mijinta da zanchen kuma yache mata zeyi bikcike in shaa Allah
BAYAN YAN KWANAKI
Zayd ne ke fitowa daga Arrivals na Nnamdi Azikwe international airport Abuja, yana sanye da sweatpants ash Color na Tomford da riga black me hoodie itama ta tomford, kunnensa saqale da AirPods kafar shi da takalmin Sketchers black color, ya saka sunshade na Chloé, dama tun lokacin da yayi waya da mammi ya fara clearing schedules dinshi saboda in dai mammi tayi kira dole ya ansa
Tafiya yake da takunsa me natsuwa yana fitowa daga arrivals din yaji ana ihun kiran “Big brooo welcome home” cikin sautin da ya tabbatar na dan uwansa ne, fahad nata washe baki kamar ranar ya fara ganin yayan nashi yazo yayi hugging yayan shi, Zaid ma yayi murmushi da yafi kama da smirk, fahad ya karbi Qaramin black luggage din da ke hannun zayd na Briggs and Riley, Suka nufi wurin da yayi parking suka bude motar suka shiga suka kama hanyar Katampe.
Mammi da kanta ta shiga kitchen ta girka ma zayd duk abin da tasan yanaso kuma tasan yayi marmari tareda taimakon cooks din gidan aka gama komi tare da jerawa kan dinning table.
Suna isowa gida direct part din mammi ya nufa ta tarbe shi cikin jin daadin da ya kasa boyuwa a fuskar ta, ya gaisheta tareda chewa “mammi na kin qara kyau” tache “Zaid ka rena ni ko Allah ya shirya ka “ sukayi daria tana chewa “muje inyi serving dinka da kaina” tana cikin sallamar masu aikin Fahad ya shigo da luggage din zayd yana chewa “iyyeh kaga yaron mammi” yazo ya zauna kusa dashi yana chewa “mammi nima kiyi serving dina” sukayi dariya duka. Pankasau da miyar ganye da yaji naman kaji mammi tayi serving dinshi suka fara chi suna dan fira cikin nishadi da natsuwa, Bayan ya qare yache ma mammi zeje part dinshi yayi wanka ya huta.
Part ne guda me zaman kan shi wanda keda parlor biyu da bedrooms 3 kowane da toilet dinshi a ciki, ko ina a part din tsab yake saboda masu aiki suna shiga su gyara koda baya nan. Direct bedroom din da yake zama ciki ya shige, ya shiga bathroom ya watsa ruwa ya fito yayi sallah ya zauna yana dudduba aiki a laptop dinshi har akayi la’asar, itama ya tashi yayi, yayi azkar din yamma, sannan ya tashi da zimmar ya chigaba da aikin da ya fara, se kawai ya hau gado ya kwanta a rigingine ya fara tunani yadda ze zame ma maganar sure idan mammi ta tado mishi da ita, yana nan kwanche har baccee ya dauke shi se kiran sallar magrib ne ya tashe shi,tashi zaune yayi yana ambaton sunan Allah sannan ya miqe yayi alwala ya fito zuwa masallaci, a Chan ya hadu da fahad sukayi sallah ya tsaya yayi azkar sannan suka fito suka shiga gida suka nufi part din mammi, sukayi fira sosai tare da ita har akayi isha sukaje sukayi suka dawo, tare da mammi sukayi dinner, sannan suka bar dinning suka dawo parlor, mammi ta juya ta Kalli zayd ta fara magana
“Zayd Kai yaro ne me biyayya duk abnda nakeso kana yin shi amma ka kasa cika min guri na daya, zaid kana qara girma da shekaru a kullun kuma nima ina qara tsufa inason in ga jikoki na” shuru ya ratsa parlorn zayd be che komi ba, mammi ta chigaba da magana “nidai na yanke hukunci kuma inada tabbacin yadda kake yimin biyayya bazaka watsa min qasa a ido ba akwai yarinyar da nasa aka yimin bincike kuma idan ba damuwa inaso kaje sokoto ka ganta” gaban zaid ya buga da mugun karfi ya dago Kai ya kalli mammi da sauri se Ta chigaba da maganar “munje sokoto bikin Safiyya a chan naga yarinyar kuma nasa haj Ruqaiya tayima mijinta Alh Usman magana ya bincika mini family din yarinyar, farko hankalina be kwanta da ita ba saboda yar gidan margayi Bashir me salati che, amma bayan da mukayi magana da hajiya ruqaiya ta tabbatar min tarbiyyar yarinyar sannan kuma ta yima alh usman magana ya yimuna bincike game da ita sosai da family dinsu saboda qawar Safiyya din che, har anje anyi magana da kanen mahaifin ta, yache akwae wani yaro da yake zuwa wurinta har an bashi damar fitowa amma shiru da alama be tashi Auren ba ni kuma ina maka shaawar yarinyar nan, ta kwanta mini sosae zayd, kawun nata ya bada dama kaje ka ganta”
Zaid beyi magana ba haryanzu amma yanata tunani, sokoto kuma? Shi da yayi kusan rabin rayuwar shi a qasar waje zaa hada shi da wata yar sokoto wadda alamu sun nuna ma from middle class or lower class family take, amma dai ko yaya ne baze iya gardama da mammi ba don sam ba halinshi bane kawai dai zeje sokoton amma zesan yadda zeyi su sasanta da yarinyar tunda anche tanada saurayi shi ko aiki da gida ma ze iya ba saurayin nata se abar maganr kawai. Wannan tunanin ya kwantar mishi da hnkali ya amince yache “mammi Allah ya kaimu lfya, Yaushe ne zuwa Sokoton?” Zuwa jibi in shaa Allah idan ka qara hutawa, tareda dan uwanka zakuje nasan kai bakada Abokin da ze raka ka, daga gidan Hajiya Ruqaiya za’a Zo airport a dauke ku, ku fara zuwa chan ka gaida su sannan ku wuche gidan su yarinyar” da “okay Allah ya kaimu” ya ansa sannan yayi mata sallama ya wuche part dinshi. Hankali kwanche yayi baccee don yana tunanin ya samu solution akan abnda ze faru a sokoto.
Sokoto
Tun da Alh Usman yaje wurin kawun maryam (kanen babanta) sukayi magana yazo har gida ya samu maman maryam ya gayamata, “zan basu damar ganin ta tunda uwayen Imrana haryanxu basu taho ba, da alama be shirya yin auren ba” maman Maryam ta dan nisa saboda tun da taji an hada sunan yaron da “rahman Balarabe” jikin ta ya dan yi sanyi, amma kawu ya kwantar mata da hankali yache abnda ya faru baya ai ya wuche kuma qila a samu daidaiton al’amurra ta dalilin wannan auren, tw gyada kai “toh Allah ya zabar muna abunda yafi zama alheri” daga nan suka chi gaba da hirar rayuwar duniya. A nan ya zauna da mama suna firar duniya har yamma saboda maryam tana makaranta, tanada lecture har 6pm.
Alh Usman kam ya yaba sosai da irin dattakon dattijon da suka gani a matsayin kawun maryam, kuma yayi ma hajiya Ruqaiya bayanin duk yadda sukayi, hajiya maryam ta kira mammi ta gaya mata kuma ta kwantar mata da hankali sosai kuma mammi ta samu natsuwa.
Maman maryam bata yimata zanchen da kawu yayi mata ba se bayan kwana uku da kawun ya sanar da ita alh usman ya kirashi ya gaya mishi zaid zezo su gaisa da maryam
Mama ta gaya mata abnda ke faruwa a natse tayi mata bayanin komi tareda bata shawarar yin istkhara domin neman zabin Allah.
Da farko Maryam ta yi tunanin Mama wasa kawae take mata, amma ganin yadda mamar ke magana yasa tasan mama ta amince da yazo ya ganta din
“Mama, aure?”
Mama ta kalle ta.
“Ehh ”
“Mama imran fah?”
“Ba aure zaa daura miki ba meramu, zuwa zeyi kuga juna kuma anjima ze taho, sannan shi Imran tun yaushe aka jiran ya turo uwayenai ayi magana, kinga yan uwana na Niger har sun fara chewa in saurayinki be tashi ba in maidake Niger a samo miki cikin yan uwa, kinsan saboda ke kawai nike zaune sokoto, banso in tahi dake Niger kiyi nisa da dan uwan babanki da diya nai, saboda kinsan da dangin uba ake ado, amma ynzu in sunyi galaba kaina sunsa na maishe ki chan toh ni zaman mi zan zauna nan inyi? Sedai mu tattara mu koma gabadaya.
Maryam ta zaro ido.
“Yau ze taho?” Don ita gabadaya cikin kalaman mama shine ya tsaya mata
Mama ta yi murmushi. Sannan tace “ashe kin jini”
Maryam tayi shuru sannan ta qara matsawa kusa da mama tace “mama halan wanena?”
“Ban san shi ba meramu amma ki kwantar da hankalinki, Ganin juna dae zakuyi Ba wanda ze tilasta miki ki aureshi in de har bakiso kinji meramun mama?”
Maryam ta gyada kai.
Amma zuciyarta tanata bugawa da sauri.
Ba don tana tsoro ba, se tunanin kar magana ta tabbata ya zatayi da imran?
A Chan gidansu imran kuma Wata dattijuwa ce da baza wuce shekaru 45 ba amma duk ta rame ta zama kamar me shekara 60 duqe take tana fama da wutar itacen da keta hayaki tun dazu amma wutar taqi kamawa hannun ta riqe da rabin parker da wuta ta cinye rabin tana hura wutar dashi, sallamar Imran da taji yana shigowa yasa ta aje parker tareda goge idon ta da hayaqin wutar ya tara mata hawaye sannan ta amsa sallamar tare da cewa
“Imrana ka dawo? Yau babu saqon dayawa hala?”
“Awo innaa na dawo, saqon ukku na kuma biyu na sama road na se guda low cost”
“Tho masha Allah, ka samo muna dan abunda zamu ci?”
“Awo ga shinkahwa nan na sawo”
“Tho Allah yayi barka, yanzu zan aza tuwon”
Nan imran ya taya innaa hura wutar sannan ta dora tukunyar tuwo dama akwae sauran miyar jiya se su dimama suci, innaa na cikin kwashe tuwon malam Bala yayi sallama, mahaifin Imran kenan, innaa ta amsa, imran kuma ya tashi ya taro baban nashi tare da yi masa sannu ganin duk gajia ta bayyana a jikin shi ga kuma alamar damuwa a fuskar ta shi,
“Malam sannu da zuwa, ya kusuwa?” Inna ta gaida shi
“Alhmdllhi Maimuna, kasuwa se godiar Allah, kawai abubuwa se a hankali dan abunda na samo nasan da wuya ya muna cehwanen yau”
“Ba komi malam imrana ya kawo muna shinkahwa gata nan har an tuqa ynzu zan kawo maka amma ka shiga ka watsa ruwa se kaji dadin cin abincin”
“Allah sarki imrana, Allah yayi maka Albarka yasa ka gama da duniya lfia”
Imran ya amsa “Amiin Baba nagode”. Imran ya kaima baba ruwa a toilet, Baba ya shiga yayi wanka se ga qanin imran ya dawo Daga Islamiyyah, mama na chewa oyoyo auta ai da har ina shirin insa hijabi in tahi bidar ka, imran yayi dariyar zanchen mama, Qanen nashi kuma ya shigo yana gaida shi.
Yadda suka zauna suna cin abincin cikin jin dadi bazakace basuda wanda zasuci gobe ba, haka har suka gama, innaa ta tattare kwanukan ta wanke su tas ta qara gyara gidan sannan ta tayi alwala ta shiga daki dan lokacin sallar magrib ya kusa. Baba ma yayi arwallah dashi da diya nai sunka fita zuwa masallaci, baba a ranshi yanata tunanin ta yadda zeyi ma imran bayanin da kawun maryam yazo mishi dashi, don yasan saboda nauyin kula dasu shiyasa Harynzu dan nashi be aje abin aure ba, gashi kawun ya same shi tun Shekaranjiya yache akwai wa’inda sunka same shi da zanchen suna tambayar ma yaron su izini ya nemi maryam, kuma kawun yache ya amince tunda an fi wata goma ta ankache ma imran ya turo amma shuru, baba ya nisa lokacin suka shiga masallaci, bayan yayi sallah kuwa adduar shi tafi karkata akan indai maryam alheri che ga yaron shi Allah ya bashi ita, in kuma ba alheri bache Allah ya ba yaron shi dangana da hakuri.
Duk da talaucin gidan su Imran gidan su tsab yake ko yaushe saboda innaa batason qazanta ko kadan wadan hakan yasa imran ma kullun zaka ganshi tsab dashi sedae ace kayanshi sun kode amma ba dai datti ba.
Asalin su imran yan garin sokoto ne cen cikin gari kofar Atiku, innaa wato maimuna da malam Bala cousins ne auren zumunta sukayi, bayan rasuwar iyayen bala wanda gidan mahaifin shi suke zaune yan uwan uba suka matsa a raba gado aba kowa nashi, hakan yasa dole aka seda gidan da su malam bala suke zaune, kasancewar sunada yawa kuma gidan ba wani babba bane yasa bawani kudin kirki suka samu ba, dama kuma malam Bala shi kadae mamar shi ta haifa Allah ya dauke abar shi, hakan yasa ya tattara dashi da matar shi maimuna da dan su Imran suka bar gidan. Cikn ikon Allah se ya samu gadin wani babban gida nan Arkillah ya zauna tareda iyalin shi, duk da be yi karatu ba amma yana shaawar karatun sosae hakan yasa ya debi kudi cikin gadon daya samu yasa Imran da ze kae shekaru shida alokacin makarantar gwamnatin dake kusa dasu, sauran kudin kuma kuma ya shiga kasuwa dasu saboda buqatunsu na yau da kullum.
Da yamma, Mama ta shigo ɗakin Maryam ta sameta zaune tayi shiru kamar me tunani seda ta kira sunan ta sanna tace
“Tashi ki shirya.”
Maryam ta kalle ta.
“Yanzu?”
“Eh.”
“mi zansa mama?”
Mama ta kalle ta daga sama har ƙasa.
“Ki sa abin da ya dace kawai ai ba wani wuri zakije ba.”
Maryam ta yi murmushi.
“Toh”
Ta buɗe wardrobe ɗinta sannan ta zaɓi wata atamfa mai kyau red and touches din green ta saka, ta daura dan kwalinta sanna ta dauko green gyale da ya dace da kayan, Ba ta yi makeup ba kamar kullum, Kawai dan gyara fuskarta tayi ta sa ƙananan yan kunne, tana cikin sawa mama ta shigo, Ta kalli yar tata
“Kin gama shirin?”
“Awo na gama mama”
“To ki nutsu banda gaggawar bada amsa”
“Tau mama”
“Sannan ki fadi iya gaskiyar ki akan komi in ya tambayeki”
“Tau Mama.”
“Sannan…”
Maryam ta kalle ta amma Mama ta yi shiru na ɗan lokaci kamar me nazarin abunda zatace sannan tace
“Babu komai Allah ya tsare yayi zabi na Alheri”
Maryam ta lura da yadda yanayin mama ya sauya amma batace komi ba ta qarasa shirin ta tsab ciki nutsuwa da sanyin jiki, ji take kamar akwae wani abu da ze faru da ita
Bayan driver da ya dauko su zaid ya kaisu sun gaida hajiya Ruqaiya da Alh Usman suka dan huta sannan suka kama hanyar gidan su maryam din, sunyi dan tafiya kafin suka iso gaban gidan wanda fahad ne ya nuna ma driver din hanya, motar ta tsaya gaban gidan, Fahad ya fito da fara’ar sa yana kallon zayd wanda ya fito shima a hankali Yana gyara agogon hannun shi na rolex, Fuskarsa babu wata alama ta farinciki ko akasin haka.
Fahad ya kalle shi
“Kaga fuskar kamar an aiko maka sammaci”
Zayd ya kalle shi
“Fahad!.”
Fahad ya yi dariya.
“To shikenan na bari.”
Sukayi sallama seda suka jira ansa sannan suka shiga cikin gidan, Kyakkyawar dattijuwar mata che Sanye da hijabi a tsaye tsakar gidan, shekarun matar basu boye kyaun fuskar ta ba, suka duqa suka gaida ta, ta ansa musu da fara’arta tayi musu iso zuwa parlor Tare da nuna musu kujeru suka zauna suna sake gaisawa da ita cikin girmamawa sannan tashi ta fita daga parlorn, Fahad ya chiro wayar sa yana dannawa zaid kuma yana zaune shuru tunanin fal ransa.
Join our WhatsApp group
Follow this link to join my WhatsApp group: ***