THE FIRST NIGHT
ABUJA
Maryam ta tashi ta zauna a gefen gadon tana kallon ƙofar da Zaid ya rufe.
Har yanzu zuciyarta tana bugawa.
Ba don yayi mata wani abu ba, A’a.
Sai dai tunanin yadda tayi nisa da mama, su anty maimouna da gwaggo A’i suna nan, su Safiyya da bahijja ma suna nan, amma tasan suma zasu wuche ne su batta a nan, ta fara tunanin wa ze zauna tare da ita nan? Don ita kam bazata iya zama daga ita se shi a gida ba
A Yanzu ita kaɗai ce.
A cikin wani sabon gida.
Tare da wanda ake kira mijinta
Ta kalli ɗakin.
Komai ya yi kyau.
Gadon babba ne sosai, ga pillows suna a jere, curtains ɗin sun yi matching da carpet, akwai ƙaramin sofa a gefe, dressing mirror, wardrobe mai girma, har da ƙaramin fridge.
Har wani dan Qaramin daki akwai a cikin dakin mai dauke da closets da aka cika su da Kaya
Komai ya yi mata kyau.
Amma zuciyarta ba ta kansu ynzu dai
Ta cire hijab ɗinta ta ajiye shi a gefe.
Ta zauna tana share hawaye.
A hankali ta ɗaga wayarta.
Ta duba missed calls.
Babu ko daya
Sai ta buɗe number mama ta Danna kira
Se da ta kutsa katsewa sannan mama ta daga
“Mama na, mun iso abuja”
Mama tayi hamdala tana yimata barka da sauka
“Mama nayi missing dinki” ya fadi cikin muryar kuka
Mama Tayi dariya “maryam Allah ya huta gajiya ya tsare min ke, kukan ya isa haka manah, ki huta ki bari gobe muyi waya” ta yi mata seda safe ta katse kiran, Hawaye suka sake cika idonta, suke fara gangarowa
A can ƙasa, Zaid yana cikin parlour.
Ya zauna shi kaɗai.
Wayarsa tana hannunsa, amma hankalinsa ba a kanta yake ba.
Ya kalli upstairs.
Sai ya sauke ajiyar zuciya.
Har yanzu se tunanin yake cewa akwai mace a cikin gidansa, Baƙuwar mace, Matarsa.
Ya dan yamutsa fuska kaɗan saboda tunanin ya masa wani iri
“My wife.”
Ya faɗa a hankali.
Sai ya girgiza kai.
“Subhanallah.”
Ya tashi ya nufi dining, Abu daya ya tabbatar a cikin kan shi, ya karbi auren nan, kuma ze kula da ita iyakar iyawar shi, baze bari wani abun chuta ya sameta ba in shaa Allah, a dinning Cooks ɗin sun shirya abinci kamar an shirya liyafa.
Rice kala kala, Chicken, grills, beefs, Soups,Fruits, Drinks, Komai akwai
Ya tsaya yana kallon abincin.
Sai ya tuna maganar Mammi.
“Ka tabbata ta chi abnci”
Ya ɗauki waya.
Ya buɗe WhatsApp ɗinshi ya nemo sunan Maryam, Ba komi, basu taba chatting ba, se ya rubuta mata message
“Ba zaki chi abnci ba ko kadan?”
Ya kalli message ɗin.
Sai ya goge
Ya sake rubuta
“Kizo ki chi abnci ko kadan ne”
Ya aika.
A upstairs, wayar Maryam ta yi vibrating
Ta ɗauka ta duba, Zaid ne, be taba yimata magana ta WhatsApp ba, ko text message ma kamar so daya ne ko biyu, ta karanta
Zaid: kizo ki chi abnci ko Kadan ne
Ta kalli message ɗin na ɗan lokaci.
Ta kasa sanin me za ta ce.
Sai ta rubuta:
“Aa Nagode.”
Ta aika.
Ba a ɗauki lokaci mai tsawo ba yache
“Okay.”
Ta sake kallon wayar.
Sai ta yi mamaki.
Shi ma haka kawai zai ce?
Ta yi murmushi kaɗan.
“Mr. Serious.” Ta faɗa a hankali.
Sai ta ji motsin ƙofa.
Ta ɗago kai da sauri
Ba Zaid ba ne, Safiyya ce ta dawo.
“Maryam.”
Maryam ta tashi da sauri.
“Safiyya?”
Safiya ta shigo da ƙaramin jikka.
“Na manta in baki wannan.”
Ta miƙa mata.
Maryam ta karɓa.
“Me ne?”
“Kayan skincare dinki, Da masu gyaran jiki sukache ki chigaba da amfani dasu. Na ga kina kuka dazu kin daga min hnkali na mance ban Baki ba”
Maryam ta yi murmushi.
“Nagode”
Safiyya ta kalle ta.
Sai murmushin ya gushe.
“Kin chigaba da yin kuka har ynzu ko?”
Maryam ta yi shiru.
Safiya ta zauna kusa da ita.
“Maryam…”
“Kin san hwa aure na kinkayi. Ba za ki chigaba da yin kuka haka kullum ba, dama ina chewa ga jakar ki na mance ban baki ba anty maimouna tache inzo in kawo miki daga nan in gani qila ma kina nan kinata kuka, ai kuwa gashi nan, ko kayan baccin da nache in kin qare sallah kisa gasu nan bakisa ba”
Maryam ta yi ƙoƙarin yin murmushi.
Safiya ta riƙe hannunta.
“Ki yi haƙuri. Komai zai yi dai dai”
Maryam ta sunkuyar da kai.
“In Sha Allah.”
Safiya ta tashi.
“Ni zan wuce yanzu, amma tashi ki shirya tukunna” ta miqar da ita ta bata rigar baccin silk che red color me kyau ta tsaya iya gwiwa, maryam ta shiga bathroom ta chnja ta fito, safiya ta tashi ta dauko humra cikin wa’inda ake mata amfani dasu na gyaran jikinta, ta shafa mata sannan ta shafa mata oil perfumes dinta, ta miqe tana fadin Toh se da safe Allah ya huta gajiya
Maryam ta kalle ta.
“Safiyya…”
“Ki kira ni kahin kiyi kwana”
Safiya ta yi dariya
“Toh In shaa Allah”
Maryam ta yi murmushi.
“Ki kwanta ki huta.”
Ta fita.
Maryam ta tsaya tana kallonta har ƙofar ta rufe.
Sai ta sake zaunawa kan gadon
Zaid yana zaune a dining, yaga shigowar safiya ta fitar ta amma ita bata Lura dashi ba
Da dare ya fara yi, gidan yayi tsit
Tana zaune gefen gado
Ta ɗauki wayarta
Ta duba lokaci.
1:15am
Ta yi tunanin ko Zaid yana upstairs ko yana qasa, se kawai taji ƙarar ƙofa daga dan nesa, Motsin ƙafafunsa alamar tafiya na qaruwa a corridor.
Zaid ya tsaya a ƙofar ɗakinta, Ya yi knocking sau biyu, Maryam ta ɗago kai.
“Waye?”
Ƙofar ta buɗe.
Zaid ya tsaya a bakin ƙofa.
Ya kalle ta, tana zaune a gefen gado ta manta rigar baccee kawai che ke jikinta se ynzu, duk ta tsawwala da yadda taga ya kalleta na dan lokaci kafin yayi sauri ya sauke kanshi qasa
“Abinci”
Ta girgiza kai.
Ya ɗan lumshe ido, yana calming din kanshi
“Meyasa?”
“Banajin yunwa” ta fadi cikin muryar kuka
Ya yi shiru, ya lumshe ido, bayason kukan nan shi kam me ze yimata ta dena ne wai?
A hankali ya furta
“Mammi will kill me.”
Maryam ta kalle shi.
A karon farko, ta ji ya yi magana ke kamar wasa
Zaid ya ɗan yi murmushi ganin yadda taga kalleshi
“Sauko downstairs.”
Maryam ta girgiza kai
“Meyasa? Ki chi abnci ko Kadan ne manah mahreeyam”
Ita kam yadda yake kiran sunan ta yana mata daadi
Ta kalle shi.
“Zan ci a nan.”
Ya gyada kai.
“Okay.”
Ya juya, Ya fita.
Bayan mintuna kaɗan, aka sake buga ƙofar.
Maryam ta saka hijab dinta sannn ta bude buɗe.
Zaid yana tsaye da tray a hannunsa.
Ya shigo ya ajiye a ƙaramin coffee table da ke wurin windown dakin
“Rice. Chicken. Fruits.”
Maryam ta kalle shi.
“Nagode.”
Be ansa mata ba se chewa yayi
“Eat.”
Ya juya zai fita.
“Yaya”
Ya tsaya, wai waye yaya? Shi? Se ya juyo
“Naam?”
“Nache Nagode”
Ya gyada kai.
“You’re welcome.”
Ya fita.
Maryam ta kalli tray ɗin.
Sai ta yi murmushi kaɗan, tana fadin Ashe ma yanada kirki
Ta ɗauki spoon.
Ta fara ci.
A ɗakinsa, Zaid yana zaune a gefen gadonsa.
Yanata tunanin, wai Ya yi aure, Ya kawo matarsa gida, tana cikin part dinsa, Amma har yanzu dai gasu nan kamar baqi, ba ya son ya matsa mata, Ba ya son ta ji tsoro, amma yanason ta saki jikinta dashi, ta yadda in akwai wani abu da takeso ko take buqata zata iya gaya mishi, yasan hakan ze dan yi wuya, musamman saboda ya san shekarunsu sun bambanta sosai, gashi ynzu ma wai shi take kira yaya, yayi dariya
Ya ɗauki wayarsa, Ya duba time, Sai ya tuno yadda take kuka jirgi da yadda yaga idanunta da kumburi haryanzu
Ya yi ƙasa da murya.
“Allah kasa kada in chi amanar yarinyar nan, Allah ka bani ikon yin abunda ya dache”
Se ya fara mata typing message
A ɗakin Maryam kuwa, tana cin abinci a hankali.
Sai wayarta ta sake vibrating
Zayd ne:
Kina lfya? Ko kanki yana ciwo?
Ta amsa mishi: lahiya lau, ba abnda ka min ciwo, ta aje wayar
Sai ta ɗaga kanta ta kalli ɗakin, ynzu haka zatayi rayuwa a nan? Ynzu fah dole ta fara koyon zama da mutumin da bata taɓa rayuwa da shi ba, bata ma taba sanin shi ba, Ta sauke ajiyar zuciya, ta tashi ta shige toilet tayi brush ta fito ta hau kan gado Ta kwanta.
Amma kafin ta rufe idanunta, ta tuna wasiƙar nan
KADA KI AURI ZAID BALARABE.
Idonta ya buɗe tarrr
Tana kallon POP a sama
“Me yasa?”
Ta faɗa a hankali.
“Me yasa ka ce kada in aure shi?”
Yasan wani abu Akan Aisha?
Sai zuciyarta ta yi nauyi.
Maryam ta juya ta kwanta.
Amma wannan daren…
ba tambayoyin aure kaɗai suka hana ta bacci ba.
Akwai wata tsohuwar gaskiya da ta shigo da ita cikin gidan.
Kuma ba za ta huta ba har sai ta gano ta.
Follow this link to join my WhatsApp group: ***