74
by @halimahz
Daada ta ja tsaki ta ce da Raudha,"Kira min Abdulhamid a waya."
Ko sallamar Abdulhamid ɗin bata amsa ba, sanda ya ɗaga wayar, kai tsaye ta ce da shi,"Ka turo min da lambar mijin yarinyar nan yanzu-yanzu."
"Wacce yarinya Daada?"
"Abdulhamid wa zance maka ina nemen lambar mijinta idan ba ƙanwarka ba."
Sanin wace Daada, yasa bai ƙar ɗorawa da wata maganar ba. Haka kuma bai jinkirta ba wajen turawa, domin gudun ma kar ta ƙara kiransa ta zazzage shi akan bata wasa da jika. Nan take ya tura mata duka numbers ɗin biyu.
Fullo ta miƙe fuuuu ta nufi bedroom ɗinsu, zuciyarta na bugawa kamar zata fito daga ƙirjinta. Daada ta bita da wani mugun harara tana jan dogon tsaki.
Daada na ta kallon kiran da yake tafiya a wayar. Kiran ya shiga amma bai ɗaga ba. Ta sake kira a karo na biyu, har yanzu shiru.
Sai da ta kira karo na uku sannan ya ɗaga. A lokacin Turaki yana tare da Bello a office. Ganin lambar Saudiyya ce yasa bai yi gaggawar picking ba. Ya ɗaga da sallama a bakinsa.
Daada ta amsa kamar abin arziƙi. Daga can ɓangaren Turaki ya kurɓi ruwa sannan ya ce,"Waye ke magana?"
Daada ta kalli Raudha.
"Munafuka, mene ma sunan shi?"
Baki na rawa Raudha ta ce,"Kamar Turaki na ji suna faɗa."
Daada ta gyara murya sannan ta ce,"Turaki ne?"
"Eh, ni ne."
"Yauwa. To suna Hassana, Kakar Fullo ta wurin uba. Ka shaida?"
Turaki ya gyara zamansa, ya rissina da kai kamar Daada tana gabansa.
"Allah sarki, Daada Ina yini?"
"Lafiya."
Turaki ya shafo wuyansa, wani irin nauyi ya sauka a ƙirjinsa. Ya ji rashin dacewar abin da ya yi tun ranar sadakar uku da ya baro Taraba. Tun daga wannan rana bai ƙara waiwayar garin ba, balle ya waiwayi lamarin Fullo, wadda ya san ya baro a can.
Ya san tana da haƙƙi a kansa. Amma fushin da ya yi da ita ya sa bai jin zai iya sake nemanta, sai idan ita ce ta neme shi. Shi ba lusarin namiji ba ne da zai bari son ƙanƙanuwar yarinya ya riƙa walagigi da shi. Bello ya ce masa ya kwantar da kai ya dinga lallamata, mace ƴar a tarairayeta ce musamman wadda ake neman soyayyarta, amma shi ba ya ganin zai iya yin hakan, a nasa ganin tun da har shi yana sonta to ai magana ya ƙare, ita ma zata so shi, zai koyar da ita hakan.
Shi ya sa ya banzatar da ita da lamarinta. Ya ɗau alwashin cewa indai ba gajiya aka yi aka kawo masa ita ba, shi da kansa ba zai nemeta ba.
Maama ta yi fama da shi har ta haƙura, ta zuba masa ido. Shi yanzu ma ya ji da bala'in Boɗejo na kullum-kullum, da fitinar da ta tsira akan taya Ilham kishi ba dare babu rana. Ta wani fannin ma sai ya ga barin Fullo ɗin a can ya fi masa a'ala a kan ya ɗaukota ya kawo ta nan, domin bai san abin da Boɗejo da Ilham za su iya aikatawa ba. Don wani lamari mara daɗi ya ke wakana tamkar akan sa ne ya fara auren mata biyu.
Sai da ya yi ajiyar zuciya tukunna ya ce,"Daada dama..."
Ta yi saurin katse shi.
"Riƙe dama ɗin ka! Zatonka biko na zo? A'a, ko ɗaya wallahi. Ajinmu da girmanmu ai ya wuce nan. Kiranka na yi dama in sanar maka cewa Kakarka ta kira waya, ta yi mana kowanne irin kalar rashin mutunci."
Turaki ya ji gabansa ya faɗi. Yaushe hakan ta faru? Me yasa Boɗejo zata yi masa haka ne. Ya gyara zamansa yana ci gaba da sauraronta.
"Ta ce muddin Fullo bata rabu da kai ba, to mu kuka da kanmu da duk abin da zai biyo baya. Tace babu batun tarewarta a gidanka. Tace ba zai yiwu daga auren ƴar sarki a ɗauko ƴar aiki ace za a haɗata da ita a matsayin kishiya ba."
Ta ja numfashi, sannan ta ƙara da cewa"Itama matar taka ta kira Fullo, ta faɗa mata ba zata iya kishi da kucaka ƴar aiki ba. Ba zata taɓa yarda a wulaƙanta darajarta da ajinta ba, saboda haka ta nemar wa kanta mafita. To shiyasa na kiraka in faɗa maka cewa ka sakar min jika saki uku rasss."
A yadda kalmar ta shiga kunnensa, har ta haifar masa da girgizar allon ƙirjinsa. Sai ya ke jin kamar bai taɓa riskar kansa a wani hali na tashin hankali ba, da ya wanzar masa da faɗuwar gaba farat ɗaya haka.
Daga duk abin da Boɗejo da Ilham ɗin suka aikata, ransa ya ɓaci, ɓacin ran da har ya haifar da matsewar wani abu a ƙirjinsa. To amma kuma kalmar ƙarshe ta Daada na batun saki, ita ta damƙi zuciyar tasa ta yi mata wani irin mugun matsewa da sai da zafin hakan ya amsa a dukka ilahirin jikinsa.
"Kana ji. Da kai da dukka tawagarka, da ku ka sani ba yanzu ba. Shi yasa har wancan mara kunyar Kakar taka ta iya kiran waya ta min rashin kunya... To Jikata dai Fullo ta fi ƙarfinka, ta kuma fi ƙarfin zaman gidanka."
Daga inda Turaki ya ke ya shafo gefen fuskarsa, yana jin tashin hankali na rufe shi. Damuwa fal a muryarsa ya ce,"Don Allah Daada ki yi haƙuri, wallahi ban san da faruwar abin da suka aikata ba."
Daada ta katse shi da sauri. "Malami tsaya mana. Yo ai ba ƙara na kawo maka ba. Idan ƙarar zan kai ai sai dai gaban alƙali... Ba dogon zancen ma fa na kira mu yi da kai ba, umarni na kira na baka kawai akan ka sakar min jika. Tun da kai ba mahaukaci ba ne na san ka san bata sonka, don haka ba uban da zai tursasa mata zaman aure da kai, balle har a samu wanda ba su kai ba, su ce za su wulaƙantata..."
"Daada don..."
"Ya ilahi! Wai ya ina magana kana katse ni ne mara kunya. Ai ka bari na gama kora maka dukka jawabina ko, tun da gaba na ke da kai, ban yi sa'a da Kakarka ba ma, balle kai haihuwar jiya... Wato kai ga ɗan banza, baka tashi auren Jikata ba sai da ka maki giyarka, tana faɗa maka ba daidai ba, tukunna ka je aka muku kalar wannan watsatstsen auren, zatonka bata da gata ko. To yanzu ka sani da gatanta. Mutuwar ubanta ta bankaɗo mata daraja da ƙima da mutunci."
Magana ya ke so ya sake yi amma dole ya danne, zai bari ne har ta gama ɗin sannan ya bata haƙuri. Zai ta tausarta har sai ta janye furucin da ta yi, don duk abin da za a yi sai dai ayi. Amma Fullo dai kam ba zai saketa ba.
"Turaki, Fullo ba salwantacciya ba ce da za a kaita gidan da wata figaggiyar tsohuwa can zata riƙa kallonta banza a wofi. Gwarama in saboda matarka ne, sai na ce Fullo ta daka shegiya daidai gwargwadon ikonta."
Ta yi shiru na ɗan lokaci, sai ta sake magana da kakkausar murya,"In taƙaita dai, Turaki kake ko waye, yanzu da muke wannan wayar ka rubuta takardar saki uku rerass, ka yo min aikenta. Idan kuma ka ƙi sakar min jika, aradun Allah zan sa a ɗaure kaf zuri'arku. Domin ni bani da kyau. Mutunci ba isata ya yi ba. Dalilin da yasa ma na fata kora maka jawabin abin da Kakarka ta yi kenan, saboda ka shaida mata akwai inda aka fita ɗanyan kai."
Turaki ya rumtse idonsa sosai.
Nan take wani irin ciwon kai ya kama shi. Ya rasa abin da zai ce wa Daada. A cikin rufe idonsa, ya dinga hasko irin jalalar da Boɗejo ta dinga yi wa Maama da Mum, tun daga farkon maganar auren da zancen tarewar Fullo. Cin mutunci babu irin wanda bata yi musu ba. Har da cewa zata sa Baffa ya sake su, su kama gabansu.
Tana ta maimaita cewa Ilham ba zata zauna da kishiya ba. Ita ma ai ita ɗaya ta zauna. Idan ban da son wulaƙanta Ilham ɗin, ya rasa da wa zai mata kishiya sai da Ƴar aikin gidansu, saboda cin mutunci, ƙarshe ma yarinya ƴar mace.
Ai da dai ace wata ƴar manyan mutanen ce Turaki ya aura, ƴar asali wadda ta fito daga tsatso mai kyau, to ko goma zai yi babu abin da zai dameta. Amma akan dai wannan gantalallan auren, zata iya cinnawa kowa wuta a ƙone.
A halin da ake ciki dai sam Turaki ba shi da sukuni. Bini-bini Boɗejo ta kirasa ta ce ya saki ƴar aikin da ya je ya aura a titi.
Ya furzar da iska daga bakinsa, yana ambaton innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. In da ya san haka auren yake cike da rashin kwanciyar hankali, me zai kai shi?
Bello na ta tambayarsa me ke faruwa, bai iya ce masa komai ba, har sai da Dada ta ji shirun ya yi yawa sannan ta ce da shi.
"Baka ce komai ba, sai fa ka sakar min jikata, kai ma ai ba ƙaunarta kake yi ba munafiki algungumi, har da wani cewa tausayinta da taimakonta yasa ka aureta, a gidan uwar wa kake tausayin na ta, yaushe rabon da ka waiwayeta? Ai duk mai hankalin da ya ji kalar wannan auren, ya san na cin mutunci ne, an shirya da wata manufa ne. To aradun Allah ko ka sakar min jikata, ko babbar kotun duniya ta rabani da kai".
A hankali Turaki ya ce,"Ki yi haƙuri don Allah Dada, ba zan iya sakinta ba...".
Ta ɗaga murya wajen saurin katse shi da cewa,"Ashe kuwa za yi jana'izarka nan kusa... Kai ba fa sulhu na kiraka mu yi ba, in sulhun zan nema in kira waccan jarababbar Kakar taka mana, to ka daina bani haƙuri babu shi a tsakaninmu. Ka sakar min jikata kawai, yanda ake jin ka ɗan gwal kai da matarka, itama haka take ƴar gwal, ba daga sama ta faɗo ba".
Ya ƙara cewa,"Don Allah Daada...".
Daada ta yi ɗiff ta kashe wayarta, ta jefar da ita a ƙasa ta yi ɗakinta.
Raudha ta bi bayanta da kallo cike da takaici, yaushe aka siya mata wayar amma tana neman ta kashe mata ita.
*Gombe, 11:00am.*
A lokacin da suka gama wayar da Daada, Turaki ya baro office ɗinsa yana jin kansa duk ya cunkushe.
Bello da ke driving ɗin ya ce da shi,"Kar ka sakawa kanka damuwa, komai zai warware in sha Allah".
Turaki ya kallesa da jajayen idonsa cikin ƙaraji ya ce,"Fisabillahi saboda Mace sai in rasa kwanciyar hankalina, ta ko'ina ji na ke babu daɗi, haba don Allah".
Bello ya sauke numfashi ya ce,"Ba Mace ba ce rashin kwanciyar hankalinka MT, kai ne ka jawa kanka matsalar duk da kake ciki, yanda ka yi gaban kanka a auren nan dole ka fuskanci ƙalubale, in ace da izinin iyayenka ka yi komai wallahi wannan matsalar ba zaka shigeta ba".
"Shiyasa na yi deciding rabuwa da ita ai tunda itama bata sona, but Maama da Mum sun hana, to ni zan haɗa har ita Ilham ɗin na rabu da su, ba zan iya da wannan damuwar ba, ko baccin kirki bana yi Bello".
Ya faɗa daidai da sanda suka ƙaraso bakin gate, Bello ya bushe da dariya. A hankali ya ce,"So ɗin Ayy."
Kafin ya sake yin wata magana tuni Turaki ya fice daga motar ya shige gida. Yana jin abokin nasa na masifa yana ce masa,"Mahaukaci! Bello kai mahaukaci ne, ba zan ƙara faɗa maka matsalata ba, babu ni babu kai."
Haba mai Bello zai yi banda dariya.
A ɓangaren Turaki yana shiga ya yi kiciɓis da Boɗejo a compound tana ta masifa, akan bai bi ta kan Ilham da bata da lafiya ba. Ta tsayar da shi amma bai ko bi ta kanta ba ya yi wucewarsa side ɗin Hajiya Madina, kai tsaye upstais ya haye, yana zuwa ya yi knocking ƙofar, daga ciki Hajiya Madina ta ɗaga ido ta kalla bakin ƙofa kafin ta ce,"Come in".
Ya murɗa handle ɗin ya shiga gabansa na faɗuwa, yana saka ƙafa suka haɗa ido, ba shiri ta ɗaure fuska kamar bata san shi ba, ta ɗaga masa hannu da cewa,"Get back please".
Ya marairaice,"Please Maama i want to talk to you, don Allah ki yi haƙuri akan laifin da ban san na yi miki ba".
Ta ɗauke idonta daga kansa ta ce,"Na ce ka fita ko".
Ya ƙarasa shigowa yana ƙoƙarin zube gwiwoyinsa a ƙasa, ganin hakan yasa ta miƙe zata bar masa ɗakin ba shiri ya rigata fita.
Ya fita yana riƙe kansa da yake jin kamar zai bar jikinsa. Part ɗin Hajiya Ramla ya wuce, tana ganinsa ta ajiye cup ɗin da ke hannunta tana tambayarsa,"Babana lafiya?".
Ta tambaya duk da ta san yana cikin matsala, amma yau ɗin tana ganin ba irin yanda ta saba ganinsa a ciki ba, damuwar ta girmama.
Ya zauna akan kujera yana daɗa riƙe kansa ba tare da ya ce mata komai ba, ta baro dining area da sauri ta zo ta zauna a kusa da shi, ta dafa kafaɗarsa tana cewa,"What is wrong with you Babana? Kai da Boɗejo ne?".
Ya ɗago ido kamar zai yi kuka ya ce,"Maama ce".
"Me ya haɗaka da Maaman taka?".
Ya kwantar da kansa a kafaɗarta, muryarsa ta yi laushi, irin na wanda ya gaji da riƙe damuwarsa shi kaɗai.
"Almost one week fa, Mum ko gaisuwata bata amsawa. Ban san laifin da na yi mata ba wallahi. And ta ƙi ba ni damar ma da zan bata haƙuri. Na mata sending apology through text message and letter, duk ta yi ignoring ɗina. Kuma ina so na yi magana da ita Mum."
Hajiya Ramla na kallonsa da tsananin tausayi ta ce,"Duk ina ina hakan ta faru?".
Ya kama hannunta cikin sanyin murya ya ce,"Kin yi busy da yawa a office Mum, kuma kinga Baffa ya hana ni zaman gidan nan".
Ta sauke numfashi ta ce,"Tashi mu je".
Ya ce,"Mum ko mun je fa ba zata saurare ni ba, korana take yi".
Ta kama hannunsa kawai suka fita zuwa side ɗin Hajiya Madina, suna shiga parlo ita kuma tana saukowa da ga upstairs, ta yiwa Turaki kallo ɗaya ta ɗauke kai ta wuce kan kujera ta zauna, ya bi bayan Mum suka ƙarasa ya zauna kusa da ƙafafun Hajiya Madina.
Hajiya Ramla ta ce,"Maama ayi haƙuri don Allah. Hukuncin ya yi mana tsauri, wallahi rayuwar bata daɗi idan kina fushi da mu. Afuwan ranki ya daɗe, ba zamu ƙara ba in sha Allahu. Ina ta ya shalele ba da haƙuri Hajiya Maama."
Hajiya Madina ta kalleta ta ce,"Bai faɗa miki laifinsa ba?".
Ya yi karaf ya ce,"Ki faɗa min Maama zan gyara. Idan kika ci gaba da fushin mutuwa zan yi Maama".
Ta kawar da abin da furucin nasa ya haifar mata. Nan da nan ta fara masifa tana cewa da Hajiya Ramla.
"Wai yaron nan saboda baida mutunci, yana so ya mayar damu ƙanan mutane, ya je dubai in ce idan sun tashi dawowa ya taho da akwatunan lefa... Shine ya kawo min guda goma sha biyu kacal, ba wannan ba ma! Na ce ya haɗo lefe but sai ya turawa Zaytuna 1ML wai ta siya abin da ta ga ya dace, wato gamu faqararru da miliyan ɗaya zamu haɗa lefe ko? In tambayeka ma! Zatonka Fullo ƴar aiki da ka sani a baya zaka kai wa lefe da zaka kashe 1ML kacal? To in haka ƙwaƙwalwarka ke faɗa maka ta yaudareka, Fullo ƴar aiki daban, Fullon da zaka kai wa lefe daban, in ka manta ka tuna, gidan da ka je ka yi gaisuwar mahaifinta, ka tuna irin mutanen da ka samu, ka san da cewa kenan tafi ƙarfin naira miliyan ɗayanka, Fullon yanzu ƴar gata ce gaba da baya kuma ƴar gidan manyan mutane, beside wallahi ko da ace Fullo tana nan a yanda ka santa tun farko, baka isa ka kawo min lefenta na miliyan ɗaya na karɓa ba, kai ka san da cewa taimakonka da ta yi tafi ƙarfin dukka arziƙin ubanka har da naka. To make it short, ka je ka sami ubanka Alƙali Dikko ka tambayesa lefen nawa suka haɗawa ƴarsu, daga nan sai ka yi abin da ka san zai ɗaga mutuncinmu, ba wanda zai ja mutuncinmu ya zube ba, dan mu ba marowata ba ne".
Kansa a ƙasa ya ce,"Maama ki yi haƙuri amma wallahi bani na tura kuɗin ba, time ɗin naira account ɗina ya sami matsala, kuma kaina ya ɗau caji da damuwar Boɗejo. Shine na sa Bello ya tura mata, kuma wallahi sai da nayi masa magana ya ce ai hakan ya isa wai almubazzaranci babu kyau".
Hajiya Madina ta zare ido tana doka masa tsawa ta ce,"Rufe min baki shashasha, shi Bellon da zai haɗa nasa lefen da 1ML ya haɗa da har ya mayar da kai ɗan iska, me yasa baka tuna masa check ɗin da na basa ya je ya haɗa nasa lefen ba? Ko kuma baka faɗa masa gidan da ka je ka sami Fullo a yanzu ba? To wallahi wallahi ba zan kai iyaka akwatu sha biyu ba, kuma ba zan kai lefen ko miliyan biyu ba, tashi ka bar min parlo".
Ya ɗago ya kalleta kamar zai yi kuka, ya marairace yana roƙonta akan ta yi haƙuri, zai yi yanda take so.
Ta ce,"Fitar min a parlo tun ina ganinka da gashin ido, ai ba iyakarta kenan ba, na ce ka je ka gano lafiyar matarka kaƙi zuwa. Yau kwana hamsin da wani abu, wanne kallo kake so mutanen nan su yi mana? Amma na lura da hakan bai dame ka ba saboda kana tare da zaɓin ubanka a cikin gidanka ko? Ka san baka sonta ba zaka iya sauke haƙƙinta ba me yasa ka aureta, wallahi Allah kamaka zai yi ni babu ruwana."
Ta yi shiru tana sauke numfashi. Kamar ba zata ƙara magana sai kuma ta ce,"Kasan maganganu marasa daɗin da Boɗejo ta zo ta yiwa mahaifiyarka kuwa? Kuma duk akan Ilham, me ta-ke nufi da mu? Auren nan mu ma da muke iyayenka muka haƙura da yanda ka je kayi gaban kanka balle ita, ta bar yarinya ta tare a ɗakinta amma ta hana kowa kwanciyar hankali, ba'a zama da kishiya ita uwar yarinyar ta zauna da kishiyoyi, haba don Allah tun yaushe ake abu ɗaya, abu mitsitsi ya ƙi ci ya ƙi cinyewa, comon tariyar da za'ai lokaci ɗaya a wuce wurin ta hana rawar gaban hantsi, ta bi tasa mahaifinka ya takura maka saboda kai baka da uwar da zata baka umarni ko me? But shikenan zan yiwa tufkar hanci, idan ta san wata ai bata san wata ba, yanda ɗanta yake bin umarninta, haka kai ma zaka bi umarnin taka mahaifiyar, ai uwa bata fi uwa ba".
Ɓacin ranta na ƙara tsananta ta waiga gefenta ta ɗauko jotter, ta falli takarda ta jefa masa da biro ta ce,"Umarni na ke baka ba ja'inja na ce muyi ba, ka saki Ilham saki ɗaya".
Ya yi saurin ɗago kai yana kallonta,"Maama in saketa kuma?".
Ya kulle ido yana jan ajiyar zuciya,"Maama itama fa Fulani Kakarta ta ce sai na saketa".
Ta buga masa tsawa ta ce,"Ba batun Fullo na ke yi ba yanzu, ka fara sakar musu ƴa tukunna".
Sannan ta kalli Hajiya Ramla ta ce,"Umarninki ne a matsayinki na wacce ta ɗau cikinsa wata tara, ta kuma haife shi da wuya bata sauƙi ba, kamar yanda itama take jin ta ɗauki cikin wata tara, ta haife bata sauƙi ba, idan ta cije ki fita cijewa, kin sa ya saki Ilham, kuma ba zai saki Fullo ba. Ayi duk uwar watsin da za a yi. Na gaji da rigimar tsohuwar nan".
Ta ƙara maida kallonta kan Turaki ta ce,"Na ce ka sakar musu ƴa ko".
Babu shiri ya shiga rubutu, _Ni Muhammad Habib Dikko na saki Rumana Hashim saki ɗaya._
Ya gama rubutun daidai da faɗowar Boɗejo parlon, kuma daidai da shigowar kiran Daada a wayar Hajiya Ramla....