THE BREAKUP
Safiya da Bahijja sun sa maryam gaba gameda maganar zaid, ita bata ma gaya musu chewa ta amince ba, amma kullun zanchen su kenan, don Allah ta yadda da zaid tunda dai imran be tashi aure ba,su dai sun matsu tayi aure, idan ana lecture maryam har bataso a qare saboda zasu fara damun ta, suyita lissafin ire iren abubuwan da zasuyi lokacin Biki da kuma irin kayan da zasu sa, maryam dai nata kunne, tayita sauraren su. Ita duk kwanakin nan babu abnda ke chi mata tuwo a qwarya kamar yadda imran ze dauki zanchen ta, tana tunanin yadda zama ze kasance tsakaninta da mutumin da sukeda banbanci da shi sosai amma ko wannan tunanin baya damunta kamar yadda zatayi da imran, a ranta take tunani, Toh wai kodai ta gayama imran gaskiyar abnda yasa ta amince? Tasan ze fahimce ta, kawai ta gaya mishi ga abnda zataje yi ba wai zaman aure zatayi ba, in yaso ta roqe shi ya bata lokaci zata dawo wurin shi idan ta gano abnda takeson ganowa, qilan ma kafin lokacin ya samu kuddin aure se suyi auren su. Taba ta da bahijja tayi yasa Tayi firgigit ta dawo daga tunanin da take,
“lfyar ki kuwa maryam? Kinsan so nawa muna kiran sunan ki?”
Maryam Tayi dariya
“wallahi na gaji ne, ai da munyi wagga lecture zamu wuche gida ko?”
Safiya ta dan kalleta
“maryam in wani abu ka damunki ki hwada muna, ko bamuda mahita ai zamu yimiki addua kuma in kika hwadi zaki rage ma zucciyar ki nauyi”
Maryam ta sauke numfashi
“babu komi gajiya kawai che”
Bahijja ta girgiza kai
“amma ba yau kadai ba duk kwanakkin ga haka kike”
maryam tayi dariya
“toh ku bari in hwada muku wani abu, na amince da dan uwan safiya amma tunani nikai yadda imran ze…” ai bata kai qarshen zanche ba sukayi ihu seda Hankalin Mutanen da ke wuchewa ya dawo kansu, suka rungume juna sunata jin daadi, bahijja hadda chema safiya asa sunanta cikin masu tafiya kai amarya Abuja wai dama so daya ta taba zuwa Abuja tanaso ta sake komawa, haka dai suka yita shirme har suka ga motar lecturer dinsu ya shigo suka tashi suka shige lecture hall. Bayan an qare lecture ma Haka safiya da bahijja suka yita surutu a hanyar su ta dawowa gida a mota har safiya na chema bahijja ta shirya su fitar da anko su fara shiri saboda tasan bazaa sa bikin da dadewa ba don anche zaid ze koma chan qasar da yake suna haka aka kawo inda bahijja zata sauka sukayi sallama ta sauka suka wuche, safiya ta chigaba da magana taga maryam tayi shuru
“barin yin shuru kikai tunda kin amince ai an gama me wuya”
maryam tayi dariya,
se ta qara da chewa
“ke in dai shan tokar da yakai ka baki tsoro toh kakki damu da kunyi aure bari zeyi in kyaun ga naki ya ratsa shi, balle ma in yagga Gashin ki, kinsan nache miki yanason gashi”
maryam ta girgiza kai
“safiya Allah ya agaje ki nidai yi sauri ki akeji ni gida bnso mama ta aza abnci nahison inyi, banso tana aikin wahala”
safiya batayi shuru ba hakanan tayita yima maryam surutu har ta kaita gida
Kwana biyu maryam tana jin kamar komai na faruwa da sauri, too fast
Tun ranar da ta ce zata amince da auren, Mama ta fara maganar kayan daki, Kayan gida, gyaran gida da kuma abubuwan da ake bukata, kullum akwai wani abu da mama ke qoqarin yi,
Maryam kuwa tana saurare ne kawai, yau ma hakane koda ta shigo gida mama na qoqarin hada kuddi a sawo jarkokin man shanu da za’asa cikin kayan gara, ta gaida mama da innar imran da Mutanen da suke tare dasu sunata yimata barka da Allah ya sanya alheri ta shige dakinta.
Wani lokaci maryam bata sanin me ake cewa idan ana magana saboda hankalinta yayi nisa,
Washe gari Mama ta shigo ɗakinta da safe,
Maryam tana zaune a gefen gado tana kallon wayarta bayan ta qare waya da zaid,
A lokacin ne zaid ya cika umarnin da mammi ta bashi na chewa ya kira maryam, tana zaune call ya shigo da unknown number se da ya kusa katsewa ta daga “salamu alaikum” aka yi shuru na dan lokaci kafin aka ansa
“wa alaikis salam” se shuru ya biyo baya se da ya dauki lokaci se kawai taji yache
“zaid”
tayi shuru don batasan me zatache ba se chan ta amsa “okay”
“Akwai abnda kike buqata? Mammi tache min an fara shirye shirye”
“Babu komi”
“Okay ki turo account details dinki zansa miki kuddi incase ko wani abu ze taso”
Tayi shiru batache komai ba se bayan wani lokaci Yayi sallama
“bye”
ta amsa “bye”
suka katse kiran
Tana zaune tana ta tunani har mama ta shigo bata sani ba
“Maryam.” Mama ta dan taba ta
“Naam”
Mama ta zauna kusa da ita.
“Kin ga yanzu maganr gaske ake shiyasa take shiga jikin ki ko?”
Maryam ta kalleta.
“Me kenan mama?”
“Auren mana.”
Maryam ta yi ɗan murmushi.
“Na sani Mama.”
“Da gaske kin shirya?”
Maryam bata amsa nan take ba.
Ta kalli qasa sannan
“Zan shirya.”
Mama ta taɓa kafadarta.
“Allah ya baki haƙuri da fahimta.”
“Ameen.”
Amma kafin Mama ta tashi, wayar Maryam ta yi ringing.
Ta kalli screen ɗin.
Imran.
Zuciyarta ta buga, Tasan yaji, tun jiya da dare ya kirata ta kasa dagawa
Mama ta lura.
“Waye?”
“Ba kowa.”
Ta kashe wayar.
Mama ta kalleta amma bata ce komai ba.
Se chan fara magana
“Jiya Haj Ruqaiya mamar safiya tazo kahin ku dawo daga makaranta, wai surukar ki ta aikota ta Ashe yayarta che, ta gaya muna base munyi komi ba ko kayan daki ko gara, sunaso kawai a daura auren a kaiki saboda mijinki ma ba mazauni bane,kuma zata aika ma surukar ki number ta don Tache a tura mata ta rinqa kira muna gaisawa, kuma itama zata rinqa leqowa akai akai taji ko ana buqatar wani abu, inason inji me kika tunani gameda haka?”
A ranta maryam tache Toh ni da ba auren zanje ba ina ruwana da wani kayan daki in ma na samu abunda zanje nema da wuri ai zansan yadda zanyi in dawo gida, a fili kuma se chewa tayi
“mama kada ki wahalr da kanki tunda sunche a bashshi, dama duk abnda zamuyi sun fi qarfin shi ai”
Mama taja numfashi
“hakane amma banso watarana koda zanche ze tashi a yimiki gori, zanje dai inyi tunani in gani, ko kayan gargajiya ne irin man shanu da garin kuka dasu alkaki da chin chin ai dole inyi miki ki samu na raba ma yan uwa nai”
Maryam gyada kai “toh mama”
Da Mama ta fita, Maryam ta sake kallon wayar taga imran ya aiko mata saqo
Imran: Can zamu iya magana?
Maryam ta rufe idanunta ta furta “Allahumma laa sahla illaa maa ja’altahu sahla wa’anta taj’alul hazna idhaa shi’ta sahla”
Ta san dole ne ta yi magana da shi.
Amma me za ta ce?
Ta amince da auren wani.
Ta yaya za ta gaya masa?
Kuma mafi muni…
Ta yaya za ta bayyana masa dalilin da yasa ta amince?
Ba za ta iya cewa tana son shiga cikin Balarabe family saboda Aisha ba.
Ba yanzu ba.
Maryam ta ɗauki wayarta.
Ta rubuta:
“Okay. Yaushe?”
Sai ta aika.
A Abuja kuwa, Mammi ta riga ta fara shirye-shirye.
“Zaid!” Mammi ta kira shi
Zaid yana zaune a parlor din Mammi yana duba wasu emails a wayarsa.
Mammi ta shigo da wani paper a hannunta tana miqa mishi
“Ka duba wannan.”
Zaid ya kalli paper ɗin.
“Miye wa’innan mammi?”
“List ɗin abubuwan da za a yi.”
Zaid ya ɗauka, Ya karanta kaɗan.
Sai ya kalli Mammi.
“Already har kunsa date haka kusa kusa?”
Mammi ta yi dariya.
“Toh ba sauri kake kanaso ka koma ba?”
Ya gyada Kai“hakane”
“Me kake so? Mu jira se zuwa Yaushe kafin mu fara shiri ko a fara tin ynzu? Kwana nawa ya rage?”
Zaid ya yi shiru.
Mammi ta zauna.
“Yaushe Ka shirya komawa Amsterdam?”
“Gobe.”
“Yaushe zaka dawo?”
“Tunda kunsa bikin kusa kusa bazan dade ba, zanyi supervising abubuwan da akayi da bana nan se in qara dudduba yadda abubuwa zasu tsaru idan na tafi, se in dawo maybe 3days kafin fara bikin”
Mammi ta gyara zaman ta.
“Kar ka yi min zanchen naka na ýan business, Wannan ba business meeting bane.”
Zaid ya ɗan yi murmushi.
“Na sani mammi, nasan idan nazo bazan koma immediately ba shiyasa”
“Maryam fa?”
Zaid ya kalleta.
“Me ya faru da ita?”
“Ka yi magana da ita?
“Eh”
“Ya kamata kaji shirye shiryen ta”
Zaid ya yi shiru.
“Mammi na tambayeta, tache ba komai, amma nache zan tura mata wani abu tayi wasu abubuwa amma bata turo min account details dinta ba”
“Ai bazata iya ba kasan tana da kunya, zan tura ma hajiya Ruqaiya kuddi ta kai kasan abubuwan da zasuyi na al’adada mu zamu bada kuddi ko mu kai kayan”
“Okay” kawai zaid yache
Mammi ta chigaba “nawa zakabada a hada kayan lefe?”
“Mammi please ki gayamin kawai nawa zan bada se in tura miki”
“Okay ka bada 30m zamu saye kayan amma idan kaje Netherlands ka siye English wears da akwatuna ko set 4-5 haka”
“Mammi ya zan kwaso kayan idan zan dawo? Kinsan da hand luggage kawai nike tafiya”
“Idan ka saye kasa ayi shipping ka aiko muna, zasu iso kafin ka iso, dama mu ai bazamu tsaya jiran ka har ka dawo ba, da wuri nikeso mu gama hada lefen”
Da “okay” ya ansa
A wurin ya tura ma mammi 40m incase ko zasu qara wani abu, mammi kuwa ta kira Hajiya Ruqaiya sukayi magana a take suka fara sayen abubuwan da zasu Samu online kafin yamma ita Mammi ta fita kasuwa ita kuma Hajiya Ruqaiya zata fara shirya kayan da zasu kai na wankin amarya.
Mammi Ta tashi zata fita daga parlor ta shiga dakinta Sai Zaid ya kira ta.
“Mammi.”
“Naam?”
“Kinada masaniyar ko Maryam tana son wannan auren?”
Mammi ta tsaya.
“Me kake nufi?”
“I mean… tana son auren ko dole aka yimata?”
Mammi ta yi shiru na ɗan lokaci.
“Ta ce ta amince.”
“Mammi ba wai ta amince ba, da son ranta ta amince?.”
Mammi ta kalleshi.
“Zaid, ka damu ne?”
“Ina tambaya ne kawai, kar in fara zama da yarinyar da zata rinqa kallon na aureta don dole”
Mammi ta yi murmushi.
“Ka tambaye ta da kanka manah ba ka kirata dazu ba” Sai ta shige daki
Zaid ya sake kallon wayarsa.
Maryam.
Ya san abu ɗaya kawai game da ita, Shekararta 23
Ya sake sauke numfashi.
Wataƙila ya kamata ya yi magana da ita kafin komai ya yi nisa.
Washegari da yamma, Maryam ta haɗu da Imran.
Suna zaune a parlor din gidansu
Imran ya kalleta.
“Me ya faru ne maryam? baba ya fara yimin wani zanche ban gane ba”
Maryam ta yi shiru.
“Maryam?”
Ta sauke numfashi.
“Imran… akwai wani abu da nake son gaya maka.”
Imran ya kalleta sosai.
“Baba ya gayamin duk abnda ya faru, anche amincewar ki ake jira”
Maryam ta ɗaga ido ta kalleshi.
“Na amince da auren.”
Imran ya yi shiru.
Kamar bai ji abin da ta faɗa ba.
“Wane aure?”
Maryam bata ce komai ba.
“Maryam…” ya sake kiranta
“Auren da za’a yimin da zayd”
“Zaid?” Ya tambaya
Maryam ta gyada kai.
“Mmmmeyassssaaaa?” Ya tambayeta a daddafe
Maryam ta kalli gefe.
“Saboda….em..amm…emm inada dalilin da yasa na amince don Allah ka fahimce ni”
“Wane dalili kenan?”
Ta yi shiru.
Ba za ta iya gaya masa ba.
Allah yasa ya fahimce ta
“Kayi hakuri.” Ta fadi cikin muryar kuka, har ga Allah tanason imran, tana fatar ta qare abnda zataje yi yi gidan nan cikin lokaci don ta dawo wurin imran dinta
Imran ya yi murmushi mai ɗaci.
“Shikenan?”
Maryam ta kasa magana.
“Kin riga kin yanke hukunci ai”
ya ɗan girgiza kai.
“Okay.”
Ya tashi.
Maryam ta kalleshi.
“Imran…”
Ya tsaya, ya dan kalleta
“Maryam Allah ya zabar miki abnda yafi zama alheri kuma ya amince dake a duk inda kike.”
Sai yasa kai ya fita
Maryam ta zauna tana kallonsa har ya fice daga parlorn
Zuciyarta ta yi nauyi.
Ba ta sani ba ko ta yi abin da ya dace
Amma ta san abu ɗaya.
Ba za ta iya barin abin da Tasan Aisha ta fara ba.
A daren wannan ranar, wayar Maryam ta sake yin ringing.
Unknown number still
Ta duba kamar an kirata da number dazu
Ta ɗaga.
“Salamu alaikum”
Shiru na ɗan lokaci.
“Wa alaikis salam”
“Mahreeyam?”
Tayi shuru ita kam baa taba kiran sunanta haka ba “Na’am.”
shiru ya biyo baya
“Inaso muyi magana”
Maryam ta gyara zaman ta tana jin kanta na sarawa
“Okay.”
“Maganar auren mu.”
Zuciyarta ta ɗan buga.
Zaid ya sauke numfashi.
“Maryam, zan tambayeki ne.”
“Toh Inaji”
“Kin amince? Kin tabbatar?”
Maryam ta yi shiru.
“Ko dole aka miki?”
Ta kalli window din dakinta tana tuna fuskar imran a dazu, yadda taga tashin hnkali da bacin rai a shimfide
Ba ta san abin da za ta ce ba.
Zaid ya ci gaba.
“Ki gayamin idan dole aka yimiki zansa a fasa.”
Maryam ta lumshe ido.
“Ba wanda ya tilasta min.”
“Kin tabbata?”
“Eh.”
Zaid ya yi shiru.
“Okay.”
Maryam ta tambaya a hankali,
“Kai fa?”
Zaid ya ɗan yi shiru.
“Me?”
“Ka tabbata kana son auren?”
Zaid bai amsa da sauri ba se bayan wani dan lokaci
“I think… inaga..ina ganin kamar lokacin auren yayi”
Maryam ta yi shiru.
“Shikenan?”
Zaid ya ɗan sauke numfashi
“Inaga shikenan.”
“Okay.”
“Goodnight”
“Goodnight.”
Ya katse kiran
Maryam ta ajiye wayarta.
Ta kalli ceiling.
Zaid bai san dalilinta ba.
Ita ma bata san nasa ba amma tanaji a jikinta kamar shima yanada nashi dalili
Amma dukansu sun ce sun amince
Kuma daga wannan ranar…
Alqalamin qaddara ya riga ya rubuta musu abnda dukansu basu sani ba
Join our WhatsApp group
Follow this link to join my WhatsApp group: ***