KIRAN KADDARA

THE ARRIVAL

by @nihaalmaalik

SOKOTO — 1 DAY TO THE WEDDING


Tun safe ake takai da kawo, gidan su Maryam ya qara cika da hayaniya.

Yau kam ba kamar sauran kwanaki ba ne, ko’ina cike yake, kowane daki akwai mutane, saboda gobe ne zaa fara bikin.

Zaayi sa lalle da safe wankin amarya da dare, washegari baza’ayi komi ba, Friday Bayan sallar Jumua kuma a daura aure, da yamma dangin ango zasu zo a dauki amarya a kaita gidan hajiya Ruqaiya se a wuche wurin walima daga chan, washegari assabar kuma zaa wuche Abuja.  

Maryam tana cikin ɗakinta tun safe, ana mata gyaran ƙarshe kamar yadda Mama ta faɗa mata jiya.

“Amarya, yau fa sai kin daure an yi dakyau don a gama komai saboda gobe zakiyi wankan lalle.”

Wata daga cikinsu ta ce tana dariya.

Maryam ta yi murmushi, ta sunkuyar da kai.

A zuciyarta kuwa, tunanin wani abu daban ne take

Gobe zaa fara bikin aurenta da Zaid Rahman Balarabe

Ta kuma tuna a cikin dakin nan nata akwai wata takarda da ta fi komai nauyi a qirjin ta

KADA KI AURI ZAID BALARABE.

Tun jiya take ƙoƙarin kada ta yi tunanin ta, Amma ta kasa, Sai dai ba ta son ta bari wani abu ya bayyana a fuskarta don haka take daurewa tana murmushin yaqe.

A nan ne su safiya da bahijja suka shigo, daga makaranta suke, se suka wuto nan, suna Gaya mata yau Anyi musu unexpected test, maryam tayi shuru tana tunanin miye makomar nata karatun a yanzu? Nan fah suka bude woredrop din kayan maryam a chewar su wai zasu shirya mata kaya saboda daga gobe babu lokaci, zasu chire na kyauta sannan su chire mata wanda zataje dashi, se jin daadi sukeyi suna fira anata raha da annashuwa, ita dai tanata bin su da idanu se indan an tambayeta abu ta ansa. 

A chan waje kuma wasu daga cikin yan uwan mama ne da innar su imran sun dawo daga kasuwa sun sawo ma maryam abubuwan da sukayi list wa’inda za’a hada mata cikin gara, dama tun da mama ta gaya musu dangin mijin mayrama sunche kar ayi komi sukayi shawara, inna ladi tache bazaayi kayan dakin ba tunda sun riga sunyi, amma ayi mata gara me kyau, komi asa mata yadda in taje zata raba ma dangin shi, sun sawo man shanu, garin miyar kuka, garin kubewa, niqaqqar gyada ta kunu, da sauran abubuwan gargajiya, sannan anyi drum drum na su chin chin, da su alkaki da diblan, da nakiya da sauran su


A chan Amsterdam kuwa, Zaid ya samu delay na jirgi, be taso ba se ana gobe za’a fara biki, zaune yake a lounge na business class yanata tunanin kar mammi taga kamar da gangan yaqi dawowa cikin lokaci, yaja tsaki kadan, yana fadin “this is why I hate regular flights” Koda akayi announcing jirgin su ze tashi ya miqe tsaye yana tura hand luggage dinshi ya nufi departure gate din da aka fadi a announcement, seda ya shiga ya zauna sannan ya kira fahad ya sanar dashi zasu tashi.


A Abuja kuwa tun safe Mammi ta tabbatar komai a shirye yake dama jira kawai suke suji idan ya taso se suyi calculating sadda jirgin ze sauka su wuche airport din in yaso da ya sauka su nufi sokoto, already ta hada duka kayan events da tasa aka dinka mishi tasa cikin babban akwati daya, kowane da matching hulla da takalmi da agogo har da turaruka da Underwears babu abnda bata hada mishi ba, seda suka bari jirgin zaid yana saura 1hr ya sauka sannan suka fito zasu nufi airport, akwai furnishing company din da mammi ta kira sukazo ta basu key din part din zaid tache kafin su qare biki su dawo tanason gabadaya komai na part dinnan a fitar dashi a saka sabo, ta gaya musu idan sun qare su rufe dakin zaid kar su bashshi a bude, daga nan suka shiga motoci suka nufi airport.

Ba ta so su yi tafiyar cikin regular flight tareda sauran mutane, bikin dan gaban goshinta ne fah 

Ta ce ba za a sayi tickets na regular flight ba,

Za su yi chartering flight, Kowa da kowa yazo aje 

A gare ta, babu wani abu da ya fi muhimmanci kamar ganin farin ciki zaid da kuma fatar su isa bikin aurensa lafiya, dangi dayawa sunzo ayi tafiyar dasu, especially yan uwan mammi, sisters dinta da aunties dinta, su hajiya raliya Balarabe, su anty Hadiza da da anty fati

Fahad ma yana tare da su da kuma abokan zaid da fahad din ya aika ma invite duk sunzo zasuyima zaid kara, a nan airport suka jira zaid ya sauka, sama sama aka gaggaisa sannan suka shiga jirgin da ze wuche dasu sokoton. 

Jirgin ya sauka a Sultan Abubakar III International Airport Sokoto da rana, Da suka fito, Fahad ya fara kallon wajen airport din yana fadin 

“Finally, sokoto we are here for my big bro”

Zaid na fitowa ya sauke ajiyar zuciya, Ya yi shiru.

Gobe ne bikin gashi tun kafin yaje Netherlands basu sake waya ba, wai da gaske dai ynzu auren zeyi kenan? Yake tambayer kanshi a ranshi 

Fahad ya kalle shi yana murmushi.

“Big bro.”

“Naam?”

“Ka shirya?”

Zaid ya yi masa kallon gefe.

“inada zabi ne?”

Fahad ya yi dariya.

“Aa Bakada shi, Kayi sake tun baya”

Mammi ta yi murmushi.

“Ka bar shi mana.”

Zaid ya yi murmushi kaɗan.


A wajen airport kuwa, Hajiya Ruqaiya tana nan tana jiran su tare da wasu daga cikin mutanen gidanta da sukazo, suna tsaye a wurin arrivals se ga su mammi da sauran Mutanen sunata fitowa, nan fah aka fara Barka da sauka ana gaisuwa 

“Assalamu alaikum!”

“Wa alaikumus salam.”

Haj Ruqaiya ta rungume Mammi.

“Barka da zuwa yar uwa”

“Yawwa Yawwa sannun ku Mun gode.”

“Ya muka same ku?”

“Lfya qalau Alhamdulillah”

Fahad ya yi sallama yana gaisawa dasu, Zaid shima yayi sallama ya gaishe su, Yana tsaye cikin nutsuwarsa yana gaisawa da manyan cikinsu, Babu hayaniya sam a tare da shi, Kamar dai yadda yake kullum.

Haj Ruqaiya ta kalle shi ta yi murmushi.

“Ango idonka kenan?”

Fahad ya fashe da dariya.

“Eh, ki ganshi dai aunty”

Zaid ya yi murmushi kaɗan.

“Barka da zuwa Sokoto,”

“Nagode anty”

Ba su ɓata lokaci ba.

An fara ɗaukar kayayyakin da suka zo da su.

Manyan akwatunan lefe suka fara fitowa, set hudu na akwatuna ne, set na farko briggs ne, na biyu kuma lv na uku kuma Pierre Cardin, na hudu Chanel, Sannan da wasu manyan light weight luggages guda biyu da kuma wasu traditional baskets da aka saka humras da mammi tayi order dinsu tun daga Chad 

Fahad ya kalli kayan yache ma zaid 

“Big bro, your wife is getting spoiled.”

Zaid ya girgiza kai.

“Aikin Mammi ne ai”

Fahad ya yi dariya.


Daga airport suka nufi gidansu Maryam kai tsaye. Saboda su gaisa kuma su kai kayan lefen, 

Zaid yana zaune yana kallon window ta cikin motar da yake, Yana kallon garin Sokoto, Gidaje, Mutane, Shaguna, hanyoyi..zuciyar shi ta kasa yadda wai auren shi zaayi. 

Fahad yana magana da wasu daga cikin mutanen da suke tare da su a motar

Mammi kuwa tana cikin wata mota daban tareda hajiya ruqaiya da hajiya raliya

Su Fahad sunata fira a mota amma Zaid hankalinsa yana wani wuri ba kan su fahad ba

Maryam.

Yaya take?

Yaya za ta ji idan ta gan shi?

Ya yi shiru.


Da suka isa gidan su Maryam, aka fara sauke akwatuna da kaya

Hayaniya ta tashi anata maraba maraba, Matan gidan suka fito, wasu suna kallon akwatunan.

Wasu suna taimakawa wajen sauke su.

Mama ta fito tareda yan uwanta da innar imran don ta tarbi mammi, sai suka rungume juna.

“Barka da zuwa.”

“Mun gode sosai.”

“Alhamdulillah kun iso lafiya? Ya hanya?”

“Lafiya ƙalau alhamdulillah” anata gaggaisawa 

A tsakar gidan dama an shirya musu wajen zama, Ana ta gaisuwa da raha Ana dariya.

Ana kallon kayan da aka kawo.

“Subhanallah.”

Wata daga cikin matan ta ce tana kallon akwatunan.

“Wannan lefen fa? Ma Shaa Allah”

Duka akayi dariya 

Fahad da zaid da abokan su da sauran maza duka suna waje

Maryam tana ɗakinta ita kadai, don tunda aka fara guda ana chewa ga dangin ango sun iso, Safiyya da bahijja da hauwa koulu suka fita suka batta ita kadai a daki, Tana jin hayaniya daga waje, Tana jin muryoyin mutane, Tanjin ana dariya, zuciyarta se bugawa take da sauri, Ta san sun iso.

Zaid ya iso.

Maryam ta zauna a gefen gadonta.

Ta kalli kanta madubi, Ta gyara hijab ɗinta, Ta ɗauki numfashi ta sauke da qarfi, Sai ta tuna takardar nan, Ta ɗan tsaya, a dd nan su Safiyya suka dawo sukaji tana fadin 

“Ya Allah…Ka sa komai ya zama alheri.”

Safiya ta kalleta se tazo ta rungume ta, bahijja na fadin “awwnnn wai Batason mu gane taji daadi shine take muna cover, da zarar an kaiki kuka shige daki zamuga yadda zaayi” 

safiya ta fashe da dariya “wallahi bahijja bakida m” 

“ai kema haka kika riqe mama kinata kuka amma tun da muka kaiki shuru” 

safiya sake yin dariya  

“ai ke idan za’a kaiki zamuga yadda zakiyi” sunata fira amma hnkalin maryam yayi nisa daga kan su.

A waje, ana ta tarbar dangin angon da abnci da abubuwan da aka shirya musu na musamman, mazan ma an shigo dasu a parlorn margayi alh bashir, an Kai musu nasu abnci da abun sha Kala Kala 

A cikin ɗakinta kuwa, Maryam tanata qarfafa zuciyarta don kada ta fallasa asirin da ke cikin ta

Domin gobe…zata dauki hanyar zama matar zaid.

Kuma daga ita har Zaid ba su san cewa aurensu zai buɗe wata ƙofa da babu ɗayansu da ya shirya shigarta ba



Join our WhatsApp group 


Follow this link to join my WhatsApp group: ***


6B6CD24D-9239-4C8D-843A-74E9E5283AB6.png