KIRAN KADDARA

BOUND BY FATE

by @nihaalmaalik

Kamar jiya, yau ma tun kafin asuba, gidan su Maryam ya sake barkewa da hayaniya.

Yau ne ranar daurin aure, bayan sallar jumua, 

Idan an daura aure dangin zaid zasu zo daukar amarya da yamma, za’a kaita gidan hajiya Ruqaiya daga chan zasu mata shiri suje walimar da dangin ango suka hada.

A tsakar gida kuwa mata suna ta shiga da fita. Wasu suna gyara kayan da za a kai wajen walima, wasu suna kula da abnincin yinin biki, wasu kuma suna shirya Maryam daga cikin ɗakinta tareda qawayen ta

Ta kalli kanta na ɗan lokaci bayan ansa mata gown fara me duwatsu silver, su safiya se zuzuta irin kyaun da tayi suke da sauran qawayen su, ita sam hnkalinta baya wajen su, A jiya ta kwanta tana tunanin wannan ranar, Yau kuma gashi tazo 

Yau za a daura aurenta da Zaid Rahman Balarabe.

Ta sauke ajiyar zuciya.

Safiya ta dafa kafadar ta

“Qawata, yaya?”

Maryam ta kalleta.

“Me ya faru?”

“Au tambayata ma kikai?”

“Duk se kuyita tambayata, don Allah ku rabu dani” ta fadi a qufule 

Safiya tafara dariya, amma ganin hawayen da suka fara zarya idon maryam yasa ta gimtse dariyar ta shiga rarrashinta

“Duk kyaun nan da kikayi amma se ki rinqa kuka, Habah kiyi hakuri manah yayana fah baze chanye ki ba mutum ne kamar ke, don Allah ki saki ran ki ayi komi kina cikin walwala kinsan da an daura aure zasu zo nan ayi hotuna, kar ayi hotuna idonki a kumbure”

Maryam tanata goge hawayen, Amma zuciyarta ta sake yin nauyi saboda tunatar da ita da safiya tayi ana chan za’a daura mata aure, Ta sake tuna takardar nan

KADA KI AURI ZAID BALARABE.

Ta rufe idanunta na ƴa seconds.

Ya Allah, ka shige min gaba


A wani ɓangaren kuwa, gidan Hajiya Ruqaiya ma cike yake da mutane.

Maza sun taru, Dangi, Abokai, Manyan mutane har business partners din zaid da Fahad yayi inviting on behalf of Zaid, Wasu suna hira, wasu suna dariya, wasu kuma suna jiran a fita a tafi masallacin jumuar unguwar su maryam da zaa yi sallah sannan a fara daurin auren

Zaid yana zaune cikin nutsuwa, Sanye yake da farar babbar riga mai kyau wadda mammi tasa aka dinka mishi saboda daurin auren, da zarar ka kalleshi kasan kaga ango, kayan sun fito da asalin kyau da haibar shi, in ka kalleshi se kache balaraben Saudi Arabia ne

Fahad ya matso kusa da shi, Ya kalle shi

“Big bro.”

Zaid ma ya kalle shi.

“Naam?”

“Yau ne fah, Allah ya kawo mu, gurin mammi ze cika”

Be ansa mishi ba, Fahad ya yi dariya

“Ka yi murmushi mana.”

Zaid ya ɗan yi murmushi.

“Allah yau zan yi maka dariya sosai idan akaje gidan su maryam zaayi hotuna bayan daurin aure ka tsaya kana mata muzurai, Zanga yadda zaka riqeta kuyi pictures, gara ma ka fara sakin fuska tun ynzu”

Zaid ya girgiza kai.

“Fahad don Allah ka kama kanka”

“Gaskiya big bro ban maka alqawari ba” ya fadi yana dariya

Zaid kuwa ya sake yin shiru.

A wannan karon, zuciyarsa ta fi bugawa da karfi 

Ba don tsoro ba, Sai dai saboda ya san cewa cikin ƴan mintuna, rayuwarsa za ta canza.

Ba zai sake kasancewa shi kaɗai ba, Zai zama mijin wata yarinya da bai ma san ta sosai ba,

Mijin Maryam.

Ya tuna lokacin da ya fara ganinta, yadda ya ganta yar qarama a gaban shi, hannunta, ya tuna hannunta da ke riqe da tray, yayi murmushi, “hannunta nada kyau” ya furta a ran shi.

Allah ya sa na yi abin da ya dace, Allah ka bani ikon kula da ita da kuma yimata adalci


Bayan sallar jumua Mutane suka zauna, An kira wakilai, An gabatar da bayanan amarya da ango.

Maryam Bashir Misalati.

Zaid Rahman Balarabe.

Aka ambaci sadaki ₦500,000.

Akayi addua sannan aka fara daurin aure.

An daura auren ZAID RAHMAN BALARABE DA MARYAM BASHIR ME SALATI AKAN SADAKI 500000 LAKADAN BA AJALAN BA

A wannan lokacin, Maryam tana zaune tare da qawayenta dayawa da sukazo, suna sauraron muryoyin da ke shigowa daga wajen gidan, maza na shigowa mata suka fara guďa, Zuciyarta tana bugawa da qarfi

Sai suka ji:

“An daura an daura”

Anty maimouna ta shigo ta kama hannunta tana rangada guda

“Saki ranki kinji, Amarya.”

Maryam ta ɗaga kai, qawayenta suka tashi 

Suna ta rungume ta.

“Allah ya sanya alheri.”

“Amin.”

A wannan lokacin, Maryam ta ji wani abu ya sauka a zuciyarta.

Ta zama matar aure.

Matar Zaid.

Ta sunkuyar da kai, Hawaye suka taru a idanunta.

Ba ta san ko bakin ciki ne ba, Ko tsoro.

Ko kuma nauyin abin da take tunani game da Aisha

Amma ta san abu ɗaya.

Babu komawa baya, an riga an daura


A masallaci kuwa bayan an daura aure anata gaisawa da ango ana mishi adduar sanya alheri

Abokansa suka zo suna taya shi murna suna ta bashi hannu,

“Congratulations!”

“Allah ya sanya alheri.”

“Amin.”

“Allah ya ba ku zaman lafiya.”

“Amin.”

Daga nan convoy din kai tsaye gidansu maryam aka wuche Tana daga daki Safiyya ta shigo “maryam ango ya iso zakuyi pictures”

Dam daramm gaban Maryam ya fara bugawa da sauri

“Ynzu?” 

“Eh manah”

Safiyya da Bahijja suka gyara mata gyalenta ya sauko ya rufe mata fuska amma tana ganin komai da yake net ne, tun da aka fara biki maryam sedai a dan shafa mata powder amma bata yadda da wani makeup ba, yau ma hakane amma wani irin musulmin kyau tayi saboda yadda kayan suka karbeta da kuma powder da aka shafa mata wadda bata saba shafawa ba,

Riqota sukayi tareda hauwa koulou da sauran abokan su a hnkali har parlor din margayi Alh bashir inda zaid yake tare da abokan shi

Maryam na Sanyo qafarta a parlorn idon shi ya sauka a kanta, itama ta ganshi daga cikin gyalen ta, sai ta tsaya na ɗan lokaci.

Shi ma ya kalleta.

Parlorn Yayi shuru..

Duk mutanen da suke kusa da su suna kallonsu suna murmushi, suna awnnn kamar suna jiran su nuna wani irin farin ciki na ma’aurata.

Amma gaskiyar magana ita ce…ba su saba da juna ba, basu ma san me zasuyi ba

Maryam kam wani irin tsoro ma takeji 

Ba tsoron Zaid ba ne kai tsaye, sai dai sabon yanayin da take jin kanta a ciki 

Yanzu fah wannan mijinta ne.

Ga kuma duk wa’inda ke wurin sun qura musu ido suna kallonsu 

Mai ɗaukar hoto ne ya gyara camera 

“Ango, Amarya, mu fara ko?”

Maryam ta kalli Zaid, Zaid ya kalleta, Suka kusanto.

Sai mai ɗaukar hoton ya fara

“Okay, ku dan riqe juna”

Duka suka tsaya.

Maryam ta ɗan ɗago ido ta kalle Zaid.

Zaid ma ya kalleta, kowannensu yana tunanin

Me ya kamata mu yi?

Zaid ya ɗan matsa kusa hannunshi ya tsaya a gefenta, har ya ɗaga hannunsa kaɗan, sai ya dakata.

Yaji nauyin taba ta, wani irin nauyi akan shi

Fahad da ke gefe ya fara murmushi.

“Big bro ka dena haka manah a riga an daura fah.”

Wasu suka yi dariya.

Maryam ta sunkuyar da kai saboda kunya.

Zaid ya yi murmushi kaɗan.

Mai ɗaukar hoton ya sake cewa:

“Amarya da ango kuyi relaxing, ku tsaya yadda kuke so ta haka hoton ze fito dakyau”

A ƙarshe Zaid ya tsaya kusa da Maryam, hannunsa yana kusa da nata ba tare da ya taba nata ba, Maryam ma ta tsaya tana kallon camera.

Click. Click. Click me hoto yanata dauka 

Amma duk lokacin da aka ce su kusanto sosai, sai sun sake jin kunya 

Sun riga sun zama mata da miji, Amma zuciyarsu ba ta saba da wannan sabon matsayin ba.

A haka dai akayi hotuna masu dan dama, hada abokan ango da qawayen amarya

Sannan suka wuche da chewar da yamma zasu dawo tareda uwaye mata saboda su tafi da amarya

Daga nan kai tsaye gidan hajiya Ruqaiya suka nufa, suna shiga gidan ya dauki guda anata adduoi ana taya mammi murna, direct wurin mammi ya nufa ya duqa a gaban ta, ta taso da shi, Ta kalle shi na ɗan lokaci, Idanunta cike suke da farin ciki Wanda ta kasa boyewa

“Alhamdulillah.”

Zaid ya sunkuyar da kai ya sumbaci hannuwanta.

Ta rungume shi.

“Allah ya yi maka albarka.”

“Amin.”

Ta janye jikinta daga gare shi.

“Ka kula da ita don Allah Zaid ita din amana che”

Zaid ya kalle ta.

“in shaa Allah mammi”

Mammi ta yi murmushi.

Ta san ɗanta.

Idan ya ɗauki abu da muhimmanci, baya wasa da shi, amma shin ya dauki auren nan da gaske?

“Tashi kuje ku chi abnci yana nan an shirya muku, ku huta anjima kadan za’aje a daukota don a samu a fara walimar cikin lokaci”

zaid ya dan bata fuska, “mammi ai su mama Ruqaiya da hajiya raliya da sauran matan zasuje tareda su fahad, ni don Allah a banni kawai” mammi tayi dariya, “ba matsala ynzu tashi kaje ka huta ka chi abnci”.

Bayan kamar hour daya da rabi hajiya Ruqaiya tache ma matan da zasuje dauko maryam su tashi su shirya ya kamata suje ynzu su dauko ta, suka tashi suka fara shiryawa, ita kuma ta leqa dakin da aka tanadar ma maryam da qawayenta da zasu zauna da ita kafin gobe a wuche Abuja, seda ta tabbatar komai ya kammala duk wani abun buqata an ajiye musu sannan ta fito suka kama hanyar gidan su maryam.

Sun shigo da sallama da guda sosai

Su maryam suna jinsu daga cikin dakinta 

Safiyya ta leqa window “laa su mama har sunzo, ynzu za’a wuche gidan mu kenan a fara shirin walima”

Maryam kam idan batayi qarya ba se tache taji qarar bugawar da zuciyar ta tayi a cikin kunnuwanta

Safiya ta chigaba, “tashi mu Chanza miki kaya kafin ache tundazu muna nan muna bata lokaci”ai bata rufe baki ba se ga anty maimouna da gwaggo A’i sun shigo, maryam ko se hawaye take ta dago ta kallesu sukayi mata murmushi sunata lallashin ta, su suka tayata aka chnja mata kaya zuwa Lafaya deep wine, mai kyau aka daura mata ta zauna dass a jikinta, wadda ta dace da atampar da ke qasan lafayar jikinta, aka rufo mata fuskar ta, Safiyya Ta ɗaukar mata ƙaramar handbag ɗinta sannan aka rakata wurin su kawu da uncle aamadou da suke parlorn margayi Alh Bashir, nasifa me ratsa jiki suka yimata sannan aka kaita wurin Su mama ladi, suma sukayi mata, da aka kaita wurin mama rungume ta kawai tayi tache mata tachi gaba da addua kuma da ibadar da tasan ta da ita, sannan aka fito da ita tareda rakiyar abokan ta da gwaggo A’i da Anty maimouna, Wannan shi ne karo na farko da za ta bar gidan Mama a matsayin matar aure.

Ta sauke ajiyar zuciya, tanata hawaye 

A waje kuwa, motoci sun cika kofar gidan.

Babban convoy! Manyan motoci masu tsada sun jere a jere, Wasu daga cikin abokan zaid tareda Fahad suna jiran su a ciki 

Hajiya Ruqaiya ta riƙe hannun Maryam suna takawa a hnkali tareda gwaggo A’i da Anty maimouna da innar imran, “Bismillah hajiya ku shiga nan” chewar hajiya ruqaiya tana musu nuni da wata babbar mota da ke dd gate din gidan, suka shiga suka zauna maryam na tsakiyar su

Mama na daga cikin gida tanata yima yar ta addua a ranta, Motar ta fara tafiya. Maryam na zaune kanta a duqe cikin lafaya tana tunanin Sabuwar rayuwar ta fara.

Da suka isa gidan Hajiya Ruqaiya, suka tarar an shirya abubuwa, Makeup artists, Fashion designers,Stylists.

Duk suna jiran ta.

Aka fara shiga da ita dakin da mammi take, ta tashi ta rungume ta tanajin farin cikin da Allah ya nuna mata ranar auren zaid dinta, idanunta cike da hawaye ta Kalli maryam “ni mamar ki che ba suruka ba kinji? In zaid yayi miki wani abu kada ki kai qara wurin mamarki ni zaki gayama, ki daukeni a mamar ki, duk abnda ke damun ki kada ki boye min, Allah ya yimuku albarka” aka ansa da ameen. Gwaggo A’i da innar imran ne suka danqa hannunta cikin na mammi, mammi kuwa ta riqeta gam, mata se guda suke tayi, daga nan aka wuche da ita dakin da za’a shirya ta, Aka zaunar da ita, Aka fara gyara mata fuska, maryam batason makeup amma ba yadda ta iya batason tayi musu gardama ganin irin qoqarin da akayi na dauko makeup artist da stylist duk saboda ita. Seda aka sake gyara mata gashi sannan aka yimata very light makeup, dama an shirya kayan da zatasa na walimar, Maryam tana zaune cikin nutsuwa tana kallon yadda komai ke gudana.

Bayan wani lokaci, aka kawo mata kayan.

Gown Che blue color me kyaun gaske, an yi mata ado da kayan ƙyalli masu sauƙi amma masu tsada, An yi mata gyale da thesame material, Ta kalli kanta a madubi

Ta ɗan yi mamaki.

“Yau tayi makeup”

Daya daga cikin matan ta yi dariya.

“Kin yi kyau ko?”

Maryam ta yi murmushi kawai

A wani bangaren gidan kuma, Zaid ma ya canza kayan zuwa nashi kayan walimar, navy blue ne, domin kayan su yi matching da nata

Fahad da kalleshi ya yi murmushi

“Big bro, yau fah se back to back kake bani, kaga yadda kake haduwa wai”

Zaid ya kalle shi.

“Dama ni hadadde ne”

“Gaskiya dama kai hadadde ne amma yau ka cika mutum…”

Fahad ya gyara masa babbar rigar.

“Ka cika mutum ynzu ka aje iyali”

Zaid bai ce komai ba saboda be cikin mood din magana 

Bayan an gama shirya Maryam, aka fito da ita.

Duk wanda ya gan ta sai ya yi murmushi.

Hajiya Ruqaiya ta kalleta daga kai har ƙafa.

“Ma Shaa Allah.” Ta furta

Maryam ta sunkuyar da kai.

Mammi ma se smiling take, a fili ta furta

“Ma shaa Allah kana laa quwwata”

“Allah ya sanya alheri.”

“Amin.”

Aka fito da ita

Maryam da Zaid mota ɗaya zasu shiga 

Aka bude mata kofa ta zauna a gefe ɗaya, Zaid na zaune a ciki ɗayan gefen.

Tsakaninsu akwai dan gap

Dukansu suka yi shiru.

Motar ta fara tafiya, Fahad ke driving dinsu, convoy ɗin ya biyo bayansu, Motoci masu tsada suka cika hanya.

Maryam ta kalli window, Zaid kuwa ya kalli gaba.

Babu wanda ya ce komai na ɗan lokaci, seda Fahad yaga basuda niyyar magana sannan ya fara magana

“Anty amarya bazaki gaida Mijinki ba? Bros kai kuma bazaka gaya mata yadda tayi kyau ba?”

Zaid be ansa shi ba, balle maryam da ke jin kamar ansa glue an manne bakin ta

Zaid ya dan juya ya kalleta.

“Mahreeyam, Salamu alaiki”

Maryam ta ɗan tsorata, kuma tana mamakin yadda yake kiran sunanta

Ta kalle shi.

“Wa alaikas Salam, Ina wuni?” Ta gaishe shi 

“Lfya qalau” ya amsa a takaice

Sai ta sake juyawa tana kallon window.

Zaid ya yi shiru.

Bai san me kuma zai ce ba.

Maryam ma ta kasa cewa komai.

Motar ta ci gaba da tafiya har zuwa wurin walima

sabuwar rayuwa ce a gabansu wadda hasashe kawai suke amma ba ɗayansu ya san yadda za ta kasance ba.


Follow this link to join my WhatsApp group: ***


A6929382-F091-4763-B705-35609C4974A7.png