FreeArewaPen original
GARWASHI
- 1views
- 2chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · Chapter 2
_Wasu yan uwan su kan zama abin alfahari, abin fata da buri, yayin da wasu kuma ake nadamar sanin su a rayuwa, ake nadamar hada jini dasu, kai wasu ma wallahi su kan zama mugun tabo a rayuwa, amma duka dai lokaci yakan zama Alk'alin yanke hukunci_..........Zaman makokin mahaifina shima wata makaranta ce guda da za a dauki Darasi Kuma irin Darasin Nan da Duniya ce kadai Kan koyar da irin shi Amma ba Wai mutane irin dangin mahaifina baZaman makokin ya kasu Kashi biyu NE a cikin gida yayin da akeyin guda Daya a waje wurin mazan...Ko dayake can din ma biyu NE akeyi inda dangin mahaifina suka kafa majalisar su ta Yan uwa Kuma dangi yayin da Alh Mustafa ma shi da jama ar da suka San shi da marigayin mahaifina da mu amalar su suna kammale wurin Alh Mustafa inda Kuma su kawu madu da kawu gide suke tasu majalisar ta Yan uwan Daddyn in sunzo wurin su suke sauka kamar yadda a Nan ma cikin gida zaman ya kasu Kashi biyu . Su Yaya Badura da yagana suna falon Daddyn inda yagana ce tazo ta ce da ammi ta Bata key din dakin Dan uwan ta Bata Kuma ja ba ta Bata sai dai da Yake Kan nasu babu komai sai handama da babakere babu Arabi ba Boko sai hadama da son Azurta Kai yasa basu waye da komai na maraya ba kasancewar ko acan garin nasu na Maiduguri kauye ne sosai shiyasa ma da yagana ta karbi makullin ta kasa bude uwar dakin Daddyn sai suka tare a falon yayin da ammi ke falon dakin ta Kuma makotan tane Wanda suke gaisuwar mutunci tare da ita musamman mama da suke ga gida ga gida Kuma ta mayar da ammi yarta saboda ko shawara da ita ammi keyi shiyasa take tare da ita Kuma mutanen unguwa ma duk da kasancewar unguwar ta G R A ce irin Rayuwar kowa tashi ta fissheshi ake ba Ruwan kowa da kowa yasa dai daiku sukan gaisa ayi barka ko gaisuwa inda can Kuma wurin su Badura duk Wanda zaizo daga Maiduguri Kai tsaye wurin su yake yada zangoRanar farko ta mutuwar Badura da yagana ne a cikin kichen suna faman dorawa da saukewa na abinci Wanda yagana ta karbo Dan makullin store Wanda ke shake da kayan abinci suka SHIGA sabgar gaban su na gurkawa da Rabawa Amma ko cokali guda ammi Bata gani da idon ta ba bare ayi Mata karar miko Mata ita da jama ar da suke zaune sai fa mama ce ta saka yarta ta dafo wake da shinkafa aka kawo Nan ammi da sulaiman don ni dai Kam ban zaci ko da dimuwa Ruwa ya ratsa makoshi na ba bare abunci Wanda su yagana ke faman hadidiyaSai bayan Isha I ne kawu madu da kawu gide suka nado tabarmin suka shigo ciki inda kawu gide ya Soma bude fridge din dake kicin yayi Arba da Naman kaji da na shanu ya kuwa kwalawa yagana Kira ta karaso inda ya Rufe ta da masifa Wai ga nama cike da na ura Amma tayi musu abinci babu nama? Ta ke ya Bata umurnin yi mishi farfesun Naman saniya a take Kuma yagana ta hau aikin dahuwar NamanHaka kawu gide yayi ta zaga gidan Kuma duk abinda ya ...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.