NUFIN ALLAH

37

by @anisamuhammadyah897


💕 NUFIN ALLAH 💕 
By
Anisa Muhammad yahaya 


 YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION YOTA


Page 3️⃣7️⃣


Ajiyar zuciya Amma ta sauke, ta kalli Anisa dake jikinta ta ƙara cewa

"A koda yaushe idan na tambayi Ammin ki baza ta sake yin aure ba kin san me take ce mun"

Kai ta girgiza a hankali tana jin yanda mahaifiyarta ta sha wahala a gidan dayake wai na mahaifin ta saboda bata da uwar da zata kula ta tsaya iya karfinta a kan lamarin ta
Kuma shine zata ƙi farin cikin Ammin ta

"Cewa take ba zata ƙara aure ba zama zata yi ta kula da ƴar da Allah ya bata tilo, so take ta kula da tarbiyyar ki, ki taso tare da ita bata son kiyi maraici duk da kin rasa mahaifin ki tun baki san shi ba, tun be taɓa ganin ɗiyar shi ba a duniya ba"

"Idan nace to ai ko tayi aure zata iya duk wannan" sai ta ce

"Gani nake kamar ba iya matan uba ne zasu iya cutar da ɗa ba, gani take ko yaya ne dole zaki cutu ta wata hanyar"

"Kuma duk yanda muka so har Anty Zuhura kasa shawo kanta taƙi, mahaifiyar ki meso da kaunar kice a duk yanayin da kika tsinci kanki, nasan yanzu da zaki faɗa mata duk yanda ta ƙaunaci haɗin nan tunda har tasan ba kya so ba zata taɓa bari ayi ba, zata gwammace ta sadaukar da wannan ta miki abinda zai faranta miki sai dai idan ya kauce wa Shari'a, to ke baza ki iya wannan dan ita ba eyye Anisa"

Harga Allah yanzu tana jin koda bata son ya Umar zata iya auren shi kodan yanda Ammin ta ke son hakan dan ita sheda ce taga wannan farin cikin akan fuskar ta 

Kuma tasan Ammi baza ta taɓa yin abinda zai cutar da ita ba, saidai wanda zai gyara mata rayuwa 

Muryar Amma ce ta katse mata tunanin da cewa

"Kiyi addu'a ki nemi zaɓin Allah, kiyi istikara Allah zai zaɓa miki mafi alkhairi, zaɓin Allah shine zaɓi, zai iya yiwa in shawo kanki ki aure shi hakan ya zamo ba alkhairi ba a rayuwar ki, za kuma ki iya ganin shi da kike gudu shine mafi alkhairi a rayuwarki shiyasa a kullum a keson ka nemi zaɓin Allah a rayuwa saboda wani abun ba zai maka daɗi ba amman Kuma haka ne yafi wani daɗin alkhairi a rayuwar ka, wani kuma aka sin haka, shiyasa indai ka nemi abu wurin Allah kaga baka samu ba daman ba alkhairi bane a gare ka maybe agaba ya zamo maka alkhairi ko kuma Allah ya cire maka shi a. rayuwa saboda ba alkhairin da zaka samu a tare da abun, shiyasa kome zai faru sai da NUFIN ALLAH kuma da neman zaɓi a gare shi, kin gane koh Anisa, kar kisa wa kanki damuwa, karki ɗaga hankalin ki, kiyi addu'a kamar yadda na faɗa miki zaki ga sakamakon Allah dan shi maji roƙon bawan shi ne duk sanda bawa yazo mai da bukatar shi, musamman ma bawa in ya kasance mai yawan ibada da hakuri"

"In sha Allah Ammah zanyi duk abinda kika ce kuma na amince indai hakan zai saka Ammi farin ciki"

Kanta ta shafa tace Allah ya miki albarka yasa ku ci gaba da zama masu biyayya da son iyayen ku

Please follow and like my account on arewapen ba dan halin wannan marubuciyar ba🥹🙏🙏





______________________
By
Anisa Muhammad yahaya 🌺 
***