Zaren Rayuwar Mu

BABI NA GOMA SHA TAKWAS

by @zainabb

Zaren Rayuwar Mu 

SATI ƊAYA nayi a cikin gida ba tare da Zaid ba naji duk gidan ya ishe ni. Shirun shi ya min yawa ta yadda banyi zato ba. Baya kira se de kullum yana turo min good morning text. A kowace rana kuma ina amsawa. Ya zame min jiki a kullum ina jiran saƙon shi. Idan yayi latti be turo ba na shiga damuwar da bana so kenan kuma duk notification da ze shigo min ina tsammanin shine se idan na duba ba shi bane ba na zama very disappointed. 

Yau tunda safe nake jiran saƙon nashi amma be turo ba. Na tafi wurin aiki da son ganin saƙon shi. Duk da aiki nake haka nake duban waya ta akai akai har se da Hanna tace “Lafiya kuwa, Hadiza?”
Murmushi na fara yi har zan ce mata babu komai se nace “I'm waiting for my husband's text”
Murmushi tayi tace “Ban taɓa jin kin ce wani abu akan mijin ki ba. Ina ta tunanin ko an miki auren haɗi ne da wani tsoho”
Dariya nayi ina ganin wacce ban taɓa irin ta ba a wurin aikina “No, my husband is a young man. I'm even older than him” nace kamar me ji da wannan gaskiyar. A da zan ji kunyar cewa na girme mijina amma yanzu i took pride in telling Hanna that I'm older than him. 
“Ma Sha Allah. This is nice. I love hearing about this. Allah ya bar ku tare”
Shiru nayi ban ce Amin ba se murmushin da nayi muka cigaba da aikinmu. 

Har na dawo gida bayan La'asar saƙon Zaid be shigo ba. Nan take raina ya ɓaci ina tunanin ko yana chan tare da wasu suna cire mishi duk abinda bana iya mishi a gida. 
Saƙon shi be shigo a waya ta ba se wuraren ƙarfe takwas na dare. Kallon saƙon na dinga yi ban buɗe ba ina ta blinking idanuna ahankali duk da nasan zan maida mishi amsa yau. Nayi tsawon minti biyar ina kallon saƙon nashi kafin na samu nace “You finally got time to message Diza?”
Kallon wayar na dinga yi da lokacin da yake wucewa tun lokacin da na tura saƙon amma be min reply ba. Minti goma suka wuce ina ta kallon waya ta tare da jin haushi sosai zuciya ta na min saƙe-saƙe daban daban. Chan se saƙon shi ya shigo “No, not that, I'm just tired. I need to sleep. Goodnight.” Baƙin cikin da naji akan saƙon shi, da ya sani be min reply ba. Duk da ban san shi da ƙarya ba kuma bana tunanin yana kula mata amma abinda nake tunani yanzu kenan saboda nasan yana ƙaunata sosai ko bacci yake ji ze iya sacrificing nashi domin muyi magana da juna. Amma kuma gashi ba haka bane ba. Ban bashi amsar saƙon shi ba na kashe waya ta ina tunanin wannan sabon al'amari me faruwa dani tare da jin haushin kaina. Yanzu abinda zanyi shine na koyawa kaina ƙin kula Zaid da rashin nuna damuwa ko ya kula ni ko be kula ni ba. Nayi surpassing duk wani abu da nake ji game dashi nayi guarding zuciya ta mu cigaba da rayuwa a yanda muke. Tunani kuma ya faɗo min a raina. Zan iya cigaba da zama dashi ahaka ba zan cutawa kaina ba ko haƙuri zan yi na zauna dashi kamar ma'aurata masu ƙaunar junansu ko haƙuri zanyi da auren nayi provoking nashi sosai ya rabu dani?.

Haka muka cigaba dashi lokacin da yayi sati biyu a Australia. Saƙo ze tura min yana me gaida ni idan da safe ne ze ce good morning idan rana ze ce good afternoon, idan kuma da marece ze ce good evening ya haɗa da i hope you're good, Diza. Shi kawai yake turowa be taɓa kira ba. Ni kuma idan ya turo ina amsawa duk da bana so. 

A ranar da ya dawo Nigeria, Muhammad ya dawo dashi gida. Gaisawa kawai muka yi ya wuce. Daga ni se shi a cikin gida. Sannu da zuwa na mishi ya amsa min fuskar shi a sake ya wuce ɗakin shi nima na wuce ɗaki na. Ban mishi girki ba ban yi komai ba da mutum ke yi idan mijinta yayi tafiya ya dawo. Shi kuma Zaid be neme ni ba. Dama nasan ba ze neme ni ba amma kuma so nake ya neme ni wanda nasan ba ze yi ba. 
Kwance nayi a gadona ina tunanin rayuwa ta. Nasan Zaid haƙuri ne yake dani saboda ko ni nasan ban kyauta ba ko ban mishi komai ba ya kamata nayi abincin da ze taho ya samu. 

Da yake gobe ranar hutu ce, se ga Yaya Hauwa da Shahida. Bata taho da Zara ba da na tambaya ina Zara tace tana inda kakannin ta. 
Yaya Hauwa na zaune a parlour tace ma tashi zata yi ta wuce dama Zaid kawai ta taho ta gani. Idanun shi na cike da gajiya da bacci yana tsaye wurin ta suna magana. “Bacci kake ji ne?”
“Yes, tired and sleepy” 
   “Yanzu wucewa zanyi kaje ka huta”
     “In sha Allah” yace ya kalla Shahida yace “Se anjima zaki tafi ko?”
Girgiza kai tayi “Tare da Yaya Hauwa zan wuce. Dama nace zan zo na gan ka kwana biyu”
Murmushi yayi yace “Nagode Shahida”
Tashi Yaya Hauwa tayi itama Shahida ta tashi tsaye. Idanun ta suka kai kan dining table namu ta gan shi wayam babu komai akai. “Ni ban san irin ku ba. Baku so ku ci abinci ne ko menene matsalar ku da girki? Ko matar taka bata iya girki bane, Zaid?” Yaya Hauwa ta faɗa idanunta sun kasa barin nawa. Sunkuyar da kai nayi saboda yanda naga Zaid yana girmama ta kamar mahaifiyyar shi. 
  “Bamu jima da gama cin abinci ba. Se anjima za'a dafa wani” Zaid ya kare ni 
“Wace anjima kenan? Yanzu ƙarfe shida”
“Ba wani abu bane me nauyi, Yaya”
“Dan Allah a dinga kula da abincin yaron nan bana son wani abu ya same shi” Yaya Hauwa tace tana nufin Zaid kuma dani take.
 
Fita suka yi ya raka su. A chan har Shahida ta shiga mota ta zauna, Yaya Hauwa tace “Kana jin daɗin wannan auren, Zaid? Wannan matar naka ban yarda da ita ba sam. She looks quiet and peaceful but I don't trust her”
   “A'a Yaya. Diza bata da wani matsala”
“Allah yasa ba kare ta kake ba. Kuma duk lokacin da na gano something about you two that's off with concrete evidence, you won't like what I'll do. I know you but I don't know your wife“
Shiru Zaid yayi har suka tafi yana tunanin idan Yaya Hauwa tasan abinda yake faruwa a gidanshi me zata yi.
Bayan ya dawo ya wuce ɗakin shi komai be ce min ba game da abinda Yaya Hauwa ta faɗa. 

A cikin satin da ya dawo na cigaba da observing nashi. Na lura baya cin abinci da zafi kuma mafi yawan dare yana shan strawberry Lipton. Na lura baya sa manyan kaya se de t-shirt da trousers kuma kamar yadda yake da tsawo haka ƙafafuwan shi suke da tsayi. Ya kan yi aski amma kuma ba'a cire mishi suma da yawa, za'a bar shi da sumar shi kamar trimming ne kawai yake. Ban taɓa sani ba se lokacin nan harda ƙwallon ƙafa yake kallo amma ba kowace ba. Nasan arsenal ne team da yake so. Da nasan team da yake so yasa na kan duba abubuwa game da arsenal. Yanzu na rage zama a cikin ɗaki na se de na fito na zauna parlour saboda kawai naga Zaid. 

Shigowa yayi goye da schoolbag a bayan shi wayar shi na riƙe a hannun shi da makullin motar shi. Birge ni yayi har se da muka haɗa idanu tare dashi yayi muttering Diza kafin ya wuce ciki. Ƙafafuwana na haɗe ina jin jikina yana chanja min. Tashi nayi na shiga ɗakina nayi wanka na sanyawa kaina ruwan zafi saboda na dena jin abinda nake ji amma kuma kamar abinda na ƙara. A parlour na dawo ina sanye da wata ƙaramar riga ta tsaya daidai guiwa ta. Inaso Zaid ya fito ya ƙara tambaya na ko nasan menene aure, yau a shirye nake da aurenmu. Be fito ba yasa na wuce ɗakin shi. Koda na shiga na samu yana tsaye kusa da vanity table ya ɗan matsa ina ganin abinda yake a cikin laptop ɗin shi. Sunan wata mace na gani an turo mishi e-mail sunan ta ba na ƴan Nigeria ba na western country ne. Ban san lokacin da na haɗe wani abu a maƙoshina ba. “Zaid” nace 
Juyowa yayi babu alamar tsoro ko firgici gare shi “Diza” ya amsa ni tare da kallon yadda nake saboda rigar kawai ce a jiki na babu komai a ƙasa na. Silk ce and not transparent. Maida duban shi ga laptop yayi yace “I met someone in Australia”
          “Work?”
     “Yes”
“That's a lie”
Kamar na faɗi wani abu me girma yasa Zaid juyowa yana kallo na yace “Ni nake ƙarya?”
Sunkuyar da kaina nayi ina jin kunya ta rufe ni. 
      “I mean....I mean you see.......
    “No, that's what you meant. I'm lying. But have I ever lied to you?”
Girgiza kai nayi na ɗago kaina ina kallon shi. I don't want to feel as if he's older than me. Juyawa ya sake yi ya gama rubutun da yake ya tura ya rufe laptop ɗin shi. Ina nan tsaye shi kuma har ya kwanta a gado looking tired yana kallo na da jiki na. 
“Me kike so Diza?” ya tambaye ni yana kallona tare da tashi tsaye. Wurina ya iso ya riƙe ni a jikin shi ya kai duka hannuwan shi a bosoms nawa yayi squeezing not roughly but softly. “Zaid” nace cikin muryar da ban taɓa yi mishi ba “I just want company that's why I'm here.”
A jikin bango ya kai jikina ya haɗe da nashi and he started kissing me with one of his hands on my bosom. My breathing was fast and audible na ɗaura hannuna akan chest ɗin shi har ina tura mishi yatsa na. 

Fuska ta da nashi ya haɗe, idanuna na rufe naji yace “I love you Diza. I just don't know what's in your head but I love you. That's the truth I know about myself”
Fuskar shi ya ɗaura a chest ɗina yana jin ƙamshin turaren da nake ina jin numfashin sa. Ban san abinda yake ji ba ya cire jikin shi a nawa ya koma ya kwanta akan gado and that's not what I wanted. I want to have intimacy with him and I know he knows it too. 
Idanun shi na rufe yace “I'm tired. Maybe some other time, Diza”
Da sauri jin haka yasa na dawo gefen shi na zauna a gefen gado ina kallon fuskar shi da idanun shi dake rufe. Hannuna nasa a nashi na riƙe tightly. “I know you're tired. Do you want me to be open and tell you what I want?”
Zaid be buɗe idanun shi ba. 
   “Zaid” na kira shi ahankali
Idanun shin na rufe yace “Uhmm Diza”
“5mins will be okay for me. I promise” na faɗa ina jin ƙarfin abinda nake ji. Yasan ya gaji yake kai hannunshi a jiki na?
“I can't do anything for you, Diza. I'm tired and sleepy” Zaid ya sake faɗa. Riƙon da nayi wa hannun shi na fara saki. “Is there any woman?” Hadiza tace. Babu wata mace da nake kulawa. Nayi wannan abun ne saboda irin wahalar da ta bani na tsawon wata biyu har ana ƙoƙarin na uku. Kenan se idan itace ke jin irin wannan abun, ita kaɗai ce za'a saukewa hakki ita ba zata sauke hakkin mijinta ba?
“No, why?”
Shiru nayi ban ce mishi komai ba bana tsammanin irin wannan abun daga wurin shi. Tashi nayi na fita daga cikin ɗakin ina jin haushin kaina da duk abinda nake ji. Ko a mafarki akace Zaid ze min irin haka ba zan taɓa yarda ba amma de gashi ya min kuma yana gani na ba aike na mishi ba. 

Tun daga ranar na ƙara kudirtawa raina cewa zan cigaba da guarding dukkan kaina. Zan dena observing Zaid na dena kallon shi da danne duk abinda nake ji a zuciya ta. Haka na fara ƙoƙari tare da avoiding ɗin shi se ma ayi ranaku ban bari na gan shi ba. Ko kaɗan wannan be dame shi ba. Nasan yana nan a cikin ranshi yana cewa ban san abinda ake cewa aure ba. 
Nayi shutting kowa out of my life kaɗaici ya min yawa yasa na shirya na tafi gidan Yaya Hauwa. Yanzu tana gida duk kwanakin nan tana annual leave ne. 
Shiga kitchen take yi tana dafa abinci gidanta na ƙamshin turaren wuta na Kajiji. Ko ina yayi shiru babu hayaniya. 
“Ya kuke ke da Zaid?” ta tambaye ni 
 “Lafiya lau Yaya”
Shiru tayi ban san abinda take tunani ba se kuma tace “Are you guys happy in that marriage?”
Murmushi nayi “Eh Yaya”
   “Na ɗauka ko kin kawo karar shi ne”
Wani murmushi na ƙara yi nace “A'a Zaid baya yin wani abu”

Na jima sosai a gidan har Khalifa ya taho ya same ni ya amsowa Yaya Hauwa saƙo. Bana ganin shi kamar yadda nake ganin Shahida. Shima kyakkyawa ne irin Yayyun sa amma se inaga yana min kama da players. Nan take naji tausayin duk wacce zata so shi da gaske duk da hasashe kawai nake yi. 

Da zan tafi shima ya taso yace na wuce dashi gida dama motar gidan Yaya Hauwa ya fita tare da ita. A cikin mota shiru muka yi babu me cewa wani abu. Da naga shirun yayi yawa nace mishi “Ka kusa gama jami'a, Khalifa?”
    “Da saura. Aji uku nake Yaya”
      “Kayi nisa ai. Yanzu saura shekara biyu. Ai 5year course ne ko?”
     “Eh, 5year course ne. Mun kusa in Sha Allah”
    “Eh, shekara biyu ba nisa yanzu. Ba jimawa zaka ji ance ka gama”
    “Yes, correct. Idan na gama inaso nayi masters”
Nodding Kaina nayi nace “That's beautiful. Nima ina tunanin masters ɗinnan amma ba yanzu ba. Kuma online University nake so na samu saboda lokaci”
     “Ki yiwa Yaya Zaid magana kije wani ƙasa kiyi masters”
Murmushi nayi ban ce mishi komai ba har na aje shi gida. Godiya yayi min ya wuce nima na wuce zuwa gida.