KIRAN KADDARA

THE GUESTS

by @nihaalmaalik

SOKOTO- 5 days to the wedding


Tun safe gidansu Maryam ya fara daukar haramar cika da yan uwa na nesa 

Tun da sassafe Mama take ta shiga da fita tana gyare gyare, Wani abu ta gyara, Wani kuma ta kira Maryam ta taimaka mata, Maryam dai jikinta kamar an watsa mata ruwan sanyi, se idan safiya da bahijja sunzo take dan sakewa suyi hira suna kwantar mata da hnkali, da zarar sun tafi shikenan se zaman shuru da tunani, dama tun shekaranjiya da kawu ya kira mama ya gaya mata ranar da akasa tache ma maryam kada ta sake fita ko zuwa makaranta. Gabadaya maryam batasan abnda ke mata daadi ba jin take kamar tache ta fasa 

Kamar kullun a kwanakin nan.  tun safe tana cikin wani irin yanayi.

A yau yan uwan mama na Niger zasu iso

Duk dangin Mama suna zaune ne a Niger Republic, saboda a can ne asalinsu yake, se Mama kawai wadda itama dalilin aure ya kawo ta Nigeria 

Tun sanda aka fara maganar aure, Mama ta kira mutanen gida ta gaya musu.

Kuma suka ce in an tsaida magana an sa date ta Gaya musu zasu zo 

Da misalin ƙarfe goma sha ɗaya na safe, aka ji horn a wajen gidan.

Maryam tana ɗaki kwanche jikinta duk babu daadi, Sai ta ji Mama ta kirata daga waje.

“Maryam!”

“Na’am Mama!”

“Inaga sun iso, fito”

Maryam ta yi saurin tashi, ta fito da sauri.

A wajen gate kuwa motoci biyu ne suka tsaya, Mutane suka fara fitowa.

Wata tsohuwa ta fito da farko (kakar mama), wadda suke kira inna ladi, tana sanye da doguwar riga da gyale a kanta.

Tana yin arba da Mama, sai ta buɗe hannunta.

“Inna ladi!”

Mama ta yi saurin zuwa ta rungumeta.

“Inna ladi hadda ke anka zo? Zaman mota baze wahalar dake ba?”

“Allah ya yimin tsawon rai ai se nazo naga auren diyar jikanya ta, in banyi zari ba ai se inche in ta haihu ma zanje suna amma ban sani ba ko rai na ze kai”

Sai dariya suke wasu jikoki na chewa mama ladi ta tsuhwa ta tahi hakanan uwayen kuma suna chewa Allah ya qara ma mamar su tsawon rai 

Maryam tana tsaye tana kallonsu tana murmushi.

Wasu maza biyu suka fito daga mota ta biyu.

Yannen mama maza ne, suka fara gaggaisawa maryam tanata gaishe su 

Dayan yache “Maryam ma shaa Allah” 

Maryam ta yi saurin zuwa wurin su

“Uncle Sannun ku da zuwa”

Babban Ya rungumeta a kunne ya rada mata “jiya kawun naki ya kirani ai yake gayamin dangin mijinki sunzo a jiya din sunyi tambaya an basu kuma sun biya sadaki 500 thousand naira” 

Se dayan ya karbi zanchen “Kin girma fa gashi Allah ya nuna muna auren ki, Allah ya jiqan mahaifin ki”

Maryam ta yi dariya.

“Uncle amaadou, kullum idan ka gan ni sai ka ce haka.”

“Saboda gaskiya ne.”

Ya kalleta daga sama har ƙasa.

“Amarya kenan?”

Maryam ta yi kunya.

“Uncle…”

“Me? Ai amaryar che”

Mutanen da ke kusa suka fara dariya.

Maryam ta sunkuyar da kanta.

Kaka ladi tache 

“Ku bari ta shiga ciki mana. Anche Tun safe take aikin gida, Gamunan ynzu munzo da Kayan gyaran jiki da masu gyara tun daga Niger ynzun nan za’a fara gyara ki”

Wata daga cikin matan ta ce,

“Amarya be kamata ta yi aiki ba dama”

Maryam ta yi murmushi.

“Ni ai zan yi babu me taya mama se ni”

“Kinyi na yau shikenan. Gobe sai ki bar mana komi”

Maryam ta sake yin dariya, tana riqe da hannun diyar anty maimouna wadda taji daadi sosai da akazo da ita duk da bata kai girmanta ba, amma sosai maryam ke shiri da ita, riqe take da hannun hauwa koulou, amma zuciyarta tana wani wuri daban, duk wannan abun da ake tunanin imran yana nan cikin ranta, ko ya yake ynzu? Me yake yi? Ya chi abnci? 

A bangaren imran kuwa tun ranar da yayi magana da maryam koda ya fito daga gidansu baya ma gani sosai, ze shiga gida ya hadu da baban shi, baban na ganin yanayin shi ya kuma ga daga gidan da ya fito a hnkali ya furta” shikenan ta faru ta qare”, daga baban imran har innar shi basu qaunar abunda ze taba musu yaro, saboda yadda shima yake qoqarin faranta musu Iyakar iyawar shi kuma be Barin su shiga kowace irin damuwa, besan baba na bayan shi ba seda yayi mishi magana “Imrana lfya kake?” Be amsa ba se gaishe da baban da yayi “baba ina yini, har ka dawo? Ya kasuwa?” Baba ma be ansa ba yanata kallon shi yana nazartar yanayin shi suka shiga cikin gida, inna ta miqe da fara’a Tana chewa “aa ya akayi kuka dawo tare?” Imran ya duqa ya gaisheta se ta lura da yanayin shi har zata tambaya se baba yayi mata alama da tayi shiru, haka imran ya miqe jiki ba qwari ya shiga dakin su, ya tarar qanenshi duk ya baza kaya kan katifar, inda lfya lau ne da se ya gyara dakin tsab, amma kawai ture kayan yayi ya kwanta, shi ya kasa baccee kuma shi ya kasa tashi, haka dai yake kwanche cikin wani irin yanayi, da Qarfe biyar ta dan gota baba da inna suka shigo dakin, inna tana riqe da yar qarama kula da take samai abnci, suka tarar dashi kwanche, “imrana tashi muyi magana da kai” baba ya kirashi 

Ya miqe zaune daqyar yana ganin jiri na Neman mayar dashi kwanche, addua yake a cikin ranshi Allah yasa su inna su che mishi abnda maryam tache mishi ba haka ba, amma kash, hakuri suka shiga bashi, baban yana chewa “kawun mayrama ni ya hwara samu da maganar, yacce mini in ka shirya ka fito kawai saboda ga wasu sunje bidar izinin magana da ita kuma alamu sun nuna a shirye suke, na hwada mai tsakani da Allah baka shirya ba, yacce toh ba matsala, bayan nan ya tahi ya hwadima mamar Ita meramun, kuma kasan bata da Abukkiyar shawara kamar innar ka, tazo ta iske innar ka da maganar, kuma innar ka tacce katta duba alaqar su Tache zata hana me bidar maryam ya bide ta tunda dai kaikam baka shirya aure ynzu ba, a bashshi yazo ita maryam din ta yanke hukunci da kanta”. Ya tsaya ya nisa sannan yachi gaba “Imrana bamuyi haka don bamu son ka ba, munyi ne saboda ko mu adda diya macce me girman maryam dole muso ache tayi aure ynzu, inda innar ka tache ma mamar maryam aa katta bari a bidi maryam ai kaga batayima mutuncin da a tsakanin su adalci ba, kayi hankuri imrana, Allah ubangiji yayi maka zabi mafi kyau da dacewa da kai, Allah ya nuna muna ka samu aiki da ze wadatar da kai da mu gabadaya” nan dai suka yita bashi baki har suka samu ya chi abnci ya dan sake, amma zanchen Gaskiya rabuwa da maryam ya taba imran don har aikin delivery dena zuwa Yayi saboda ko yaje se yayita shirme, ya dauku kayan wancan ya kaima wancan, haka dai ya aje aikin na dan lokaci yache se ya samu daidaiton tunani tukunna


Da rana, gidan su maryam ya cika, innar su imran da wasu cikin maqotansu sun shigo, Wasu suna magana.

Wasu suna dariya, Wasu kuma suna tambayar abubuwan da aka shirya.

Akwai wani irin farin ciki da Maryam ta dade bata ji ba, dangin Mama suna zuwa Sokoto lokaci-lokaci, amma ba kasafai suke taruwa haka ba.

Maryam ta zauna kusa da anty maimouna qaunar mama wadda suke uba daya

“Kin shirya aure kuwa?”

Maryam ta yi murmushi.

“Ban sani ba anty”

“Ba ki sani ba?”

Maryam ta girgiza kai tana dariya.

“Komi na ta faruwa da sauri.”

Aunty ta taɓa hannunta.

“Allah ya sanya alheri, ai kina addua ko? Komi zeyi dd in shaa Allah”

“Allah ya yadda.”

Aunty ta yi murmushi.

“Allah ya sa ya kula muna da ke.”

“Ameen.”

Maryam ta yi shiru.

Ba ta san yadda za ta bayyana komai ba.

Ba ta san Zaid sosai ba.

Kuma ba wai tana shiga wannan aure ne saboda ta san zai kula da ita ba.

Ta shiga ne saboda ta binciko wani Abu gameda yar uwar ta Aisha.

Maryam ta kalli mutane da ke zaune a parlor.

Sai ta ji kamar tana kallon rayuwarta tana canzawa a gabanta.

Da yamma, Maryam ta shiga ɗakinta, Ta rufe ƙofar.

Sai ta zauna a gefen gado, Wayarta tana hannunta, Ta duba message ɗin Zaid da ya aiko da safe.

“Salamu alaikum hope komi lfya?”

Ta karanta sau biyu.

Sai ta yi tunani.

Zaid.

Wai mijin da zan aura nan da kwana 4, Anya kuwa?

Kalmar ta yi mata wani irin nauyi, Ta ajiye wayar.

“Ya Allah…”

Sai ta kalli hoton Aisha da ke gaban madubin ta

“Da ace kina nan.”

Se kuma Ta yi shiru.

“Da kin gaya min abinda kika gano.”

Hawayenta suka cika idanunta, Amma bata bari sun zubo ba, Ta goge su da sauri.

“Zan gano in shaa Allah” Ta furta a hankali.

“Ko da sai na shiga gidan nan kuwa”

Tana nan zaune shuru tana jin hayaniyar yan Niger daga waje, se taji an banko qaofar ta da qarfi ana sallama, dama ta sani, Indai ba safiya da bahijja ba wa ze yimata haka, suka zauna a gajiya suna aje ledodin da ke hannun su. “Maryam tashi ki gani mun hidda anko da zamusa wurin walima, kinsan nache miki mama tache in an dauko ki daga nan an kaiki gidan mu za’ayi walima da daddare kahin a wuche Abuja washegari”, chewar safiya

Maryam bata ma dago ba “Kuyita ganin kayan ku tunda ku zakusa bani ba”

Bahijja ta harare ta “ai se kin tashi kin gani Banson walakancin bnza, duba kigani ta daga material din, bamusan wane color din kayan zakusa ba, shiyasa munka hidda me brown kinga zeyi matching da kowace kala” ai kuwa material din yayima maryam kyau sosai, “toh duk sauran wannan ledodin me ke ciki? 

Bahijja ta Kalli ledodin sannan ta amsa “mun sawo 20 pieces ankon ne kar ache mu kadai munkayi, in akwai wanda kaso se ya dauka, Sauran ledodin kuma yan abubuwa ne da munka san zaki buqata” 

se kuma ta miqa ma maryam wata leda 

“ga wannan mama tache a kawo miki” 

maryam ta karba ta bude, bedsheets ne ciki masu mugun kyau, se kuma turarukan wuta da humras, maryam ta karba tayita godiya har ta kira maman bahijjan a waya tana ta yimata godiya.

Seda ta qare waya sannan tache a chire mata anko guda biyu, daya za’a ba hauwa koulou diyar anty maumouna, daya kuma zaa aika gidan kawu aba me sunanta


A Netherlands kuwa Zaid na shirin dawowa Abuja yau saura 5 days kuma ya yima mammi alqawarin ze dawo 3days to bikin, ba don haka ba ai da yayi zaman shi tunda za’a iya daura auren ko baya nan, dama tun da yazo ya saye duk abnda mammi tasa shi ya aika, dama ba shi ya je ba, list din da ta aiko kawai ya tura ma secretary dinshi shi yaje ya saye komai yayi musu shipping.

Yana zaune yana tunani wai auren shi nan da 5 days, Shi? Wai da gaske? Shi har ynzu ma ya kasa gayama kowa amma zeyi ma Fahad magana yache ya gayama duk wanda ya kamata, se yaji wayar shi tayi ringing, ai kuwa Fahad din ne ke kira

“Big bro.”

Zaid ya ɗaga kai.

“Naam?”

“Shirye shirye sunyi nisa fah, kusan komai an qare, masu dinkin da mammi tache in kai ma kayan ka jiya suka kawo, an saye hula da takalmi da komai”

Zaid ya gyada kai.

“Okay”

Fahad ya chigaba “yaushe zaka dawo? Na chema mammi a qirga mutum nawa zasuje sokoto daga nan Abuja don a saye ticket tache inaa private jet takeso duk wanda keson yaje ya shirya kawai ai arziki ne”

Zaid ya jingina da kujerarsa.

“Okay, hakan ma Yayi”

Fahad ya yi dariya.

“Big bro, aure fah zakayi amma gabadaya bakayi kama da ango ba, you’re not giving the vibes”

Zaid yayi murmushi

“kana ganina ne? In tashi in fara rawa ne?”

Fahad ya fashe da dariya.

“Maybe.”

Zaid ya girgiza kai.

“Allah ya shirya ka.”

Fahad ya sake yin dariya.

“Okay, okay.”

“Flight Dinka gobe Qarfe nawa ne? Ai 12 ta buga sora kwana hudu?”

Zaid yache “5pm Nigerian time”

“Okay zanzo in dauke ka in shaa Allah”

Zaid ya gyada kai

“Fine.”

Har zeyi cutting call din se kuma ya tsaya

“Big bro.”

“Naam”?

“Kar ka damu kaji?”

Zaid be che komi ba, Fahad ya qara chewa

“Wani lokaci, sai ka bar abubuwa su faru yadda za su faru kawai”

Se ya katse kiran

Zaid yayayita kallon wayar 

Ya yi shiru.

Hakane, in bar abnda ze faru ya faru kawai

Ai shine kawai abnda nikeyi dama…

Amma bai san cewa abubuwan da suke shirin faruwa ba za su kasance kamar yadda kowa yake tsammani ba.

Domin a Sokoto…Maryam tana shirin shiga gidan shi, Kuma tare da ita…

ta na ɗauke da sirrin da babu wanda ya sani.


Sokoto 

Ranar da dangin mama suka iso washegri da yamma se ga hajiya Ruqaiya tareda wasu mata suka kawo kuddi 2 million naira sukache kuddin sa lalle da wankin amarya sabada sunyi shawara tsakaninsu sunga gwara su bada kuddi akan su saye abubuwan, tunda basu san dame dame zaa buqata ba, sunzo da turaruka luxury oils da kuma khumrori masu muguwar tsada na ji da fadi. 

Tarba ta mutunci suka samu wurin dangin mama sannan akayi raha da fira suka chi suka sha abncin da aka tanadar musu, sannan suka wuche gidajen su 


Join our WhatsApp group 


Follow this link to join my WhatsApp group: ***

9469F9A2-E924-4FB1-99A4-2FD7E356D711.png