ZAWARA.

CHAPTER 19.

by @1239900

ZAWARA.











NA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✨✍️ 











PAGE 19.








Fuskar Nasibah ɗauke da mamaki da fara'a ta nufi wajen Yasmin dake tahowa da gudu suka haɗu a hanya suka rungume junansu. Sai da suka gama murnar ganin juna sannan su Nawwarah da Nadiya suka miƙa wa Yasmin hannu suka gaisa suna murmushi. Nawwarah da bata gani tai shiru sai ta ce.

"Lallai Yasmin Abuja ta karɓe ki,kin ga yanda ki ka ƙara cika da kyau kuwa? Shi kansa Yayanku na ga ya ƙara haske da kyau,amma fa kamar ya rame ko Nadiyah?"

Kafaɗu Nadiyah ta ɗaga mata kawai alamar itama bata sani ba.

Fari Yasmin ta yi ta ce.

"Thanks. Ko Yah Yusrah ma haka ta ce wai na fita girma yanzu."

Da jin sunan Yusrah a bakin Yasmin sai gaban Nasibah ya yanke ya faɗi. Nan take walwalarta ta ɗauke,cikin sanyin jiki ta ce wa Yasmin.

"Mu bari mu ƙarasa gida,ki je kada Yaya Mai Kyau ya gaji da jiranki."

Murmushi Yasmin ta yi ta juya ta kalli Giɗaɗo da ke ta satar kallonsu lokaci zuwa lokaci. Cike da fara'a a fuskarta ta ce.

"Ai ke muka zo ɗauka Nasibah,yanzu haka da kika gammu mun je can gida ne Baba ya ce min baku taso ba,shine na roƙe shi na ce ya kawo ni har nan mu ɗauke ki mu tafi da ke gida. Kin san yau Goggoji ke cika shekara 70 a duniya,so mun yi planning mata surprised party,yanzu haka Malam Sadi ya tafi Airport ɗakko ta."

Haɓa su Nawwarah suka kama suna kallon yanda Yasmin ke magana cike da yanga da iyayi. Nasibah kuwa sai ta ce.

"Ina ta je na ji kin ce an tafi ɗakko ta daga Airport?"

"Umarah ta je."

"Ayyah."

Shine kawai abinda Nasibah ta ce. Nawwarah na shirin yin magana Giɗaɗo ya ce.

"Ku zo nan."

Da sauri Yasmin ta nufi wajensa ta tsaya a gefensa,Nawwarah da ta mace wajen kallonsa ke mara mata baya,ta na isa gabansa ta durƙusa har ƙasa ta gaishe shi,kamar ba zai amsa ba ya daure ya amsa da ƙyar. Kallon Nadiyah da ke gaishe shi ya yi ya ɗaga mata yatsa. Nasibah kuwa sai ta raɓe a gefe ta ce.

"Yah Mai Kyau ina wuni?"

Duk yanda Giɗaɗo ya so ya yi musu faɗa akan ƙin gaishe shi da basu yi ba sai ya ji ya kasa,murmushi ya sakar mata ya ce.

"Ai na zaci ba za ku gaishe ni ba. Ke kuma ɗan rakiyar taki ya gaji mu tafi ko?"

Ya ƙarasa maganarsa yana kallon Nasibah. Ita kuma sai ta juya ta kalli su Nawwarah. Ganin damuwa a saman fuskar Nasibah ne ya sanya Giɗaɗo cewa.

"Ku shiga mu rage muku hanya mana."

Jiki na rawa Nawwara ta nufi bayan mota saitin direba ta zauna. Idanuwanta banda kallon Giɗaɗo babu abinda suke yi, zuciyarta kuwa ta jima da hango ta a gidan Giɗaɗo matsayin matar aurensa. Gaba Yasmin ta shiga suka saka Nasibah a tsakiya. Babu ɓata lokaci ya ja motar suka bar makarantar. Lokaci zuwa lokaci Giɗaɗo ke ɗaga kai ya kalli Nasibah da take zaune a matuƙar takure saboda jin nauyi da kunyar irin kallon da yake jifan ta da shi.

Su na zuwa bakin layin su Nawwarah Nadiyah ta ce.

"Mun gode Allah Ya saka da alkhairi Yayah."

Burki Giɗaɗo ya ci ya tsayar da motar suka sauka Nawwarah na kashe murya da fari ta ce.

"To Nansy sai mun haɗu gobe a school ko?"

"Allah Ya kaimu."

Nansy ta ce tana ɗaga musu hannu. Mota Giɗaɗo ya ja suka nufi gidan Gwani Ibrahim Yunus. Su na isa suka tarar da gidan da mutane jefi-jefi suna shiga da motocinsu cikin gidan,wasu kuma sun yi parking a wajen gidan suna takawa da ƙafa suna shiga ciki. Mai gadi na ganin motar Giɗaɗo na dosowa gidan sai ya sake wangale gate ɗin ya tsaya yana miƙa masa gaisuwa. Cike da mutuntawa suka gaisa ya ja motar suka shige ciki. Ita dai Nansy zaune take tana kallon manyan mata masu ji da kyau da kuɗi su da ƴaƴansu mata da maza na ta shiga gidan,wasu na yaren hausa wasu na fulatanci. Mota na gama tsayawa Yasmin ta fita ta buɗe wa Nasibah ɓangaren da take zaune sannan ta kama hannunta,a tare suka yi wa Giɗaɗo godiya suka shige sashen Goggoji. Ko da suka shiga sai suka ga ƴan'uwansu na Gombe da mazauna Kano a parlour suna ta fulatanci suna dariya. Har ƙasa Yasmin da Nasibah suka durƙusa suka gaishe su sannan suka shiga ɗakin Yasmin dake a sashen Goggoji. Rufe ƙofa Yasmin ta yi ta ce.

"To yi sauri ki shiga banɗaki ki yi wanka,bari na shiga ciki na kawo miki abinci. Yauwa kar na manta idan kin yi wanka kawai ki ɗaura towel zan ɗakko kayan da za mu saka a can sashen Hajiya."

"Kin san Allah ba dan na gan ki da Yah Mai Kyau ba da sai in ce ƙarya ki ka zuba min kika kawo ni gidan nan. Haka kawai nake jin gabana na faɗuwa Yasmin."

Dariya sosai Yasmin ta yi sannan ta ce.

"Amma dai ba faɗuwar gaba saboda tsoron za a dake ki a gida kike ji ba ko? Dan ke na riga da na san kin ci dubu sai ceto."

Dariya itama Nasibah ta yi ta fara cire kayanta tana ninkewa tare da sakawa a jakarta ta ce.

"Ke yanzu baki san har gobe idan na shuka wani rashin hankalin su Baba zage wa suke su yi min matsiyacin dukan ganga ba ko?"

Hannun ƙofa Yasmin ta kama ta ce.

"Gaskiya ban yarda ba,dan kuwa ni na san yanda Baba ke ji da ke ko wani ya gani zai dake ki ba zai bari ba."

Ta na gama magana ta rufe ƙofar ta yi gaba,a daidai wannan lokacin Nasibah ta shiga toilet bakinta ɗauke da addu'ar shiga banɗaki tana tuna yanda Baba ke jibgarta yana nuna mata ba sani ba sabo idan ta tsallake layin da ya shata mata. Tsayawa ta yi tana kallon ƙarafan dake cikin banɗaki,da taɓa nan murɗa can ta haɗa ruwan wanka ta yi sannan ta yi alwalar sallar azahar ta ɗaura towel ta fito. Zama ta yi a bakin gado tana nazarin rayuwar masu kuɗi,wasu masu kuɗin suna da matsanancin girman kai da nuna wa talaka ƙiyayya a fili,wasu kuma suna da sassauƙan hali da son mutane tare da yawan kyauta. Yasmin na daga cikin yaran masu kuɗin da ke son mutane tare da kyautata musu,domin kuwa ba ita kaɗai take yi wa kyauta ba,duk wanda Allah Ya tsaga da rabonsa Yasmin na yi masa kyautar duk abinda ta kula mutum na da buƙata.

Sallamar Yasmin ce ta dawo da ita cikin hayyacinta ta kalle ta riƙe da wasu riguna ƴan kanti masu masifar kyau,dogaye ne har ƙasa da ƙananan hijabs sai sababbin bra da pant da under skirt. A bayanta kuma mai aikinsu Baba Laraba ce biye da Yasmin ta dire musu abinci Nasibah ta gaishe ta ta tafi. Cike da damuwa Yasmin ta ce.

"Sakko ki ci abinci bari na duba miki ɗankunne a cikin tsofaffin nawa,har da ɗankunne fa na ba wa su Yah Yusrah saƙo amma ta siyo kaya babu ɗankunne."

"Ayyaa babu komai,ai ko haka zan iya saka wa tinda hijabin irin mai rufe kunnen nan ne."

"Humm ke dai rabu da Yah Yusrah,ni na rasa meye a tsakaninku da bata son a yi zancen ki,yanzu ma fa kafin mu je gidanku sai da ta yi ta ƙananun maganganu,Yah Giɗaɗo ne ya yi mata kyakkyawan gargaɗi akan wata magana da take ta ɓoyo."

Wani irin yawu Nasibah ta haɗiye muƙut ta hau zare ido,ji take yi kamar ta sanar da Yasmin gaskiyar abinda ya haɗa su da Yusrah,amma nauyi da kunyarta ya hana ta magana. A yau ta sake tabbatar da sata halin banza ne,hali ne na marasa kunya da tsaurin ido,hali ne na marasa tsoron Allah suke cin haƙƙin bayinSa. Alƙawari ta yi wa kanta duk rintsi duk wahala har abada ba za ta sake taɓa abun wani ba.

Jiki a mace ta yi sallah sannan suka zauna suka ci abinci. Suna gamawa suka shirya Yasmin ta yi wa Nasibah simple make up suka feshe jikinsu da turaruka masu daɗin ƙamshi suka fita babban parlourn Goggoji. A tsakiyar parlourn Nasibah ta ga an girke wani ƙaton cake mai ɗauke da hoton fuskar Goggoji da shekarun da ta cika a duniya,gefe guda kuma ga abinci nan kala-kala da drinks da plates ɗin da mutane za su yi serving kansu. Ƴan mata ne da ba za su wuce sa'annin su Yasmin ba ke tsaye a kusa da cake ɗin suna ta yi masa hotuna da videos. Babu jimawa wajen ya ɗauki murna tare da yaren fulatanci kowa na yaba kwalliyar Goggoji da ta ci wani tsadadden leshi ta zuba gwala-gwalai kamar ba tsohuwa ba. Haƙoranta masu ɗauke da haƙorin makka fari da golden ne suka bayyana. Kafin ta ƙaraso tsakiyar parlour ta isa wajen zaman da aka tanada dominta Giɗaɗo da Yusrah tare da Hajiya Yalwa sun shigo wajen. Hankalin Giɗaɗo gaba ɗaya yana kan wayarsa da yake amsawa har suka isa gaban kujerar da Goggoji ta zauna babu jimawa. A gefenta Giɗaɗo ya zauna yana ci gaba da amsa wayarsa. Nan da nan ƴan'uwa da masu hoto da aka gayyato a wajen suka fara ɗaukan su hotuna. Giɗaɗo na gama wayar ya ajiye a saman table ya matsa kusa da Goggoji ya ɗora hannunsa ɗaya a kafaɗarta aka ci gaba da ɗaukan su a hotuna. Haka taron ya ci gaba da tafiya cike da walwala da nishaɗi. Nasibah na gefe ta kasa sakin jikinta duk kuwa da irin yanda Yasmin ke ta janta cikin danginsu. A hankali Giɗaɗo ya tashi daga kujerar da yake ya nufi inda Nasibah ke tsaye. Ba tare da ta kula ba ya sa wayarsa ya ɗauke ta a hoto ya bi ta gabanta ya bar parlourn. Ya na fita Yusrah ta je wajenta ta tsaya tana binta da wani irin maƙasƙancin kallo ta ce.

"Wai ke me yasa ba za ki kama kanki ki zauna a inda Allah Ya ajiye ki ba;baki da aiki sai bibiyar yaran masu kuɗi? To ina so wannan ranar ta zamo ta ƙarshe da za ki sake shiga sabgar ahalinmu. Itama Yasmin ɗin zan same ta sai na ci ubanta akan jawo mana gayyar ɓarayi har cikin gida suna gane mana sirrinmu."

Tuni fuskar Nasibah ta jiƙe sharkaf da hawaye. Zuciyarta banda ƙuna babu abinda take yi mata. Gudun kada Yasmin ta gane halin da take ciki sai ta zame ta koma ɗakin Yasmin ɗin ta shige banɗaki ta yi zamanta tana risgar kukan takaici. A wannan rana Nasibah ta tsine wa ɓarari da shi kan shi sunan satar ya fi shurin masaƙi. Haka party ya ci gaba da gudana babu wanda ya san inda Nasibah ta tafi ta ɓoye.

A can gidan Malam Sanda kuwa da misalin huɗu daidai Samir ya dawo daga Abuja,ko gida bai je ba ya nufi gidan Malam Sanda domin ganin abincin ruhinsa da ya kasa zama a waje ɗaya saboda tunaninta da ya yi masa yawa. Ya na zuwa ya tarar da Malam Sanda babu lafiya,sai ya rubuta masa magunguna ya ba wa Usman kuɗi ya je ya siyo masa har da yar gasasshir kazarsa da Nutrimilk. Ko da ya tambayi inda Nasibah take sai Malam Sanda ya ce.

"Ai wannan yarinyar ƴar gidan marigayi Gwani Ibrahim Yunus ta zo ita da Yayanta neman Nasibar, sai aka yi rashin sa'a bata dawo daga makaranta ba,shine fa yarinyar nan da yake tana ƙaunar Nasibah sosai ta ce za su je makarantar su ɗauke ta,yau Kakarsu ke cika shekaru 70 a duniya za su yi mata walima."

Cike da matsananciyar damuwa Samir ya miƙe ya ce.

"Haba Baba! Ya za ka ba wa wani ƙato dama ya je har makaranta ya ɗaukar min mata?"

Kafin Malam Sanda ya ce wani abu Samir ya miƙe ransa a matuƙar ɓace ya bar gidan. Kai tsaye gidan su Giɗaɗo ya nufa zuciyarsa na hasaso masa irin kyau da kamalar Giɗaɗo. Ya san cewa Giɗaɗo na da aure, amma ba zai taɓa manta irin kallon da ya yi wa Nasibah ba a lokacin da suka je bikinsa shi da Nuh.

Tafiyar mintuna 8 ne kacal suka kai Samir gidan. Ganin gate ɗin gidan a buɗe kuma gidan ya cika da motoci ne ya sanya shi yin parking a waje ya fito daga motar yana tunanin yanda zai yi ya ga Nasibah.


A daidai wannan lokacin kuma Giɗaɗo na kwance a saman makeken gadonsa ya saka hannunsa ɗaya a ƙasan kansa ya tallabo kan nasa yana kallon hoton Nansy da ya yi wa kyakkyawan ɓoyo a cikin wayarsa. Ajiyar zuciya ya sauke ya ce.

"NaNSy Ƙaya."

Murmushi ya saki mai sauti sannan ya sake cewa.

"Ina son rigimarki da shagwaɓarki."

Kamar wanda aka janyo haka ya miƙe zaune ya kalli bakin ƙofar shiga ɗakinsa. Rigarsa ya saka ya ɗauki wayarsa ya fito harabar gidan. A jikin gate ɗin gidan ya hango Yasmin na ta lallashin Nansy akan ta zauna za su mayar da ita gida ko da da daddare ne. Ƙi Nasibah ta yi ta na ta share fuskarta,da dikkan alamu kuka take yi. Nan da nan Giɗaɗo ya ji zuciyarsa ta ƙuntata ya nufi wajensu da sassarfa. Ya na zuwa Samir da ke takowa zuwa wajen su Yasmin ya isa wajen fuskarsa a murtuke. Tsayawa suka yi dika su huɗun suna yi wa junansu kallon kallo. Da ƙyar Samir ya danne abinda yake taso masa daga ƙasan zuciyarsa ya ce.

"Ke wuce mu tafi gida tinda an gama walimar."

Gira Giɗaɗo ya haɗe waje ɗaya sannan ya ce.

"Kai kuma ɗin wanene a wajenta da za ka zo ka ce ta bika ku tafi?"

Murmushi mai sauti Samir ya saki saboda ya kula da alama bai gane shi ba. Jinjina kai ya yi ya ce masa.

"Ni ɗin mijin da zan aure ta ne. Ke! Wuce mu tafi."

Nasibah da ta ci kukan gargaɗin da Yusrah ta yi mata sai ta zagaye Yasmin da ke riƙe da hannunta ta wuce zuwa motar Samir. Har Samir ya ja motar suka bar wajen Giɗaɗo bai sake yin ƙwaƙƙwaran motsi ba. Ya jima a haka kafin ya fizgo kalmar.

"Mijindazaiaureta?"
(Mijin da zai aureta?)

Kai Yasmin ta jijjiga masa ta ce.

"Allah Yah Giɗaɗo ƙarya yake yi,ko da bikinku ma haka ya zo ya ja ta ya mayar da ita gida ba dan tana so ba."

"To amma Yasmin ke da kika saka mu zuwa har gidan iyayenta muka ɗakko ta me ya sa kika saka ta kuka?"

Jiki a mace Yasmin ta ce.

"Yah ba ni na saka ta kuka ba,na hango su ita da Yah Yusrah suna magana,kafin in ƙarasa wajensu na nemi ita Nasibar na rasa,to na ma yi zaton ko gida ta tafi sai na fita waje na hau neman ta amma ban ganta ba,daga baya ina shiga ɗakina na ganta a bathroom tana kuka. Shine fa ta ce min wai na yi haƙuri da ƙawancen mu daga yau ba za ta sake zuwa inda nake ba."

Kai Giɗaɗo ya kama yana jin tsananin takaici da tsanar Yusrah na nunkuwa a cikin ransa. A fusace ya koma sashensa ya zauna a parlour. Cikin wani irin mawuyacin hali ya furta.

"Nasibah ke kaɗai ce macen da ke saka ni a cikin wani irin yanayi na farinciki wanda na rasa tun bayan rasuwar Ummina. Dan haka ba zan taɓa bari ki suɓuce min ba face na mallake ki."

Cikin zafin nama ya ɗauki makullin motarsa ya rufe sashensa ya fito waje. Malam Sadi ya kirawo domin ya tuƙa shi saboda nauyin da ya ji jikinsa ya yi masa,dan kuwa sosai kalaman Samir suka jefa shi a cikin tsaka mai wuya. Malam Sadi na karɓar makullin mota Giɗaɗo ya shiga gaba suka ja motar sai gidansu Nasibah wato Nansy ƙaya........