CANJIN BA ZATA

Babi na hudu

by @maryamlitee

🌟🌟CHANJIN BA ZATA 🌟🌟



        By

 MARYAM IBRAHIM LITEE


Babi na hudu


 Na fasa kuka,  Ummu da ke zaune ta tasa cikinta gaba take tanbayata, Taa...   aa  rasu! Ummu mun rasa Amina,  Amina ta rasu Ummu". Sai da nayi da na sanin gaya wa ummu dan halin da ta shiga ga tsohon ciki". Kwanakin da suka biyo baya sun zo mana a tsanance kwarai, Koda yaushe za ka same mu shiru da ummu da salma, wani lokacin kuma mu yi ta kuka,  Gamu mu kaÉ—ai a gida, Sai da aka yi sati sannan mutanen gidan su ka dawo, ciki har da yayarmu,  Mutuwar ta taÉ“a kowa a gidan, dan lokaci zuwa lokaci za ta aiko mota cike da kayan abinci a raba duka gidan, hatta sutturu zata aiko ta ce a raba wa masu bukata,Hadda kuÉ—i aba magidantan su yi cefane. Wani zance mara daÉ—i ana zaman makokin aka sace kit É—in ta da take adana gwala_gwalantaSai na riÆ™a tuna zuwanta na Æ™arshe in da ta ce ma innarmu "In sha Allahu innarmu  in dai na rabu da cikin nan lafiya ya zama dole in sai da wasu gwala gwalaina, in zo in bada aikin gyaran gidan nan".Ban mantawa innarmu murmushi tayi Ta ce"Ke ai da wuya kuÉ—inki su yi auki, kullun kuÉ—inki na cikin hidimta mana, ubangiji dai ya yi albarka ya raba ku da cikin nan lafiya, tare da kowace musulma me É—auke da shi". Su innarmu basu dawo ba, babanshi ya roÆ™i su zauna har tayi arbain dan Æ´an gaisuwar kullun Æ™ara zuwa suke, ga mijinta ya shiga ruÉ—ani mai yawa Su biyar ne zaune can hada Haj Æ™anwar kakarmu Ranar da tayi arba'in Æ™annan babanmu maza suka yi mota guda  suka nufi Abujan  da niyyar su Æ™ara ma juna gaisuwa, sai su taho da su Innarmu  Haka kuwa akayi Washegari sai ga su sun dawo, Kallo É—aya za ka yi wa innarmu ba za ka so Æ™arawa ba, Yadda duk ta bi ta yamutse. Uwar É—akanta kawai ta wuce ta hau gado, rufe ta muka yi muna ta kuka masu shigowa yi mata gaisuwa suka yi ta bamu haÆ™uri. A ranar cikin dare ummu ta haihu cikin Æ´ar gajeruwar naÆ™udata samu santalelen yaro, Innarmu ta fita ta taso Haj kishiyarta da Baba Rakiya, dan da nan suka gyara me jego da É—anta. Æ™arfe biyu suka yi sallama kowace ta koma É—akinta. Da safe me jego kamar ba ita ta haihu ba, Allah kenan me yin yadda ya soIta Amina ko haihuwar ma bata kai ga yi ba, Allah ya amshi abinsa. Da safe mutane suna ta shigowa barka har dare, Uban É—an ma a ranar ya iso daga katsina. Cikin dare na farka na ji motsin innarmu da na saurara sai na ji sautin kukanta a hankali,da sauri na tashi na  zauna kusa da itaInnarmu me ya same ki ? Shiru tayi da farko sai da na maimaita na ce Innarmu ki yi haÆ™uri duk mai rai mamaci ne,Ina so akan wannan ma ki sa haÆ™uri".Ta ja numfashi  ta share hawayen da ke gudu kan kuncinta, Ba mutuwar uwata  nake ma kuka ba, Ina kukan al'amura da dama, Muhimmi cikin su shi ne rasa mahaifinku da na yi a lokacin da na fi kowa bukatar shi, musamman kasantuwar Æ´aÆ´ana mata ne, Ina da buÆ™atar shi kusa da ni". Na ce Ki yi haÆ™uri innarmu Ke É—in ma ai jaruma ce, da ki  ka fi wasu mazan tsayuwa a kan ƳaÆ´an su."ta ce "Shuhaina ki yi haÆ™uri   saboda ke  na ke wannan kukan".na rufe baki "Na shiga uku!  Innarmu me na yi maki? ta ce "Ki yi haÆ™uri, amma ba ki yi min komai ba, abinda nake so da ke, idan har ni ce mahaifiyar ki, Ina kuma da Æ™ima a wurinki,to ki yi haÆ™uri da abinda zan gaya maki, kuma ki rungumi Æ™addara".Na ce "Na ji,In sha Allah kuma zan yi yadda kike so". duk da dai cikin Æ™arfin hali nake, gabana faÉ—uwa yake, dan na san abinda zai sa  ta kuka ba Æ™aramin abu ba ne. ta ce A jiya da hantsi za mu taho  an hallara a falon mahaifin Ahmad ana Æ™ara wa juna gaisuwa sai Babanku ya'u ya matsa kusa da shi ya ce "A madadina da yan'uwana mun yanke shawarar ba Ahmad Æ™anwar mariganyiyar,  uwarsu É—aya Ubansu É—aya, kuma watanni kaÉ—an suka  rage ta kammala karatunta."nan da nan Alhajin ya shiga godiya, Ya ce idan ba damuwa a faÉ—i sadakinta tunda akwai jama'a sai a É—aura, Babanku ya faÉ—i sadaki Dubu hamsin, nan take Alhajin ya biya, aka ce jama'a su shaida aka É—aura maki aure da mijin Æ´ar'uwarki."Ya zuwa lokacin da ta kawo nan kuka nake iya Æ™arfina, ina fyace hanci Na buga kaina a bangoIna cewa yau na san ni marainiya ce, na rasa mahaifina, dan da shi ne nasan ba zai min haka ba, ya ba wanda bai ce yana so na ba. Ihu nayi da Æ™arfi Ina "Wayyo na bani ya ma za'a yi in auri mijin Amina?Ban ankara ba sai dai na ji Innarmu ta make baki na. "Yi mana shiru, ba ki da hankali?  Ba ki san dare ba ne, ki tado mana jama'a? Ashe ke ba za ki yi haÆ™urin da kike cewa in yi ba? Ba sai mu bar wa Allah komai ba ya warware mana? Daga haka Alwala tayo ta haye Sallayarta, Ni kuma zama nayi na jingina da bango na haÉ—a kai da gwiwa, Kuka na ke wanda zuwa safiya fuskata ta kunbure, ko kokon da na dama ban sha ba, ban ma da niyyar zuwa makaranta. Baba ya'u ya yi sallama a Æ™ofar É—akinmu,  sai da ya zauna muka gaishe shi ya gaisa da Innarmu, ya ce "Fatima ba ki ce komai ba kan sadakin shuhaina". wani É—an murmushin da bai kai zuci ba tayi,  "Ni kuma a taÆ™aice wace hujja gare ni ta cewa a bani sadakinta? ya ce "In na lura Fatima sai in ga kamar fushi kika yi".ta girgiza kai "Ko É—aya, tunda an riga an É—aura to me kuma zaka ce? ya ce "Ato bare duk wanda rai ya yi wa daÉ—i baran me shi ne, Na ga wannan gata ke nayi mawa, don idan ta samo kan ta tuna da ni sai ta fara kawo maki, yanzu ba ga Zinatu ba wane faÉ—i tashi ne ban yi ba kafin yuwuwar auren ta? amma yanzu wa ta sani idan ba uwarta ba,har makka ta kai tani kuwa ko sansanin alhazan ban je ba".Innarmu ta tari numfashinsa, "Abinda nake so ka gane, kar mu sa wani hange cikin wannan aure, mu riÆ™e shi da zuciya É—aya, Mu yi addu'ar Allah ya sanya masa albarka Amma wata niyya tamu ta daban ba wannan ba,za ta iya janyo manamatsalar da idan ta zo ba za tayi mana daÉ—i ba".Ya ce "Haka ne" ya  tashi ya fitaUmmu ta dafe baki, "Yanzu fa  shi kenan ya riÆ™e sadakin nan ba zai bayar ba? "Innarmu ta ce Uhum! kawai Baba sani ya shigo yana ta ba Innarmu haÆ™uri Ya ce "Shi tsoron da yake ji masu kudin nan ba'a yi masu irin wannan karan tsayen.ta ce "Ba komai Allah ya sa hakan ya zama alheri". Ranar suna yaron Ummu ya ci suna Najib. Na ci gaba da zuwa makarantata. Satin Ummu uku da haihuwa Baba ya'u ya shigo gidan cikin sauri, ya ce a ba shi tabarmi ga uban  Ahmad nan da mutane. Ya É—an jima da zuwa aka kira Innarmu su gaisa, ya yi mata godiyar karamcin da aka yi masu, Ya ce ya zo ne ya Æ™ara yin godiya, kuma a account É—in Amina, an samu dubu É—ari biyar da ashirin, Mijinta ya ce ya yafeSai suturunta duk an zo da su, Kuma shi ma Ahmad É—in wai yana nan zuwa dan yanzu haka ba ya Æ™asar, kan wani aiki da ya taso masa,kuma ya ce kar a sayi wani kayan É—aki, dan ba zai iya zama gidan da ya zauna da Amina ba, ya koma cikin asibitin da yake aiki nan za'a kai ni. Ina jin muryar Baba ya'u ya na cewa "Ina Shuhainar ta gaida surukinta? Karkashin gado na shige.Ya shigo har ciki yana ce wa Ummu "Ina shuhainar?  ta ce "Ai ko ta fita"Tsaki ya ja ya juya, Mahaifin Ahmad ya cika mutanen gidan da kudi sannan ya tafi,Zo ka ga fara'a wurin Baba ya'u, ya samu abun san shi.Har Ummu tayi arba'in ta koma, ba Ahmad ba labarinsa, ga gulmar da ta fara yawo a cikin gidanmu, Wai ai dama kwaÉ—ayi ne, In ba dan an ga kuÉ—i ba ƳaÆ´a take da su, ballantana ace zata riÆ™on su,Ko shi bai santa ba? ba za a jira ya ce yana san ta ba. A yanda ma ake bada labarin wai Innarmu ce ta roÆ™i ya aure ni,Wata aminiyar ta ta Æ™ut da Æ™ud Haj baraka ta zo tana tanbayar Innarmu gaskiyar maganar, ta ce mutanen gidanmu ke zuwa gidansu da labarin idan an tabbatar da ba ta nan, Ita kuma idan ta dawo sai mutan gidan su su gaya mata. Daga ni har Innarmu  mun shiga halin takura a cikin gidan,Ina dai zuwa makaranta ne, amma gani nan ne Har muka fara zana jarabawar (WAEC)  É—inmu, da Æ™yar na sa ma zuciyata salama na fuskanci jarabawar, Ranar da muka kammala paper karshe ina dawowa gida, Sujjada nayi ma ubangiji da na É—ago idona na malalar da hawaye, Innarmu wadda ke zaune tana yankan É—inki ta dube ni, "Ki yi haÆ™uri Shuhaina kowane bawa da irin Æ™addarar shi a rayuwa,haka idan Allah ya shirya rubutaccen al'amari baya kankaruwa, an É—auke alÆ™aluma kuma takardu sun bushe, Matar mutum kabarinsa." Daga haka ta ci gaba da yankanta. Wasa wasa sai da aka Æ™ara wata guda, Ranar na dawo islamiya da hantsi mota na gani galleliya tana ta sheÆ™in É—auke ido,cikin hasken ranar da ya fara É—agawa,Ƙwarai na yaba kyan motar a raina, Na wuce cikin gida, abinda na lura mutanen gidan sai kallona suke,ban damu ba, na wuce É—akinmu, Innarmu na samu kan sallayarta, na san ita É—in ma'abociyar sallar walha ce, "Innarmu na dawo,  Yusuf É—in ya kawo cefanen kuwa? Ina son yi da wuri ,gidan ummu za ni in gano Najib." Cikin sanyin murya ta ce "Bar girkin nan Shuhaina, je ki yi wanka". Na ce "Nayi kafin in tafi makaranta". Ba tare da ta dube ni ba ta ce "Na ce ki je ki Æ™ara yi"Ban saba musu da ita ba sai na wuce, Sai da na dawo wankan, ta ce in yi kwalliya me kyau, zama nayi nayi kwalliyar ta ce in É—auko kayana sababbi in saka,Ba musu nayi yanda ta ce,Hijab ta umartan in saka Gwoggo Rakiya ta leÆ™o "Yawwa ta kammala? Sai ta juya, tare suka dawo da hajiyar mustafa kishiyar innammu, Suka ce ma Innarmu  "Sai ki sa mata albarka dan suna jiranmu su yi mata faÉ—a". ta ce "Allah ya yi maki albarka, ya bada sa'a" ta sa kai ta shiga uwar É—akanta, Sai sannan na fahimci abinda ke shirin faruwa da ni, Kawai sai na sa kuka. Za su kama ni mu fita na ce"Zan É—auki wayata"  hada Æ™aramin Al-Æ™ur'anina na na É—auko, da hisnul muslim, É—akin gwoggo ladi aka kai ni, Inda muka samu duka Æ™annen babana sun hallara, faÉ—a suka yi min, da nasihar in bi aure. Baba ya'u ya ce"Duk mun fita, bin mu aka yi, aka ce mu zo, Mijinki ya turo mota a tafi da ke.A raina na ce "Ka ji wai direba dan rashin galihu".Da muka fito direba ya taso da sauri ya buÉ—e Æ™ofofin motar, Mu huÉ—u ne a baya, Baba ramu a gaba, da yake ita tana da jiki, Ƙannen babana duk suna tsaye, Mutanen gidan ma duk sun leÆ™o suna ta É—aga hannu, Wani Æ™ududu na ji ya taso ya tokare ni, ko  Æ´an'uwana ba a bari sun zo mun yi sallama ba, dai dai da salma bata nan, Yusuf kuma cikin dare ya iso daga kano, inda yake karatu, bamu gan shi ba sai da safe,  leÆ™owa kawai ya yi ya gaida Innarmu,  ya ce  Bari ya je yayo cefane ya dawo, ya ce min "Akwai labari Shuhaina,  bari in dawo. Kafin ya dawo na tafi makaranta, Sai dai idan ya dawo ace mashi an tafi da ni. Kuma dangin uwata ko É—aya basu tsaya an É—auka ba,duk da yake sune dangin nata, amma ai da ko Haj an aika mawa.Mun iso marabar jos, nayi Æ™oÆ™arin tsaida hawayen da ke bin fuskata, Na dubi su Baba Rakiya, barci duk ya yi awon gaba da su. Tunanin babana yana ta bijiro min, da kuma tarihin shi da aka bani.