THE FIRST APPEARANCE
WALIMA VENUE
Motar su ta kunna kai cikin harabar wajen walima a natse, sauran motocin suna binsu a baya, Tun kafin su ƙarasa shiga, Maryam ta fara ganin yawan motocin da suka cika wajen.
Manyan motoci ba kalar wadda babu, Luxury SUVs, Prados, Rolls Royces, Wasu daga cikin motocin dangin Zaid, wasu na abokansa, wasu kuma na business partners ɗinsa da Fahad ya gayyata, Wajen ya cika maqil ba masoka tsinke.
An yi masa ado cikin salo mai kyau, ba tare da an cika shi da abubuwa marasa amfani ba.
Flowers, Lights, kujeru, An tanadi wajen maza da wajen mata daban, Maryam se kallo take
Wannan ba irin taron da ta saba gani ba ne, ta juya ta kalli zaid, akayi dd da shima ya juyo,
Sai idanuwansu suka haɗu cikin na juna
Maryam ta sauke kanta da sauri
Fahad da ke driving yana kallonsu ta mirror, Ya yi murmushi shi kaɗai.
“Mun iso fah…”
Babu wanda ya amsa.
“Anya zaku taba yima juna magana kuwa?”
Zaid ya kalle shi daga mirror.
“Fahad.”
“Okay, okay nayi shuru”
Yayi parking dd wurin da zasu sauka, bakin entrance, ya tsaya.
Wasu daga cikin matan suka zo suka buɗe wa Maryam ƙofa.
Hajiya Ruqaiya tana jiran ta a wajen, tana kallonta seda tache Subhanallah saboda ganin kyaun maryam dukda ta ganta kafin su fito gida
“Amaryar mu, sannu da qarasowa”
Safiyya ta riqo hannun maryam ta fito daga mota, Hajiya Ruqaiya ta kama hannunta daya, “Ki yi murmushi mana.”
Maryam ta yi murmushi.
“Wannan murmushin ai kamar za ki yi kuka.” Safiyya ta fashe da dariya
Maryam ta yi dariya kaɗan.
“Yawwa koke fah”
A gefe guda, Zaid ya fito daga motar.
Wasu daga cikin abokansa suka zo suna magana shi.
“Big man!, hannunta fah zaka riqe ku shiga ku zauna”
“Congratulations! Finally ka zama mutum kamar mu”
Zaid ya yi murmushi Kadan yana amsawa.
“Nagode”
Fahad ya fito daga motar shima.
Ya kalli Zaid sannan ya kalli Maryam.
“Anty kiche ya riqe hannunta su shige ciki, an riga an daura fah”
Hajiya ruqaiya tayi dariya tana fadin “ai haka za’ayi”
Zaid ya qaraso wurin da maryam take, gabadaya idon abokan su suna kan su, sunata yimusu video
“Ranka ya dade riqe mata hannu manah” chewar Fahad
Zaid be kalleshi ba, ya miqa mata hannu, a hankali ta saka hannun ta saman nashi, anata daukar su hotuna kala kala
Zayd dai yaji shi a cikin wani irin yanayi da ya kasa ganewa, be taba riqe hannun macce ba ko yan uwan shi, gabadaya hankalinshi ya tafi akan kallon lallen da ke kan farin hannun ta
“Easy bro kada ka chinye hannun” fahad ya rada masa a kunne”
Zaid ya dawo cikin hankalin shi amma yana yi yana Dan matse hannunta don jin yake kamar hannun ze kucce mishi idan be riqe dakyau ba.
A bangaren maryam zuciyarta ke bugawa da wani irin saurin gaske
Takawa suke a hnkali mutane suna bayan su ana raka su zuwa wajen da aka tanadar musu, waqar maher Zain ta paradise tana playing a hnkali
Mutane sunata kallonsu, anata video da hotuna da wayoyi, idan ka kallesu se ka zata ko wa’innan amarya da angon larabawan saudia ne suke zaune a Nigeria
Zaid kuwa tafiya yake cikin nutsuwa kamar yadda ya saba.
Amma a cikin zuciyarsa, yana jin yadda duk idanu suke kansu.
Ya kalli Maryam ta dan gefe, Kalar blue ɗin ya yi mata kyau, duhun kayan yasa farar fatarta ta haska sosai, gyalen ya rufe kanta sosai se dan Gashin da ya fito daga kanta kadan, Makeup ɗin da bata saba ba yasa fuskar ta fito tarr, da yake simple ne face dinta be chanja ba se qara kyau da tayi
Ya sake kallon gabanshi
Yarinyar nan tana dakyau ma shaa Allah yake fadi a ranshi
Sai ya danne tunanin, Ba lokacin tunani ba ne.
Suka taka har wurin zamansu suka zauna,
Maryam a gefe ɗaya, Zaid a ɗayan gefen, harynzu kuma be saki hannunta ba, sam hankalin shi be bashi ya saki hannun ba, se ma qura ma hannun ido da Yayi yana kallo, Hakan ya sa Fahad da wasu abokansa da suke kusa suka fara murmushi, Suka rinqa sako mishi magana qasa qasa daga inda suke zaune amma sam shi beji su ba, hankalinsa yayi nisa, Maryam ta ji su, ta sunkuyar da kanta qasa, bazata iya qwache hannunta ba, Sai da aka fara waazi ya dan yi nisa sannna masu daukar hotuna suka taso ɗaukar hoto
“Ku kalle ni nan.”
“Kuyi dariya.”
“Ango, dan matsa kusa da amarya.”
Zaid ya kalli Maryam, Maryam ta kalle shi.
Ya dan kusanto kaɗan.
“Yawwa yayi.”
Click.
“Bari a qari wani.”
Click.
“Amarya, Kalli mijin ki”
Dam qirjin maryam ya buga, ta dan ɗago ido ta kalli Zaid, Zaid ma ya kalleta.
Click.
Maryam ta sake sauke kanta da sauri
Su Safiyya da ke wurin suka yi dariya.
“Amarya kunya take ji.”
Maryam ta yi murmushi, sannan suka hauro suma akayita daukar hotunan dasu, su hajiya Ruqaiya da Mammi da su hajiya raliya da su anty hadiza da anty fati duk sukazo, haka su Anty maimouna da gwaggo A’i da innar su imran da sauran dangin mama na Niger hadda su kaka ladi duka aka taso akaita hotunan tarihi.
Bayan ɗan lokaci, aka fara yawo da abinci.
Maza suna gefen su, Mata ma suna nasu wajen, Anata waazi.
Maryam tana zaune tareda mijinta kanta a qasa, Ta lura da wani abu, Ko a cikin taron mutane, Zaid yana da wata irin nutsuwa.
Sai ta tuna yadda ya yake zaune ranar da ta fara ganinsa da Kuma yadda ya taimaka mata da tray ɗin hannunta, Ta ɗan yi shiru.
Missa ma zan rinqa jin tsoro? Da ganinshi yanada sanyin hali baze yi wuyar sha’ani ba
Amma nan take tunanin ya tsaya.
Balarabe.
Sunayen da Aisha ta rubuta cikin takardun ta, Takardar Warning da aka aiko mata, Maryam ta sauke ajiyar zuciya.
Akwai abin da take nema.
Kuma har yanzu ba ta san inda za ta fara ba.
A wani ɓangaren kuwa, Fahad yana tsaye yana kallon Maryam, Murmushi yake yi, Amma idanunsa ba faraa che a cikinsu ba.
Ya lura da yadda maryam take a takure kamar tana tsoron zaid, Da kuma yadda idan wani ya ambaci Zaid da sunan Mr. Balarabe, fuskarta tana dan chanza yanayi na ɗan lokaci kamar tana tunani, Sai wani daga cikin mutanen da ke kusa da shi yayi mai magana
“Fahad, lfya?”
Ya dawo da murmushin shi
“Lfya qalau fah”
“Ynzu dai zaid Yayi settling saura kai.”
Fahad ya yi dariya.
“Hakane nima kar ku damu”
Suka chi gaba da firar su
Anata hidimar walima, Hajiya Ruqaiya ta zo kusa da Maryam.
“Yaya kike?”
“Alhamdulillah.”
“Kin gaji ko?”
“Kaɗan.”
“Ki ci abinci mana, gashi an ajiye muku tun dazu”
Maryam ta yi murmushi.
“Na qoshi mama”
Hajiya Ruqaiya ta kalli Zaid.
“Zaid.”
Ya juyo
“Na’am?”
“Ka kula da amaryarka, tunda aka daukota daga gidansu bata chi abnci ba”
Zaid ya kalli Maryam, Sai ya kalli Hajiya Ruqaiya.
“In shaa Allah.”
“Good.”
Ta yi murmushi ta tafi.
Maryam ta yi shiru.
Sai Zaid ya kalle ta.
“Kin gaji ne?”
Maryam ta ɗago kai.
“Eh kadan”
“Ki chi wani abu ko kadan ne”
“Se anjima in Shaa Allah”
Sai ya ɗauko plate me snacks da aka ajiye musu ya ajiye kusa da ita.
Maryam ta kalle shi.
“Nagode”
“You’re welcome.”
Sai ya chigaba da kallon gabanshi
Ita kam maryam ya zaayi ta gaya mishi da wanne hannu zata chi snacks tunda hannun daman ta yake riqe dashi, shi kamar ma ya manta chewa yana riqe da hannunta.
Wani irin shiru ne ya sake shiga tsakaninsu se sauraren wa’azin suke
Da dare ya fara yin nisa, walimar ta fara lafawa
Wasu baƙi sun fara wucewa, Maryam ta gaji sosai.
“Mu wuce ko?” Zaid ya rada mata
Maryam ta ɗaga kai.
“Awo”
Zaid ya kalleta ya maimaita “Awo” a fili yana dariya, itama dariyar tayi tana dan jin kunya
Ya tsaya yana jiran ta tashi.
Maryam zata miqe ya tayata gyara rigarta ta miqe tsaye, A lokacin da za su fita, Hajiya Ruqaiya ta zo ta rungume Maryam.
“Kiyi wanka ki kwanta kafin mu qaraso, kinsan gobe akwai tafiya Abuja, ya kamata ki huta”
Maryam ta yi murmushi.
“In shaa Allah mama”
“Anty ki dan ba safiya wani Abu ta miqo muna mota, bata chi komai ba” chewar zaid
“Ai ko bari in bayar ynzu ta miqo muku”
Suka juya suna ta dan gaishe da manyan mutanen da suka rage a wurin, suka nufi motar.
Ya bude mata ta shiga, shima ya zagaya ya shiga. Ba tareda Fahad suke ba, Driver ne zeyi tukin, seda suka jira safiya ta kawo saqon sannan driver ya tayar, suka fara tafiya, Maryam ta kalli window tana jin kamar ta roqe shi ya kaita gida taga mama, lokaci ya Ɗan wuce, maryam na jin gajiya sosai, Ta jingina da kujerar motar, Ta rufe idanunta, Ba ta san abin da zai faru gobe ba, Ba ta sani ba ko gidan da take shirin shiga zai kawo mata amsoshin da take nema ba, Bata sani ba ko Aisha ta bar wani abu a baya wanda zai kusan kaita ga gaskiyar da ta dade tana nema ba, Kuma ba ta san cewa mutumin da take zaune kusa da shi…
shi ne mutumin da rayuwarta za ta fara haɗewa da tasa fiye da yadda take zato.
Motar ta ci gaba da tafiya zuwa gidan haj Ruqayya
Kuma a wannan daren, ba wai Maryam ce kaɗai take shiga sabuwar rayuwa ba.
Zaid ma ya shiga tasa
Follow this link to join my WhatsApp group: ***