KIRAN KADDARA

THE DISTANCE BETWEEN US

by @nihaalmaalik

Maryam tayi baccee da tunanin abin da ya faru daren jiya, har mafarki seda tayi, wai ga wani Abu nan kamar aljani ya fito daga qofar nan ya biyota da wuqa yana chewa “meyasa kika bude ni? Ba anche kada ki bude ba?” 

Zaid ya fara tashi tun kafin Asuba saboda yadda take riqe dashi tana hawaye cikin baccin Tana fadin “kayi hakuri wallahi ban bude ba” gashin kanta gabadaya ya watse a kan kirjin shi, tana qanqame dashi, a hnkali yake addua yana tofa mata yana shafa kan ta har yaga ta dena sannan ya jayeta jikin shi a hnkali ya gyara mata kwanciyar ta, ya shiga bathroom yayi brush yayi arwallah ya fito yasa jallabiyar shi ya hau carpet ya tada sallah, Yayi raka’a biyu sannan yayi adduoi ya zauna yanata istighfar seda akayi kiran farko se Yayi raka’atanul fajr sannan yaje yana tada maryam a hnkali, cikin baccee taji ana kiranta, “mahreeyam” ta bude ido a hnkali tana kallon shi da idonta masu cike da baccee, ya dade yana kallonta yanda tayi mishi wani irin kyau da lumsassun idonta da take kallon shi dasu “tashi kiyi sallah ni zan tafi masallaci” a zabure ta miqe tana girgiza kai, “don Allah kayi a nan kada fita” ta fadi a rikice idanunta suka fara ciccikowa, “okay calm down, bazan fita ba, tashi kije kiyi arwallah se muyi tare” ta miqe da sauri ta shiga toilet, duk yadda kyau da tsaruwar toilet din yake bata bari ya dauke hnkalinta ba, ta dauko sabon brush da ta gani ta bude tayi sauri tasa toothpaste ta fara brush se taji kamar qarar bude kofa, a rikice ta bude kofar bathroom din sai kuwa taga zaid baya dakin, da gudu ta nufo waje da brush a bakinta sukayi karo a qofar yana dawowa riqe da hijab dinta, seda ya riqota da kyau sora kadan ta fadi qasa, yana furta “Subhanallah” 

Yadda ya ganta a gigice sora kadan dariya ta kucce mishi, ya riqe ta ya kaita har qofar toilet “kiyi arwallah ki fito” da sauri ta wanke bakinta tayi arwallah ta fito, yana zaune da hijab dinta a hannu ya miqa mata ta karba tasa ta tayar da raka’atanul fajr, yana zaune ta qare ta fara adduoi har sukaji ana tayar da sallah daga masallaci, ya miqe yayi iqama ya tayar da sallah maryam na binshi a baya, seda suka qare sukayi adkhar sannan ya kalleta, “ina kwana” ta gaida shi, ya dan gira yana kallonta, be ansa ba se tambayar da yayi mata “kin qare adhkar?” Ta gyada kai, ya miqa hannu ya dauko Qur’anin da ke aje a wurin ya fara budewa yana tambayar ta “kinyi sauka?”

“Eh” 

“Hadda fah? Kinayi?”

“Eh inayi”

“Hizb nawa kika haddace?”

“Na kammala haddata duka tun ina SS1” 

Zaid ya dena bude Qur’anin da yake ya dago yana kallonta “da gaske”

Ta gyada Kai 

“Ynzu kowace sura na jawo zaki iya chi gaba?” 

“In shaa Allah zan iya”

Ya rufe ido yayi dan tunani se ya bude yayi bismillah ya karanta mata aya ta 16 cikin suratul maryam, a cikin ayar taji yadda ya fadi sunan maryam dd, a ranta take chewa ashe ya iya fadin sunan dakyau, da qira’ar shi me daadi ya karanta ayar har qarshe, karatun ya yima maryam daadi kamar tache ya kada ya tsaya, se tayi bismillah ta chigaba, yadda take fitar da karatun da kyau cikin wata irin qiraa me daadi da ratsa zuciya, ya rufe ido yana sauraren ta seda ta karanta ayoyi 15 se yache “ai zakisan wannan tunda suratul maryam che” tayi murmushi kawai, se ya jawo mata aya ta 32 cikin suratul an’aam, ta chigaba da karantawa a natse ya lumshe ido yana sauraren ta, ya sake jawo mata aya ta 8 cikin suratul anbiya’ nan ma ta chigaba da karatun, idonshi a lumshe a ranshi yana chewa dole inje har sokoto in yima malaminta kyautar gida da mota da kujerar hajj da umrah, sauraren ta yake yadda take karanto qisoshin annabawan har seda ta kai qarshen surar, seda yaji tayi shuru ya bude ido ya kalleta, ya furta “Subhanallah” ita dai kallonshi kawai take ya sake chewa “Allah Yayi miki albarka yasa ma karatun ki albarka, Allah yasa alqurani ya zama hujja garemu ba hujja Akan mu ba”

“Ameen” ta amsa tayi shuru

“Ya sunan malamin da ya koya miki Qurani?”

Seda Tayi murmushi saboda tunawa dashi sannan ta ansa “Malam Muhammad”

“Idan na biya mishi umrah da hajj na bashi gida da mota yayi?” 

Ai batasan ya akayi ba se gani Tayi ta tashi ta rungume shi “nagode Allah ya saka da alheri ya biya maka buqatun ka”

Seda jikin shi Yayi tsamm daqyar ya iya ddaita natsuwar shi sannan ya sake tambaya “shi ya koya miki tajweed?” Ta gyada kai alamar eh 

“Hadith fah? Wane littafi da wanne kikayi na Hadith?” 

“Da arba’unan nawawi muka fara sannan mukayi umdatul ahkaam, daga nan se aka fara yimuna wasu littafan 

“littafan wane da wane kikayi?”

Ta zayyano mishi su kuma abnda ya sake kashe shi da mamaki duk hadiths dinnan da littafan suna kan ta, wai a makarantar su duk abnda aka koya musu haddacewa sukeyi, a ranshi ya raya dole yaje ya gyara makarantar nan kuma duk yabi malaman da alheri kuma zesa a ware kuddi da za’a rinqa aika musu kowane wata, ya kalleta ya furta “barakallah feek hayaateee” ta dan a kalleshi jin sunan da ya kirata dashi se ya sake fadin “Allahumma ja’alnaa min ahlil Quran” da ameen ta ansa se kuma ya sake chewa “Rabbana hab lanaa min azwaajina wa zurriyatanaa qurrata a’yun wa ja’alna lil muttaqeena imaamaa” ta amsa da ameen, se ya miqo hannu ya dafa goshinta ya karanta “Allaahumma innee as'aluka khayrahaa wa khayra maa jabaltahaa 'alayhi, wa a'oodhu bika min sharrihaa wa min sharri maa jabaltahaa 'alayhi” ta amsa da “ameen” ta daga ta kalli window, rana ta hasko alamar gari ya washe se ta miqe tayi salatu duha yana kallonta da ta qare ta jingina da gadon baccee na dan daukar ta har yachi qarfin ta, yayi dariya ya matso ya dauketa ya kwantar da ita kan gado, ya rufe curtains din da rana ke shigowa ta ciki, sannan ya dauko laptop dinshi, ya chire jallabiya ya hauro kan gadon ya dago kan ta ya kwantar akan chinyar shi ya chire mata hijabi yana shafa gashin ta a hnkali, se ya mance da aikin da ze duba yanata kallonta har baccee ya dauke shi shima. 

Ita ta fara tashi ta ganta kan chinyar shi, shi kuma yana zaune ya jingina da kan gadon jikin shi ba riga, ta qura mishi ido gabanta na wata irin faduwa bata taba ganin namiji haka ba riga ba, kuma ya akayi take kwanche kan kafar shi, ta saki ido tana yimishi kallon tsab, seda ta gama kallonshi iya son ranta qasa qasa tache yayi kama da larabawa hasken su ne kawai beyi ba, ta kai hannu ta taba fuskar a hnkali kamar wadda zata taba wuta, ta shafa sajen shi, ta tashi a hnkali ta fita tana gudun kar ta tashe shi, ta fito ta tsaya tana kallon gidan, koina haske tar kamar ba shine jiya tayita jin tsoro da dare ba, ta sauke ajiyar zuciya ta nufi dakin ta

Zaid kuma dama idonshi biyu duk kallonshi da takeyi yana sane, kyaleta kawai yayi, yanajin har abnda ta fadi, da kuma taba shi da tayi, seda ta fita ta rufe qofa ya bude ido yayi dariya 

Bayan ta shige dakin ta wanka Tayi ta shirya cikin wata Arabian gown maroon, ta gyara gashinta ta daure, yau tana marmarin kunun gyada, Seta sauka downstairs da tunanin zatayi dayawa qila shima zaid ze sha don taga jiya da alama yaji daadin tuwon da tayi

Da ta shiga parlour, ta tarar da Zaid zaune yana duba wayar shi

“Ina kwana.” Ta gaida shi 

Yayi shuru ya kalleta na dan lokaci, ya kalli gashin kan ta da ta gyara ta qulle wuri daya ga wasu sun zubo ta gaba, color din rigar maroon yasa hasken fatar ta ya fito tarr, a chan qasan maqoshin shi ya furta “ya khaliq” sannan ya daidaita natsuwar shi ya amsa mata “kin tashi lfya?.”

Be jira ta ansa ba Sai ya miƙe.

“Kin chi abnci?”

Maryam ta yi murmushi.

“Kunun gyada nikeso bari in shiga kitchen in hada, zaka sha?”

Zaid ya gyada kai “zan sha” a ranshi yana tunanin wannan yar yarinyar na nufin ta iya girki? Jiya hadda chewa wai ita tayi tuwo

Ita dai ta juya ta nufi kitchen, tasa cooks suka gyara mata wake sukayi blending ita kuma paste din gyada da mama ta hada mata cikin kayanta ta gyara ta dama kunu se qamshi ke tashi ta juye a flask ta soya qosai da waken da aka gyara mata, tasa aka dauka aka jera mata a dining within 1hr ta gama komai

Ta nufi parlour ya tsaya kusa dashi “yaya na gama” 

Be Che komai ba ya taso ya nufo ta, ya riqe hannunta yana murzawa a hnkali Suka nufi dining tare, zaid ya shanye mug din kunu da maryam ta zuba mishi ya sake zubawa, ga qosai yayi daadi sosai yanata tunani Ynzu kenan dai ita tayi wannan girki?

Maryam tana cin abinci a hankali.

Zaid yana duba wayarsa lokaci-lokaci.

Sai wayar ta yi ringing.

“Hello?”

Ya saurara.

“Yes, send it to my email.”

Ya yi shiru.

“I’ll review it.”

Sai ya kashe wayar.

Maryam ta kalle shi.

“Aiki ko?”

“Eh”

“Yau ma zaka je office?”

“Qila inje, banajin daadin jikin kwanan nan”

Ta gyada kai 

“Jiya ma naji jikin ka yayi zafi, ka sha magani?”

Sai Zaid ya kalle ta be ansa ba se yache 

“Kinada plan for today?”

Maryam ta girgiza kai.

“Aa”

“Good.”

Ta kalleshi 

“Good? Why”

“Nima se in zaune a gida kawai in sha magani in huta”

“Eh ka huta Gaskiya, akwai abnda kakeso ka chi? Se in dafa maka”

Yayi dariya, kafin ya amsa akayi sallama

A daidai lokacin ne Mammi ta shigo

Maryam ta miqe da sauri tazo ta rungume ta

“Mammi jiya naji tsoro da dare, nache ma yaya ya kaini wurinki yache Wai shima baze iya hita ba tsoro yake ji” ta qarasa maganar a shagwabe hawaye suna cikon idonta

Mammi ta harari zaid 

“Kai kakeba yarinyata tsoro ko?” 

Kafin ya ansa maryam ta riga shi “aa bashi bane amma dai be kaini wurinki ba wai shi tsoro yakeji shima”

Mammi tayi dariya tana kiran sunan shi

“Zayd.”

Shima Yayi dariya ya ansa

“Naam mammi ina kwana”

Bata ansa mishi ba ta juya ta kalli Maryam “Jiya yarinyata ta aiko min da tuwo da miyar taushe me daadi sosai, yau ma se gashi an aiko min da kunun gyada da qosai, naji daadi sosai kofi uku nasha na kunun” maryam Tayi dariya zaid kuma mamaki ya kama shi a ranshi yake fadin nayi arziki Jiya ban qaryata ta ba da Ynzu naji kunya, yana cikin tunanin yaji muryar mammi

“Muje zayd zan nuna maka wani abu”

Zaid ya kalli Maryam

“Bari inje in dawo.”

Mammi Taji daadi sosai yanayin da taga suna zama a ranta tana addua Allah ya qara musu fahimtar juna

Maryam ta gyada kai

“Se ka dawo Allah ya tsare”

Ta koma parlour

Mammi ta fita Zayd ya bi bayanta suna takawa zuwa compound

“Zaid.”

“Naam?”

“Maganar karatun maryam, nasa maka ido kwana biyu amma naji kayi shiru?”

Zaid ya yi shiru na ɗan lokaci.

“Karatu?”

“Eh. Ai tana karatun ta kaje ka auro ta”

Yayi murmushi Ya gyada kai

“Mammi ku dai kuka auro min”

“Ohh toh in bakaso bani yarinya dama tache wurina zata dawo”

Zaid Yayi dariya sannan Yayi magana

“Tachi gaba da karatun mammi, ai bazan hana ba”

Mammi ta yi murmushi, alamar Taji daadin maganar

Zaid ya kalle ta.

“She’s young, yakamta ta samu sound education.”

“Na sani shiyasa nayi maka maganr”

“Bai kamata aure ya hana ta karatu ba.”

Mammi ta gyada kai.

“Exactly my point”

Ta ɗan yi shiru.

“Ka tambaye ta abinda take karatu a sokoto”

“Lokacin da mukaje sokoto Fahad ya tambayeta tache international relations take karatu”

“Ko za’a karbo transcript dinta se a nemar mata baze ko Nile? Ko kuma open university?”

Zaid ya yi tunani.

“Maybe not Abuja.”

Mammi ta kalle shi.

“Me kakeso? Ta koma sokoto tayi zaman karatu ne?”

Zaid ya sauke ajiyar zuciya.

“Mammi cikin next week zan koma Amsterdam.”

Mammi ta gyada kai.

“Na sani ai, ko baka nan ai be kamata ache ta koma sokoto ba”

“Ina nufi zanje tare da ita se ta chigaba da karatun a chan”

Mammi ta yi shiru chan tache 

“zakaje da ita tayi karatu a Chan din?”

“Eh”

“Ka tabbata za ta iya karatu a chan?”

Zaid ya kalli ƙasa na ɗan lokaci, yana tunanin Gaskiya ynzu bayajin ze iya yin nisa da ita, ba sonta yake ba, shi ina ruwan shi da soyayya, amma dai kwana biyu dinnan ya saba ganinta kusa dashi beson suyi nisa, kuma ai hakkinshi ne ya kula da ita don haka be kamata yaje ya batta ba, ya dan sauke numfashi 

“Zan duba suitable university for her a chan, wadda suke karatu da turanci yadda ba se ta tsaya koyon dutch ba”

Mammi ta yi murmushi.

“Haka yayi dd, Amma ka yi magana da ita tukunna, Kada ka yanke mata hukunci kai kaɗai, duk da dai kanada damar yin hakan amma gwara dai ka shawarce ta zefi”

Zaid ya gyada kai.

“Okay In shaa Allah”

“Shikenan.”

Yayi mata sallama ya juya zai tafi

Sai Mammi ta kira shi

“Zayd”

Ya juyo.

“Ka kula da ita kaga yarinya che qarama please”

Ya yi shiru na ƴa seconds.

“Ynzu ma ina iyakar qoqari na mammi”

“Na gani Gaskiya, Allah ya yimuku albarka”

“Ameen mammi na”

Se ya juya ya koma part dinsu

Maryam tana zaune a parlour tana duba wayarta lokacin da Zayd ya dawo.

Ta ɗago kai.

“Sannu da zuwa”

Ya zauna kusa da ita 

“Me kike dubawa?”

Ta nuna mishi wayar 

“Safiya che ta turo min scan dinta, zamu samu baby in shaa Allah” ta fadi cikin jin daadi

“Kinason baby ne”

“Awo wallah inaso”

Zaid ya bushe da dariya yana kallon dan Qaramin bakinta da ya furta maganar, a cikin ranshi yache “Kam balai”, yana maimaita awo wallah 

Maryam tayi rau rau da ido zatayi kuka

Yayi sauri ya dawo kusa da ita ya riqe hannunta yana murzawa tareda gintse dariyar shi

“Yi hakuri tunani nike idan kika samu baby wa ze rinqa kula dashi? Naga kema haryanzu se an kula dake, ki bari se idan kin qara girma yadda zaki iya kula da babyn”

“Wallahi zan iya, ai a maqotan mu idan an haihu ina zuwa inyita daukar baby”

“Toh shikenan kada ki damu kema zaki samu naki in shaa Allah”

Ta gyada kai, ya chiro handkerchief dinshi yana goge mata hawyaen 

“Zan tambaye ki wani abu.”

Maryam ta kalle shi.

“Toh”

“About makaranta.”

Ta ɗan yi mamaki.

“Makaranta?”

“Eh, Kinaso ki chigaba da karatun ki?”

Maryam ta gyada kai.

“Eh inaso”

“International relations kikeyi ko? Shi zaki chigaba?

Maryam tayi mamaki, ba dai tun lokacin da ta gayama Fahad be manta ba

“Eh shi nikeso”

Zayd ya gyada kai

“Okay Good.”

Ya ɗan yi shiru.

“zaki chi gaba in shaa Allah.”

Maryam ta kalle shi.

“Zan koma sokoto ne?”

“Aa zan Nemo miki wata makaranta”

Ta ɗan yi mamaki.

“A nan?”

Zayd ya kalle ta.

“A Amsterdam.”

Maryam ta zaro ido

“Amsterdam?”

“Yes.”

“Ni?”

Zaid ya ɗaga gira.

“Toh wa ke wurin nan bayan ke?”

Ta yi murmushi.

“Ban taba tunanin zan je Amsterdam ba, Amma… yaushe?”

“next week nikeson komawa”

Maryam ta yi shiru.

“Ni kum fah?”

Zaid ya kalle ta.

Tare zamuje in shaa Allah 

Sai ta sunkuyar da kai tana tunani

“Okay.”

Zaid ya lura da yadda fuskarta ta sauya.

“Me ya faru?”

“Ba komi” ta fadi hawaye na sauko mata

Ya kalleta ita ko kuka kyau yake mata ya fadi a ranshi, bayason kuka sam, balle na macce

“Maryam.”

Ta kalle shi.

“Ina tunanin zan qara yin nisa da mama kuma bnsan kowa a chan ba”

Zaid ya yi shiru.

Sai ya ce:

“Ni kin sanni ai, Zan kasance tare da ke ai”

Ta dan kalle shi.

Kalmar ta tsaya a zuciyarta.

Ba ta san me za ta ce ba.

Zaid ma kamar ya gane abin da ya faɗi

Sai ya gyara zama.

“Makaranta zakije ai, karatu ze dauke miki hankali, kuma se kiyita waya da mama kullun”

Maryam ta yi murmushi.

“Nagode.”

“Ba se kinyi godiya ba, its my duty”

“Still Nagode”

Zaid ya gyada kai.

“Okay.”

Sai ya miƙe.

“Kiyi tunani akai”

Ta gyada kai.

“Zanyi”

Ya wuche ya fara haurawa sama Har Ya fara tafiya, Sai ya tsaya.

“Mahreeyam”

“Naam?”

“Kada ki damu akan rayuwar da zakiyi an Amsterdam.”

Ta kalle shi.

“Zan tabbatar da kina cikin kwanciyar hankali ko Yaushe in shaa Allah”

Ya chigaba da tafiya, Maryam tayi shuru tana kallon shi har ya shiga dakinshi ya rufo ƙofar

Sai ta yi murmushi ba tare da ta sani ba, yana shiga dakin shi yasha magani ya dan kwanta

Maryam na zaune tana tunanin wane girki zata yimishi tunda baya jin daadi

Ta dauki waya ta kira mama tana gaya mata maganr ma karanta da zayd Ya yimata 

“Allah ya bada sa’a ya taimaka”

Maryam taji mama ta ansa a sanyaye

Tanajin firar da yaran mama sukeyi qasa qasa, ta sauke ajiyar zuciya tasan dai yanzu mama batada kewa, se taji muryar mama

“Kiyi ma mijinki godiya, ya aiko muna da kayan abnci da nan Gidan da gidan su imran, masu yawa sosai har mu wuche shekara bazasu qare ba don haka mun fara abncin sadaka muna raba ma almajirai kullun da dare, kuma ya hada da kuddi masu yawa sosai”

Maryam tayi shuru don ita kam batasan ma yayi ba

“Allah ya saka da alheri”

Suka qare waya da mama ta tashi ta shiga kichen, couscouse tayi tasa vegetables sosai a ciki sannan tayi kidney sauce me daadin gaske, ta dauko kazar ta da tayi marinating tasa a oven ta sasaita temperature din da takeso sannan Tayi timing ta kunna, ta koma ta hada coconut juice, kafin ta qare kazar ta gasu, ta dauko food warmers ta zuba na mammi taba cook din da ke kitchen din tache ya kai sannan ta debi nasu tasa a food warmers ta kai dining ta jera da kanta, sannan sauran ta zube ma cooks din a food warmer din da ke matsayin nasu

Daki ta wuche tanata duba abubuwa a wayar ta, se ta shiga portal na UDUS ta fara duba university information dinta, ta fara tunani

Amsterdam, University, Ita maryam zata karanta International relation a international country 

Ta fara jin wani irin sabon excitement.

Ba wai saboda zataje Amsterdam kawai ba.

Saboda a karon farko tun da ta zo gidan nan, ta fara tunanin rayuwarta bayan wannan auren da kuma abnda tazo yi, Sai wayarta ta yi ringing, Unknown number.

Maryam ta kalli screen, Anyi hiding number, ta dauka ko kar ta dauka?

Sai ta ɗauka.

“Salamu alaikum”

Shuru baa amsa mata ba

“Hello?” Ta sake fadi

Shiru.

Ta kalli screen.

Call ɗin ya yanke.

Zuciyarta ta ɗan buga.

Ta tuna saƙon da ta samu dazu da zayd ya fita tareda mammi from unknown number

“Ki dena binciken abnda yayarki ta bincika.”

Ta ajiye wayar.

Sai ta yi tunani.

Ko shine ya kirata?

Da yamma, Maryam ta fito garden.

A wannan karon ba ta zauna a bench ɗin da ke nesa da ƙofar ba, Ta tsaya a tsakiyar garden din, Ta kalli hanyar, kofar na nan rufe, CCTVs ɗin ma suna nan.

Ta yi taku biyu zuwa wajen.

Sai ta tsaya, Ba za ta shiga ba, Ba yanzu ba.

Ta dai kalli ƙofar ne daga nesa, se ta lura da wani abu, Akwai ƙaramin haske a gefen ƙofar, Kamar sensor light.

“Hmm.”

Ta yi magana a hankali.

Sai ta ji footsteps a bayanta.

Ta juyo da sauri.

Hajiya Raliya che, ta tsaya, Ta kalli Maryam, ta kalli ƙofar.

“Kin sake zuwa nan ko?”

Maryam ta yi shiru.

“Ban shiga b ai”

Hajiya Raliya ta kalle ta.

“Na sani.”

“Amma Hajiya…”

Hajiya Raliya ta ɗaga hannu.

“Bar wajen nan”

Maryam ta kalle ta.

“Don Allah Me yasa hajiya?”

Hajiya Raliya ta yi shiru 

A wannan karon fuskarta ba ta da tsauri sosai.

Ta fara magana a hnkali 

“Maryam Wani lokaci, rashin sanin abu shi ne kwanciyar hankli da kuma kariya”

Maryam ta tsaya.

“Kariya daga me?”

Hajiya ta kalleta sosai.

Sai ta sauke ajiyar zuciya.

“Ki yarda da ni kawai”

Maryam ta yi shiru.

Hajiya ta juya zata wuche, Amma kafin ta tafi, ta tsaya, Ba tare da ta juyo ba, ta ce:

“Ba Zayd ne abin da ya kamata kiyi kwankwanto ba..Zaid besan komi ba”

Maryam ta daskare.

Ta kalli hajiya.

Amma Hajiya Raliya ta chigaba da tafiya

“Hajiya!”

Hajiya Raliya ba ta juyo ba.

Maryam ta tsaya tana kallonta har ta wuce

Sai kalmar ta tsaya a zuciyarta.

Ba Zaid ne abin da ya kamata ki ji tsoro ko kiyi kwankwanto ba, shima besan komi ba

To…

waye?

Se dare zaid ya fito daga daki duk da ba baccee yake ba, yana hutawa ne kawai, ya kashe duka wayoyin shi, jikin baya mishi daadi

Maryam tana kitchen cook suna taimaka mata tana hada cupcakes 

Ya tsaya a bakin ƙofar kitchen.

“Hayatee”

Ta juyo.

Duka cooks din suka fita

“Ka fito? Ya jikin? Sannu”

“Yawwa Thank you.”

Ya kalli abin da take yi.

“Cake kike?”

“Eh”

Ya kira cook din dake waje yache su chigaba

Sai ya kalli Maryam, ya riqe hannunta yana murzawa ya jata zuwa dinning

“Meyasa kike wahalar da kanki?”

“Bana son zama ban yi komai ba.”

Zaid ya ɗan yi murmushi.

“Na lura da haka”

Ta kalle shi.

Ya lura da yadda take kallonsa.

“Menene?”

Tayi saurin janye idonta.

“Ba komi.”

Zaid ya kalle ta na ƴa seconds “naji saukee kada ki damu”

Ta gyada kai

Tayi serving dinshi ta dauko wani plate zata zuba nata se ya karba, ya nuna mata kujerar da ke kusa dashi alamar ta zauna nan, ya dauko spoon ya qara a plate dinshi yache “my chi tare” suka fara chi a hnkaki.

Bayan sun qare chin abnci suka zauna parlor na dan lokaci, tasowa yayi ya dawo kan kujerar da take ya kama hannunta ya riqe yana murzawa a hnkali, marym kamar ta bude baki ta gaya mishi ita dai in yana murza mata hannu jin take kamar ana mata shocking tun daga kanta har tafin kafar ta amma dai ta daure, Tanata kallon tv amma tunanin ta yana kan maganar su da haj raliya, shi kuma Zayd yana tunanin yadda abncin da tayi yayi mishi daadi, kamar ya tashi ya qara amma kuma kada ta rena shi,  suna zaune a haka dai har Daren ya dan fara nisa, Maryam dan fara jin baccee amma se ta dauko wayarta ta fara dubawa, tana kallon university information ɗinta da ta duba da rana, A karo na farko, Amsterdam bai yi mata kama da wani wuri mai nisa ba, taji kamar wani wuri ne da za ta iya rayuwa, Wani wuri da…Zaid zai kasance tareda ita

Tana haka wayarta tayi vibrating…Unknown number.

Message ɗaya ne, Maryam ta buɗe.

“Ki kiyaye gargadin da nike miki”

Zuciyarta ta buga.

Ta sake karantawa.

Sau biyu, Sau uku.

Sai ta kalli zayd taga hankalin shi yana kan wayar shi, tana nan kwanche tana tunani har baccee yayi gaba da it.

Zaid ya fara jin baccee ya dago ya kalli maryam yaga har tayi baccee abunta, a hnkali ya dauketa irin daukar jarirai, seda yayi switching socket din tv sannan ya fara hawa stairs a hankali don kar ya tashe ta, dakin shi ya shiga da ita ya kwantar da ita kan gado, bathroom ya wuche yayi brush ya dawo ya chire rigar jikin shi ya kwanta a hankali kusa da ita, jawota yayi jikinshi ya dora kanta a kirjinshi yana shafa gashin ta, ya kalli fuskar ta ya sauke ido kan dan Qaramin lips dinta, abubuwa uku suke burgeshu a jikinta, da hannayenta da gashin ta da lips dinta, ya taba biyu amma yana tunanin Yaushe ne ze kai ga taba na qarshe? A hnkali ya dora hannunshi a kan lips dinta, ya murza su, se ta turo su gaba kamar tayi pouting, yayi murmushi yana tuna dazu da tache tanason baby hadda hawayen ta, a hnkali ya furta inyi renon ki sannan inyi renon baby kenan, kawai ya gyara mata kwanciyar ta sannan ya kashe lamp din, Yayi adduoin baccee ya tofa mata ya rufe ido amma ya kasa baccee, gashi bayason yayi dogon motsi ya tada ta

Yanata murza hannunta da hannu daya, dayan kuma yana shafa gashinta yana shaqar qamshin ta


Follow this link to join my WhatsApp group: ***


115EDE9D-23A0-47DB-B03F-294247B19F57.png