NUFIN ALLAH

39

by @anisamuhammadyah897


💕 NUFIN ALLAH 💕 
By
Anisa Muhammad yahaya 


 YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION YOTA


Page 3️⃣9️⃣

Dining ɗin ta nufa ta zauna daga ɗan nisa da shi 

Tuwon ta kalla sai kuma ta fara ci, har lokacin tana iya jin idanun shi akanta

Shima warmers din dake gaban shi ya janyo ya saka tuwo ɗaya ya zuba miyan dan duk zaman da yayi a wurin har su Ammi suka gama suka koma parlour beci ba

 Ammi ce ma tace"ahah Babban yaya kai baza ka ci abincin ba"

"Zanci Ammi bana jin yunwa ne yanzu"
 Shima Ahmad da ya gama sallama ya musu dan ana neman shi

Spoon ya ɗauka ya fara cin tuwon dashi, ɗagowa tayi ganin ya ja spoon taga yana ci da shi,
"ikon rabbi tuwo da spoon iyayi dai kawai" ta faɗa a ranta

Tana ƙoƙarin kauda kanta ne suka haɗa ido, sai ya ɗaga mata gira yana kai tuwo bakin shi, kai ta juyar tana ɗan taɓe baki

Itafa har yanzu bata gama yarda wannan ya Umar din dai da tasani shi ke sonta ba bama haɗi ta ina zata ma far yarda da wannan batun, ita fa bata ga wani alama ba,anya ba iyaye ke kiɗar su suna rawansu ba, ba suke son kawai haɗa wannan al'amarin ba kuwa

Kallon shi ta ɗan ƙara yi, so take taga ko da wata karamar alama ne da zai sa ta yarda shi ɗin ne 

Rai ya ɗan haɗe jin tana ta kallon shi ya ɗago kanshi daga danna wayar da yake daidai yanda ita kaɗai zata ji yace

"Nifa ban cika son kallo ba in ba haka ba Tom" ya jijjiga kai yana cigaba da kallon ta ranshi a ɗan haɗe 

Tun suka haɗa ido tayi saurin janye wa, jin wai yana cewa baya son kallo yasa ta ƙara ɗagowa ta kalle shi, kasa kasa tace

"Amma kai ai ka iya kallo harda na haramun, mutum sai shegen kallon tsiya amman shi wai kar akalle shi'' ta faɗa harda wani murguɗa baki

Murmushi yaso yayi amman ya maze dan yaji abinda ta faɗa ga tana maganar tana wani cuno ƙaramin bakinta gaba

"To ya za'ayi dani, ai mallakina nike kallo ba na wani ba"

Da sauri ta ɗago tana kallon shi ya wani maze kamar ba daga bakin shi maganar ta fito ba, idan ba dan tasan Muryar shi ba kuma tasan su biyu ke zaune a gurin sai ta musa shi ya faɗa

Dan yanda ya wani ƙara haɗe rai yana danna wayar shi kamar ma besan tana existing a gurin ba sai ta iya rantsewa besan me take ba

"Nace miki bana son kallo koh" ya ɗago idanunsa ya saka anata, kauda kanta tayi, ji tayi ma zaman dining din ya ishe ta sai kawai ta miƙe da plate ɗin abincin ta tayi kitchen 

Murmushin gefen baki yayi dan shi kansa yasan ba tayi expecting Jin hakan ba, wani tunanin ne ya dawo cikin kanshi,

 Ahmad yafaɗa mai yanda suka yi da Abba, tunani da fargaba take ya dirar mai karfa ace ta ce bata sonshi,yasan shikenan ya gama, tun jiya yake wannan fargaban amma azahiri in ka ganshi ba zaka ce wani abu na damun shi ba 

Ko ɗazu daya ganta yayi tunanin ko gudowa tayi dan kar Abba ya ƙara tambayar ta opinion ɗinta, shifa besan ta yanda zai Fara bane shiyasa, da ya dade da Kama wannan zuciyar dake wahalar dashi

Karasa cin abincin nashi yayi dan ɗazu ba wani ci yake ba sai akin kallon ta da yake 

Saida ta gama cin abincin, tana cikin wanke plate ɗin harta gama zata kife ya shigo, nashi plate ɗin ya ajje mata a sink ɗin ya ɗauki cold water a fridge ya fita bece da ita komai ba, itama bata ce masa komai ba ta ƙara wanke nashin 

Fitowa tayi ta nufi ɗakin ta ta kwanta ta rufe idon ta, tana tunanin yanzu koda ta yarda wane irin zama za tayi da shi 

Ganin tunanukan bazasu kai mata bane yasa ta lalubo wayar ta ta cigaba da kallon da take, amman ina ba ma ta fahimtar me take yi se su da take hasaso wa a cikin wayar, kifa wayar tayi akan gadon ta kama kanta tana faɗin 
''na banina nikam, banga ta yanda wannan al'amari ze yu ba anya zan iya kuwa, zan iya amincewa kuwa??..''


Follow and like my account on arewapen ba dan halin wannan marubuciyar ba dan Allah 🥹🙏🙏🙏🙏🙏

______________________
By
Anisa Muhammad yahaya 🌺 
***