KIRAN KADDARA

THE WARNING

by @nihaalmaalik

ABUJA 

Washegari da safe, Maryam ta farka da wani irin yanayi da ba ta saba da shi ba, ita bata farin ciki, haka ma bata bakin ciki, Gatanan dai kawai

Ba kamar yadda ta saba tashi baccee a gida ba,

A can, ko kafin ta buɗe ido, tana jin muryar Mama, ko wasu sun shigo cikin gida wurin mama

Amma yanzu…Shiru.

Ta kalli gefen gadon.

Babu kowa, ita kadai babu ko motsi

Ta zauna a hankali, ta miqe tsaye

Ta leqo kofar dakin ta

Ta kalli ƙofar ɗakin Zaid da ke can gefe.

A rufe take

Ta yi shiru na ƴa seconds.

Sai ta koma dakinta ta rufe 

Bayan ta yi wanka, ta fito cikin simple Riga half boubou da pencil skirt kanta babu dankwali

Zata sauka downstairs se kofar dakin zaid ta bude, ya fito sanye da jallabiya cream color ya kalleta, ta gaida shi, be amsa ba yayi shiru yana kallon Gashin kanta, ta manta sam batasa dan kwali ba, se jin tayi yana chewa “meyasa kikesa extension a Gashin ki?” Tayi shuru ta kasa ansawa, ya chigaba “kije ki chire shi banason ganin anasa extension duk yadda gashin ki yake ki gode Allah” ta ansa ta “toh”

 “Daga chan ki saka veil kizo muje part din mammi, jiya kinche mata wurinta zamuyi breakfast” batache komai ba ta juya ta nufi dakinta, yana nan yana tunanin dama curly hair din da ke saukowa daga gaban goshinta extension ne? Shi da yake Allah Allah watarana ya kai hannunshi ya taba, Meyasa zata saka extension toh? Ai extension baya sallah se kuma wata zuciyar tache mishi wannan qaramar yarinyar tasan abnda ke sallah da wanda baya yi ne? yayi tsaki qasa qasa ya tsaya nan ya jirata ta fito sanye da veil ta rufe kanta, suka wuche part din mammi

Da suka shiga parlour, ta ga Hajiya Raliya zaune ita kaɗai.

Zaid ya gaidata ya hau upstairs ya nufi dakin mammi

Maryam ta gaida ta itama

Hajiya Raliya ta ɗago kai.

Ta kalli Maryam fuska ba walwala

Bata amsa gaisuwar ba se chewa tayi 

“Kin tashi lfya?”

“Alhamdulillah”

Maryam ta zauna a wani sofa.

Hajiya Raliya ta kalle ta.

“Maryam.”

“Na’am?”

“Ki yi hankali a zaman ki gidan nan”

Maryam ta kalle ta.

“Da me?”

Hajiya Raliya ta ɗan tsaya.

Sai Chan ta ansa

“Da komai.”

Maryam ta yi shiru.

“Ban gane ba.”

Hajiya Raliya ta gyara zaman ta.

“Ba komai bane ake buƙatar ki gane, ki kauda ido kan abnda be dame ki ba”

Maryam ta kalle ta sosai.

“in shaa Allah hajiya”

Raliya ta ɗauki wayarta.

Ta buɗe screen ɗin tana dannawa kamar ba ta son ci gaba da maganar.

Maryam ta zauna tana tunani.

Me take nufi?

Daga upstairs Zaid ke saukowa daga dakin mammi, ya kalli Maryam.

“Har kin chi abincin?”

“Aa”

“Muje dining din, mammi na zuwa”

Maryam ta tashi ta bishi

Hajiya Raliya ta dan kalle su suna tafiya, Idonta ya bi Maryam har ta ɓace daga parlor ta shiga dining, Sai ta sauke ajiyar zuciya.

Mammi ta qaraso dining din, a riga an shirya komai nw breakfast din an ajiye a dining, maryam ta gaidata ta ansa mata cikin kulawa tana tambayar ta ya ta kwana? zasu fara cikin abunci se ga anty fati da anty Hadiza sun qaraso dining din, ita hajiya raliya chewa tayi a kai mata nata a parlor, anty Hadiza ta diba taje ta kai mata se ga Fahad ya qaraso, suka zauna sunata gaisawa suka fara chin abnci 

Fahad ya Kalli yayansa 

“Ina kwana, newlyweds.”

Maryam ta yi murmushi.

“Ina kwana.”

Zaid ya harare shi

“Fahad.”

“Okay, okay nayi shuru”

Mammi ta yi dariya, Su anty fati ma sukayi dariya 

“Ka barsu su ci abinci.”

Breakfast ya fara chi a hnkali kamar baze sake magana ba, Maryam ta natsu taha chin abnci, Sai Fahad ya tambaye ta:

“Anty Maryam kin fara son Abuja ynzu ko?”

Ta yi murmushi.

“Har yanzu ban ga komi ba ai”

Fahad ya gyada kai.

“Then zamu fita yawo, zan kai su anty fati airport daga chan zan nuna miki gari”

Maryam taji daadi zata fita waje 

Zaid ya harare shi.

“Bazata fita yau ba”

Fahad ya yi dariya.

“Meyasa? Zaman gidan ze isheta ai”

“Zan fita da ita”

Maryam ta kalli Zaid.

Fahad ya ɗaga gira.

“Toh dama haka ya kamata ai.”

Mammi ta yi murmushi.

“Yaushe ka fara son fita in ba aiki ba zaid.”

Zaid ya yi shiru.

Anty Hadiza tayi murmushi “ynzu ai yanada wadda zata taya shi yawon shiyasa”

Maryam ta sunkuyar da kai tana murmushi.

Bayan breakfast Fahad yache ma su anty Hadiza idan sun shirya su kirashi, sukache a shirye suke kayansu kawai za’a hau sama a dauko musu, yache toh ze jirasu a mota, 

Zaid ya tashi ya kalli maryam “tashi muje ki shirya”

Yayi sallama da su anty Hadiza ya fita bayan ya gayama mammi zeje ya shirya ya fita, itama maryam tayi sallama da Su anty fati, tana jin a jikinta zata dan ji kewar su, ta sallami mammi tabi bayan zaid

Ko da ta fito yana tsaye yana jiranta be che komai ba ya fara tafiya tana bin shi har suka isa part dinsu, dakinta ta shige shima ya shiga nashi, Bayan dan lokaci Yayi mata knocking kofa ta bude

“Zanje office.”

Maryam ta kalle shi.

“Office?”

“Eh”

“Branch dinku na nan?”

“Eh”

“Akwai abnda kike buqata kafin in tafi?”

Maryam ta girgiza kai.

“Aa”

“Okay.”

“Kada ki zauna ki wuni a daki, ki fito parlor kiyi kallo ko wani abu.”

Maryam ta kalle shi, kamar tache dama bazaka fita dani ba kuma ka Hana a fita dani? Se Tayi shiru tana qoqarin danne kukan da ke taso mata

Maryam ta kalle shi har ya sauka qasa tanaji ya bude kofar parlor ya fita, daga nan ko hawaye suka fara aikinsu, tana arranging sauran kayanta tana kuka har ta qare, ta dauki waya ta kira mama

“Salamu alaikum mama Ina yini?”

“Lfya qalau maryam, kuna lfya? Ya me gidan ki?” 

Se ta tuna da abnda yayi mata “Yana Lfya” ta ansa sannan ta tambayi mama “mama ba ke kadai che a gida ba ko? Anche an baki yara, dawa dawa halan?” 

“kawun ki yabani me sunanki don ta tayani zama, antyn ki maimouna ma ta barmin hauwa kafin hutun su na makaranta ya qare”

“Mama suna tayaki aiki ko?”

Mama tayi dariya “kedai ki kula da kanki kinji? Allah ya yimiki albarka, bari in tashi in shirya hita zanyi” sukayi sallama ta kashe wayar, ta sauke qasa Ta zauna a parlour, Ta ɗauki wani littafi da ta gani a wurin tana budewa Amma hankalinta baya kan littafin.

Maganar Hajiya Raliya ta dawo mata.

Ki yi hankali.

Da komai.

Ba komai bane ake buƙatar ki gane.

Maryam ta rufe littafin.

Ta tashi, Ta nufi kitchen.

Ta tsaya tana kallon cooks suna aiki suka gaisa

Daga nan ta nufi garden ta qofar kitchen din 

Gidan yana da babban garden a bayan compound.

Tanata tafiya a hnkali tana tunani

Sai ta ga wata hanyar da take kaiwa wani side na bayan compound din, Ta tsaya, Ta kalli wajen na dan lokaci, daga chan qarshe Akwai wata ƙofa qarama a wurin, kamar a rufe take, Maryam ta matso kusa, Ta lura akwai CCTV camera a saman, Ta tsaya.

Sai ta ji muryar mutum a bayanta.

“Maryam.”

Ta juyo

Haj Raliya ce.

Maryam ta yi murmushin yaqe kaɗan.

“Hajiya.”

Haj raliya ta kalli ƙofar.

Sai ta kalli Maryam.

“Me kike yi nan?”

“Ba komi. Ina yawo ina ganin gida ne.”

Hajiya Raliya ta matso kusa.

Ta yi magana cikin nutsuwa.

“In zakiyi yawonki ki dena isowa ta nan.”

Maryam ta kalle ta.

“Akwai wani abu a wurin ne?”

Haj Raliya ta yi shiru.

“Ba komai wurin”

“Toh meyasa bazanje ba?”

Hajiya Raliya ta kalle ta sosai.

“Saboda ba duk ƙofar da kika gani ba ce ze zama dole ki buɗe.”

Maryam ta yi shiru.

Hajiya ta ƙara:

“Kada ki shiga abin da bai dame ki ba maryam

Maryam ta ji zuciyarta ta buga.

“Amma…”

Haj Raliya ta katse ta.

“Ki ji ni ko?”

Maryam ta yi shiru.

“Ki kula da kanki.”

Ta juya ta fara tafiya.

Maryam ta tsaya tana kallonta.

Me ke ciki? Tayi maganar a ranta


Da yamma, Zaid ya dawo.

Maryam tana parlour zaune parlour 

Ya shigo yana ɗauke da laptop bag.

“Salamu alaikum”

Maryam ta ɗago kai.

“Wa alaikas salam”

Ta tashi ta karbi jakar shi 

Ya kalle ta, yana jin wani iri, wai shi ya dawo gida aka karbar mishi jaka?

“Nagode”

Ta ajiye bag ɗin, taje ta dauko ruwa da glass cup ta zuba ta bashi yasha taje ta maida sannan ta dauki jakar ta hau sama ta bude dakin shi, tana bude qofar qamshin turaren shi ya cika hancinta, gabadaya dakin qamshin shi yake, se ta manta da jaka tazo kawowa ta tsaya tana kallon dakin, komai na dakin cream color ne, dakin ya hadu kuma ya tsaru matuqa, sauri tayi ta aje jakar ta juya ya fito ta dawo parlor, ya lura da yanayinta tun da ya shigo, 

“Lfya kike?

Maryam ta yi shiru.

“Lahiya lau”

“Akwai abunda ya faru?”

“Aa”

Zaid ya kalle ta.

“Kin tabbata?”

“Eh”

“Abnci fah? Zaka chi ynzu? Yana dining”

Ya tashi ya nufi dining 

Ta zuba mishi abnci ya fara chi ya tambayeta ita fah? Tache ai bata dade da tachi ba

Sai ta tambaye shi

“Yaya”

Ya dan matse fuska

“Naam?”

“Akwai wata qofa da na gani a bayan garden”

Zaid ya ɗan tsaya da abncin da yake chi 

“ kofa?”

“Eh, Wata qarama haka.”

“Me ya faru?”

“Na ganta ne kawai.”

Zaid ya kalle ta.

“Kada kije ta wurin, kawai kiyi yawon ki a garden ba ta side din ba”

Maryam ta lura da canjin muryarsa.

“Meyasa?”

Ya yi shiru.

“Saboda bata cikin part dinmu.”

“Okay?”

Maryam ta gyada kai.

“Okay.”

Ya chi gaba da chin abnci a hnkali 

Amma Maryam ta lura, a karo na farko tun da ta shigo gidan…

Zaid ya guji ba ta amsar wata tambaya da tayi

Da dare, Maryam tana cikin ɗakinta zaune cikin prayer corner

Ta buɗe notes ɗinta na waya Ta rubuta:

Hajiya Raliya — ta yimin warning.

Bayan garden — qaramar qofa a rufe

Zaid ma ya guji bani ansa

Ta tsaya.

Sai ta kuma ƙara:

Meyasa?

Ta ajiye wayar 

A gefe guda kuma, Zaid yana cikin office ɗinsa na cikin gida

Ya zauna yana aiki.

Amma hankalinsa ya koma kan abin da Maryam ta tambaye shi.

wannan qofar

Ya sauke ajiyar zuciya.

Ya san wannan tambayar ba za ta tsaya nan ba.

Maryam ba irin mutanen da za su ga abu su qyale ba che 

Shi ya lura da hakan tun ranar da ya fara Lura da ita, ya kula Tana lura da komai.

Kuma yanzu…ta fara lura da abubuwan da be kamata ba, shi tun tashin shi yasan dai babanshi yana ajiye records da abubuwa a cikin wurin, babu me shiga se shi kadai, koda wasa su basu taba zuwa wurin ba

A can wani sashe na gidan, hajiya Raliya tana zaune ita kaɗai a dakinta a zaune, Ta kalli wayarta, Ta buɗe wani contact, Ta tsaya, Ta kasa kira.

Sai ta ajiye wayar.

“Ya Allah…”

Ta faɗa a hankali.

Amma abin da Raliya ke tunani 

Kamar fah Maryam ba za ta daina bincike ba.

Kuma ƙofar da aka ce kada ta buɗe…

ita ce ƙofar da zuciyarta take ingizata sanin abin da ke bayanta.


Follow this link to join my WhatsApp group: ***


1FF413D5-DCB4-41CA-9579-6E06AC5CD780.png