INUWAR KADDARA 🖤

GARGADI 🫣

by @meelahbazata978

INUWAR ƘADDARA 🖤

Book 1

Page 8 ✍️

Ko da motar ta isa unguwar, a gaban wani katafaren gida ta faka. Jagwa ya kashe motar, yayin da Sayyid yake zaune har lokacin bai motsa ba. Duna ma yana cikin motar yana kallon gidan.

Ba yau ne karon farko da Madugu ya sa Alhaji Haladu a cikin tunaninsa ba. Duk da yana masa aiki, amma tun daren da ’yan sanda suka biyo shi, wani abu ya zauna masa a rai. Domin kuwa, ’yan sandan nan ba su san wanda suke bi ba, amma shi ya san cewa ba haɗuwa ce kawai ta sa suka biyo shi ba, ko kuma ace akasi, tabbas turosu aka yi. To, wanene yake da wannan zarra? Da ya yi nazari a kan abin da ya faru, sunan Alhaji Haladu ne ya fara zuwa masa a tunaninsa. Hakan ya sa ya ji ya kamata dole ya zo ya ja masa kunne.

Sai da ya ɗan jima a motar, ba shi da niyyar fitowa, har sai da Jagwa ya ce:

“Madugu, mun iso fa.”

“Da ya ke makaho ne ni.”

Ya faɗa yana gyara hannun rigarsa. Sanin baƙar magana ya gaya masa ya sa Jagwa ya yi dariya kawai, bai ce komai ba. Sai da ya ƙara mintina kusan biyar kafin ya fito daga motar cikin i  sa,da izza,ya doshi gidan.

Jagwa da Duna suka bi bayansa zuwa cikin gidan. Mai gadin gidan yana hango Madugu, ya yi sauri ya juya zai ɓuya. Duna ya katse hanzarinsa da faɗin:

“Malam, dawo, ba mu da case da kai dan wahala.”

Dawowa ya yi ya wayance, yana murmushin dole tare da yi musu barka da zuwa, kuma idanunsa suna ƙasa. Ba ya son kallon Madugu.

Wani zuwan da Madugu ya yi gidan ne ya yi niyyar shiga, lokacin ma shi da Duna ne kawai suka zo. Mai gadin sabo ne, bai san waye Madugu ba. Aikuwa, yana wani fankama wai ba za su shiga ba sai Alhaji ya san da zuwansu. Mari ɗaya Madugu ya masa da hannunsa, ya faɗi a gurin ya sume. Dama kuma ba ya son duka da hannu, domin hannunsa ba shi da kyau. Haka ko, idan ana faɗa, in dai shi ya yi sara da kansa, to sai ka ji jiki sosai. Hakan ya sa duk sanda Madugu ya zare adda, kowa sai ya gudu, domin kuwa danyen aiki yake yi.

Jikin mai gadin yana rawa yake faɗin:

“Barka da zuwa, Madugu uban tafiya, ja gayya mai jan aiki...”

Ɗaga masa hannu ya yi, ganin yana niyyar janyo wani dogon kirari, ya ce:

“Kansila na nan?”

“Eh, Ranka ya daɗe Madugu.”

“Sanar da shi madugu bisa hanya.”

Mai gadin ya yi saurin shiga cikin gidan. Ba a daɗe ba, sai ga shi ya dawo, yana mai nuna musu hanyar shiga.

Sayyid ya nufi ƙofar falon cikin takunsa na nutsuwa. Jagwa da Duna suna biye da shi. A hankali yake tafiya kamar wani sarki, su kuma suna take masa baya kamar fadawansa.

Ko da suka shiga falon, Alhaji Haladu ya kasa sukuni, sai muzurai yake yi, duk da yadda yake ƙoƙarin daidaita yanayinsa domin kada Madugu ya fahimta. Suna shigowa, ya fara washe haƙora yana faɗin:

“Madugu! Ashe kai ne. Barka da zuwa, ai ban san kana hanya ba.”

Kujerar da take fuskantarsa ya zauna, su kuwa Jagwa da Duna suna tsaye a bayansa.

Madugu ya zuba masa ido na wasu daƙiƙu kafin ya yi magana da sautin da ya sa Alhaji Haladu ya zaro ido.

“Sai kuma ka tura ’yan sanda su kama ni ko?”

Nan take murmushin da yake ta ƙaƙalowa a fuskarsa ya ɓace. Ya kalli Madugu, sannan ya gyara zamansa yana dubansa.

“Wa ya gaya maka haka? Haba dai, Madugu, ta yaya zan saka ’yan sanda su kama ka? Wane ɗan sanda ne nawa yake da wannan gwarin gwiwar?”

“Kansila, na san wanene kai. Sanin ɗanka yana hannuna ya sa kake ƙoƙarin kuɓutar da shi ko ta halin ƙaƙa. Sannan kuma, abin da nake so na sanar da kai shi ne, ɗanka ba zai dawo ba har sai yarinyar da ya yi ƙoƙarin cutarwa ta samu lafiya.

" Sannan kai ne za ka biya kuɗin komai da ya danganci samun lafiyarta. Sannan gargadi na ƙarshe shi ne: ka yi wa ɗanka gargadi. Idan ba haka ba, tabbas Madugu zai sake masa sabuwar kaciya. Idan shi ne ɗan taure, na rantse maka da Huwarrahmanu, duk sanda ya sake ƙoƙarin haiƙewa wata yarinya, sai na yi masa dandaƙa. Idan aure yake so, ka yi masa aure, idan ba haka ba...”

Ya yi ƙwafa ba tare da ya ƙarasa ba. Sosai jikin Alhaji Haladu yake rawa. Ya fi kowa sanin shaidar cin Madugu, domin shi ne ya taimaka masa a gurin neman ta ƙarar kujerar da yake kai.

Alhaji Haladu ya yi saurin miƙewa tsaye, yana kallon Sayyid kamar wanda aka yi wa albishir da mutuwa. Yana so ya danne fushinsa, amma hakan ya gagara. Ba ƙaramin ƙaunar ɗansa yake yi ba, kuma duk abin da yaron yake yi, yana sa ne.

“Haba, Madugu, ka san irin mutuncin da nake da shi a wannan gari. Wannan yaron ɗana ne tilo, kuma duk abin da ya yi, ai ana iya zama a tattauna a gyara, ba sai ya kai mu ga haka ba.”

Sayyid ya ɗan karkatar da kansa, idanunsa a kan fuskar Alhaji Haladu, yana yi masa wani kallo irin na wanda ake son kama masa hankali.

“Da ka tuna da zama a tattauna tun farko, da ba ka yi ƙoƙarin tsallake iyakarka ba, da ba ka tura ’yan sanda domin su ɓatar da ni ba.”

Gaba ɗaya Alhaji Haladu ya rasa abin cewa. Domin yana ganin abin da ya yi shi ne zai kuɓutar da ɗansa daga hannun Madugu. Yau tsawon kwana uku kenan yaron yana hannunsa, kuma da kansa Madugu ya zo ya gaya masa cewa ɗansa yana gurinsa, kuma zai yi masa hukunci daidai da abin da ya aikata. Babu yadda bai yi ba a kan ya yi haƙuri ya kyale masa yaron nasa, amma ya ƙi. Hakan ya sa ya yi tunanin tura ’yan sandan a wannan dare domin su ɓatar da shi, sai dai kuma da suka ga fuskar Madugu, duk suka ja da baya. Ganin tunanin ba zai fisshe shi ba ya sa ya ce:

“Madugu, ka yi haƙuri. Wataƙila an samu rashin fahimta ne, amma ni ban tura ’yan sanda zuwa gare ka ba—”

Katse shi ya yi ta hanyar ɗaga masa hannu, yana kallon Jagwa.

“Ya ba ku 200k, kuɗin jinyar yarinyar, sannan ya haɗa muku da Maltina katan uku, madara ma katan uku.”

Yana gama faɗin hakan, ya yunƙura zai tashi. Da sauri shi ma kansilan ya miƙe ya ce:

“Madugu, ka san ba zan guje wa abin da ka ce ba. Amma don Allah, ka sake shi a wannan karon. Ba zai sake maimaitawa ba, na yi alƙawari.”

Madugu,ya kalle shi na ɗan lokaci, yana sake kallon falon da kyau.

“Samun sauƙin yarinyar shi ne dawowar ɗanka.”

Take fuskar Alhaji Haladu ta nuna rashin jin daɗi, amma sai bai ce komai ba, ya jinjina kai domin ya san kome zai ce, ba zai saki yaron ba. Wani tunani Alhaji Haladu ya yi, hakan ya sa ya ƙara gyara tsayuwarsa. Ya sake ƙoƙarin magana cikin nutsuwa.

“Madugu, zan yi magana da shi. Na rantse maka ba zai sake ba.”

Sayyid ya ɗan yi murmushi.

“Idan ma ya sake, na rantse da Assamadu, sai dai ka haifi wani. Idan iskanci zai yi, ya je gidan karuwai.”

“Wannan shi ne gargadina na ƙarshe. Idan ɗanka ya sake kusantar wata yarinya da niyyar cutar da ita, ba zan sake zuwa gidanka domin in yi maka bayani ba, sai dai ka zo ka ɗauki gawarsa, ko kuma in ba Rocky ya cinye ta.”

Ya juya ya ci gaba da tafiya, sai dai ya kai bakin ƙofa kafin ya ɗan tsaya cak. Bai waiga ba, ya ce:

“Ku kwaso kayan!”

Ya sa kai ya fita daga falon. Hanyar store ɗin gidan ya nuna musu da hannu, suka tafi yin abin da aka saka su. A maimakon uku-uku da ya ce, su Jagwa sai suka ɗauko biyar-biyar, wai su ma su ƙara yawa.

Alhaji Haladu yana tsaye yana kallonsu har suka fita da kayan, zuciyarsa kamar za ta yi bindiga tsabar baƙin ciki. Dole ma sai ya yi maganin Madugu, muddin wani abu ya samu ɗansa.