RIKON KA'KA

Chapter 11

by @rukyelmuaz

RIKON KAKA 

By 

Rukayyat (Rukyelmuaz)

YOUNG TALENT ASSOCIATION WRITER'S (YOTA)

Book 1

Chapter 11

Shiru ya yi yana tunanin to taya Baba baisan ainihin inda iyayen shi suke ba baisan komi game da dangin shi ba zai ce zai bashi aure. "Shikenan naga kamar bai amince ba kuyi haƙuri da ɓata muku lokaci da nayi" Kamar daga sama yaji maganar Malam Sule wannan maganar ita ce ta yanke shurun da ya gifta a gurin domin kowa amsar shi ya ke sauraro. "A'a wallahi na amince babu wani abu da zaka nema agurina in kasa aikatawa ko da rayuwata ce zan iya bayarwa domin ta ka Baba" Ya kai ƙarshen maganar yana ƙasa da idanun shi.

Amsar da ya bayar ita ce ta zama matakin ƙulla auren shi da Hafsat ɗin shi ƙanwar shi mace da biyu ta yake jin rayuwa da ita yafi mishi komi a duniya kyautar Allah daga Mama Badiyya mahaifiyar shi wacce ta nuna mishi soyayyar uwa wacce ya rasa. Anan ta ke aka ɗaura auren Ahmed Basam Mahi da matar shi Hafsat Sulaiman  wanda sadakin ma Malam Sule ne da kan shi ya bayar.

Bayan an ɗaura aure Malam Sule ya tara su da dare ga shi ga Ramu ga Hafsat ga Ahmed a cikin turakar shi, nan ta ke babu ɓata lokaci ya sanar da su abinda ya tarasu ya aurar da ɗiyar shi Hafsat ga Ahmed. Nan take Ramu ta nuna rashin amincewar ta domin ita a ganinta ta ya za'a ba Ahmed aure bayan ba'a san dangin shi ba dole a warware wannan auren Malam Sule ne ya dakatar da ita akan abinda take ƙoƙarin aikatawa, tun da aka fara maganar Hafsat kanta na ƙasa bata ce komi ba sai wasa da gefen hijabinta da take yi Malam ya kalleta ya ce "Hafsat kin amince?"  Kin ɗago da fuskanta ta yi sai kawai ta rufe ido da hannu ganin hakan yasa ya ce "Ku wuce Allah ya muku albarka, amma Ramu ki tsaya zan yi magana da ke". Ahmed ya fara fita a ɗakin Hafsat tabi bayan shi suka fita ta wuce ɗaki shi kuma ya fita don wallahi yanzu duk wata kunyarsa take ji tunda aka ce wai an ɗaura musu aure to wai dama in aka ma mutum aure kunya yake ji ita dai ba ƙawaye gareta ba bare ta tambaya ko taji labarin yanda abun yake. Malam Sule ya yi ma Ramu nasiha ya bata haƙuri domin yasan ita ma tana da hakki akan Hafsat domin mahaifiya ce a gareta maganar shi ta shigeta sosai hakan yasa duk jikinta ya yi sanyi kuma tayi ma auren fatan alheri da samun natsuwa Allah yasa mutuwa zata raba yaji daɗin addu'ar ta sosai hakan yasa yaji kamar ya sauke wani nauyi dake kan shi ne. 

"Duk wani abu da ya dace ki faɗamin nan da kwana ukku nikeson ta tare a ɗakin mijinta" 

"Amma Malam kwana ukku baiyi kusa ba?"

"A'a baiyi ba Ramu ki shirya duk abinda ake buƙata insha Allah nan da kwana ukku zasu tare a nasu gidan"

"Shikenan Allah ya basu zaman lafiya me ɗorewa"

"Ameen ya Allah Ramu"

Suna gama magana Ramu ta fito ɗakin Hafsat ta shiga ta ganta kwance idonta na kallon ƙofar shigowa. "Bakiyi bacci ba?" Tayi tambayar tana kallon Hafsat dake kwance ƙoƙarin tashi ta yi zaune amma Ramu ta ce "A'a kwanta in bacci zaki yi da safe sai muyi maganar?
"A'a kawai dai ina kwance ne ba bacci zan yi ba Mama"

Guri Ramu ta samu ta zauna a gefen gadon ita ma Hafsat ta shi ta yi zaune tana jiran jin abinda Ramu zata ce. "Hafsat ni uwa ce kin san ba zan cutar dake ba ki faɗamin gaskiya in bakison Ahmed ba zan bari ayi miki dole ba"

Shiru Hafsat ta yi bata ce komi ba sai kawai kallon ƙasan gadon da take kai ta ke yi.

"Kika yi shiru ke nike sauraro"

"Ni ban san me zance ba ne shiyasa"
"To kina son shi?"

Shiru ta yi kawai nan ma bata yi magana ba.

"Uhmmmm" Ramu ta sauke ajiyar zuciya tana tunanin kada a cutar da marainiyar Allah fa amma shikenan Allah yasa hakan ya zama alkairi tashi ta yi ta fita ɗakin bayan ta fita Hafsat ta koma ta kwanta amma har yanzu ta kasa bacci tunani daban daban ta ke yi to yanzu shikenan ta zama matar Ahmed to ai ba soyayya suke yi ba yanzu shikenan ya tashi daga Ahmed ɗin da ta sa ni ya dawo mijinta da irin wannan tunanin har bacci ya ɗauketa.

Bayan kwana ukku kamar yanda Malam ya ce hakan aka yi yau Hafsat zata tare a gidanta ba wani taro ya ce ayiba dangin mahaifiyarta ne da nashi dangin kawai aka ɗanyi taro. Malam da kan shi ya basu gidan da zasu zauna gidan baya da nisa da gidan Malam. Da kan shi ya kai Hafsat har gidanta domin a cewar shi mahaifine yafi da ce wa da ya kai ƴar shi ɗakin mijinta bayan ya kaita ya haɗasu da Ahmed ya musu nasiha sosai sannan ya bar gidan.

Rayuwar Hafsat da Ahmed gwanin sha'awa duk wani fari ciki tana samu agurin Ahmed wata soyayya wacce ta ninka wadda yake ma ta a baya yanzu ita yake nuna ma ta watan su biyu da aure Allah ya azurta ta da samun ciki kowa ya yi murna sosai kullum Ramu saita aiko ma ta da ƙanzon tuwo don tunda ta samu cikin tafi son ƙanzon tuwo kuma wanda ba ita bace ta tuƙa shi. Ahmed ji ya ke kamar yafi kowa sa'a a duniya shima zai tara family ɗin shi zaiga jinin shi a duniya.

Wani lokaci, Malam Sule ya zo har gida ya samu Ahmed domin yana son su yi magana mai mahimmanci bayan ya zo ya samu Ahmed ya ce "Ya da ce yanzu ka fara wata babbar sana'a tunda ka fara tara iyali ga ciki Hafsat na da shi"

"Dama ina son zan ringa shiga Niger ina kai kayan abincin da muke nomawa amma sai shekara mai kamawa, tunda yanzu muna ƙarshen shekara in komi ya gama zuwa gida" 

Ahmad ya ba Malam amsa yana jiran jin abinda Malam zai ce.

Malam ya yi murna sosai sannan ya ce "In don wannan ne babu matsala ka fara da hatsin da ke cikin rumbu a gida"

"Nagode Baba nagode ya saka da alheri ya biya ka da gidan aljanna"

Ahmed ya ji daɗi ya rasa dame zai sakama Malam a duniya ya yi godiya sosai har sai da Malam ya dakatar da shi bayan Malam ya koma gida ya sanar da Ramu abinda suka yanke da Ahmed batayi musu ba saima fatan farin ciki da addu'ar sa'a da nasara da ta yi.

Shima a ɓarayin Ahmed yana shiga gida da farin ciki ya sanar da Hafsat. "Dama zuwan da Baba ya yi yanzu munyi magana akan zan fara wata babbar sana'a to na yanke shawarar fara zuwa Niger kai hatsi"

Tayi farin ciki sai dai ita tsoron ta ɗaya gaskiya bata son ya rin ga yin  tafiyar kwana don tun da sukayi aure sau biyu ya yi tafiyar kwana tunda ya lura bata so duk damuwa ta bayyana a fuskarta hakan yasa ya fahimta damuwarta rarrashinta ya yi ya kwantar mata da hankali.

Kamar yanda Ahmed ya tsara kuwa haka akayi ya fara zuwa Niger yana kai kayan masarufi kuma Alhamdulillah cikin lokaci ƙanƙani Allah yasa ma sana'ar albarka don yanzu ya gyara musu gidansu cikin Hafsat ya shiga wata na tara.

Yau ya kasan ce Ranar Alhamis ne Ahmad yana gida yana ƙaƙorin fitowa zuwa gidan Malam wanda zuwan ya zama kamar ibadah in har yana gari dole sai ya kai gaisuwar.

"Kai bawan don Allah ina ne gidan Malam Sule mai Almajirai" Wani mutum ne dogo da rawani irin na buzaye yake tambayar wani mutum da zai wuce, kwatan ce ya yi masa sannan ya wuce.

Malam Sule na zaune a cikin soro yana karatu yaro ya shigo ya sanar da shi ya yi baƙo Malam ya bada izinin a ce ya shigo baƙon ya shigo fuskar shi rufe ta ke da rawani irin na buzaye bayan ya zauna suka gaisa da Malam.
"Amma ban gane ka ba bawan Allah ina fatan lafiya" Malam Sule ya yi maganar yana kallon wannan baƙon.
"Ehhhh gaskiya baka sanni ba kuma nima bansan ka ba" baƙon ya faɗa yana gyara zama ya yi ma Malam ɗin baya ni a taƙaice da abinda ya zo nema da wanda ya ke nema, Jakkar shi da ya ke rataye da ita ya fara ƙoƙarin buɗewa Malam dai yana ta bin shi da kallo bayan ya buɗe jakkar ya fiddo wata takarda ya miƙama Malam babu gaddama ya amsa takardar ya fara karantawa bayan ya gama karantawa ya sauke ajiyar zuciya ya ce. "Bari in sa a kira shi" Malam ya miƙe ya fita ya bar wannan baƙon a gurin yasa yaro ya je ya kira Ahmed domin ya san yana gari.

A hanya yaron ya haɗu da Ahmed ya taho domin gaida malam kamar yanda ya saba kullum yaron ya sanar da shi Malam yana neman shi.

Malam na zaune shi da baƙon babu wanda ya sake magana sallamar da suka ji ne yasa dukan suka kalli gurin da akayi sallamar a tare suka amsa bayan ya shigo ya samu guri ya zauna Malam ya ɗago ya kalli Ahmed suka haɗa ido.
"Barka da safiya Baba"
"Yauwa barkanmu dai ya iyalin naka"
"Suna lafiya suna gaishe ka"

Ahmed ya maida kallon shi zuwa ga baƙon ya miƙa masa hannu suka gaisa Malam ya ce "Ahmed baƙo kayi" 
"Baƙo kuma Malam"
"Ehhh." 

Malam ya ce yana miƙa ma Ahmed takardar da baƙon ya bashi hannu yasa ya karɓa ya buɗe ya fara karantawa saƙon da ke cikin takardar.

"Assalamualaikum warahamatullah zuwa ga ɗana gudan jinina a duk lokacin da zaka duba wannan takardar nasan bani duniya, nasan a duk inda kake kana danasanin ka san ce wa a matsayin ɗana amma ina son ka sa ni bawai na barka bane don kar in sauke nauyin da Allah ya ɗauramin ba, a lokacin da na kawo ka wannan makarantar ana shari'a dani ne abokan kasuwancina sun yaudare ni sun saka na amshi kuɗin jama'a za mu yi kasuwanci da ga ƙarshe kuɗin suka lalace amma halin ɗan Adam sai suka cire kansu suka ce ni kaɗai ne babu yanda zan yi tunda ni ne na karba, kuɗi ne masu yawa kuma koda za'a bada dukiyata bazan iya biya ba hakan yasa da aka ce in bada dukiyar da nike da ita ko nayi zaman gidan yari na zaɓa zaman gidan yari, ka san mai yasa don banason ka tashi cikin rayuwa mara gata na adana duk dukiyata domin ka rayu cikin kwanciyar hankali kada kasha wahalar rayuwa, bayan na fito daga gidan yari ina son in zo in dawo da kai gida amma ciwon ajali ya hana ganawar mu don Allah ka ya femin sannan duk san da wannan wasiƙar ta shiga hannunka ina roƙon da kayimin addu'a ko zan samu salama dukiya ta ni Mahi gaba ɗaya ta Ahmed Basam Mahi ce halak malak Allah yama albarka sarƙar da ke tare da kai ita ce makullin dukiyarka wacce mahaifinka ya tara ma ta hanyar halak ina fatan baka rasata ba Nagode Allah ya shirya ka ya baka kariya addu'arka na da matuƙar mahimmanci a gare ni. 

Ahmed fuskarsa ta canja ya yi ƙasa da kai.

"Kayi shiru baka ce komi ba Ahmed" Malam ya faɗa yana kallon Ahmed.

"To me zance Baba bani da abin da zance ni"
Baƙon ya ce "Kaine keda abin cewa mana"

"Ga takardar da mahaifinka ya bari kafin ya mutu da kuma wasiyyar da ya bari a baka ka karanta baka ce komi ba ai dole kayi magana"

Shi dai Ahmad ya kasa ce wa komi jin su kawai ya ke yi bai san mai zai ce ba hankalin shi ya ta shi kenan duk wannan daɗewar da ma abinda ya faru da mahaifinsa kenan ya sadaukar da mutuncinsa da arzikinsa don kawai shi Ahmad ya yi rayuwar farin ciki wasu hawaye suka fara zubowa da ga idanunsa.

Malam Sule ne ya katse shirun da gurin ya yi
"Allah ya jiƙan shi amma kai waye a gurinsa?"

Ya yi ma baƙon tambaya yana kallon shi yana jiran amsar shi.

***