KIRAN KADDARA

THE FIRST JEALOUSY

by @nihaalmaalik

Yau ma zaid ya fara tashi daga baccee, maryam na kwance ta shige jikin shi sosai, ya kalleta a ranshi yana tunanin tanada son jiki sosai, ya qura mata ido yanata kallonta, ya shafa gashinta yana sauke ajiyar zuciya, ya kalli face dinta, ya qura ma dan qaramin bakinta idanu, yayi murmushi yana tuna yadda take shagwaba tana turo shi, ya kwantar da ita a hnkali, yaje yayi brush yayi arwallah, yayi nafiloli kafin a kira sallah, seda aka fara kiran sallah yaje ya shafa fuskar Maryam, ta bude ido a hnkali tana kallon shi, ya dade yana kallon fuskar ta da idanunta da ke cike da baccee, daqyar muryar shi ta fito a hnkali ya furta “sallah” ta tashi ta shiga bathroom, Tayi brush da arwalla sannan ta fito, ya miqo mata hijab tasa Tayi raka’atanul fajr sannan yaja su sallah, koda suka qare sukayi adhkar, hannunta ya riqe yayi tasbihi da fingers dinta, maryam kam se ji take kamar jikinta yana vibrating, seda suka qare adhkar gabadaya, kamar jiya yau ma seda yasa maryam tayi mishi karatu sosai, ya lumshe ido yanata saurarenta, seda rana ta fito yaga alamar tana jin baccee sannan yache su kwanta, tashi yayi ya chire jallabiyya maryam tayi sauri ta rintse ido ta haye gado tana rufe har fuskar ta da blanket, kallonta yayi se yayi dariya ya dauko laptop dinshi sannan ya hauro gado ya bude ta yana dudduba abubuwa, seda ya qare abnda zeyi, maryam tayi nisa da baccee lokacin, kashe laptop din yayi ya ajiye a bedside, ya janyo maryam jikin shi a hnkali, ya zare mata hijabi a hnkali sannan ya rungumeta ya koma baccin shima

Koda maryam ta bude idanu se ta farka da tunanin saƙon da ta samu jiya

Tun da ta zo wannan gidan, abubuwa suna ta faruwa a hankali kullun, suna barin ta da tambayoyi, tana dago kanta ta ganta dap da fuskar zaid, kai!!! ya akayi take cikin jikin shi haka? Shi yake janyo ta? Ko ita ke zuwa cikin baccee? Dama tun lokacin da suna baccee a kan gado daya da Aisha kullun se Aisha tayi complain wai tans shigewa jikinta, watarana har fushi Tayi ta koma baccee dakin mama amma kwana daya mama ta koreta tache bazata iya da wannan shigewa jikin mutum da takeyi ba Kamar mage, amma ai ko ita ta matso ya kamata ya rinqa ture ta tunda mama da Aisha ma haka suke mata, amma shi taga har rungumeta ma Yayi sosai, ta Kalli fuskar shi, indonshi a lumshe yana baccee cikin wata irin natsuwa, a ranta tache shi kam ko baccee yakeyi a natse yake yin shi, tanajin wani iri a jikinta, ita dai tunda ta dena jin tsoron ynzu zata koma dakinta da baccee, Batason yadda yake baccee ba riga, gashi ynzu so biyu kenan tana tashi baccee a jikin shi, ta kalli lips dinshi tana ganin yadda suka bada wani shape, lip dinshi na qasa yafi dan cika, na sama kuma be kai girman na qasa ba amma yanada wani irin shape kamar cupids bow, gasu very smooth, ta kai hannu ta taba su a hnkali, ya bude ido ya kalleta, qurr suka yima juna na yan sakanni kafin qwaqwalwar maryam tayi processing ta gaya mata abnda ya kamata tayi, da sauri ta wuntsila don ta sauka daga kan gadon seda ta kife a qasa dama qarshen gadon suke, ta tashi ta sheqa ta fita da gudu, dariya yaketa yi daga nan kwance yana kallonta har ta fice 

Dakinta ta shige ta zauna kan gado tana maida numfashi, gabadaya kunya ta rufe ta, a ranta take raya bazata fita daga daki ba se taji fitar shi daga gidan, juyawa tayi se taga wayar ta a kan gadon, tana budewa se taga cikin notes take, Ta kalli abubuwan da ta rubuta 

Aisha.

Northern Crest Holdings.

Rahman Balarabe.

Hajiya raliya.

Ƙofar da ke bayan garden.

yanzu kuma gashi wani yana mata magana jiya kamar yana kallonta.

Ta sauke ajiyar zuciya.

“Allah ka taimake ni.”

Ta tashi tayi wanka

Bayan ta gama shafa mai da abubuwanta, tasa wata silk gown, brown color, batason ta fito amma wata irin yunwa takeji, tun tana daurewa har ta yanke shawarar tayi sauri ta sauka tayi abnda zatayi ta dawo kafin ya fito

Da ta fito daga ɗakinta, da sanɗa ta wuce kofar zaid wai kada yaji motsin ta, amma tana fara sauka stairs ta ganshi zaune a parlour, Yana sanye da black wando da light blue shirt, ya nannaɗe sleeves ɗin nasa sun ɗaga sama da wuyan hannu, ya jingina kan kujerar da yake zaune Yana waya.

Maryam ta tsaya, ba ta son ta katse shi, kuma tanaso taji wayar shiyasa bata wuche ba, abnda yake fadi ya dauki hnkalinta har ta manta da abnda tayi dazu, a ranta take raya kamar da macce yake waya kuma gashi yana dan murmushi, Anya kuwa? Wacece wannan?

“Yes, I saw the documents.”

Ya saurara.

“No, send me the updated version.”

Ya ɗan yi shiru.

“I’ll review everything before the meeting.”

Maryam ta wuce ta baya ta zauna a wata sofa.

Zaid bai lura da ita ba.

Sai bayan ɗan lokaci, muryarsa ta sauya kuma

Ba kamar yadda yake magana da ma’aikatan office ba.

“Oh…really? so how is Amsterdam?”

Maryam ta ɗago kai taga ya yi murmushi kaɗan kamar yana kallon wadda yake waya da ita

“Really?”

Ya saurara.

“I miss our office meetings.”

Maryam ta yi kasaqe tana kallon shi

Zaid ya ɗan yi dariya.

“Yes, I miss that too.”

Kunnenta ya tsaya cak kansa.

“And i miss the coffee you serve me there.”

Ya yi murmushi.

“Yes And the late meetings…”

Ya yi shiru yana sauraro.

“Yeah. Those too.”

Maryam ta sauke ajiyar zuciya.

Ta kasa fahimtar abin da ya sa maganar ta dame ta, Ba ta san matar ba, Ba ta san relationship ɗinsu ba, Amma yadda Zaid yake magana da ita…Ya bambanta da sauran office calls din da yakeyi

“I’ll see you soon, In Sha Allah, bye”

Sai ya kashe wayar.

Ya ɗago kai.

Sai ya ga Maryam tana kallonsa.

“Ina kwana.”

“morning.”

Zaid ya kalle ta.

“Yaushe kika sauko? Kin jima?”

“A’a.”

Ya gyada kai.

Yanaso ya tsokane ta amma Sai ya lura da yanayinta.

“Me ya faru?”

“Ba komi”

“Kin tabbata?

“Eh.”

Ya kalleta na ƴa seconds.

“Okay.”

Ya koma kan wayarsa.

Maryam ta yi shiru, Amma a zuciyarta…Tana tunani 

Da wa yake waya?

Ta yi saurin kawar da tunanin.

“Toh ni Me ya shafe ni?”

Ta faɗa a ranta.

Amma zuciyarta ba ta amsa mata ba

Koda ta wuche kitchen oats ta dama musu tanata tunanin wayar nan da Yayi har ta qare ta juye a bowls, ta yanka strawberries a sama sannan ta zuba blueberries ta dauka ta ajiye dining 

Bayan sunyi breakfast, Zaid ya ce mata:

“Kije ki shirya.”

Maryam ta kalle shi.

“In shirya?”

“Eh Zamu fita, zamuje immigration office”

“Immigration office?”

“Yes. Zamu fara passport process dinki, nayi magana da comptroller general, yache muje ynzu zaayi yau a bamu”

“Yanzu?”

“Eh manah.”

Maryam ta yi murmushi.

“Okay.”

Ta tashi.

Ta koma dakinta ta shirya, ta saka atampa super holland me blue da brown ta daura dankwalin, ta saka Qaramin matching veil ta dauko qaramar jakarta ta channel ta sauko, zaid yana kallonta tana saukowa, a qasa qasa ya furta “ya khaliq” ganin yadda Tayi kyau.

Bayan kusan 30mins suka fita gidan don seda suka shiga wurin mammi suka gaida ta

A cikin mota, Maryam tanata kallon garin Abuja ta window.

Wannan ne karo na farko da ta fita da Zaid tun da suka zo.

Zaid yana driving a natse, Ta kalle shi.

“Yaya”

“Naam?” ya amsa amma a ran shi yana tunanin yau dole ya gaya mata ta chanja yadda zata rinqa kiran shi, shi zayd ma ya ishe shi

“Waccan matar…”

Ya kalleta na ɗan second, ya maida hnkali ga driving 

“Wace mata?”

“Wadda naji kuna magana da safe.”

Zaid ya dawo da idonsa kanta

“Wadda ta kira daga Amsterdam?”

“Eh.”

Ya maida hnkali kan driving “Business associate ce.”

Maryam ta gyada kai.

“Oh. Okay”

Sai Zaid ya tambaye ta:

“Meyasa kika tambaya?”

“Ba komai”

Ya kalle ta na ɗan lokaci.

Sai ya maida hankalin shi kan driving.

Maryam ta kalli window, Tanajin kunyar kanta.

Me yasa na tambaye shi?

A immigration office, sun bi komi step by step kafin a kai su wajen capturing passport photograph.

Maryam ta zauna a gaban camera.

Photographer ɗin ya gyara setting din laptop dinshi da camera a Saman ta

“Please look straight.”

Maryam ta daidaita zamanta, Amma curls ɗinta sun sauko a gaban goshinta.

Photographer ɗin ya ce:

“Your hair is covering part of your face.”

Ya miƙa hannunsa zai matsar da gashin daga goshinta.

Kafin hannunsa ya taɓa ta..

Zaid ya matso da sauri..

“Let me.”

Ya ɗaga hannunsa ya cire curls ɗin a hankali daga gaban fuskarta, ya mayar da su gefe.

Photographer ɗin ya ɗan tsaya.

“Okay.”

Zaid ya ja baya.

“Now?”

“Yes. Perfect.”

Maryam ta kalli Zaid.

Shi kuma ya koma gefe kamar babu abin da ya faru.

Photographer ɗin ya ɗauki hoton.

“Done.”

Maryam ta sauka.

Ta matso kusa da Zaid, Sai ya juya ya fare tafiya

“Zo muje.”

Ta bi shi.

Amma a ranta…Wannan Zaid ɗin fa…Anya shine wanda ta fara gani?

Bayan sun gama passport process, suka wuche mota, a qa’ida passport yana kai 7 days amma su gasu rana daya an gama komai har sun fito saboda magana ake ta kuddi

Ya bude ma Maryam ta shiga mota ta zauna

Sannan ya shiga driver’s seat, Ya kunna motar fuskar shi a daure

Daga immigration direct suka nufi embassy.

A hanya, Maryam ta chigaba da tunanin matar da ta yayi waya da ita tana “maimaita business associate” a ranta

A zuciyarta, ta fara jin wani abu da ba ta saba ji ba, Ba fushi ba, Ba haushi ba, Wani irin rashin jin daadi, Ta yi ƙoƙarin kawar da shi, Amma duk lokacin da ta tuna yadda Zaid ya ce:

I miss our office meetings, and the coffee you serve me

Zuciyarta tana ɗan nauyi.

Me yasa na damu haka?

A embassy, bayan sun shiga, suka fara wasu procedures.

Wani mutum ne ke kula da paperwork ɗinsu.

Emmanuel shine sunan da ke rubuche a kan dan qarfen da ake ajiyewa a gaban kowane ma’aikachi a wurin

Ya kalli documents ɗin.

“Mr. Balarabe?”

“Yes.”

“Your wife?”

Zaid ya gyada kai.

“Yes.”

Emmanuel ya kalli Maryam.

“Mrs. Balarabe.”

Maryam ta amsa 

“Yes”

Ya karɓi passport ɗin.

“Everything seems fine.”

Sai ya kalli Maryam.

“Your hair is beautiful.”

Maryam ta ɗan yi mamaki.

“Thank you.”

Emmanuel ya yi murmushi.

“Are those curls natural?”

Maryam ta gyada kai.

“Yes.”

“Wow.”

Ya yi dariya.

“I rarely see curls like that.”

Maryam ta yi murmushi.

Zaid yana tsaye kusa da ita fuska a daure, Ya yi shiru yana danna waya amma duk hankalinshi yana wurin su 

Emmanuel ya kalli Maryam sosai.

“Are you sure you’re from Nigeria?”

Maryam ta yi dariya kaɗan.

“Yes.”

“Really?”

“Yes I am”

Emmanuel ya yi murmushi.

“You are too beautiful to stay in this country.”

Maryam ta yi shiru, Ta ɗan ji kunya.

“Thank you.”

Zaid ya kalli Emmanuel.

Fuskarsa a daure

Emmanuel ya ci gaba da magana.

“Your husband is lucky.”

Zaid ya amsa mishi

“I know, now do what you’re suppose to do, we’re in a hurry”

Maryam ta kalli Zaid, Ta kasa riƙe murmushinta.

Emmanuel ya miqo mata wani paper.

“I’m sorry Please sign here.”

Maryam ta karɓa.

Zaid ya kasa cire idanunsa daga Emmanuel, yana mishi wani kallo me kamar harara

Sai Emmanuel ya kalli Zaid.

“Everything okay, sir?”

“Yes.”

“Sure?”

“Yes.”

Amsar ta fito da sauri kuma da qarfi fiye da yadda Zaid ya shirya fitowarta 

Emmanuel ya yi murmushi kaɗan.

“Alright.”

Maryam ta kalli Zaid.

Ta fara fahimtar wani abu.

 Kamar haushi yakeji

Ba ta san dalilin ba, me aka mishi kuma?

Da suka fita daga embassy, suka shiga mota.

Zaid ya yi shiru, Ya kunna mota, Ya fara driving, Maryam ta kalle shi.

“Yaya”

“Naam?”

“Lafiya kake?”

“Lafiya” ya amsa

“Sure?”

“Yes.”

“fuskar ka ta chanja ba kamar yadda muka fito gida ba”

“driving nike shiyasa”

Maryam ta yi murmushi.

“Amma dazu kana driving kana magana har waya kayi”

Zaid bai ce komai ba.

Ta kalle shi.

“Emmanuel ne?”

Zaid ya ɗan matse steering ɗin.

“Me yayi?”

“Okay bq komai na dauka ya bata maka rai da ya barka a tsaye”

Shiru…ya ratsa

Bayan ƴan mintuna, Zayd yaja tsaki

“Ya cika surutun banza”

Maryam ta dan yi mamaki.

“Waye?”

“Emmanuel.”

Ta kasa riƙe dariyarta.

“Maybe.”

Zaid ya kalle ta.

“Miye abun dariya?”

“Nothing.”

“Mahreeyam”

Ta yi murmushi kadan

“Ba komai fah”

Ya koma kallon hanya.

Sai Maryam ta lura da yadda ya yi shiru.

A hankali ta sunkuyar da kai.

Yaji haushi da Emmanuel ke yimin mgana? No ba haka bane kawai yaji haushi ana bata mishi lokaci ne

Sai zuciyarta ta yi wani irin tsalle.

Tanata ƙoƙarin ɓoye murmushin da ya bayyana a fuskarta.

Zaid kam haryanzu fuska a daure, Amma a cikin zuciyarsa…tunani yake

Meyasa naji haushi da yake mata magana?

Bai samu amsar ba.

Da suka dawo gida, Maryam ta shiga ɗakinta.

Ta cire veil, Ta zauna gaban mirror, Ta kalli gashinta, Sai ta tuna photographer ɗin dazu, da Yadda Zaid yayi sauri ya matso ya chire hannun shi ya gyara mata gashin 

Sai ta tuna Emmanuel.

Your hair is beautiful.

You are too beautiful to stay in this country.

Sai ta yi murmushi.

Amma daga nan, tunaninta ya koma ga Zaid da wayar shi ta safe.

I miss our office meetings.

Murmushin ya ɓace mata

Ta ɗauki pillow ta rungume.

“Me yasa na damu?”

Ta faɗa a hankali.

Ta yi shiru.

Sai ta ce:

“Ko…dai…ina kishin sa ne?”

Ta buɗe idanunta sosai.

Ta girgiza kai.

“Allah Ya kiyaye ni ba soyayya nazo yi nan gidan ba”

Ta tashi da sauri kamar tanaso ta kori tunanin.

A ɗayan ɓangaren gidan, Zaid yana office dinshi na cikin gida, Laptop ɗinsa a gabansa.

Amma hankalinsa baya kan komi

Yana tunanin embassy, Yana tunanin Emmanuel.

Yana tunanin yadda mutumin ya kalli Maryam.

Ya sauke ajiyar zuciya.

“Too beautiful to stay in this country…”

Ya maimaita kalmar a ransa.

Sai ya ɗan yi tsaki.

“Ridiculous.”

Amma bayan seconds kaɗan…

sai ya yi murmushi.

Ya tuna yadda Maryam ta kalle shi a cikin mota.

Emmanuel ya bata maka rai ne?

Ya rufe laptop ɗinsa.

Sai ya fahimci wani abu da bai shirya amincewa da shi ba.

Bai ji daɗin yadda wani namiji yake kallon matarsa ba.

Kuma abin ya dame shi fiye da yadda ya kamata.

Da dare, Maryam tana zaune a kan gadonta tana duba documents ɗin passport da embassy.

Zuwa Amsterdam yana ƙara zamar mata real.

Ta tashi ta chnja kaya zuwa simple English gown ta sauko ta shiga kitchen cook yana taya ta da gyara abubuwa, ta girka coconut rice da chunks din kifi a ciki, sannan ta hada pineapple juice, tasa abincin a warmer ta kai dining ta ajiye, ta koma kitchen ta diba tasa ma mammi a food warmer ta bada a kai mata.

Parlour ta dawo ta kunna burner dinta saboda taji qamshin abncin har cikin parlor, ta zauna ta kunna tv, zaid be fito daga office dinshi ba seda aka fara kiran sallar magrib, yaje masallaci ya dawo, yana shigowa itama tana saukowa daga upstairs itama ta idar da sallah, miqe hannun shi yayi ta tsaya tana kallon shi yayi mata alamar tazo, ta tako a hnkali tazo gabanshi ta tsaya, ya riqe hannunta ya jata suka zauna kan kujera, yana murza yastunta a hnkali ya fara magana “yaushe zaki dena chemin yaya?”

“Toh ai bazan iya kiran sunan ka ba”

“Ki kirani zayd kawai ko kuma Kisa min wani sunan idan bazaki iya kirana da sunana ba, banason yaya” 

tayi shuru tana tunani

“Toh me zanche maka?” 

Ni ba ina che miki mahreeyam ba? Kuma ina kiran ki hayatee? Kema ki nemo naki”

“Toh zanyi tunani”

“Zuwa Yaushe” 

“Zuwa sati daya”

“Aa kiyi tunanin kafin muyi baccee se ki gayamin”

“Kai kai yayi sauri ai”

“In lokacin yayi baki samu ba se in qara miki lokaci”

“Toh shikenan”

Dining sukaje suka chi abnci, shi kam zaid yana mamakin yadda maryam ta iya girki a cikin ranshi, yana chin abncin ji yake kamar kunnuwanshi suna motsawa, ga pineapple juice din yana shiga har cikin kan shi, seda suka qare suka koma parlor suka zauna

Suna zaune akayi isha, ya fita masallaci ita kuma ta hau sama, a masallaci ya hadu da Fahad, da suke dawowa suna magana zaid ke gaya mishi chewa yanaso yasan yadda zaayi wannan yaron da akache da yana son maryam a samar mishi aiki a northern crest, koda basu buqatar ma’aikata ayi creating vacancy a daukeshi kawai, kuma a bashi salary me kyau shi ze rinqa turo kuddin da za’a rinqa biyan shi, Fahad na dariya yake fadin kai dai so kake ka yimishi dannar qirji tunda ka yimishi fin qarfi, zaid yayi shuru yana tunanin inda yaqi yadda ya auri maryam ai da yayi ma kanshi, ko a haka ma shi ya yadda ze chigaba da renonta saboda ynzu dai kam bayajin akwai abnda ze rabashi da ita, a dd nan suka iso tsakiyar babban compound din inda kowa ze dauki hanyar part dinshi, zaid yana yima Fahad insisting cikin satin nan a nema ma imran vacancy sannan kuma bayason yasan chewa kawai alfarma akayi aka dauke shi, yafi son a nuna mishi ya chanchanta ne, a kirashi interview and everything, yanaso abi normal procedure yadda imran din bazeyi zargin alfarma aka mishi ba, Fahad na dariya yake fadin bakada matsala ranka ya dade zaayi komi a qare cikin satin nan ba tareda an bari yayi zargin komi ba, a haka suka rabu.

Koda ya shigo ba kowa a parlorn se qamshin turaren wuta da ke tashi a hnkali, sama ya hau ya wuche dakinta, be ganta ba amma yaji motsi a bathroom se ya kwanta rigingine kan gadon yana tunanin ayukkan da ya bari be qarasa ba, amma kuma baze iya qarasawar ba, yana kwanche yaji fitowar ta, ya bude ido yana kallonta, bata lura dashi ba, ta nufi dresser tana daure da towel fari a jikinta, ta  daure kanta da ribbon chan sama gudun kada ruwa su jiqa shi, amma ga wasu curls sun sauko duk sun jiqe suna maqale a goshinta da wuyan ta, ta zauna tana shafa mai a natse har ta qare, yana kallonta ta tashi ta nufi closet ta dauko kayan baccee riga navy blue zatasa se kawai taji muryar shi yana fadin “kisa waccan white din, su nikeso” da wani irin sauri ta juyo ta kalleshi a razane sannan da gudu ta shige chan quryar dresser din da sauri tasa kayan, ta dade a tsaye ta kasa fitowa, tanata tunani a ranta, ga wata irin kunya da takeji, tun Yaushe ya shigo? A take ta tuna da abnda tayi dazu da safe, se taji kamar qasa ta bude ta shige ciki, yana nan kwanche seda ya gaji ya tashi ya leqa, ya ganta a tsaye se ya shiga, kanta na qasa tana jinshi amma ta kasa dago kai Wata irin kunya duk ta mamaye ta, “Inata jiran ki kin banni kina nan zaman ki” tayi shiru se ya matso gab da ita ya kama hannunta yana murzawa a hnkali, yasa dayan hannun shi ya dago fuskar ta suka hada ido yaga hawaye kwanche a idonta, seda ya matso daf da fuskar ta a hnkali chan qasan maqoshin shi  ya furta “wa ya taba min Mijn kleintje” ta runtse idonta da karfi jin yadda numfashin shi ke sauka a fuskar ta, hawayen da ke idonta suka gangaro, seda Yayi murmushi don yasan kukan me takeyi, yasa hannu ya goge mata hawayen, se ya jawota jikinshi ya rungumeta, suna a haka tsawon lokaci se kawai taji ya dauketa ya fara tafiya, so take ta gaya mishi zata gyara gashinta amma ta kasa, bata bude idonta ba har ya kwantar da ita yaja mata duvet se taji ya bude qofar bathroom ya shiga, ta bude ido a hankali taganta kwanche a kan gadon shi, se ta tuna da “wa ya taba min Mijn kleintje” miye kuma wannan? Wane yare ne yayi, jin qarar bude qofa yasa ta rufe idonta da sauri, tanajin motsin shi ya shiga closet dinshi a chan ya shirya yasa wandon pj da jallabiya ya kabbarta sallah, har yayi shafa’i da witr idonta biyu, yayi addua me tsayi sannan ya chire jallabiyar jikinshi ya hauro gadon, a ranta tana fadin toh meyasa wai baya baccee da riga? Tana cikin tunanin taji yana shafa mata addua a jiki, wani irin shock taji yabi jikinta, Kamar jikinta ze fara rawa, ba kama bane don kam har ya fara rawar, zaid Yayi murmushi ya gane idonta biyu, a ranshi yache bari in ga qarshen tsoron, a hnkali ya jawota jikinshi, jikinta be fasa rawa ba, ya matso da ita jikin shi sosai sannan ya dora bakin shi akan nata a hnkali ya fara kissing dinta, maryam numfashinta daukewa Yayi gabadaya taji ba iska a kofofin hancin ta, Tana Neman inda zataji iska ta shaqa taji yana sake matse ta jikinshi, se kawai kuka ya kucce mata, ya dan dago fuskar shi ya kalleta yana murmushi, yaga haryanzu idonta a rufe se hawaye ke gangarowa daga ciki, yayi murmushi “wane suna zaki bani?” Shuru maryam kam ba baki se kunne, ya sake maimaita tambayar amma shuru se yayi murmushi kadan “tunda ma baccee take Bari in dan qara, dama na dade ina kallon lips dinnan, a take ta bude ido qur suka hada ido fuskar su tana dab da juna tayi sauri ta rufe idon, zaid kam dariyar shi seda Tayi dan sauti, “ki gayamin suna na ko in chigaba ne?”

A hnkali ta furta “My Giant, zan rinqa kiranka my G in a short form” 

ynzu kam sautin dariyar da Yayi hada girgiza kai, “lallai nine ma giant din, toh shikenan na yadda, dazu da nache miki wa ya taba min Mijn kleintje kinsan abnda nache?” 

Ta girgiza kai alamar aa

“chewa nayi wa ya taba min my little baby, kinga shikenan ni giant ke kuma baby” 

“Toh ni ba baby bache na girma ai”

“Toh ni da kikache min giant ni giant ne?”

“Amma ai kanada girma sosai ka fini girma”

“Toh ai tunda na fiki girma shiyasa kika zama babyna, babyna ni kadai”

Tayi shuru batache komai ba

Ya rungumeta yayi kissing goshin ta

“Good night Mijn kleintje”

Shiru batache komi ba, “bari in dan qara tunda ta koma baccin, cikin sauri ta furta “Goodnight”

“Banson goodnight kawai se kin hada da sunan da kika bani”

Seda ta turo baki sannan ta fadi “Goodnight MyG”

Yayi hugging dinta yana fara kissing bakin da ta turo, wani irin shock Maryam ta sake shiga wanda ma yafi na farkon, daqyar ma ta samu kukan ya fara fitowa don ta dauka ko ma ta suma ne, zaid kam bayason yabar abnda yakeyi amma yana jin kukanta cikin kan shi, ya jaye bakin shi Yayi hugging dinta ya matse ta a jikinshi “shhhhh ya isa, ba ke kika turo min bakin ba” ai maryam tsit tayi ko dogon motsi bata sake yi ba har baccee Yayi gaba da ita

Seda zaid yaji ta fara sauke ajiyar zuciya alamar baccinta ya fara nisa sannan ya sassauta riqon da Yayi mata shima yana qoqarin yin baccin 


Follow this link to join my WhatsApp group: ***