THE FIRST IMPRESSION
Mama ta shiga dakin maryam da sallama amma shuru maryam bata ansa ba, da alama hankalin maryam din baya nan dan bata ma san shigowar ta ba Seda ta dan taba ta “maryama”
“Na’am Mama?”
Cikin kwantar da murya da sigar rarrashi tace
“Ki kwantar da hankalin ki kinji, ba dole zaa miki ba ai kin san ba kyau wulaqanta mutum, tashi ki dauki ruwa da abnci ki kai musu, gaisawa kawai zakuyi babu wanda ze miki dole idan baki so”
“Toh”
Maryam taje kitchen ta ɗauki silver tray da ke dauke da food warmers da plates da spoons, ta kama hanyar parlor
Zaune suke shuru a parlorn, chan Fahad ya dago Kai ya kalle shi.
“Lfya kake bro?”
“Lfya” ya ansa a takaice
“Dama ba son zuwan kakeyi ba dai”
Zayd ya ɗan kalle shi.
“No, Ina tunani ne kawai”
Fahad ya yi murmushi.
“Ka jira kaga yarinyar tukunna kafin ka yanke hukunci”
Zayd yayi shuru kawae dan ya riga ya yanke hukuncin
Bayan kamar minti biyu Fahad ya sake kallon Zayd
“Har yanzu kana tunanin abin da ya sa ka yadda ka zo?”
Zayd ya dan kalleshi Kadan
“Me kake nufi?”
Fahad yayi murmushi
“Ka sani ai. Tun lokacin da muka taso daga Abuja kaketa zurfin tunani”
Zayd ya jinginar da kanshi jikin kujerar yayi shuru
“Ba ni da abin cewa.”
“Ko kuwa kana nadamar zuwan ba”
Zayd ya sake kallon shi na dan lokaci
“Nache maka tunani nike”
“Amma fuskarka abu daban take nunawa.”
Zayd ya girgiza kan shi
“Fahad.”
“Na’am, ranka ya dade.”
Fahad ya ansa yana dariya, Zayd ya harare shi
“Ka sani banzo nan saboda kaina ba. Mammi tace inzo kuma dole in zo”
“Na sani.”
“Toh meyasa kake damuna?”
Fahad ya daga kafada
“Nothing. Ina ganin kawai ya kamata ka ɗan rage wa kanka wahala.”
Zayd ya daure fuska
“Wahala? Ni ne dan wahala kenan?”
“Eh manah Kai Kullum kana aiki. Office, meetings, flights, emails… idan ba Amsterdam ba, kana wani country wurin meeting ko aiki .”
Zayd ya juyar da fuskar shi
“Wannan shine yanayin aikina.”
“Na sani. Amma ba shine rayuwa gaba ɗaya ba.”
Zayd ya qyale shi kawai dan ranshi ya fara baci
Fahad ya sake jeho mishi wata tambayar
“Bro wai shekarar ka nawa yanzu?”
Zayd ya harare shi
“Fahad…Ka san shekaruna ya kake min wannan tambayar?”
“Na sani. Ina tunatar da kai ne.”
Zayd ya sauke ajiyar zuciya sannan yace
“Go straight to the point”
Fahad yayi dariya
“Ka yi aure ka bani wuri ko nima zanyi”
Zayd ya harare shi
“Ni na hanaka auren?”
Fahad ya kyalkyale Daria yache
“Wai kaga irin wannan kallon da ka yimin kamar na ce ka sayar da kamfanin meridian axis”
“Fahad wani lokaci ina ganin auren kamar ya fi wahala akan tafiyar da company, kuma kar inje in kasa kula da yarinyar mutane”
“Saboda haka ne ya kamata ka yi shi zaka gane daadin zama kanajin motsin mutum tare da kai, Kuma wallahi hankalinka se yafi kwanciya kayita businesses dinka a natse ”
Zayd ya girgiza kai
“Ba haka abin yake ba Fahad”
“To yaya yake?”
Zayd ya dan yi shuru sannan yache
“Ba na son yin aure saboda kawai mutane suna ganin lokaci ya yi, inaso inyi idan na shirya”
Fahad ya gyara zama yache
“Ban ce ka yi saboda mutane ba.”
“Then?”
“Ka yi saboda kanka”
Zayd ya dan kalleshi irin kallon nan dake nufin toh ni nache ina buqata ne
Fahad ya chigaba
“Baka taɓa ba kanka damar yin tunanin rayuwar ka ba. Kullum kana tunanin aiki, company, Mammi, family… ya kamata kayi tunanin rayuwar ka, ya zakaji in ka fara soyayya? Yaya soyayyar take? Ya zakaji in ka samu abunda kakeso wanda be danganci aiki ba? Inaso in kaga yarinyar nan yau ka bata chance ni nasan zaka so ta in dai ka bude zuciyar ka”
Ya ɗan yi shiru, se yache
“kai kuma fa?”
Fahad yache
“Shi ya sa nake son ka ba wa kanka chance, inaso mammi ta sallameka ko zata waiwayo ni, ynzu duk hankalinta tashe yake danta yana chan Amsterdam ya fara tsufa ba aure” ya qarasa maganar yana murmushi me kamar daria
Zayd lumshe ido
“Ba komai yake da sauƙi ba, Fahad.”
“Na sani.”
“Baka san abubuwan da ke cikin kaina ba.”
“Gaskiya ne, Amma na san ɗan’uwana.”
Zayd ya kalle shi Kadan, surutun ya fara isar shi
“Wataƙila abuda kake nema beda nisa da kai ynzu haka”
Zayd ya daga gira
“Me kake nufi?”
Fahad yayi murmushi
“Ba komai.”
““Fahad.”
“Na ce ba komai.”
Zayd ya girgiza kai kawai
Daga nan suka ji takun tafiya a hnkali yana zuwa parlorn da suke zaune
Fahad ya Kalli qofa, Zayd kuma ya sauke kanshi qasa yana danna waya sakamakon wani saqo daya shigo wayar.
maryam ta shigo dauke da sallama, suka ansa mata, kanta a qasa ta shiga a natse, ba ta kalli mutanen da ke zaune ba sosai amma ta dan dago kai ta kalli inda taji muryar da aka ansa mata tafi qarfi, sukayi ido hudu da Fahad, hankalinta ya dan tashi da wani irin shock tache “KAI..” batasan a gabanta akwai inda carpet ya dan taso ba, qafarta ta sarqe, Tray ɗin da ke hannunta ya karkache abubuwan da ke kai suna qoqarin zubewa tareda ita
“Subhanallah” ta furta tana qoqarin gyara balance dinta
A daedae lokacin Zayd ya tashi da sauri ya kama tray din ya riqe ta samu ta saya dakyau, Idanunta suka haɗu da nasa, da qarfi zuciyar maryam ta buga, yayi sauri ya sakar mata tray din, Fahad na yimata sannu amma Ta kasa magana.
Zayd ma ya yi shiru ya koma ya zauna, Acikin wannan ɗan lokacin, babu wanda ya ce komai.
Seda ta ajiye kayan sannna ta juyo ta gaishe dasu a natse, Idonta ya kai kan fahad, ta gane shi a take amma ta rasa me zata che mishi (shi ke sonta? Ko kuma yaya?) se tayi shuru batache komai ba, suka amsa gaisuwarta a tare se shuru ya biyo baya, Maryam na zaune kanta na qasa
Amma akwai wani abu daban da ta kasa fahimta.
Ba tsoro kawai ba ne kesa qirjinta na irin wannan luguden.
Zayd kuwa fuskar shi tana qasa kamar ma besan akwai mutane a parlorn ba
A karon farko tun da ya shigo gidan, fuskarsa ta sauya kaɗan.
Ba murmushi ba, ba kuma daure take ba
Fahad ya katse shirun
Sunana fahad Rahman Balarabe ga kuma yayana Zaid Rahman Balarabe, Allah yasa kinyi maraba da ganin mu
Maryam kai kawai ta gyada a zucciyata tana nanata sunan Rahman Balarabe
“Bro, ku gaisa dakyau bari in jira a mota”
Maryam ta ɗan firgita amma bata nuna ba
“Aa ka zauna kawai” zaid ya fada
Bayan dan shuru kawai taji muryar sa kamar daga sama
“Sannunki, kina lfya?”
“Alhamdulillah lahiya lau”, maryam ta ansa” ya dan yamutsa fuska a ran shi ya maimaita “lahiya lau”
Ya sake chewa “Ya gida?” “Tache alhamdulillah”
Shuru suka sake yi se Fahad ne yache mata “school dinku daya da safiya ko?”
“Awo” ta amsa a gajarche, ai saura kadan Fahad ya fashe da dariya jin Hausar amma yayi saurin datsewa, zaid da ke zaune Kamar gunki seda ya murmusa a ranshi yana mamakin hausar, se kuma Fahad yache “wane course kuke?”, international relations a Usman danfodiyo university”
Se ya sake chewa
“Why international relations?”
Maryam ta ɗan yi tunani.
“Inason jin abubuwa game da qasashe da kuma banbancin su”
Fahad ya gyada kai yana dariya qasa qasa
Bayan ɗan lokaci, Fahad ya miƙe.
“Mu tafi ne?”
Zayd ya kalle shi yache
“Eh muje”
Fahad ya yi dariya.
“Idan Baka tashi tafiya ba ka gayamin kawai se in jira ka a mota”
Maryam dai kanta na qasa
Suka miqe a tare zasu wuche maryam tache “baku chi abncin ba” fahad yayi murmushi tareda kallon zaid “ni na qoshi alhamdulillah ban sani ko dai shi, zaid ya sa hannu Aljihu ya dauko bundles na euros dinda ke ciki ya ajiye kan tray dinda ta shigo dashi dazu, be chanja kuddin shi zuwa naira ba tun da ya dawo Nigeria, dan be siya komi ba fahad ne ke siyan abubuwa, kamar beji abnda suke cewa ba ya sa kae ya wuce ya bar fahad nayi mata sallama, Ta juya itama ta dauki hanyar dakin mama tareda da kudin da tray din duka.
Tun a mota zaid ke tunanin yau kam Allah ya hadashi da basakkwata tun da yake be taba jin anche Awo ba se yau, yayi murmushi, daga cen gidan hajiya Ruqaiya suka koma bayan anyi isha’i mijinta Alh Usman ya shigo part din da aka sauke su don su gaisa, a nan ne zaid ke tabbatar da cewa wai maryam diyar margayi Bashir me salati che, ya kalli Fahad da wani irin kallon mamaki se Alh Usman ya chigaba da yimishi bayani akan bikciken da yayi gameda ita da kuma gidan su, zaid be che komi ba, daga nan suka ci gaba da hirar su ta duniya da businesses dinsu. Har dare yyi sannan yayi musu sallama ya wuce part dinsu, su kuma suka kwanta baccee.
Washegari hajiya Ruqaiya ta shigo part din da suke tareda masu aiki da suka dauko mata abnci, tanata tsokanar zaid “gabadaya family dinmu kafi kowa kyau amma in ka auri maryam zaka dawo na biyu, in kuma kuka haihu nasan yaran zasu ma fiku kyau” shi dai zaid smiling kawai yake se fahad ne ke tayata magana, sunata yabon irin kirki da natsuwar maryam, bayan sun gama breakfast, driver din hajiya Ruqaiya ya kaisu airport suka koma Abuja.
A chan kuma Maryam na aje tray din a kitchen dakin mama ta nufa tayi sallama ta shiga, “mama wai kinji yan gidan Rahman balarabe ne”
mama ta amsa “na sani maryam”
maryam tayi shiru sannan taba mama kudin da zaid ya aje kan tray mama ta karba tana kallon kudin “kingode sosae” maryam kanta ya daure amma dai bata che komi ba se fara tunani da tayi tho shi Fahad din ne yake sonta ko yaya? Aa bashi bane tunda har taji yache “bari in tashi in baku wuri ku gaisa” wata zuciyar ta bata amsa kenan wannan dan uwan nashi ne me daure fuska kamar besan abunda ake kira dariya ba? Nufin ake ta auri wannan me daure fuska kamar fuskar shanu? Fuska babu Annuri Tabb Wallahi bazata iya ba.
Da dare, Zayd yana part dinsa cikin ɗakinsa.
Jirgin zuwa Netherlands yake tunani yaushe ya kamata ya koma
Ya zauna a gefen gado yana kallon wayarsa.
Ya kamata ya kira office.
Ya kamata ya duba emails.
Ya kamata ya shirya komawarsa.
Ya kamata yaaa… se wani tunanin ya fado mishi
Idanun ta da ta kalleshi lokacin da ya riqe mata tray, yadda ya ganta yar qarama a gabanshi, da kuma innocent fuskar ta, Mahreeyam, ya kira sunanta ahankali yadda shikadae zeji,
yadda ta kalle shi lokacin da ya riƙe ta a tsorache
Ya ɗan girgiza kai.
“Me ke damuna ne?” Yayi saurin kawar da tunanin da chewa saboda wata macce bata taba matsowa sosai kusa dani ba shiyasa
Ya faɗa a hankali cike da son ba kanshi kariya, nan hankalin shi ya dawo kan wayar sa dake haske ya duba yaga Fahad ne.
“Hello.”
Shiru be ansa ba fahad yache
“Ka yi shiru ne?”
“Ina tunani.”
“A kan me?”
Zayd ya dan yi shuru kamar me nazarin abun cewa se kuma yace
“Ba komai.”
Fahad ya yi murmushi a ɗayan ɓangaren
“Na san ka fah big bro.”
“Fahad…”
“To, na yi shiru.”
Kiran ya katse
Zayd ya sake kallon wayarsa.
A wannan daren, karon farko bayan shekaru masu yawa, aikin da ke gabansa bai zama abu na farko a zuciyarsa ba.
Akwai wani abu wannan yarinyar da bai san komai game da ita ba.
Sai dai sunanta kawai, Maryam!
Yanata tunani gobe idan mammi ta tambayeshi ya akayi me zeche? A haka har ya fara jin baccee ya tashi yayi alwalla yayi shafa’i da witiri ya kwanta
Join our WhatsApp group
Follow this link to join my WhatsApp group: ***