GARWASHI

Chapter 10

by @gidaniko422

*_Kowane bawa yana da kalar kaddarar sa, sai dai kaddarar mutum tamkar inuwar sa ce, kana tafe tana biye a bayan ka, da ace muna ganin kaddarar mu da da yawan mu mun kauce mata, sai dai kash al'amarin ba'a hannun mu yake ba yana hannun Ubangiji_*



*Akwai complete din littafin nan a documents akan 1k kacal, mai bukata yayi min magana akan wannan layin, ****


............."Wato ba zaki rabu da mutanen can ba ko? Ba zaki rabu da masu sallah ba duk kashedin da nake miki ko? Bance miki kar ki kuma zama kusa dasu ba? Amaka ta fada tana  kama min kunne tankar zata fige min shi daga Inda yake tana zare min idanu,   na turo baki gaba cikin jin haushin amaka da take shirin fige min kunne, Ashe bansani ba na kara bawa Amaka haushi, sai kawai naji ta zauna akaina da manyan kuturanta Wai naji nauyin ta akaina 

Ta kuwa zaune ni  tana fadin "Ai tunda dai na raba ki da mutanen can masu salla bayan na fada miki mayaaudara ne  masu tallatawa mutane Addinin su ko bai nema ba, matukar baki rabu da mu'amala dasu ba to zan saka kakkaifar wuka in yanke kine in bawa karnuka naman ki matukar na karajin kin kuma yin  magana da masu bare har su soma hure miki kunnuwa suna fada miki ciwon ki bana hospital bane to na ina ne don kaniyar Ku ke dasu?

Sai da ta gaji don kanta kafin ta daga ni tana masifa, Amma ko kadan banji Ina son in Rabu da kawaye na sa take son na rabu da su ba,sai dai duk yadda Amaka zatayi dani akan su sai dai tayi,

Haka na ci gaba da Rayuwa cikin ukubar matsalar jinnu wanda ni kadai na san halin da nake kasancewa idan ciwon ya tashi, sai dai duk Ranar da ciwon ya motsa sai dai mu tare a Asibiti  kashe kudi mu dawo gida da tarin kwayoyin magani wanda bana samun sauki ko na sisin kwabo

A lokacin da na gama karatu ne nayi candy Maazi Nkem ya siya min mota me tsada ta garari na soma SHIGA gari ina murza sitiyari, a kuma wannan lokacin ne na soma kalular zuwa coci, dama can tun ina karama bana son zuwa coci, kuma ni da kaina ba zance ga dalili ba, Amaka kuma tace da wa aka hada ta ba ni ba? Duka dai akan zuwa coci Nasha shi amma na kafe akan kin zuwa coci, Amaka kuma ta soma kai koken ta ga malaman coci tana kuma Mika kokon barar ta ga malaman cocin Akan ciwona inda ake ta min ADDU'A yayin da Maazi Nkem kuma  Yake  ta bayar da kyautar kudi da kaya ana kawowa coci, yayin da ni kuma naji kwata kwata bana son zuwa cocin a duk Ranar lahadi Amaka kan tasa Ni gaba muje ba don baso ba, wani lokacin ma a mota zamuje amma sai na san yadda nayi ta sulale na bar cocin, a duk ranar lahadi kuwa Amaka sai ta jinga min shegen duka musamman ma idan na gudu nayi  kalula ko karyar ciwona, tun Amaka Bata farga da abinda nake nifi  ba har dai ta gane son zuwa ne banayi ta Kuma ce ban Isa ba wallahi, bisa Dole take tasani gaba muje Amma da mun Isa sai na fakaici idon ta na sulale na bar cocin na koma gida ko inyi wani wurin,


A cikin wannan lokacin ne Kuma na samu admissions zuwa  jami'ar garin Legos a matakin farko, cikin wata irin sa'a kuma  muka sake hadewa da kawaye na makaranta wato su sumayya Ahmed yabo da fauziyya Yar Amana muka sake kullewa fiye da Baya, 
Zuwa wannan lokacin kuma  na farajin Ina Sha'awar irin kayan da suke sakawa musamman hijabi da dogayen Riguna dama abinda suke rufe fuska, amma na San ko giyar wake Nasha ban Isa na Kai irin kayan nangida ba bare nace zan saka su, bare kuma  Amaka ta gani bare na kaisu jikina.


Na dubi Sumayya bayan mun fito daga lacca nake duban ta cikin Sha awar shigar ta ta atamfa da katon hijabi harma da Nikabi
"Wai sumayya kin taba fada min ciwona bana Asibiti bane na Alkur anin kune ko? Ta soma yaye nikabin fuskar ta tace ''Eh  haka ne Justina, kin San shi iska duk tsiyar sa yana tsoron alku'ani, idan har Allah ya taimake ki rukiyya sau daya tak sai ta rabaki da wannan wahalar ta shekara da shekaru, da yardar Allah,karatu kawai za'ayi ki Rabu da ciwon ki don aljanu ne fa suke shigar mutum. Kuma sunfi shigar Mata mafi yawan lokuta Matan dake yawan zama babu Dan kwali ko Babu suturar kirki irin wannan na jikin ki, Suma fa wai Sha'awar matan suke. ku Kuma ba zaku iya saka irin kayan mu ba. Na sauke ajiyar zuciya don naji na gamsu da bayanin ta kwarai matuka,
Nace 
"To ni yanzu yaya zanyi da Alkur'anin naku in warke ne? Zan rungume shi ne ko kuwa  sakawa ake a Ruwa a sha? koko yawo zan Rika yi dashi? Sumayya tayi Dariya tana fadin 
"A a karanta miki shi za'ayi sai kiga shi iskan da yake jikin ki yayi magana sai a raba ku, cikin ikon allah sai kiga kin samu sauki, Amma fa sai Allah ya yarda kinsan komai Allah ne ke yin sa,

Nayi shiru don nasan Amaka ba zata yarda da hakan ba Dole nayi shiru Amma a Raina Ina tunanin Yaya za ayi ayi min karatun? Kuma ta yaya zan samo hanyar da za'ayi min karatun har a gama Amaka bata sani na?

Haka na kasance cikin tarareabi, Ina ta fama da ciwo in ya tashi Nasha maganin bature in Kuma lahadi tayi na sulale Amaka tayi ta Sababi tana fadin ba zanje ayi min ADDU A ba ko? to Allah yasa asake wata lahadin bakije ba kiga abinda zai faru

Ban damu ba ni fatana kawai na samu Wanda zaiyi min karatun nan don kullum abin sai karuwa zuwa gaba yake, akasin da da nake kwanciya ciwo yanzu bugeni ake na Fadi tamkar matacciya, kuma idan na fadi bana sanin wanda yake kaina, magani kuwa babu Wanda ba a nemo min ba Amma babu wani ci gaba,

Mun Isa jihar imo wato mahaifar ma'azi Nkem da Amaka inda ake bikin Yar sarkin garin namu na imo wato Igwai Oyedugun, wannan Sarki hamshaki ne wanda masarautar sa take da karfi kuma yake da karfi a jihar sa ta Imo dama mutanen sa, ma'azi Nkem da Amaka mutane ne masu tsananin biyayya da girmama wannan sarki nasu,  Kuma Wanda Maazi Nkem Yake matukar girmamawa  tamkar ya duka ya bi ta kanshi ya wuce . Wannan girmamawa da Maazi Nkem yakewa  sarki igwai yasa suke matukar mutunci shima igwai yake son ma'azi Nkem har yake shirin bashi wata sarauta,Amaka ta samu matsayi sosai a wirin matan igwai guda biyu Wanda basa zaman lafiya a tsakanin su kasancewar karamar matar sarkin ce ta haifi magajin sarauta. Ita kuma uwar gida mata gare ta, Nima na samu SHIGA a gidan igwai harma na zamo kawar yarsa onye wacce itace ake shagalin auren nata har muka iso imo, don takanas igwai ya aikowa ma'azi Nkem tikitin jirgi muka taho bikin Onye,  Maazi Nkem kuma ya lodo dukiya wai ya kawowa sarki, amaka ma ta lodo tata muka iso,

Kai tsaye fadar sarki igwai  muka Fara Isa mukayi gaisuwa ma'azi Nkem da Amaka suka ajiyewa igwai dukiyar da suka kawo mishi gudunmuwa, yayi musu godiya sosai ya dafa kaina Yana yabawa kyauwuna Yana Kuma yi min ADDU A cikin yabawa da nuna kauna,

Aka Soma gudanar da shagalin biki irin na gidan sarauta Amaka kuma tana can cikin gidan igwai wurin matar sarki suna ta gudanar da nasu shagalin Nima Ina cikin su onye amarya wadda na ji wai Dan sarkin abar ne zata Aura,
Duk wasu Kaya na shagalin bikin irin na gidan sarauta an tanade su an Kuma Rabawa mahalar ta bikin Wanda Nima na samu kasona na wata Riga doguwa Mai hannun shime ta wani material mai tsananin kyau da tsada kalar gold wadda aka Dan Rufe kirjin ta da wani less me shara shara Kuma aka tsuke kasan ta ta yadda ta bayyana kuturin Wanda ya sakata 

Wurin da za ayi taron katon filine Wanda ya ke a cikin gidan sarautar, Kuma aka hada wasu manyan manyan itace aka hada wuta tana ci ganga ganga, abinda zai naka mamaki shine me ya kawo wannan guman guman wuta kuma? Shi dai wannan taron biki sunan shi agare, amarya ce da dangin ta zasu taru, haka ma ango da dangin sa zasu iso, za'a gayyato amarya da ango su iso gaban wutar a bawa amarya namijin tantabara shi Kuma Angon abashi macen tantabara su zo gaban   wutar Nan da take ci, kakar amarya ta wurin uwa zata zo ta saka Dan kamfan amarya a cikin wutar tare da wasu tufafin ta,  idan Amarya ta taba sanin wani namijn kafin Angon nata to tantabarin hannunta zai mutu nan take, idan kuwa Bata taba sani kowa ba to na tantabarar hannun Angon nata zai mutu............

_Kar ku Bari ayi Babu ku don wannan Labari daban yake da sauran_


Sunana Hadiza Bara'u Gidan iko ke cewa saduwar ALHERI💃🏿


Masu tambayar farkon labarin su duba cikin channel din mu na gidan iko don samun farkon labarin