FARAR TUMFAFIYA

Page 5

by @ummuaffan

‎...FARAR TUMFAFIYA.
‎
‎
‎
‎©UMMU AFFAN
‎

Ina masu buƙatar kyawawan atamfofi da  lace, mayafai, shoes and bag. Tare da kyawawan kayan kitchen na 'yan gayu masu kwaliti, zaku iya tuntuɓar ASHNURR COLLECTION wacce ke Kano kwari market domin ƙarin bayani ku tuntuɓeta a lambar waya kamar haka *** Tana aika kayanta ko ina a cikin aminci.

Shin kuna da labarin AK ASHKAD COLLECTION to ku matso kusa ku ji, ita ce wacce take kawo muku kyawawan  abayas na gani a faɗa na shiga ko wanne guri kai tsaye, haka tana kawo muku  kitchenwares masu kyau da aminci cikin farashi mai rahusa zaku iya tuntuɓarta a 070444564938 ko *** shafinta na Instagram ashkad_collection adireshinta Daura, Katsina State tana aika kayanta ko ina cikin aminci.


‎
‎Page *5*
‎
‎
‎
‎Yayyafin da aka soma ya fara sauka jikinta ne ya dawo da ita hayyacinta, Da sauri ta miƙe ta fara yayumar shanyarta kafin ta shige ɗakin Andi da sauri ganin lokaci guda ruwan ya sakko, sai dai cak ta tsaya jikinta na rawa ga kaya niƙi-niƙi a hannu sakamakon wata tsawar da Kawu Balarabe ya buga mata tana shugowa parlourn.
‎
‎"Mugun halin iyayenki ai daman ba zai taɓa bari kiyi abin ƙyirki ba, kizo ki sakar mini kurwar ɗa kafin in illata ki!"
‎
‎Girgiza kai Barirah take hawaye na zuba kamar an buɗe ruwan fanfo. "Kawu ba ni ba ce, ban san komi ba game da abin da ya sami Yaya Usman, wallahi ban san komi ba." Ganin yadda jikinta ke rawa sosai kayan hannunta ma sai faɗuwa suke ba tare da ta lura ba, da sauri Iyah tazo ta rungumeta, ai kuwa nan take ta rushe da wani gigitaccen kuka.
‎
‎"Ka gani ko? Kome yarinyar nan take yi Sabuwa ce ke ɗaure mana baya, to ni bazan yarda a kassara mini ɗa a banza ba, ko ka ɗauki mataki ko ni da kaina na illata yarinya."
‎
‎"Haba Rakiya! Idan hannunka ya rufe ai baka yankewa ya yarda, Barirah taku ce ni banga amfanin wannan mugun ƙulli da baƙin zare ta kuke ƙulla mata ba, har yanzu Barirah yarinya ce ƙarama da ke son tallafa da koyi daga iyaye, shin daidai ne a matsayinta na 'yar yayar mahaifiyarki wacce ta riƙe ki kuma ƙanwa ga mijinki ta kasance a haka?"
‎
‎Ta dubi Kawu idanuwanta na zubda hawaye.
‎
‎"Shin daidai ne kai a wurinka ɗiyar ƙanwarka ta kasance haka a cikin gidanka? Balarabe kayi nazari kayi tunani kafin yanke hukunci, Barirah ba ta da kowa a yanzun da suka fiku, kar wani maƙyirci ko hasashen da babu tabbas ya sa ka aikata mata wani mummanan abin."
‎
‎"Kiyi mana shuru Sabuwa, domin ke baki san komi ba, Barirah da ki ke ganin yaɗin mage ce da kowa ya sha ta sai ya yi amai, kuma kara da kiyashi ɗaukar mara sani irinki!"
‎
‎Cewar Andi cikin tsawa da ƙaryata kalaman Iyah don kar ma Kawu ya fara hasashen yafiya ga Barirah akan abin da ita da shi duk sun sani ita ce silar komi.
‎Ƴ
‎"Daman bazan yanke hukunci kai tsaye ba, fatana kawai ta saki Usman ya dawo hayyacinsa, yaro mai kazar-kazar yaro mai ƙoƙari da neman na kansa shine zai dawo haka!"
‎
‎Jin furucin Kawu Andi ta shige ciki fuuw kamar kumurci tsabar fushi, Kawu ya dubi Barirah ransa ɓace ya daka mata tsawa.
‎
‎"Zaki sake shi ne ko sai kinyi taurin kai irin na uwarki ne, don daman barewa ai ba zata yi gudu ɗanta ya yi rarrafe ba, ke idan ban da imani da jini har zan iya riƙonki ne? Ko ki dawo da rayuwar Usman yadda take ko na faɗawa mutanen unguwar nan tarihi ya maimaita kansa, a ƙone ki da rai kowa ma ya huta!"
‎
‎Iyah ta saki Barirah daga jikinta, ta fice yayin da Barirah ta zube a gurin tana rantse-rantsen ba ta aikata komi akan Usman ba, sai dai ihu da ƙururuwar Saudatu ne ya dawo da Iyah parlourn yayin da Andi ma ta fito daga bedroom ɗinta ita ma kamar an jehota daga sama.
    ‎Gabaɗaya suka yi kan Saudatu wacce ta fara ihu da nannaɗewa kamar macijiya, tana wani irin ihu duka jikinta yana lanƙwashewa ga wata kumfa kamar ta dafin maciji na fita daga bakinta, girgizata suke Andi na ihun kiran sunanta amma ba amsa, lokaci guda tayi wata miƙa sai ta sandare rai ya fita daga gangar jikinta. Ƙururuwa da ihu Andi ta saki da gudu ta nufi Barirah wacce ke duƙe inda Iyah ta bar ta ba tare da ta miƙe ba, tun da ta hango yanayin da Saudatu ke ciki ta ƙara ƙasa da kai ta rasa ma wacce duniya take ciki.
‎
‎
‎DK
‎Yana zuwa bayan ya yi buƙatunsa a makewayi da ke masallacin alwala ya ɗaura ya shige da sauri don har ana niyyar tada sallah, bai fito ba ko da aka idar ya zauna yana ta lazumi da addu'o'insa har aka kira Isha'i, bayan sun idar fitowa ya yi zuwa gida, kai tsaye ya shige cikin gidan nasu har ɗakin Inna.
‎   Zaune ya iske su da ƙannansa Maryam da Ummul suna cin abinci a faranti guda su ukun duka, ya kalli abincin shinkafa ce dafadukar manja ta haɗe ta wani chaɓe sosai da ita, sai dai yaji a ransa gidajen masu kuɗi da mangyaɗa suke girki amma su 'ya'yan malam Shehu yawanci girkinsu na manja ne, kuma zaka ga abincin masu kuɗi washar-washar da shi su kuwa nasu a caɓe, ko da yake ya taɓa tambayar Inna me yasa abincin ke chaɓewa ko tana cika ruwa ne? Sai ta ba shi amsa da idan an cika ruwa abincin yafi auki kuma ita idan za tayi dafaduka tana saka daddawa kuma ma dai tafi jin daɗin ganinta a haka, wai masu yi tayi washar-washar wata ma ko dahuwa ba tayi, har Ummul na saka musu baki a ranar tana faɗin, sai dai idan mutum bai iya dahuwarta ba ne, amma ana dafa shinkafa da taliya suyi ɗai-ɗai kuma sun dahu kawai dai Inna tana musu girkin tsofaffi ne mai daddauwa da su citta, yafi yadda na maganar Ummul don tabbas abincinta yana chaɓewa amma hakan bai hana shi ya yi daɗi a baki sosai a ido ne dai za kayi tunanin sai a hankali, kuma yasha cin wasu abincin a gidansu Mansoor sai yaji na Innarsa yafi daɗi duk da waccen a ido yafi kyau.

‎Yana zama Inna ta miƙe ta ɗauki wani madaidaicin faranti ta ciko masa shi da shinkafar ta ajiye a gabansa.
‎
‎"Sannu Inna!"
‎
‎Ya faɗa murya ƙasa-ƙasa yana kallon yadda suke cin abincinsu a natse kuma cike da nishaɗi.
‎
‎"Yauwa Sadaukin Inna, ɗazun ka fita babu abin da kaci, nasan ba wata sana'a gare ka ba balle na ce ko ka sayi wani abin a waje!"
‎
‎
‎Cokalin da ta saka mi shi a saman abincin ya ɗauka tare da kai abincin bakinsa bayan ya ɗiba a cokalin, sai da ya tauna ya haɗiye ta buɗe idanuwansa akan Inna, fuskarsa da murmushi.
‎
‎
‎"Inna kullum ɗaukata ƙaramin yaro ki ke, ai bazan zauna ban ci komi ba wuni guda sai ka ce mai azumi?"
‎
‎
‎"Eh ai nasan kana yin azumin, litinin da alhamis yau kuwa ba ɗaya daga cikin ranakun ba ne."
‎
‎
‎Gyaɗa kai kawai ya yi yana cin abincin cikin natsuwa, sun riga shi gamawa Ummul ce ta ɗauke komi ta kai inda suke girki sannan ta dawo, Maryam ta ce.
‎
‎
‎"Yaya dankalin ɗazun mun cinye da su Ummul, Sadiya ta ce a kawo maka inji ta."
‎
‎Ta faɗa tana nuna Ummul da tayi ƙasa da kai tunowa da irin tsawar da ya daka mata ɗazun, Inna ta amshe zancen da cewa, "Ai yarinyar nan tana da ƙyirki kam, idan na fita fa gaisuwa sama gaisuwa ƙasa, dankali kam ai ba ranar da ba ma cinsa a gidan nan, har ce ma yarinyar nan nayi ta daina aiko mana ai sai ta kwashe 'yar ribar muna cinyewa."
‎Ummul da Maryam suka saka dariya gogan naku kuwa ko a jikinsa, sai ma sake kama gida da yayi jin abin da Maryam ke faɗa.
‎
‎
‎"Ai Inna kamun ƙafa take da ke don ta taɓa faɗa mini tana ƙaunar Yaya ne, kuma ido ba mudu ba ai yasan kima, wannan rawar ƙafar da take da walakin goro a miya."
‎
‎
‎"Ai kuwa idan haka ne tayi kuskure, me zanyi da ita?"
‎
‎
‎"A'a Sadauki kar fa nan gama muji ana aje a kai gaisuwa, ba na son cika baki kuma idan Allah ya ce matarka ce ai sai ka ga labarin ya sauya!"
‎
‎"Don Allah Inna kar kiyi mini baki, wannan yarinyar ba ta cikin tsarina."
‎
‎Inna ta girgiza kai ta miƙe tana faɗin.
‎
‎"Kai ma wa zai ba ka aure yanzu ba ka da sana'ar yi? Ni ce ma ke ɓata bakina."
‎
‎
‎Bai ce mata komi ba har ta fice daga ɗakin, shi kuma yaci gaba da cin abincinsa fuskarsa a tamke, suma su Ummul suka fice daga ɗakin don sun san halinsa baya wasa da su, za dai ayi hira yana jansu a jiki amma maganar wasa ko raini babu ita a tsakaninsu.
‎
‎
‎Misalin ƙarfe tara da rabi na dare yana ɗakinsa kwance, daga shi sai boxer da singlate akan katifarsa, ƙa'ida ne baya iya barci da kayan jikinsa sai dai ya bar ƙananu, wayarsa ce a hannunsa ya sa hannu ya kunna data, ya tsaya na minti biyu saƙonni suka gama shugowa, don tun jiya da dare da ya hau online bai kuma hawa ba sai yanzu, hannu ya kai ya danna saƙon Mansoor wanda ya turo masa misalin uku na rana da mintoci.
‎
‎"Sadauki, nayi tunani sosai akan maganarka ta zuwa China, kuma har bincike na saka a yi mini a ɗazun ɗin, sai dai daga majiya mai ƙarfi da na jiyo tabbas zaka iya zuwa da kuɗin da ka ce zasu isheka zuwa da dawowa ma daga nan gida Nigeria har ƙasar Sin, sai dai fa ka sani babu batun kuɗin inda zaka zauna a ciki, tafiya irin wannan tana da haɗari sosai a China akwai gidan da zaka kama duk wata akan 1.5m shine wanda zaka samu komi a ciki kamar toilet kitchen da ɗaki mai yalwa kuma a cikin gari, idan kuwa ka ce a wajen gari ne, to zaka iya samun na ɗari huɗu biyar amma kar ka manta kuɗin da zaka kashe daga can kafin ka shugo cikin gari suma zaman kansu suke, a shawarce ka haƙura da fitar nan ka kama kanka a ƙasarka."
‎
‎
‎Ganin voice note a ƙasa ya kunna tare da ƙara matso da wayar kusa da kunnensa sai yaji Mansoor na tambayar wani mutum ne yake ɗaukar masa.
‎
‎"Don Allah kayi mini bayani akan buranen da ke China da wanda yafi tsadar rayuwa a cikinsu!''
‎
‎Muryar da bai san ko ta waye ba yaji ta fara magana.
‎
‎"Shanghai. Ana ɗaukarsa a matsayin ɗaya daga cikin birane mafi shahara kuma mafi tsadar rayuwa a China, cibiyar kasuwanci da harkokin kuɗi ce, tana da manyan gine-gine da rayuwa mai tsada.
‎Beijing. Babban birnin China ne, ya shahara saboda gwamnati, tarihi, da manyan jami'o'i, rayuwa a nan ma tana da tsada.
‎Shenzhen. Cibiyar fasaha (technology) ce, kuma hedikwatar kamfanoni da dama tana nan, yana cikin biranen da suka fi saurin bunƙasa kuma rayuwa tana da tsada.
‎Hong Kong. Yana daga cikin wuraren da suka fi tsadar rayuwa a duniya, musamman saboda farashin gidaje, haka kuma yana da muhimmanci a harkokin kuɗi da kasuwanci.
‎Idan za a zaɓi guda ɗaya da ya fi shahara wajen kasuwanci da rayuwa mai tsada, mutane da yawa za su ambaci Shanghai. Idan kuma ana magana kan mafi tsadar gidaje da rayuwa gaba ɗaya, Hong Kong na daga cikin mafi tsada a duniya."
‎
‎Sadauki yaja wani dogon tsaki lokacin da ya kammala karanta jin saƙon, ko an faɗa masa abin da yake son ji kenan? Lallai ya ƙara yarda Mansoor kallon wanda bai san komi ba yake masa, oh yana faɗa masa tsadar ne saboda yasan bai da ko sisin kobo, saboda takaici ma kashe datar ya yi ba tare da ya amsa masa ba ya tashi zaune tare da kama kanshi da ya sara mashi, ya daɗe yana tunanin watarana Mansoor zai ce kawo takardunka in nema maka aiki a kamfanyn Daddy, kuma ya sama masa gurbi mai kyau kamar yadda shima yake aiki a matsayin manager a kamfanin, amma bai taɓa cewa hakan ba, duk da yasan wannan ɗin abu mai sauƙi ne a wajen Mansoor, ya kuma jan tsaki zuciyarsa na raya masa ya yi duk yadda zai yi ya bar ƙasar nan, hakan ne zai dasa baƙinciki a zuciyar maƙiyansa, don duk da Mansoor na nuna babu ya shi a gare shi fiye da sauran abokansa bai gamsu da hakan ba, idan har haka ne ba zai bar shi a gantale babu aiki ba, sannan ya kawo mishi shawara don ya taimaka masa da wani abu ya nuna bai ra'ayin ya ga shima yaci gaba a rayuwar nan.
‎
‎Haka dai ya kwanta ransa babu daɗi har barci ɓarawo ya sace shi, washe gari kam bayan ya dawo sallar asuba wanka ya yi, ko tsayawa shan kokon da Innaa tayi masa tayi bai yi ba ya ja babur ɗinsa ya fice, bai ma san ina zai je ba, tafiya yake saman titi cike da tunanin hanyar da zai fi don samun kuɗin nan, bai ankare ba yaji ya bige wata matashiyar budurwa a titin, ƙara ta fasa, ai kuwa shima ya tuntsura ya bigi wata bishiya take shi da mashin ɗin suka yi ƙasa, da sauri ya taso ya yo kan budurwar ganin yadda ta bugu da wani dutse take ƙoshinta ya fashe, ta saki ƙarar azaba, hakan bai kuma hanata ƙara yunƙurawa ba za ta ƙara takewa a na kare, da sauri ya ruƙota yana faɗin.
‎
‎
‎"Subuhanallah! Kin ji ciwo fa!"
‎
‎Ta ɗago manyan idanuwanta da sukayi ja kamar ma har da jini a gefensu da ya taru ga goshinta yana jini, suna haɗa ido ta fincike jikinta a nashi za ta kuma gudu suka ji muryar wani yana magana.
‎
‎
‎"Barirah ki tsaya!"
‎
‎
‎Da sauri ya kuma cewa.
‎
‎"Bawon Allah riƙe mini ita kar ta gudu!"
‎
‎
‎Nan ta fara ciku-cikun kwace jikinta ganin yadda karaf ya kuma danƙeta duk a zatonsa mahaukaciya ce.
‎
‎
‎Barirah.
‎Lokacin da Andi tayo kanta rufe ta tayi da bugu tako ina tana faɗin.
‎
‎"Kin kashe ta, wallahi kema sai kin mutu, ba za a kai Saudatu kushewa ita ɗaya ba sai dai a haɗaku tare." 
‎
‎
‎Barirah ba ta da niyyar ƙwatar kanta tana zaune Andi na kirɓarta idan banda kuka babu abin da take yi. Kowa jikinsa a sanyaye yake ganin abin da ya faru hatta Iyah ta kasa ƙarfin halin ƙwatar Barirah haka Andi ta dunga dukanta sai da ta gaji ta daina, Gashi an fara kiraye-kirayen sallar magriba a lokacin, Kawu Balarabe da Yaya Aliyu da shima ya dawo daga fitar da ya yi sai Faruk suka wuce masallaci, Iyah ma jiki a sanyaye ta wuce nata ɗakin domin gabatar da sallah aka bar Usman kwance wanda cikin ikon Allah an samu ya daina jijjigar tun da Saudatu ta rasu sai dai jikinsa bai daina rawa ba haka bakinsa a sake yana dilalar da miyau.
‎
‎
‎Andi ta dubi Barirah kallon wulaƙanci da ƙasƙanci, ba tasan ya akayi ba sai gani tayi kanta ya ɗago sama fuskarta akan ta Andi wacce idanuwanta suka zaro sai ta ga kamar wuta ce ke ci a cikin idanuwan nata, yayin da Andi kuma ta ga ruwa na fitowa daga idanuwan Barirah yana shiga nata, da ƙarfi taji anyi ƙasa da kanta kamar an sake shi da ƙarfi don sai da ta saki wata ƙara tsabar zafin da taji. Tsakin Andi ta jiyo mai ƙara ta shige ɗakinta, ganin haka ta miƙe jikinta duk ciwo yake mata, da kyar ta kai kanta fanfon harabar gidan tayi alwala don tuni yayyafin aka daina sai dai hadarin bai gama sauka ba har lokacin, ta ɗauko hijabinta ƙofar ɗakin Iyah a gurin tayi sallah a zaune don ƙafuwanta ma ciwo suke mata sakamakon yadda Andi ta dunga jefa mata duk abin da yazo hannunta.
‎
‎
‎Tana ji bayan an idar da sallah ana sanarwar rasuwar Saudatu a masallacin, tare da cewa za a yi Jana'izarya ƙarfe takwas na safiya anan ƙofar gidan, sallah take amma haka taji kuka yazo mata mai ƙarfi, haka ta idar da sallah tana kuka, haka su Kawu suka dawo da wasu mutane, maƙota kuwa tuni suka fara shugowa gidan tun sanarwar da akaji.
‎
‎
‎Iyah ma na idar da sallah ta koma parlourn Andi, haka maƙota suka dinga shugowa, nan aka suturta Saudatu aka sakata a cikin makara da safe za a kaita gidanta na gaskiya.
‎(Mutuwa kenan shin da ace Saudatu ta san a yau zata koma ga mahaliccinta za ta aikata kuskure irin wanda ta aikatawa Barirah, wai ace da gaske ne haka halin Barirah yake mai zai sa tsanar tayi tasiri har haka ga Saudatu wacce ba tafi sa'ar Barirah ba? Wallahi mu kuka da kanmu kuma mu kiyayi duniya mutuwa zata iya zuwa a ko wanne irin lokaci ba tare da mun sani ba)
‎
‎Kawu Balarabe da Aliyu ne suka koma sallar isha'i su Kawu ba su shugo gidan ba sai wajen tara, har lokacin Barirah na ƙofar ɗakin Iyah rakuɓe tana kuka, ko kallon inda take ba su yi ba suka wuce ɗakin Andi. Wajen sha ɗaya na dare Yaya Aliyu ya fito kinkime da Usman ya shiga ɗakinsu, ita ma jiki a sanyaye ta shiga parlourn Iyah ta kwanta saman kujera, ta taɗe kwance ba tasan lokacin da barci ya ɗauketa ba, tun da ta farko wajen huɗun dare kuwa ba ta iya komawa barcin ba, sai ta fito tsakar gidan tayi kwance sanyin asuba na dukanta, haka ta dunga rawar ɗari ga zazzaɓi ya rufe ta, ruwan sanyin da taji an watsa mata ne ya saka ta tashi a gigice tana kurma ihu.
‎
‎
‎"Kuka yanzu ki ka fara shi, sai idan ma kin ga an binne ki da rai ne zaki fara mai dalili."
‎
‎
‎Sosai furucin Andi ya shiga kwanyar kanta, sai ta ƙara gigicewa ko sallar asuba ba tayi ba, don kwanciyarta wurin zazzaɓin da ya rufe ta ga ƙarin sanyin da takesha ta cure guri guda har ta fara bacci-bacci ba tare da ta sani ba, sai dai ruwan da Andi ta watsa mata jinsa tayi tamkar ruwan ƙanƙara, duka jikinta ya jiƙe ga rawar sanyin da ya ƙaru haƙoranta har ƙara suke tsabar yadda suke karuwa da juna.
‎
‎
‎Tana gurin aka fito da gawar Saudatu za a fita ayi mata sallah ƙofar gida, gidan ma cike yake da maƙota sai lokacin ta lura, ana fita da Saudatu Andi ta kama hannunta ta yi waje da ita. Suna baya aka yi sallar gawar Saudatu, an ɗauketa za a tafi Andi ta ce sai dai fa a haɗa ta da Barirah, nan fa hayaniya ta fara tashi wani malami ya ce.
‎
‎
‎"Haba baiwar Allah, mutuwa fa tana kan kowa me yasa ba zaki yi haƙuri kiyi dangana ba tunda wanda yafi ki sonta ya amshe ta, kuma shine ya baki ita tun farko."
‎
‎
‎"Malam kayi shuru kawai, amma muddin aka tafi da gawar Saudatu to ita ma Barirah sai an binne ta da ranta, wallahi bazan yarda ta kashe mini 'ya ba kuma ita ta zauna a duniya, sai dai ayi haihuwar guzuma 'ya kwance uwa kwance."
‎
‎
‎"Subuhanallah! Subuhanallah! Anya matar nan tana da hankali?"
‎
‎
‎Cewar wani mutumi, nan fa guri ya kaure da hayaniya 'yan cikin gida ma tuni suka fito aka dinga surutu kamar ba gidan mutuwa ba......


***


Ina masu buƙatar kyawawan atamfofi da  lace, mayafai, shoes and bag. Tare da kyawawan kayan kitchen na 'yan gayu masu kwaliti, zaku iya tuntuɓar ASHNURR COLLECTION wacce ke Kano kwari market domin ƙarin bayani ku tuntuɓeta a lambar waya kamar haka *** Tana aika kayanta ko ina a cikin aminci.



Shin kuna da labarin AK ASHKAD COLLECTION to ku matso kusa ku ji, ita ce wacce take kawo muku kyawawan  abayas na gani a faɗa na shiga ko wanne guri kai tsaye, haka tana kawo muku  kitchenwares masu kyau da aminci cikin farashi mai rahusa zaku iya tuntuɓarta a 070444564938 ko *** shafinta na Instagram ashkad_collection adireshinta Daura, Katsina State tana aika kayanta ko ina cikin aminci.

Kuna da labarin UmmuAffan GHT Supplement, tana sayar da Supplement na kamfanin ght masu kyau da inganci tana garin Kaduna tana aika kayanta duk inda kuke a faɗin ƙasar nan dama wajen ƙasar nan, kai tsaye kuyi mata magana ta lambar waya kamar haka *** sayen na gari mai da kuɗi gida, sai kunzo.