KIRAN KADDARA

THE NEW HOME

by @nihaalmaalik

Bayan sun iso gidan hajiya ruqaiya zayd ya fito ya taya ta bude qofa saboda yanayin rigar ta, ya miqa mata hannu ta kama ta fito daga motar, zata janye hannun nata taga ya riqe yanata kallo, shi kanshi besan abnda ya gani a hannun ta ba, amma tun dazu da ya riqe yaji a ranshi chewa babu wanda ze qwache wannan hannun daga gareshi, riqe yake da hannunta daya, dayan hannun kuma yana riqe da snacks din da safiya ta miqo mata, seda ya rakata har kofar dakin da aka tanadar mata sannan ya miqa mata ya wuce shima wurin da ze kwana.

Sauran mutane sun dawo daga walima, bayan dan surutun da ya tashi na masu firar yadda walima ta kasance, wasu sunyi wanka sun kwanta, Gidan ya yi shiru fiye da yadda yake a baya, Yawancin baƙin da suka zo walima sun tafi.

Wasu daga cikin dangin Zaid ne kawai suka rage.

Maryam ta gaji sosai, Tun da suka shiga gidan, aka taimaka mata ta cire kayan walima, tayi wanka aka bata kayan baccee masu laushi tasa, Qawayenta da aka dauko su wasu a nan aka kawo su, hadda hauwa koulou da bahijja, suna tare da ita sunata fira, ta kwanta a hankali, Kwanakin nan sun yi mata tsawo,

Sa Lalle.

Wankin Amarya.

Daurin aure.

Walima.

Gobe kuma Tafiya

Sabon matsayi.

Matsayin Matar Zaid.

Ta lumshe idanunta.

Amma kafin bacci ya ɗauke ta,  tunanin ya sake shigowa zuciyarta.

Gobe za ta tafi Abuja.

Gidan Zaid.

A karon farko za ta zauna da shi a matsayin matarsa.

Ta sauke ajiyar zuciya.

Ya Allah, ka shige min gaba.

Sai taji an banko qofa da karfi se ga muryar safiya tana fadin surprise tana shigowa janye da akwatin ta, maryam ta tashi zaune tana murna, safiya ta sheqo ta rungume ta, “Dr yache inzo in Kwana tunda gobe da safe zamu wuche Abj, ya bani izini in kwana nan kawai”

Maryam tanata jin daadi, suka fara fira har baccee ya dauke safiya da sauran qawayen, maryam ta tashi tayi arwallah ta fara sallah tana yima kanta addua akan sabuwar rayuwar da zata fara, se ta fara tunanin mama ai kuwa kuka ya kucce mata, ynzu wa ze rinqa taya mama aiki? Ita kadai zata rinqa baccee a gida? Tanata tunani kala kala har baccee yayi gaba da ita


Da safe, aka tashe ta tun da wuri, tayi wanka tasa kaya mara nauyi, su safiya se kai da kawo suke suna shirya yadda tafiyar zata kasance, safiya taje tasa aka hado breakfast aka kawo ma maryam da sauran kawayen su da ke dakin, abnci kala kala da sauran abubuwan buqata duka, seda suka tabbatar maryam tachi sannan suka qyale ta, Tana zaune shuru, Ta kalli wurin da take, ta sauke numfashi, toh ai da saukee nan duk cikin sokoto ne, amma anjima kadan fah sokoton gabadaya zata bari,Yau za ta tafi Abuja.

Bayan duk sun qare chin abnci se stylist din jiya suka shigo aka fara shirya ta, yau ba a yi mata makeup ba, Tafi son natural look.

An gyara mata gashi a sauƙaƙe sannan aka daura mata yellow Lafaya mai kyau, Launin ya yi mata kyau sosai, An yi masa ɗan embroidery mai sauƙi, aka rufo mata fuskar ta dashi 

Maryam ta tsaya a gaban mirror, Ta kalli kanta, Ta yi shiru, bahijja ta fara tsokanar ta “ki bari mu hwada miki kinyi kyau base kin kama kallon madubi ba, ai kema kinsan ke din qarshe che indai wurin kyau ne” ina maryam bata ma jinta, ta fadah tunani, Ba ita ce yarinyar nan da ke tashi daga gadonta kwanaki kaɗan da suka wuce ba, Yanzu tana cikin sahun matan aure.

Ta kalli ɗakin da take ciki a hnkali ta furta “shi kuma wanda za’a kaini ko yaya yake?” Bahijja che taga tanata surutu amma kamar maryam batasan tanayi ba, ta matso ta taba ta, ai kuwa tana juyowa suka hada ido se kuka sharr, bahijja ta jawo ta suka zauna ta rungume ta kawai tana shafa bayanta, sauran qawayen ma sukayi shuru dakin yayi tsit. 


A falo, Hajiya Ruqaiya da Mammi suna zaune suna jiran a qare shirye shiryen tafiya, Hajiya raliya ma tana tare dasu, Wasu daga cikinsu ma sun riga sun shirya duka suna zaune, an aika driver yaje gidan su maryam ya dauko wa’inda za’aje Abuja dasu amma se akache ai da anty maimouna da gwaggo kawai su bisu suje ba se anyi taro ba, se kayan gara da aka kwaso, seda kowa ya shirya sannan safiya ta shiga dakin ta tarar maryam na kuka a jikin bahijja, hakuri ta bata sannan ta gaya mata ai su anty maimouna suna parlor, suka samu ta tsagaita da kukan sannan suka gyara mata fuska suka fito riqe da ita 

Hajiya Ruqaiya ta kalli Maryam.

“Ma Sha Allah.”

“Yellow ɗin nan ya yi miki kyau, ko da yake diyar tawa ko me tasa kyau yake mata”

Maryam ta sunkuyar da kai.

Mammi ta zo ta gyara mata lafayar ta rufo mata fuska

“Maryam ynzu zamu bar Sokoto.”

Maryam ta kalli Mammi ta sunkuyar da kai

“Komai zai yi dd In shaa Allah kinji? muje”

A hanya suna mota, Maryam ta kira Mama a waya, “Mama.” Ta fadi cikin muryar kuka, “Na’am meramun mama”

“Zamu tafi airport ynzu.”

“Allah ya kai ku lafiya.”

“Ki kira ni idan kin isa, kukan ya isa haka kinji 

“Zan kira ki.”

Mama ta yi shiru na ɗan lokaci.

Sai ta ce:

“Maryam…”

“Na’am?” Ta amsa da muryar kuka still

“Ki kula da kanki kinji?”

Hawayen Maryam suka gangaro da qarfin su

“In shaa Allah mama”

“Allah ya sanya zaman ki da mijinki ya zama cikin natsuwa da salama”

Ta katse kiran

Maryam ta goge hawayen.

Hajiya Ruqaiya ta matso kusa da ita Ta rungume ta.

“Ba ki bar Mama ba ai . ZaKi riƙa kiranta kullum.”

Maryam ta gyada kai.

A hanyar airport kam motoci ne convoy na gaske

Duka an kwaso kayan maryam har da gara, Maryam tana zaune cikin yellow Lafaya, kanta a ɗan duƙe.

Tana kallon garin Sokoto ta window.

Ta kalli titunan.

Gidaje.

Mutane.

Shaguna.

Wannan garin da ta rayu a cikinsa tun yarinta, Yanzu gashi tana barinsa, Ba don tafiya hutu ta dawo ba, Ba don ziyara ba.

Ta tafi ne zuwa sabon gidanta.

A filin jirgin, wani chartered flight ne yana jiran su.

Kamar tafiyar farko ta Zaid da iyalinsa zuwa Sokoto, ba regular flight suka ɗauka ba.

Ynzu ma Mammi ta shirya musu tafiya cikin sauƙi.

Aka fara shiga da kayayyaki.

Aunty maimouna da gwaggo A’i seda suka tabbatar komai na maryam yana tare da ita.

Zaid ya zo kusa da ita

“Komi lfya ko?”

Maryam ta ɗago kai.

“Lahiya lau” sora Kadan said yayi dariya amma da yaga yanayin yadda fuskar ta da idonta sukayi ja alamar ta chi kuka, Kuma ynzu ma Neman dalili take ta chigaba, se ya gintse dariyar shi kawai, ya sake dan kallonta, Yayi shuru yana lura da Idonta da yayi ja, ga kuma ruwan hawayen da ke kwanche a cikin idon

A cikin ransa yache “subhanallah” sannan ya furta mata

“Muje?”

Ta gyada kai

Ya yi shiru.

Sai ya bata hannu “sauko muje” ta riqe hannun shi ta fito daga Motar, tana son ta qwache hannunta don tana jin kunya amma be saketa ba, yana riqe da ita har suka shiga jirgin, Maryam ta bi shi zuwa wurin da zasu zauna, seda ya taimaka mata ta zauna sannan shima ya zauna, ya saka mata belt sannan yasa nashi, tun da jirgin ya tashi take goge hawaye, yana kallonta yana jin wani iri a ranshi, bayason kuka balle na maccee, kuma shi be iya rarrashi ba, sedai yayita miqa mata tissue kawai, fuskarta tayi jaa sosai Idonta yayi luhu luhu, se ya Kalli yadda take goge hawayen, yaga hannunta, shi dai wannan hannun yana burge shi, besan meyasa ba amma hannunta nada kyau, ya kama hannun ya riqe ya fara murzawa cikin nashi a hnkali, se yaga tanata rage kukan, har ta dena gabadaya se ajiyar zuciya take saukewa, be saki hannun ba yana nan riqe dashi har suka sauka 


Jirgin su ya sauka a Abuja lfya,

Da suka fito, motoci suna waje a jere already suna jiran su.

An ɗauki kayayyakin Maryam.

Aunty maimouna da gwaggo A’i akache su shiga mota tare da ita.

Wasu daga cikin dangin Zaid suka bi bayansu, Wasu kuma suka yimusu sallama suka wuche gidajen su suna fadin se sun shigo ganin dakin amarya, Zaid yana cikin motar da ke gaba.

Motocin suka nufi Balarabe mansion a Katampe 

Maryam tana kallon Abuja ta window.

Babban gari ne.

Traffic.

Manyan gine-gine.

Mutane suna ta zirga-zirga.

Komai ya bambanta da Sokoto.

Ta ɗan matse hannuwan ta

Zuciyarta ta fara bugawa.

Ba don tana tsoron Abuja ba.

Sai dai saboda tunanin inda suke nufa da ita

Gidan Zaid.


Da suka isa gidan Balarabe, gate ɗin aka buɗe a take motocin suka shiga ɗaya bayan ɗaya.

Babban family house ne.

An shirya shi sosai.

Akwai babban compound.

An raba gidan zuwa parts daban-daban.

Kowane sashe yana da nasa privacy.

Maryam ta kalli gidan daga cikin lafayar ta

Sai ta yi shiru.

Mammi ta fito.

Ta zo ta rungume ta.

“Welcome to Abuja, my daughter.”

Su anty maimouna suka fito.

Sai Hajiya Ruqaiya ta fara yimusu bayani

“Ku zo kawai mu kaita part dinta Tayi wanka ta huta, nasan an qare shirya komi by now cooks din ma sun gama jera abnci”

Ta juya zuwa wajen sashen Zaid tana fadin 

“An Riga an shirya muku komai a chan”

Gwaggo A’i ta zaro ido “aa mu zamu ajiye ta da qawayen ta a chan se mu dawo sashen mammi bazamu tsaya tare dasu ba” Anty maimouna ta karbi zanchen “Ai yamma yayi suma qawayen idan sun qare abnda zasuyi se su same mu a bangaren mammi din mu kwana a chan”

Hajiya ruqaiya tayi dariya “toh muje mu rakasu ita da qawayen”


Da aka kai kofar bangaren, sukasa ta tsaya tayi addua ta shiga da qafar dama

Ta kalli wajen ta cikin lafayarta

Komai sabo ne.

Sababbin royal sofas.

Sabon dining set

Sabbin curtains.

Sabbin carpets.

Sabbin kayan deco

Sabbin lamps.

Daga gani sabon tsari akayi ma part din ba yadda yake a da ba

Har bedroom ma an canza komai.

Bed.

Closets 

Dressing area.

Bedside tables.

Komai sabo ne

Hajiya ruqaiya ke fadin wow gaskiya interior company dinnan da mammi Tayi contacting sun san aikin su, komi ya ji dakyau 

Maryam se aikin goge hawaye take cikin lafaya batada lokacin kallon aljannar duniyar da ke gabanta

Hajiya Ruqaiya ta chigaba

“Kitchen, parlour, bedrooms, bathrooms, komai an chanja fah, mammi Batason ki zo ki ji kamar an kawo ki cikin part din tsohon tuzuru.”

 Su gwaggo A’i suka yi dariya sunata yaba kyau da tsaruwar gidan maryam

“Ma Sha Allah.”

Hajiya Ruqaiya Ta matso kusa da ita.

“Wannan gidan fah naki ne yanzu, har da shi me gidan ma” Maryam ta sunkuyar da kai daga cikin lafayar hawayenta na qara gudu, “Ki kula da Kayan ki da mijin ki”

Seda suka kaita har sama dakin da yake matsayin nata sannan Daga nan suka fita suka bar maryam da qawayenta, seda qawayen suka zagaye gidan kaff banda dakin zaid da mammi tache ma masu furnitures idan sun qare su rufe su bayar da key cikin gida, ai kuwa sun ga gida kuma sun ba idonsu abnci 

Maryam tana upstairs a inda aka zaunar da ita a matsayin dakinta ta takure cikin lafayarta, wasu daga cikin su suka shigo sunata yaba kyau da tsaruwar gidan, wasu kuma suna qasa sun zauna a parlor 


A wannan lokacin, Zaid ya shigo tareda abokan shi, sun tsaya parlorn da friends din maryam ke zazzaune, suka gaida su suka ansa, sannan abokan sukache toh a dauko musu amarya, hauwa koulu che ta hau taje tayi ma safiya da bahijja magana suka sauko da ita aka zauna akayi sayen baki,  zayd dai yana zaune shuru ba abunda yache har aka chi aka sude, abokan maryam sun sha mamaki saboda abokan zayd sun basu kuddi fiye da yadda suka buqata don dollars ma suka basu, Sannan sukayi sallama suka fita, Zayd ya tashi ya rakasu sannan ya dawo ya shige dakin shi yabar qawayen maryam a parlor, dama tun da ya fita raka abokan shi Safiya da bahijja suka dauki maryam suka raka ta dakinta tayi wanka ta chanja kaya sannan safiya ta zabo mata rigar baccin da zatasa ta bata ta fara magana, toh maryam mu zamu wuche part din mammi zamu kwana, in kinyi sallolinki kin qare wannan rigar baccin zakisa ki kwanta, hawayen da maryam ta tsayar dakyar suka sake balle mata tayi hugging dinsu, daqyar suka kwantar mata da hnkali suka fita suka batta

Ta dan jima zaune taga zaman beda wani amfani ta tashi tana kalle kalle a dakin se ta hango wata corner da akayi domin sallah, an shinfida carpert din sallah me kyau da kuma shelf da aka aje Qurani da littafan addo’i, take tasa hijab dama tanada arwallah ta kabbarta sallah tanayi tana hawaye.

Zaid kuwa tunda ya shiga dakin shi bathroom ya fada ya sakar ma kanshi ruwan sanyi, ya dade yana shan ruwa sannan ya fito, yana fitowa yaji wayar shi tana ringing ya duba yaga mammi che

“Hello mammi na”

“Zaid yaya?”

Yayi shuru

Mammi tache

“Matar ka tana lfya ko?”

Still be che komi ba

Sai suka yi shiru.

Zaid ya yi dan murmushi kaɗan.

“Mammi ki kwantar da hnkalin ki”

“Ku chi abnci yana nan cooks sun jera muku a dining, ka tabbata ta chi abnci don Allah, kaga tun safe rabon ta da abinci”

“Okay in shaa Allah” 

A wannan lokacin kam zayd ya fada tunanin “wai aure nayi ko reno aka bani?”

Jallabiya yasa se ya fito ya nufi hanyar da yake tunanin nan ne dakin ta, Tayi sallah tana zaune tana kallon dakin da akache nata, Dakin da aka shirya mata, Gidan da za ta zauna a ciki da Zaid.

Sai ta ji motsin mutum a bayanta.

Ta juya.

Zaid ne a tsaye yana kallonta,

Su kaɗai.

A karo na farko.

A cikin gidansu.

Zaid ya kalle ta.

Maryam ta kalle shi.

Su biyu ne kawai.

Zaid ya yi shiru na ƴa seconds yana kallon yadda ta sha kuka fuskar ta jawur ga Qaramin bakin ta yayi pink sosai, ya sauke ido a hannunta, hannuwan nan nata dai ke suke burge shi, tana motsa yatsun alamar tasbihi take, ya dauke numfashi a hnkali ya tambayeta

“Kina lfya?”

Maryam ta gyada kai don tana gudun ta bude baki maimakon magana kuka ya kubce mata

Muje mu chi abnci 

Ta girgiza kai alamar bazata chi ba

Se ya nuna mata gadon

“Toh kwanta ki huta.”

Maryam ta Kalli gadon

Ya fara tafiya, Sai ya tsaya, ya juyo 

“Please kukan ya isa haka kiyi baccee ki huta”

Ta gyada kai

Ya fita ya jawo mata kofa 

Zaid ya tsaya daga wajen kofar dakin 

ya sauke ajiyar zuciya.

A ƙarshe… dai ynzu wannan yar yarinyar matar shi che? Wadda bata wuche ya dauketa ya goya ba, wata zuciyar tache matarka che manah gashi kun sun iso gidan ku, Amma ba ɗayansu da ya san yadda rayuwar da za su fara yi a cikin wannan gidan za ta kasance ba, Maryam ta zo da tambayoyin da take neman ansa, Zaid yanada rayuwarshi da bai shirya rabawa da kowa ba.

Kuma yanzu…

dukansu suna ƙarƙashin rufin gida ɗaya.


Follow this link to join my WhatsApp group: ***


81FDEDD1-B9EA-4B8C-BD0B-4D74CFBCCFAE.png