MATAR GIDA PAGE 79
*MATAR GIDA BOOK* 2
*SHUUKRAN*/022
*YOTA ASSOCAITION*
P79
Wani irin yanayi mai wuyar fassaruwa Unaisa ta tsinci kanta ciki taji ruhinta na neman rabuwa da gangar jikinta wani irin duhu ya gifta ta idanunta gaba ki ɗaya duniyar ta yi mata duhu na wasu sakanni, ji da ganinta sun dauke na wasu ƴan mintina cike da son gaskata abinda kunnawanta suka jiyu mata cike da tsantsan firgici ta kalle Ɗalha tana zaro idanuwa jikinta na kyarma ta ce ''me ka ce?" ta kare magana da sigar tambaya da fita hayyaci babu nitsuwa tare da ita ko kaɗan idanunta sun yi ja sosai,Ɗalha har sannan idanunsa kanta ko kaɗan bai ji wani abu me kama da tausayi ko nadamar sakin ta da ya yi ba a zuciyarsa,hasalima har sannan cike yake da ɓaci rai,wata iriyar murmushin da ta tafi kuka ciwo Ɗalha ya yi kafin ya buɗe baki da kyar ya ce ''ki fitar min daga gida bani son ganin ki na ba ki mintina biyu rass ki tattara ki bar min gida ke da mutanen ki'' daga haka ya juya da niyya barin wajen Unaisa ta yi saurin shigowa gabansa ta ce ''dan Allah ka rufa min asiri ka yi min rai ban fahimce ka ba me ka ke nufi? me saki? wani irin saki?" gaba ɗaya Unaisa bata cikin hankalin ta babu nitsuwa tare da ita ko kaɗan bata ma san abinda take faɗi ba,abu ɗaya take son ji daga bakin Ɗalha da sauran mata dake parlour,so take ta ji da kunnuwanta Ɗalha ya ce ya fasa sakin,ba iya fasawa ba ya ce bai yi sakin ba gaba ɗaya,tana tsaye gabansa ta kuresa da idanunta da suka yi ja sosai tsabar tashin hankali,kallon ta Ɗalha ya yi har ya buɗe baki zai yi magana sai kuma ya fasa ya bi gefen ta ya wuce so yake ya fita daga parlourn kar sheɗan ya yi nasarar sa shi ya aikata abinda zuciyarsa ke raya masa,zuciyarsa na raya masa ya kai wa Unaisa duka wani irin bugu zuciyarsa ke tunzurasa yama Unaisa sai dai ba zai iya hakan ba ko ba dan cikin dake jikinta ba,shi ba mai dukan mata bane ba zai iya dukanta ba,Unaisa da ta gama fita hayyacin ta ganin Ɗalha ya bi gefenta ya sa cikin sassarfa tana jin yadda cikinta ke murɗa mata ga wani abu mai kama da ruwa na bin kafarta ko kaɗan ba wannan bane gabanta cikin sauri ta kuma shiga gaban Ɗalha wasu irin hawaye na sauka fuskarta a hankali ta ɗaga hannu da niyar riƙe hannunsa amma sai ya yi saurin matsar da hannunsa bai bata damar riƙe hannunsa ba Unaisa ta koma kamar wata mahaukaciya ta kalle Ɗalha idanunta cike da tashin hankali da kiɗima ta ce ''ka ce wasa ka ke ka fasa ba sakina ka yi ba,ba sakin aure ka ke nufi ba'' ta kare magana tare da riƙe hannunsa ɗaya da duka hannayenta,cike da ɓacin rai da kunan zuciya Ɗalha ya kalle Unaisa da kyau zuciyarsa na masa zafi sosai ya ce ''sakin ki na yi Unaisa..abinda ki ke so shi na ba ki sakin ki ke so shi yasa na saki ki'' shiru ya yi ya sake wata murmushi mai ciwo kafin ya mayar da dubansa ga su Hajiya Bilƙisu ya ce ''ina maki fatan zama da ƴan kungiya da ki ka zaɓa sama auren ki lafiya Allah ya haɗa kawunan ku'' da wani irin sauri Ɗalha ya warce hannunsa da Unaisa ta rike wanda hakan ya yi sanadiyar faduwar Unaisa ƙasa,fadowar ta zo mata da tsaustayi ta faɗi kan cikin dake jikinta wata iriyar azababbiyar ƙara ta sake tare da riƙe bayanta nan take jini ya ɓallo mata,Ɗalha da tun sanda ya warce hannunsa ya sa kai ya nufi hanyar fita daga parlour sarai ya jiyu muryar Unaisa tana kuka sai dai bai ko waigo ba,bai san faɗuwa ta yi kan ciki ba a tunanin sa kukan sakin da ya yi mata ta ke yi,bayan fitowarsa Dalha Fauziyya ta biyu bayan da sauri tana kuka tare da kiran sunansa amma bai juyo ba,Hajiya Zulfa'u da Zainab tare da sauran mata dake parlourn suka yu kan Unaisa da wani irin sauri,Hajiya Bilƙisu kuwa taɓe baki ta yi tare da dauke kai gefe,da taimakon sauran matan Hajiya Zulfa'u ta sa Unaisa mota tare da wasu mata biyu ƴan kungiya ta nufi asibiti da Unaisa sosai Unaisa ke zubar da jini wanda hakan ba ƙaramin tayarwa Hajiya Zulfa'u hankali ya yi ba,Zainab na biye da su motarta har suka isa wata asibiti mafi kusa da gidan Ɗalha bayan isowarsu asibiti likitoci sun shiga aikin ceto rayuwar Unaisa da abinda ke cikinta lokacin tuni an tayar da sallar magriba wasu masallatai,bayan Hajiya Zulfa'u ta kai Unaisa asibiti Hajiya Bilƙisu ta fita daga gidan Unaisa hankalinta kwance ta shiga motarta ta nufi hanyar gidanta tuƙi take hankali kwance kamar wacce aka yiwa albishir da aljannah,da yawa yawan matan kungiyar da abin ya faru gabansu jikinsu ya yi sanyi haɗe da tausayin Unaisa wanda wasu daga cikin su basu ji komai ba,ko darr basu ji ba,haka dai taro ya watse babu daɗi,Hajiya Zulfa'u tare da Zainab ne kaɗai asibiti sauran mata biyu da suka shiga motar Hajiya Zulfa'u sun tafi gida ganin gari ya rufa dan tuni an idar da sallar magriba an kusa kiran sallar isha'i hakan yasa suka yiwa Hajiya Zulfa'u da Zainab sallama cewar za su kira su a waya su ji yanayin jikin,karfe takwas da wasu mintina likita ya fito daga ɗakin gaggawa inda Unaisa take mayar da dubansa ya yi ga Hajiya Zulfa'u ya ce ''ya ya alaƙar ki da marar lafiyar?" ba tare da dogon nazari ba Hajiya Zulfa'u ta ce ''ƴata ce''likita ya jinjina kai kafin ya ce ''munyi nasarar tsayar da jinin sai dai ta rasa jini da yawa sannan sakamakon firgice da tashin hankali da ta shiga hakan ya haifar mata pre mature lebur wato naƙuda ba tare da lokacin sa ba,sannan jarirai dake cikinta rayuwarsu tana haɗari yanzu haka zamu yi mata tiyatar gaggawa dan ceto rayuwarta da kuma abinda ke cikinta, yanzu dai muna bukatar sa hannu mijinta kafin mu fara aiki,ku kira sa ya zo ya sa mana hannu,dan Allah kar ya dauki lokaci in ya ɓata lokaci za a iya rasa ita uwar ko abinda take dauke da su'' likita ya kare magana yana son barin wajen Hajiya Zulfa'u da Zainab har likita ya ƙare magana babu wacce ta iya cewa komai musamman Zainab da mamaki ya gama rufe ta tana mamaki daman cikin dake jikin Unaisa ya girma?irin wannan tunanin Hajiya Zulfa'u ke yi cikin zuciyarta,kallo ɗaya zaka yiwa Unaisa ka fahimci akwai ciki jikinta amma in ba faɗa ta yi ba,ba lallai mutum ya san cikin jikinta ya girma ba,da sauri Hajiya Zulfa'u ta kalle likita dake shirin barin wajen ta ce ''mijinta baya ƙasa ko zan iya sa hannu likita ka taimaka ka ceci rayuwarta'' ta kare magana tana kuka tabbasa kukan gaske Hajiya Zulfa'u ke yi ba kukan munafurci ko karya ba,tausayinta ya lulluɓe likita sauke numfashi ya yi kafin daga bisani ya ce ''babu damuwa ki biyuni ofis zan ba ki Form sai ki cika ki sa mana hannu'' yana gama faɗin haka ya bar wajen cike da mamaki Zainab ke kallon Hajiya Zulfa'u dake faman bin bayan likita da sauri za ta je cike Form,Zainab ta yi saurin riƙe hannu Hajiya Zulfa'u tare da janyu ta fuskarta cike da mamakin Hajiya Zulfa'u ta ce ''Hajiya kin kuwa san abinda ki ke? yarinya da iyayenta da mijinta ki ce za ki saka hannu a mata aiki,Allah ya kiyaye ba fata nake ba amma in wani abu marar kyau ya biyo baya za ki shiga matsalah'' Zainab ta kare magana cike da damuwa kallo ɗaya Hajiya Zulfa'u ta mata kawai ta ce ''zainab yanzu ba lokacin wannan maganar bane,ba ki ji abinda likita ya faɗa ba ya ce in ba a iya gaggawar mata aiki ba za a rasa ta da abinda ke cikinta dan Allah Zainab ki bari na sa hannu a ceto rayuwar yarinyar nan koma me ya biyo baya'' Hajiya Zulfa'u na kokarin barin wajen Zainab ta kuma jefo mata wata tambayar ta ce ''in aka yi aikin ba tare da yardar mijinta ba zai iya karar ki'' a takaice Hajiya Zulfa'u ta ce ''a shirye nake na yi shara'a da shi'' daga haka bata sake bi ta kan Zainab ba ta bi bayan likita zuwa ofis ɗinsa
Bayan fitar Ɗalha daga ɓangaren Unaisa kai tsaye ya wuce part ɗin Amirah,kallo ɗaya Amirah ta masa ta fahimci yana cikin ɓacin rai hakan yasa tun bayan sannu da dawowa da ta masa bata sake bi ta kansa ba,da wuri ta sa yara bacci yau,ko sallah Ɗalha bai fito ba magrib da isala'i duk a ɗakinsa ya yi,ganin bai fito cin abinci ba yasa Amirah ta bisa da abinci ɗakinsa,daman ita ke da girki sallama dauke bakinta ta shiga ɗakin,motsin ruwa da ji bathroom yasa ta fahimci yana bathroom waje ta samu ta zauna bayan ta ajiye tray ɗin abinci ta yi tagumi ko ba a faɗa mata ba ta san Unaisa ce ta ɓata masa rai ita kanta ta yi mamakin Unaisa sosai ta kuma jinjinawa rashin hankali irin nata,ta so zuwa part ɗin Unaisa ta dubata amma sai ta yi tunanin bari zuwa gobe ta shiga ta san dole ba a tashi taro da dadin rai ba,tana nan zaune har ya fito sanye da bathrope kallo ɗaya yama Amirah ya dauke kai kamar ita ta masa laifi ita dai bata tanka sa ba,tana nan zaune ya gama shirya kansa cikin brown jallabiya ganin ya gama shiryawa yasa Amirah yin magana cikin kwantar da murya ta ce ''barka da dare ya hanya?" shiru Ɗalha ya yi tare da zama yana buɗe flask ɗin abinci da ta shigo masa da shi bayan ya gama buɗe flask ɗin ya ɗago ya kalleta ya ga shi ta take kallo nan take ya damƙi fuska kafin a ɗaƙeli ya ce ''l want to be left alone tnxs for the food kina iya tafiya'' sosai abinda ya faɗa bai ma Amirah dadi ba amma sai ta danna zuciyarta bata ce masa komai ba a hankali ta yunƙura tare da miƙewa tsaye da niyyar barin ɗakin kamar yadda ya faɗa,ta zo daf da inda yake zata wuce ya yi saurin riƙe mata hannu tare da janyu ta jikinsa kadan ya rage su ɓarar da abincin da ta ajiye masa,kallon fuskarsa ta shiga yi ranta ɓaci amma tana kokarin ɓoye ɓacin ranta bata son ya fahimci ranta ya ɓaci,hannu ɗaya ya kai ya rufe flask ɗin abinci sai da ya tabbatar ya rufe komai,duk abinda yake idanunsa a kanta kafin ya ce ''ke ce silar komai..damuwowi da matsaltsalun da na riƙa fuskata tun kafin auren yarinyar nan har izuwa yau ke ce silah'' wani yawu mai ɗaci Amirah ta haɗeyi Ɗalha ya saba gaya mata baƙaƙen maganganun tun ba yau ba tana hakuri tana shanyewa amma a yanzu baza ta dauka ba,a tunanin sa wannan Amirah,Amirah da ya sani da ce bai san ta canza ba kokarin tashi daga jikinsa Amirah ta shiga yi sai dai ba bata damar hakan ba,cikin ɓacin rai ta yi magana cikin ɗan ɗaga murya ta ce ''cika ni fita zan yi'' Ɗalha bai kula ta ba sai cewa ya yi ''tun daga ranar da goyon Rayyan ya haɗe maki da cikin su Suhail da Ummu Abiha ƴan biyu ki ka fita hayyacin ki tun daga wannan ranar tunanin ki ya canza,ni mijinki ne Amirah amma abinda na lura dake tun waccan lokacin abubuwa biyu zuwa uku sune gaban ki na farko yadda za ki kula da yaran ki da gidan ki na biyu aikin ki,ba ki taɓa fashin zuwa aiki ba amma sau da yawa na kan dawo gida na tarar kin yi bacci wani sa'ilin a parlourn bacci ke daukan ki ba tare da kin sani ba,ranar da na yi sa'a ba ki yi bacci kafin na dawo ba to da mun shiga ɗaki za ki nuna min kin gaji ke kawai na biya bukatata na barki ki yi bacci ni kuma ina son mu yi dogon wasa kafin mu fara komai, ba ki taɓa hanani hakki na ba,amma ba ki da lokacina tabbas kina min girki kullum kuma duk sanda na buƙaceki kina bani hakkina amma ba a yadda nake so ba,ban damu shekaru nawa muke da aure ba l just want you to be lovely and sexy always'' tun sanda ya fara magana hawaye ya shiga sintiri fuskar Amirah maganganunsa sun yi mata ciwo sosai amma can ƙarƙashin zuciyarta ta sani gaskiya ya faɗa amma bai taɓa fito ya faɗa mata ba sai ya riƙa jifanta da kalmar ƙazama,cikin kuka da ƙonar zuciya ta ce ''me yasa ba ka taɓa faɗa min ba sai ka riƙa kirana da kazama bayan ka sani ni ba kazama bace?" wata iriyar murmushi ya yi da bai kai ciki ba ya ce ''ina faɗa hakan ne dan ki gyara so nake na zaburar da ke amma duk a banza'' shiru ya yi na wasu ƴan sakanni can ya ciza lips ɗinsa kafin ya ce ''karshe sai cewa ka yi na sama maki ƴar aiki,tabbas kina bukatar ƴar aiki sai dai ba ki san yadda ake magana da miji ba,kina neman abu daga gareni amma duk sanda za ki zo tambaya ta wannan abin sai ki zo min a hargiste wani sa'ilin da kin fita wanka kike zuwa sanye da bathrope da shawer cap,wani sa'ilin da kin gama wanke toilet jikin ki duk warin izel wani rana kina tsaka da girki za ki fito riƙe da wuƙa ko alaiyahu,tabbas kina da tsafta kuma kokari sosai wajen kula da yara da gida amma kin manta mijinki sannan ba ki iya magana da ni ba'' shiru ya yi na wasu ƴan sakanni yana jin yadda Amirah ke kuka a hankali ya kai hannu ya riƙe haɓarta ya zubawa fuskarta ido ''cikin wata iriyar murya ya ce ban taɓa daina sonki ba duk sanda na kalle ki ke ɗin nake gani fara siririyar yarinya marar magana yarinyar da na faɗa soyayya da ita a jami'a ke ɗin ce dai Amirah'' daga haka ya kai bakinsa daidai kunnenta ya yi magana kamar raɗa ya ce ''kina da matsala wajen kwanciya ya kamata ki koya salon kwanciya iri daban daban'' shiru ya yi yana sauke numfashi can ya buɗe baki da kyar ya ce ''duk sanda ki ke da wata bukata wajena ku mutum ki ke so na kashe zan kashe koma waye ki faɗa min zan kashe, duk sanda muka zo kwanciya ki faɗa min bukatar ki koma mai zan yi maki shi sai dai akwai salon da mata ke amfani da su,ba bari za ki yi sai na zo gadan gadan ki dakatar da ni ki ce kina son kaza ba,bazan taɓa sauraron ki ba,ba kuma zan yi abinda ki ke son ba,saboda haka ki ajiye kunya a gefe ki koya sarrafa miji'' cikin tsananin kuka Amirah ta ce ''amma tsawon zama na da kai kusan shekaru goma ba ka taɓa faɗa min ba,mai yasa sai yanzu ka ke faɗa min?"murmushi mai sauti Ɗalha ya yi kafin ya ce ''yes that is namiji for you namiji zai iya zaman aure da ke tsawon shekaru masu yawa ba zai taɓa faɗa maki wasu abubuwan da ki ke masa wanda baya so ba,wani ma har ya mutu ba zai faɗa'' daga haka ya yi shiru na wasu ƴan sakanni sai kuma ya daura da ''saboda ni namiji ne kuma bahaushe haka mu mazan hausawa muke sau da yawa da mu zaunar da matan mu mu faɗa masu kurakuren da suke mana mun zaɓi mu sake su wanda sau da yawa saki ɗaya muke masu,ko mu ƙaro aure gani muke hakan zai sa su fahimce kuskuren da suka aikatawa su gyara wanda da yawa basu fahimta karshe sai auren ya mutu baki ɗaya'' Amirah ta ɗago jajayen idanunta ta zuba masa cike da ɓacin rai ta ce ''kamar dai yadda ka yi min'' Ɗalha ya yi murmushi kawai bai ce komai ba daga haka ya shiga rarrashinta ya dauki a ƙallah mintina talatin yana aikin rarrashin Amirah da ban baki,da kyar ya samu ta sauko kafin ya ci abinci,ko kaɗan bai faɗa mata abinda ya faru tsakaninsa da Unaisa ba ita ma bata tambaya ba,bayan ya gama cin abinci Amirah na shirin fitar da flask da ya yi amfani da su ya riƙeta gam flask ɗin da bata fitar ba kenan,a wannan daren Ɗalha bai sarara mata abubuwan da bai taɓa yi mata su ba tsawon rayuwar aurensu wannan daren ya fito fili ya nuna mata,babu ko kunya zai ce mata yi haka ɗaga nan sauke can juyu nan juyu can,da fari Amirah ta nuna ita fa kunya take ji amma bayan ta tuna maganganun da ya faɗa mata ɗazu ta ajiye kunya gefe guda ta shiga bin umurninsa wannan dare ya kasance ɗaren da Amirah da Ɗalha baza su taɓa manta sa ba
*SHUUKRAN*