40
💕 NUFIN ALLAH 💕
By
Anisa Muhammad yahaya
YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION YOTA
Page 4️⃣0️⃣
Ammi ce bayan magarib lokacin Ammah ta tafi ita kuma Mommy ta koma part din su ta shigo ta sami Anisan
Dan daman tun sanda ta zo gidan take jin kamar wani abu na damun ta, abinda ya sa bata tambaye ta ba saboda yanda su amma suka nuna nasu kulawar shiyasa tayi kawaici ta share kamar bata gani ba
Kuma taga alamar tana son ta faɗa mata wani abu ɗazu shiyasa tun lokacin hankalin ta na kanta, zuciyar ta Allah Allah take ta ƙebe da ɗiyar tata taji meke damun ta
Zama tayi kusa da ita, ta dafa ta tace
"Me kike son ki faɗa mun ɗazu ne"
Jin abinda tace ne yasa ka ta fara tunanin me zata ce mata dan bata taɓa boyewa Ammi komai da ya shafeta ba amman yau zata fara dan ba zata so abun da zai sosa mata ranta ba, bata son abinda ze karya wa mahaifiyarta farin cikin ta hayatyn ta rai
"Amm daman fa Ammi na kasa Bama Abba amsa ne da ya tambaye ni, kuma nasan ko gobe ko jibi zai nemi jin ra'ayina amman ni kunya nake ji shine nake son fa ke ki faɗa mai da kan ki na amince"
Fadar kalamar ta amincen ma sai da yasa ta jin wani abu a cikin ranta kamar ta ƙaryata kanta
Dan sauke ajiyar zuciya Ammi tayi, tana jin farin ciki aranta, amman haka kawai take jin ba iya shikenan ba
"Iya shikenan kawai ba abinda yake damunki"
"Me kika gani hayatyna?"
"Gani nayi kamar ba iya maganar dake bakin ki ba kenan"
"A'a Babu komai hayaty na" ta faɗa tana rungume Ammin, ita ma rungume ta tayi tana mata adduo'i a ranta
"Ammi na ina sonki sosai, You have gone through alot, Allah ya biya kida Aljanna Ammi na, Allah ya jiƙan Abhie"
Kanta ta shafa hawaye na cikowa idonta tace
"Ameen ameen Anisa ameen, Kuma Allah ya muku albarka yasa ku cigaba da haɗa kanku fiye da yanzu, ya baku zuri'a ɗayyiba"
Kanta ta kwantar kan kafaɗar Ammi tana sauke ajiyar zuciya, ta tabar wannan shine abinda ya dace tayi tana da yaƙinin in Sha Allah wannan ne mafi alkhairin decision da ta yanke ko dan faranta wa Ammin ta rai Allah itama zai duba ta
Zata Fara ƙoƙari taga ta sanya koda ƙanƙani ne na son shi kodan Ammin ta, zata rage tsoron da take mai ta kalle shi a matsayin mutum kuma matsayin ɗanuwanta, yayanta, kuma me ƙoƙarin taka matsayin mi..... Kasa ƙarasawa wa tayi ta lumshe idon ta wani tsoron na ƙara shigar ta
Wani nannauyar ajiyar zuciyar ta sake saukewa ta lumshe idanunta tana kara rungume Ammi n
Sun ɗan jima a haka sannan Ammi tace
"An kira isha let's go and pray"
Tom tace tana zame jikinta ta yi toilet, da kallo Ammi ta bi bayanta tana tuna mahaifinta da bai taɓa ganin jinin shi ba a doran duniya, itama bata taɓa ganin fuskar mahaifinta ba saidai hoto
Koda suka zo kwanciya Ammi zata tafi Anisa tace so take su kwana tare
"Yau kuma keda idan nace kizo mu kwana kike guduwa idan ba wani tsoron naki ya kawo ki ba"
"To Ammi ai lokacin da ban yau daban, ni dake nike son kwana"
Ko bayan da zasu kwanta, alarm ta saka na ƙarfe 2 na dare, dan ta tashi tayi addu'a kamar yanda tama Amma alƙawari
Da kyar ta tashi wajen 2 din abunka da ba'a saba ba, sallah tayi raka'a 6 tayi adduo'i tayi istikara
Ammi ce jin motsin ta ta tashi ta ga tana sallah, wani sanyi taji a ranta dan koda akwai dalili, hakan ya nuna mata ƴarta ta fara girma da hankali, ta fara sanin muhimmancin kai wa Allah lamari ba shiritita da shirme da take ba ko zaman kuka
Ko a ɗazu taji tane kawai da tace ba komai amman ita tasan dole da akwai wani abun, bata tursasa mata ba ne saboda tasan tayi hakan ne dole dan wata ƙila abin in ta fada mata zai dame ta, shiyasa bata tursasa mata ba karma memakon ta faɗa mata gaskiya ta mata ƙarya
A gurin ta zauna ta cigaba da addu'a daga baya ta ɗauko Qur'ani ta fara karantawa ba ita ta bar gurin ba sai bayan da tayi sallahn asuba
Tun kafin ta koma bacci taji nauyin da zuciyar ta tayi da fargabar da take akan auren ta da ya Umar na ɗan yayewa tana jin wani kwanciyar hankali tun bayan ta gama karatun quranin
'' in Sha Allah zanyi zan iya zan cika wa ammina farin cikin ta '' ta faɗa a ranta tana kallon Ammi dake zaune kan dadduma
Follow and like my account on arewapen ba dan halin wannan marubuciyar ba dan Allah 🥹🙏🙏🙏🙏
______________________
By
Anisa Muhammad yahaya 🌺
***