CHAPTER 1 I
CREATED BY AISHA HAMZA*
_MUAYSHGRAPHICS_
22/9/2023
Bismillah da sunan Allah mai rahama mai jin kai wannan 📖✍️ littafi rayuwar Maryama na kirkireshi ne domin abubuwa da yawa duk da cewa zai iya kamanceceniya da rayuwar wani ko wata amma ni ba rayuwar kowa na kwaikwaya ba nayi ne domin fadakarwa da kuma nishadantarwa domin rayuwar Maryama rayuwa ce wadda yawancin abinda yake faruwa kenan a zahiri a rayuwar mu ta yau da kullum a wasu gidajen
_Na sadaukar da littafi na ga ƴan uwana mata Anty surayya Anty shamsiyya Anty zainab yaya Ummi yaya Maryam yaya Safiyya sai ƙannena Jamila da ƴargwal rukayya da husna Khadijah da Halimatu_
~Book 📚 1~
•Bismillah•
_RAYUWAR MARYAMA_
*ByY A'ISHA HAMZA*
*Dukda cewa hadari ya haɗu gari yayi tsit kowa yana cikin gida ba abinda kakeji sai kukan* *tsuntsaye kasancewar angama sallah maghrib cida kawai akeyi amma Maryama tana qasan bishiyar qofar gidan malam sani ta kwanta kanta a cikin cinyoyinta tasa hannu ta toshe kunnenta kana ganinta kasan a matuqar tsorace take da fargaba*
*Maryama yarinyace da bazata wuce ƴar shekara biyar ba zuwa shida sunan babanta malam habu mahaifiyarta kuma bata kai shekara biyu ba Allah ya amshi abinsa Maryama tanada yayye biyu amma duk maza ne sadiqu da Najib bayan rasuwar mahaifiyarta ne malam habu yaqara Aure ya auri balaraba yar wajen amininsa hadi ita take kula masa da yaransa'''''' tunda balaraba Allah ya azurtata da samun haihuwa a gidan malam habu fitinar yau daban ta gobe daban*
*Kullum Maryama saedae ta yini a waje har sai babanta yadawo daga wajen aiki da yake yana gadin wata ma,aikata su kuma yayyennata su ma basa zama a gida Sadiqu shine babba zai kai shekaru goma sha biyu sai najibu da bai wuce shekara tara ba amma ahaka Balaraba tace Dukansu sun isa neman kuɗi saboda haka bamai zaman mata gida saedae ta girka tabasu suci dukda cewa Mahaifinsu ke nemowa ai sangartasu za,ayi badan malam yaso ba da yace tabar Najib sai yaqara girma amma da yake shima malam habu sai yanda tayi dashi haka ya haqura yasa mata ido domin tace sam ita bata yarda da wannan zancen ba*
Karki bari karku bari kar mu bari abamu labari top 3 Na A'ishatu Hamza🤟 🤗 basai na faɗa muku ba littafaine wanda daga jin sunayen su zaka gane cewa na musamman ne
Da sauri sauri malam habu ya nufi kofar gidan malam sani a inda ya hango yarinya dukda yasan cewa a ranshi ba wadda zata kasance a wajen sai ƴarsa* _Maryama koda ya,iso inda take ya taɓata da sauri ta matsa tana qoqarin yin kuka koda tabude idonta dukda kasancewar duhun da gari yayi sakamakon hadarin daya haɗo bata kasa gane mahaifin nata ba tace baba kadawo malam habu ya dibeta cike da tausayi yace eh nadawo manana da yake sunan da yake kiranta dashi kenan sunan mahaifiyarsa ya sanya mata_
*Cikin gida ya nufa suka shiga koda yayi sallama hannunsa riqe da na Maryama ba kowa tsakar gidan sakamakon yayyafin daya fara safkowa kai tsaye ɗakin balaraba ya nufa cikin sauri saboda ruwan yafara qarfi*
*Zaune balaraba take tanacin taliya da mai da yaji da qaramar ƴarta a hannunta safinatu''' ta rungemeta tana bacci sai babban Hafiz akan tabarma daga gefenta da nashi kwanon yanacin nasa abincin*
_Jin sallamar malam habu da tayi yasa taɗago ta dubeshi sannu da dawowa malam_
_Malam habu ya dibeta yace yauwa balaraba ah ah yau Kuma taliya aka dafa mana naɗauka tuwo zakiyi saboda ɗumamen safe ko_
*Balaraba tace wlh malam nagaji da tuwon nan shiyasa na canja mana malam ya zauna gefen gado yana faɗin toh ai shikenan hakan ma yayi tareda jawo hannun Maryama yana faɗin zonan kema kici Abincin saiki kwanta koh*
*Balaraba takalli malam cikin fushi tana faɗin wlh malam bazata kwanar min a ɗaki ba tamin fitsarin kwance abincin ma taɗauki nata tawuce can ɗakin ƴan uwanta taje taci nayi shara bazata ɓatamin ba*
_Malam ya girgiza kai cikin ɓacin rai yace haba Balaraba yanzu yarinyar nan bata isa tazauna a inda kike ba kiyita koranta itafa yarinyace me tasani yanda yaga Balaraba tanata kumburin fuska saiya kwantar da Muryarsa toh shikenan naji bazata kwanar miki a ɗaki ba amma barta taci abincin kafin ta tafi koh haba Balaraba matar malam habu ai nasan bakya fushi malam ya faɗa yana sakin murmushi yakai dubansa zuwa ga Balaraba kamar dai ɗazun fuskartata ba yabo ba fallasa tace masa toh kawai_
*A qofar dakin da ƴan uwanta suke kwance ta zauna tanata faman kyarma saboda sanyin gari ga ruwan da akeyi kamar da bakin ƙwarya sakamakon dakin nasu duk shirgine a cikine suma a gefe suke rarraɓawa su kwanta'''*
*zaune take tana kallon qofar ɗakin da* _mahaifinta yake ciki wato dakin balaraba amma tanaji tana gani haka tabaro ɗakin tadawo qofar ɗakin yayyen nata ta zauna ''' sanyin da yafara mata yawane yasa tafara kyarma jikinta yanata faman rawa_
*A hankali Sadiqu ya leqo domin yaji alamar mutum a wajen yadauka ko masu shiga gidajen mutane da dare suyi musu ɗauke ɗauke da sauri yaƙarasa fitowa zuwa inda take yace ke Maryama tashi ki koma ɗaki mana da sauri ta dubeshi don bataji* *motsin fitowa daga ɗakin ba tace yaya tace bazan kwanan mata a ɗaki ba nikuma inajintsoron kwana Ni kaɗai a ɗakin can ta nuna wani daki wanda can Balaraba ma bata barshi ba saeda ta cikashi da tarkacenta asalin dakin kuma na mahaifiyarsu Sadiqune*
_A hankali yaja hannun Maryama yace mutafi ɗakin mu ki kwanta Maryama_
*Binshi tayi yana riqe da hannun ta suka shige ɗakin wani ɗan buhu naga yajawo wanda yake gefen tabar marsa* *wadda duk ta cinye ya shimfida ma kansa*
*sana ya ɗauko wata riga ya shimfida ma Maryama akan tabarmar tasa yace kwanta kinji a hankali* *takai kafaɗunta kasa ta kwanta ya kuma ɗauko wata rigar yaqara lulluɓeta da,ita* *sakamakon sanyin da yaga tanaji*
*Saeda tafara bacci kamar yanda najibu yake ta baccinsa tun ɗazu sana Sadiqu yasamu yaɗan kishingiɗa kafaɗarsa domin samun nasa baccin ahaka suka wayi gari*
_Kamar yanda suka saba kasancewar damuna ce suna zuwa gona da malam habu da yaran nasa yasa suka tashi tun kafin balaraba tafito tafara musu Bala,i_
*Kowa yanemi maɗebinsa kasancewar sunada rijiya a maqotansu can suke ɗiboma Balaraba ruwan aikin gida kafin su tafi gonar*
_Da sauri balaraba tafito daga dakinta tana kiran kai kai ku tsaya da sauri suka duƙa kasa suna faɗin maman Hafizu ina kwana bata amsa musu ba tafara daga yau banason ruwan rijiyar gidan malam sani da kuke ɗebomin kuje can gaba tayi musu_ *kwatance da wani gida da suke da tanki suke bada ruwa kasancewar ruwan nasu na famfo ne anfison shi saidai nisa da suke dashi*
_Ba yanda malam habu baiyi da Balaraba ba akan tadinga tarbar ruwan sama tunda yanzu Allah ya albarkace su da damuna amma taqi tace ƙura da iska duk suna shiga bazata tarba ba haka ya haƙura ya rabu da'ita_
*Ba musu suka ɗauki hanya har inda zasu ɗebo mata ruwan suka dawo lokacin malam habu ya shirya ya haɗa kayan tafiya gona suna shigowa tabasu abinda zasuci a kwano suka zauna suka ci dukda basu ƙoshi sunma riga da sun saba da hakan suka tashi suka wuce gona da malam*
_Maryama tana kwance dakin yayyen nata tunda safe data tashi takasa fitowa domin tana tsoron haɗuwa da Balaraba_
_Da sauri tashiga dakin tana faɗin ƴar jakar uba bazaki fito ba Maryama ta dibeta a kiɗime tace maman Hafizu ina kwana Balaraba tace kinci ubanki da kwanan kinsan aikin da zakiyi amma kullum saina tuna miki ko_
*Ah ah tafaɗa cikin sauri da tsoro tana faɗin yanzu zanyi dama dukan da Balaraba takaima bakinta yasa tayin shuru tana riqe baki tasan idan ma tayi kuka wani sabon dukan ne*
_Tashi ki wuce ja,irar banza Balaraba tafaɗa tana ƙara neman wani abin dukan da gudunta tafita waje tahau haɗa kayan wanke wanke abinka ga wadda shekarunta basu kai ba haka taketa faman haɗasu a burkice takai wajen wanke wanken wani abin ma da bai wuce ta tattara duka taɗauka ba da guda guda take kaiwa tagama taje gidan malam sani domin ta ɗebo ruwa a rijiya haka takejan gugan yana janta abinda zatayi guga uku tagama amma sai tayi guga biyar zuwa shida Allah yasa ma rijiyar tasu batada zurfi shiyasa take samun sauqinta_
*Tagama wanke wanken nata takai kayan inda ake ajiye su duk taɓata jikinta kamar yadda aka saba kullum tadawo ta rakuɓe gefen dakin balaraba tana kiran maman Hafizu nagama wanke wanken*
_Daga dakin tace saura shara ko munafuka kika maƙelemin a ƙofar ɗaki Maryama tayi ƙarfin hali tace maman Hafizu yunwa nakeji don Allah idan naci Abincin sai inyi sharar_
*A fusace tafito da ɗan karanta a hannu tafara kwaɗa mata akai toh ki gayawa duniya bana baki abinci nabarki da yunwa munafuka kawai kin tashi ko saina farfasa miki fatar jikinki*
*A hankali Maryama ta miqe ta ɗauki tsintsiya domin harta fara jin juwa ga filin gidan nasu yanada girma ga duk ƙasa tako ina kana shara ƙura na baɗe ka*
_Na sadaukar da wannan page zuwa ga maman Saheeb kuma maman Muhammad ina sonki ƴar uwata❤️💋_
Karki bari karku bari kar mu bari abamu labari top 3 Na A'ishatu Hamza 🤟 🤗 basai na faɗa muku ba littafaine wanda daga jin sunayen su zaka gane cewa na musamman ne