KIRAN KADDARA

THE FIRST MORNING

by @nihaalmaalik

Sokoto

Imran ya samu halartar daurin maryam, yana kallon zaid da Jamaar shi tunda suka shigo masallacin, idon shi sunyi jawur kamar an zuba jini a cikinsu, haka ya duqar da kanshi har akayi hudubar jumua aka qare sannan akayi sallah, yana zaune a masallacin, dashi akayi komai a masallacin har aka qare aka daura aure, ya tashi ya tafi yayi musafaha da zayd, yayi mishi Allah sanya alheri, zaid ya amsa mishi yana miqa mishi hannu, a Yayin da suke riqe da hannun juna imran ji yake kamar wuta che ke riqe da hannun shi saboda irin Zafin da yakeji, ji yake kamar ya kama wuyan zayd ya matse shi har numfanshin shi ya dauke ko kuma ya karya wuyan gabadaya, amma sunan Allahn da yaketa ambato a ranshi sukayi tasirin danne mugun tunanin da yake, zayd kam se godiya yayi mishi da murmushi don be sanshi ba, hakanan ya fito masallacin a daddafe be ma gani sosai ya shige gida ya kwanta. 

Ba tareda innar imran akaje kai maryam Abuja ba, saboda zazzabi me tsananin zafi da imran keyi, sannan kuma idan ta tafi babu Wanda ze tsaya gida ya rinqa yimusu abnci

Seda imran ya dauki kwana biyu kafin ya fara dan sakin jikin shi har yana iya chin abnci Kadan, inna da baba har addua suke yimishi cikin ruwa su bashi yasha, a hnkali ya fara warwarewa har ya samu saukee, mamar maryam ma tana kula dashi sosai, akai akai tana zuwa duba shi kuma tana dafa abnci tasa a food warmer taba hauwa koulou ta kai mishi.


Abuja

Da Asuba zayd yazo qofar dakin maryam bayan ya dawo daga masallaci ze tashe ta tayi sallah, yayi knocking amma shuru se ya bude kofar a hankali da sallama be ganta ciki ba, har ze fita se ya hangota a prayer corner Tayi baccee da Qurani a hannunta, ya rufe Quranin ya ajiye, ya dauketa a hnkali ya maidata kan gado ya kwantar da ita, sannan ya jawo quilt ze rufeta se idon shi ya sauka kan hannuwanta da suka fito ta cikin hannun hijab, se ya tsaya yana kallonsu, ya ajiye quilt din ya zauna ya riqe hannuwanta duka biyu yana murzawa cikin nashi, ya riga yayi adkar din safe tun a masallaci amma beyi tasbihi ba ya dawo saboda zazzabin da yake ji, se kawai ya fara tasbihi da yatsun ta, har yayi qa qare sannan ya ajiye mata hannayenta yadda zataji daadin baccin, amma se ta qanqame hannun shi tana jawo shi tana chewa “mama na taho ki kwanta kusa dani please” cikin muryar kuka da shagwaba, yayi dariya qasa qasa yana fadin “Gaskiya wannan yarinyar reno aka bani” 

Da dubara ya gyara ta ya rufe ta da quilt sannan ya fita ya wuche dakin shi, baya jin daadin jikin shi, kamar zazzabi yake ji, ya yanke shawarar zuwa anjima idan yaji still yana jin abnda yakeji beyi saukee ba kawai ze kira dr, ya dauko laptop dinshi ya fara duba emails se kawai ya tuna da yadda yaga tana baccee kan daddumar sallah, da yadda ya dauketa, kamar yadda batada girma hakama batada nauyi, ya tuna hannunta, hannun nan da ya rasa meyasa yakeson su, yayi murmushi kawai yana jin zazzabin na qara sauko mishi, qila stress din hidimar bikin nan ne, ya dan kishingida a gado ya rufe ido.

Hasken safe da ya fara shigowa ɗakin Maryam a hankali ta cikin curtains ɗin da aka rufe rabin su aka bar rabi a bude yasa Maryam ta buɗe ido.

Na ɗan lokaci, ta manta inda take, ita dai bayan tayi sallar Asuba tasan ta kwanta a kan dadduma a Chan prayer corner din dakin, ya akayi ta dawo kan gado?

Ta kalli sama tana kallon qatuwar hadaddar chandelier din da ke maqale, Yau a nan na kwana

Ta juya ta ɗaya gefen, Sabon ɗaki, Sabon gado, Sabon gida, Sai komai ya dawo mata cikin kai

Tana Abuja.

Tana Gidan Zaid.

Tayi aure.

Ta sauke ajiyar zuciya.

Ta ɗauki wayarta daga bedside table.

7:08 AM.

Ta ga messages da yawa.

Safiya,Anty maimouna, Qawayenta, Duka bata duba ba se ta kiran mama direct da tayi don taji ya ta kwana, mama ta daga kiran, “Salamu alaikum mamana kin tashi lfya?” 

“Lfya qalau Alhamdulillah maryam, ya kika tashi?” mama ta tambaya

“Lfya qalau Alhamdulillah mama, Inata kewar ki”

Mama tayi dariya “toh tashi dai ki shirya kahin a hwara shigowa gidanki don nasan ko wanka bakiyi ba” sukayi sallama ta aje wayar

Sai ta buɗe chat ɗin Safiya.

Safiya: Hy Kin tashi kuwa Mrs. Zaid Balarabe? 😂 How was the first night?😂 Mu dai gamu nan zamuje airport zamu wuce sokoto, mammi tache kada muje yimiki sallama don kar mu tashe ki baccee kin gaji dayawa kuma tasan idan kikaga zamu wuche zakiyi kuka, love you take care”

Maryam ta kalli message ɗin.

Ai ko idanunta suka cicciko 

Tayi mata reply:

“Jiya nache ki kirani kahin kiyi Kwana kinka qyale ni, shine ynzu zaki wani che mini kun wuche? In ma wasa kikai toh ki bari”

Safiya ta amsa nan take.

“😂😂😂 Good morning, Anty Amarya.”

Maryam a qufule kawai ta danna mata kira

Tana dauka ta fara magana “ku zo na tashi, kuma kar ma kiche min da gaske kun wuche”

Safiya tayi dariya “wallahi gamu mun iso airport, nan da minti kadan ma jirgin mu ze tashi”

Ai maryam bata sake chewa komi ba kawai ta kashe kiran, ta duba messages din anty maimouna da sauran qawayen ta taga duk sallama suke mata suna chewa sun tafi, se kuma godiya da tsarabar da mammi ta basu” ba wanda tayi ma reply saboda haushi. se hawaye kawai ke zuba a Idonta, seda ta chi kuka me isarta sannna ta miqe daga gadon, taje tayi brush tayi arwallah Ta yi salatu duha 

Bayan ta gama, ta zauna na ɗan lokaci tanaso Tayi addu’a.

Ta bude baki “Ya Allah…”

Ta yi shiru se hawaye 

Ta rasa me za ta roƙa da farko.

Zaman aure?

Sabon gidan?

Aisha?

Zayd?

Mama?

Sai ta ɗaga hannayenta.

“Ka sa komi ya zama alheri a garemu duka”

Ta sauke hannayenta.

Amma kafin ta tashi daga wurin, ta sake tunawa da wasiƙar nan 

KADA KI AURI ZAID BALARABE.

Ta daɗe tana kallon carpet ɗin da take kai tana tunani

Me yasa?

Ta kasa samun amsa, amma a ynzu tanada tabbacin ta chire tsoron komi a ranta, ynzu dai gatanan a cikin gidan, babu kowa tareda ita, dole ta qarfafa zuciyarta ta fuskanci abnda tazo yi, ta tashi ta shiga bathroom, Ta yi wanka ta fito.

Ta sa wata simple gown ta lace mai kyau, ta gyara gashinta sannan ta fito daga ɗakin.

Ta tsaya a corridor, Gidan shiru, Ta fara saukowa stairs a hankali, Da ta isa ƙasa, ta ji motsi daga kitchen, Sai ta nufi wajen.

Akwai cook daga ciki yana shirya breakfast

“Good morning, ma.”

Maryam ta ɗan yi murmushi.

“Good morning.”

“Breakfast is almost ready.”

“Okay.”

Ta kalli dining table.

An shirya komai.

Tea, Coffee, Eggs, Bread, Fruits, Pancakes, Da sauran abubuwa.

Maryam ta zauna.

Bayan ƴan mintuna, ta ji motsin ƙofa.

Ta ɗago kai, Zayd ne.

Yana sanye da simple black trousers da white T-shirt, Hannunsa ɗaya riƙe da wayar shi, ɗayan kuma makullin mota

Ya tsaya da ya gan ta, Maryam ta ɗago kai.

“Ina kwana.”

“Kin tashi lfya mahreeyam?.” Ya fadi yana ƙarasowa wajen dining, kai kawai ta gyada, ita dai yadda yake fadin sunan ta yana mata daadi, Ya zauna opposite ɗinta.

Na ɗan lokaci babu wanda ya ce komai.

Maryam ta fara jin yanayin ba daadi yana mata yawa, Zayd ya ɗauki cup ɗin da ke gabansa ya hada coffee seda ya kai baki ya kurba sannan ya dago zeyi magana, ya kalle ta.

“Kinyi baccee dakyau kin huta gajiya?”

Maryam ta ɗan gyada kai 

“Eh nayi alhamdulillah”

“Good.”

Suka sake shuru

Ya tashi ya zuba mata abubuwan da ke kan table din sannan ya kalleta “tea or coffee” ta amsa da “tea” ya hada mata tea ya ajiye mata tareda abncin a gabanta

Ta fara ci a hnkali 

Sai ya chigaba da magana

“Kin chanye duk abnda na baki jiya?”

Maryam ta kalle shi.

“Kadan na rage”

Ya gyada kai.

“Good.”

“Nagode.”

“Ya dan daga gira alamar godiyar ta mi che?”

“Da abncin da ka kawo min”

Zayd ya kalle ta na ƴa seconds.

Sai ya mayar da hankalinsa kan coffee dinshi ya kurba sannan ya furta

“You’re welcome.”

Bayan breakfast, Maryam ta zauna a parlour, Idonta cike da hawaye, qiris take jira su fara zubowa, Zayd kam daki ya koma yana jin jikin se a hnkali. 

Ita dai Tanata kallon gidan daga nan zaune, Yanzu da rana ta hasko komai, sai ta fara ganin abubuwan da ba ta lura da su jiya ba.

Manyan  windows.

Bookshelves.

Frames

Akwai wata doguwar hallway da ta haɗa wasu dakuna a qasan 

Ta kalli stairs ɗin se ta ganshi yana saukowa, ta sunkuyar da kai, Ya tsaya ya dan kalleta

“Kin zagaya kinga yanayin gidan ki?” Shi kanshi seda maganar ta yimishi wani iri bayan ya fadi

Maryam ta kalle shi.

“Ta girgiza kai”

“Okay, muje in nuna miki”

Ya fara tafiya, Maryam ta tashi ta bi shi.

Ya nuna mata kitchen.

“Kitchen ɗin nan mostly cooks ne suke amfani da shi. Amma idan kina son ki yi wani abu da kanki, se ki shigo kiyi.”

Ta gyada kai.

Sai ya nuna mata wani ƙaramin sitting area.

“Wannan kawai dan wurin zama ne, qila idan kinyi baqi masu yara bakiso su bata miki parlor,

Suka ci gaba da tafiya yanata nuna mata, Akwai guest rooms, Akwai ƙaramin office, Akwai prayer room, Akwai garden a bayan gida, inda take hangowa ta window din parlorn 

Zaid yana tafiya a gaba, yana nuna mata abubuwa cikin nutsuwa.

Maryam tana biye da shi.

Sai suka isa wata ƙofa.

Zaid ya buɗe.

“Wannan office ɗina ne na cikin gida

Maryam ta kalli wajen.

Office ne mai girma.

Babban desk.

Computers

Books.

Files.

Shelves.

Komai a tsare sosai

Maryam ta tsaya bakin ƙofa.

“In shigo?”

Zayd ya kalle ta.

“Bismillah”

Ta shigo, Ta kalli bookshelves.

Akwai littattafan business.

Technology

Real estate.

International trade.

Ta kalli ɗaya daga cikin books din.

Amsterdam Business Review.

Sai ta kalli Zayd

Ta sake kallon office ɗin taga signage din da aka rubuta sunan kampanin

“Meridian Axis Group…” ta furta

Zaid ya kalle ta.

“Kinsan kampanin ne?”

“Aa inaga kamar na taba jin sunan ne kawai.”

“Okey”

Da suka fito daga office ɗin, wayar Zayd ta yi ringing.

Ya duba.

Fahad.

Ya ɗaga.

“Hello.”

“Bro.”

“Naam?”

“Ya first morning?”

Zaid ya kalli Maryam.

Ta yi kamar ba ta ji ba.

“Lfya qalau”

Fahad ya yi dariya a ɗayan gefen.

“Fine kawai?”

“Fahad!”

“Okay, yi hakuri dama na shigo wurin mammi tache in kira tanaso taji ya kuka tashi.”

Zaid ya yi shiru.

Fahad ya sake tambaya 

“Maryam fa?”

Zaid ya kalli Maryam.

“Tana lfya.”

“Good.”

“Mammi tache in gaya maka Ka kula da ita”

Zaid ya dan yamutsa fuska

“Na ji”

“Se anjima”

Kiran ya katse 

Zaid ya ajiye wayar.

“Fahad ne yana gaida ke”

“Ina ansawa, zanje in gyara kayana”

Kai kawai ya gyada mata ta fara hawa sama

Se wani tunanin ya fado mata, Fahad yache mata yasan Aisha, Toh ko shi zata fara tambaya ne?

Sai ta tambayi kanta:

Shin Fahad ya san wani abu? Idan be sani kuma ta tambayeshi ai daga nan zata iya sashi ya fara zargin ta

Har rana ta yi, Maryam tana zaune a ɗakinta tanata gyara kaya, Akwatunta har yanzu bata gama buɗewa ba, bataso a tayata tafison Tayi arranging komai yadda takeso, Ta buɗe ɗaya daga cikin boxes, Wasu kayan da safiya ta hada mata ne a ciki, Sai ta ga wani ƙaramin envelope ya fado, Ta ɗauke shi, Na Aisha ne, saboda rubutun kanshi na Aisha ne, Maryam ta kalli ƙofar ɗakin, ta ganta a rufe, Ta zauna a gefen gado, Ta buɗe envelope ɗin a hankali, Akwai ƙaramin paper a ciki, Rubutun Aisha ne tabbas, Maryam ta gane handwriting ɗinta nan take, Ta fara karantawa.

“Tabbas akwai wani abu da ba daidai ba dake faruwa a cikin iyalan Rahman Balarabe”

Zuciyar Maryam ta buga, Ta ci gaba da karantawa

“Amma sai na samu hujja tukuna kafin in gaya wa kowa… domin idan abin da nake zargi gaskiya ne, to wannan zai sauya komai, kuma akwai wani abu da har yanzu ban gano ba…”

Maryam ta tsaya, Hannunta ya fara rawa, Ta juya paper ɗin, A baya akwai wasu kalmomi.

“Northern Crest Holdings.”

“Old land records.”

“Rahman Balarabe.”

Maryam ta lumshe ido.

Rahman Balarabe.

Mahaifin Zaid kenan

Sai ta ji kamar numfashinta ya tsaya na ɗan lokaci, Ta sake karantawa, A ƙasan paper ɗin, akwai date.

Three years ago.

Maryam ta riƙe paper ɗin sosai.

“Me kika gano ne Aisha?”

Ta faɗa a hankali, Sai aka buga ƙofar.

Maryam ta yi saurin ɓoye paper ɗin ƙarƙashin pillow.

“Waye?”

Muryar Zaid ta shigo dakin daga waje.

“Zayd ne”

Maryam ta yi saurin ɗaukar envelope ɗin ta saka shi cikin drawer.

“Bismillah”

Ya buɗe Ƙofar a hnkali ya shigo, Ya kalle ta.

Ta lura da yanayinsa ya ɗan canza kamar beda lfya shima kallon yanayinta yake kamar a tsorace take 

“Me ya faru?”

Maryam ta girgiza kai.

“Bb..bb..bakkomai” ta fadi a rarrabe

Zaid ya sake kallon ta.

“Kin tabbata?”

“Eh”

Ya yi shiru.

Sai ya ce:

“Mammi tache muje part dinta anjima muyi dinner a chan.”

Maryam ta gyada kai.

“Okay.”

Zayd ya juya ze tafi, Sai ya kuma tsaya.

“Mahreeyam.”

“Naaam?” Ta ansa tana qara jin yadda yake kiran sunanta yana mata daadi

“Akwai abnda kike buqata?”

Ta kalle shi, Na ɗan lokaci, kamar tache inaso in tambayeka gameda mahaifinka, Game da Northern Crest, Game da Aisha, Amma ta tuna.

Ai besan abin da ta zo nema ba, besan dalilin da yasa ta aure shi kenan ba

Sai ta girgiza kai

“Aa ba komai”

Zaid ya gyada kai.

“Okay.”

Ya fita.

Maryam ta jira har ta ji ƙofar ya rufe kofa 

Sai ta buɗe drawer ɗin, Ta fito da envelope ɗin, Ta kalle shi.

A yau ta samu abu na farko da zai iya kai ta ga amsar da take nema.

Northern Crest Holdings.

Old land records.

Rahman Balarabe.

Ta ɗauki wayarta,Ta buɗe notes, Ta fara rubutu

Abubuwan da Aisha ke bincike

  1. Northern Crest Holdings
  2. Old land records
  3. Rahman Balarabe

Ta tsaya, Sai ta ƙara rubuta

Meyasa Aisha ta bache?

Ta ajiye wayar 

A waje, Zaid yana tafiya a hnkali ze shiga dakin shi, Bai san cewa matar da ya auro Maryam ta riga ta fara neman gaskiyar da iyalinsa suka ɓoye shekaru da suka wuce.

Kuma wannan karon…

ta riga ta samu sunan da za ta fara bincike akai


Follow this link to join my WhatsApp group: ***


794F838E-ADEB-4F2B-B78B-E3202D2F2DE3.png