THE LAST DAYS
SOKOTO
Imran ya taba submitting CV dinshi a portal na northern crest holding kusan shekara daya da rabi da suka wuche, kwanakin baya ma yaji sanarwar zasu fara daukar ma’aikata don hake beyi qasa a gwiwa ba ya sake tafiya ya kai cv dinshi wannan karon ba online ba, kwatsam se Email ya gani wai yazo interview ranar Monday da safe, ya gayama inna da baba tun lokacin sunka duqufa addua, Monday koda ya tafi ya tarar da wasu mutane biyu da za’a yima interview din, ya zauna tare dasu, daya bayan daya aka rinqa kiran su suna shiga ciki, koda akazo kan imran ya shiga aka yimishi tambayoyin da za’a yimishi sannan aka duba takardun shi, a take sukache ze iya fara aiki daga gobe, aka hada shi da wata mata ta nuna mishi office dinshi kuma tayi mishi bayanin irin aikin da ze rinqa yi, aka kuma bashi takardar aikin shi yasa hannu, a kan takardar akwai albashin da za’a rinqa biyan shi a rubuche, miliyan shidda a shekara, kenan dubu dari biyar kowane wata, imran dai babu abunda yake fadi se alhamdulillah har ya iso gida, ya tarar da inna da baba suna zaune suna addua Allah yasa dan su ya dache da alheri yayi mishi zabi mafi kyau, yana kallonsu yayi murmushi, baba ya miqe yana jero ma Allah hamdala, imran da inna ma haka suka yita maimaitawa alhamdulillah, seda suka natsa ya fara basu labarin yadda interview din ya kasance se ya qara da “mu uku ne amma inajin ba wanda aka dauka akan albashin da ya kai nawa, naga ma ni kadai akaba office”, inna da baba se hamdala suke tayi, inna ta Kalli imran murna fal fuskar ta “anjima ka shiga ka nuna ma mama” ya amsa da “toh in shaa Allah”
Da yamma imran ya shiga gidan su maryam da sallama, hauwa koulu ta ansa mishi tana qarawa da “ka shiha parlour bari in kira mama”
Ya shiga ya zauna, ita kuma taje ta gayama mama sannan ta dauko mishi lemu da chinchin ta daura kan tray ta kawo mishi
Bayan ta aje Yayi mata godiya ta fita, a ranshi yana qara ganin yanayinta da maryam, se ga mama ta shigo, ya gaida ita a natse sannan ya gabatar mata abun alheri, mama tayi matuqar jin daadi sosai tayi addua da hamdala ga Allah, sannan suka chigaba da firar su, a cikin firar take gaya mishi baban hauwa koulou ya yadda ta tsaya wurinta ta fara university, don haka tanason tasan process din da za’a bi a nemo mata admission, “mama ai inaga kamar an fara registration na jamb, zan iya bincikawa inji inyaso duk sadda ta shirya se in kaita cafe ayi mata”
“Wane shiri zatayi? Ai indai ka shirya Kazo ka kaimin ita kawai” ya amsa da “toh in shaa Allah zuwa gobe tunda yanzu yamma yayi”
Nan ya chigaba da fira da mama har akayi kiran sallar magrib sannan ya tashi ya fito ze tafi masallaci, hauwa ta debo ruwa zatayi arwalla ta ganshi ya fito se ta miqa mishi butar “gashi ka fara yi tunda masallaci zaka tafi” ya karba yana godiya yayi arwallah ya fita.
Maryam che zaune a dakinta da wani irin feeling a ranta, zaid ya fita office yau, gabadaya gidan se yayi mata ba daadi, kwana biyun nan ta saba jin motsin shi cikin gida, tana zaune tanata tunani toh idan suka tafi chan wata qasa da babu me jin yarenta se shi kadai ya zatayi? Ba ta sani ba ko tunanin zuwa Amsterdam ne kawai ke damunta ba, Ko kuma hadda tunanin yadda rayuwarta da ta Zaid da ke canzawa a hankali.
Ta kalli akwatunan da ke gefen wardrobe, dazu kafin ya fita yache mata ta fara hada abubuwan da zata buqata don kada tayi mantuwa, ya kuma che kada ta dauki kayan sawa, tanata mamaki meyasa zeche kada ta dauki kayan sawa? Ze siya mata wasu ne?
Har yanzu babu komai a cikin akwatunan
Amma Zaid ya riga ya gaya mata cewa tafiyar next week ne
Next week yache..
Next week kuma jibi ne
Ita maryam zataje Amsterdam.
Ta yi murmushi kaɗan.
Ta rufe idanunta, A kwanakin baya, Amsterdam ya kasance mata wani wuri mai nisa..Yanzu kuma..tanajin kamar wani wuri ne da zata fara wata rayuwar
Ta tashi ta shiga bathroom tayi wanka, Da ta fito, ta shirya cikin simple long gown mai launin olive green ta gyara kanta ta daure da hair ruffle bata saka dankwali ba
Ta sauko downstairs.
Se taga Zaid yana zaune a parlour.
Yana sanye da black joggers da plain white T-shirt, yana kallon laptop dinsa da alama aiki yakeyi, tanata kallonshi da mamakin Yaushe ya shigo
Yaji motsi ya ɗago kai ya gan ta, Ya tsaya yana kallonta na ƴan seconds.
“Hy”
“Hello”
Ta zauna.
Zaid ya kalleta.
“Kina lfya?”
“Alhamdulillah”
“Good.”
Sai Maryam ta kalli gaban laptop ɗinsa.
“aikina zaki duba min”
Maryam ta yi murmushi.
“Kin fara jin nishadin tafiyar ne?”
“Hmm.”
“Ko dai harynzu?”
Ta yi murmushi.
“Dama inaso inji zan zauna a hostel ko off campus saboda insan irin abubuwan abnci da zan dauka”
“Tare dani zaki zauna, Meyasa zaki zauna hostel ko wani wuri?”
Maryam ta yi shiru.
Sai ya gyara zaman shi
“I mean…ki zauna dani kafin kiyi settling”
Maryam ta sunkuyar da kai.
“Na fahimta.”
“Maganar university din…Akwai Wanda nayi magana dashi”
“Har kayi magana?”
“Eh.”
“Wace university kenan?”
“Nayi mishi magana ne kawai nache zamu duba few options kafin muyi deciding”
Maryam ta yi murmushi.
“Okay.”
“Inaso kuma kiyi deciding da kanki?”
Ta yi shiru.
“Ni?”
“Yes. Karatun ki ne ai”
Maryam ta yi murmushi sosai.
“Nagode sosai amma ka zabar min kawai”
Zaid ya kalleta.
“In shaa Allah”
Sai ya miqe tsaye
Ta sauke ajiyar zuciya.
A hankali ta furta
“Allah Ya saka maka da alheri.”
Washegari da rana, Maryam tana bedroom tana tattara wasu abubuwan da za ta tafi da su.
Ta buɗe wardrobe, Ta fara ware kayan da za ta ɗauka.
Sai ta ji knocking.
“Come in.”
Hajiya Raliya ce.
Maryam ta yi murmushi.
“Hajiya ina wuni?”
Hajiya Raliya ta shigo
“Kin fara packing?”
“Eh. Kadan Kadan”
“Zaki tafi tare da Zaid ne ai, kada ki kwashi unnecessary kaya, ki dauki abubuwa kadan da zaki buqata, in dai zaid ne ya Riga yasa an shirya komi a Chan already har kayan sawa ma”
“Ai shima haka yache min”
Hajiya Raliya ta sauke ajiyar zuciya.
“Ki kula da kan ki dai, Banda shiga abnda be dame ki ba
Maryam ta tsaya.
“In shaa Allah”
Hajiya Raliya ta kalle ta.
“ba wai ina nufin ki ji tsoron Zaid ba fah”
Maryam ta yi shiru.
“Hajiya ni nakasa gane me kike nufi?”
Hajiya Raliya tayi murmushi Kadan
“Toh ai Amsterdam ba Abuja bane ko sokoto shiyasa nache ki kula”
Maryam ta ɗan gyara zaman ta
“Me ke Amsterdam din?”
“Ki tafi da hankalinki da natsuwar ki kar kije chan ki bache” ta fadi tana murmushi
Sai ta miqe zata fita
Amma kafin ta fita, ta tsaya.
“Maryam.”
“Na’am?”
“Idan kin ga wani abu da bai yi miki ba kada kiyi shuru ko ki dauke ido…ki gayama zaid”
Ta fiche daga dakin
Maryam ta tsaya.
Wannan karon maganar Hajiya Raliya bata bata mamaki ba
Se kawai ta chigaba da aikinta
Da yamma Fahad ya shigo part din
Ya tarar da Maryam a parlour.
“Anty Maryam.”
“Fahad.”
Ya zauna opposite ɗinta.
“So…”
Maryam ta kalle shi.
“So what?”
“Zaki tafi Amsterdam abinki ki bammu, ni ban sani ba se mammi ke gayamin dazu”
Ta yi murmushi.
“Makaranta zan fara a Chan”
“Eh haka mammi ke gayamin, duk da dai banji daadi ba antyna zata tafi ta banni, shi da akayima aure saboda ya zauna nigeria ynzu kuma ze dauki matar ya gudu”
Maryam ta yi murmushi.
“Ba vacation zamuje ba fah”
“I know. School zakije shi kuma ze chigaba da business dinshi”
Ya kalleta.
“Toh kinason zuwa dai ko?”
“Eh”
“Good.”
Sai ya yi shiru.
“Akwai wanda kika sani a chan?”
Maryam ta girgiza kai.
“No bnsan kowa ba”
“Kar ki damu ai Zaid yasan Mutane da yawa sosai a Chan.”
Ta ɗan kalleshi
“Kamar wa da wa kenan? Business partners ko abokai kawai?”
Fahad ya yi murmushi
“Business people, abokai, abokan kasuwanci”
Se kawai Maryam ta tuna matar da ta kira Zaid ranar da sukaje embassy a take yanayinta ya chanja
Fahad ya lura da yanayinta.
“Anty maryam lfya?”
“Ba Komi.”
Ya yi murmushi.
“Kar ki damu. Amsterdam babban gari ne kuma yayana knows how to survive there.”
Maryam ta yi dariya.
“Ya san komai kenan a garin?”
“Kusan komai ma.”
Sai ya miƙe ze tafi
“Anyway, duk abnda kikeso kafin ku tafi ki gayamin”
“Nagode.”
“Kar ki damu antyna”
Ya fara tafiya, Amma kafin ya fita, ya juyo ya kalle ta.
“Anty Maryam.”
“Naam?”
“Kuyi enjoying time dinku a chan, kuma don a Allah Munaso ayi muna guzurin dan Amsterdam ko yar Amsterdam”
Bata gane abnda yake nufi ba se tayi murmushi kawai
Fahad ya fita.
Yana fita daga parlour, murmushin da ke fuskarsa ya ɓace.
Ya Kalli kofar na ƴa seconds.
Ya fadi “Amsterdam”
Ya sauke ajiyar zuciya.
Wannan tafiyar ba ta cikin abubuwan da ya shirya
Se dare Zayd ya dawo daga fitar da yayi, Yana dan fita ne don ya kammala wasu abubuwa kafin su wuche
Maryam tana dining area tana cin abinci ita kaɗai.
Ya shigo.
“Assalamu alaikum.”
“Wa alaikas salam.”
Ya ajiye keys.
“Abnci kike chi baki jira ni ba?
“Bismillah zo mu chi”
Ya zauna.
“Me kike chi?”
“Semo”
Ya kalle ta, se ya dauki plate ya bude warmer din shima ya zuba semo da miyar kubewa wanda taji stock fish da naman rago, bayan ya chanye wanda ya debo seda ya qara ya sake chi yana jin daadin abncin har cikin kan shi
Da suka qare ta tattare plates ta kai kitchen shi kuma ya hau sama, bayan ta fito daga kitchen itama sama ta hau ta shiga dakinta tayi wanka ta fito ta shafa mai sannan ta shirya cikin kayan baccee riga da wando purple color, tana zaune a kan gado akayi knocking qofar,
“Waye?”
Se ya bude kofar ya shigo ya zauna kusa da ita, da alama wanka yayi don Gashin shi yanada alamar ruwa
“Hajiya Raliya ta shigo dazu?”
“Eh.”
“Batasan zamuyi tafiya ba se dazu da safe kafin in fita da na shiga part din mammi”
“tache kana planning komi ahead ynzu Haka already ka shirya komai kahin mu isa”
Yayi murmushi
Shiru ya ratsa tsakaninsu.
Sai Maryam ta bude baki
“Yaya”
Be amsa ba Shuru kamar baya dakin se kallon hannunta yakeyi
“My G”
“Naam Mijn kleintje”
“Gidan ka an Amsterdam kai kaɗai kake zaune?”
“Yes se ma’aikata kadan masu gyara gidan”
“Tun yaushe?”
“Tun shekarun da nike zaune a chan.”
“Ba ka gajiya da zaman?”
“Wani lokaci ina gajiya.”
“Me yasa baka dawowa Nigeria?”
Zaid ya ɗan yi tunani.
“Aiki.”
“Aiki kawai?”
Ya kalle ta.
“Toh wa zan tafi in bamma aikin.”
Maryam ta yi murmushi.
“Maybe yanzu zaka samu wasu abubuwa da zasu sa ba bazaka rinqa jin kadaici ba”
Zaid ya tsaya.
Ya kalleta.
Maryam kamar ta gano abin da ta faɗa.
Tayi saurin chewa
“I mean… karatuna ..zanyita yimaka tambayoyi dayawa kafin in wuche hostel”
Zaid ya yi murmushi kaɗan.
“Of course.”
Amma cikin zuciyarsa chewa yake…
Yarinya ba hostel din da zakije tare zamu zauna
“Muje ki rakani”
“Ina? Ynzu? Dare yayi ai
“Eh, garden zamuje, ya miqe tsaya
Ta saka hijab dinta suka fita garden suna takawa, Fitilun garden din suna haska wurin da wani irin cool view suna tafiya kusa da juna, Maryam ta ɗan kalli Zaid.
“Yaya! Ehm..umm..my g”
“Naam”
“Inyi tamabaya?”
“Eh”
“Waccan matar ta Amsterdam…”
Zaid ya kalleta.
“Wace mata?”
Maryam ta yi saurin sunkuyar da kai.
“Bashshi kawai”
Zaid ya yi murmushi.
Ta zumburo bakinta
“Mijn kleintje”
Shiru bata ansa ba
“Sunan ta Nadia.”
Ta ɗago kai.
“Nadia?”
“Eh, Tana managing one of our Amsterdam offices.”
Maryam ta gyada kai.
“Oh, Okay.”
Zaid ya ci gaba da tafiya, ya kalleta.
“Me ya faru kike tambayar ta?”
Maryam ta tsaya cak.
“Ni? Ba komai, kawai inaso in sani ne” ta fadi a shagwabe tana turo baki
Ya yi murmushi ya tsura mata ido, tana qara kyau sosai idan ta turo bakin nan
“Anya kuwa ba komai?” Ya fadi yana murmushi
“Baka yadda bane kake min dariya”
“Toh inaga kamar ban yadda ba.”
Ta qara turo baki kamar zatayi kuka
Zaid ya yi dariya a hankali ya ja lips dinta da hannun shi yana fadin “idan kina turo min bakin nan kama shi zanyi”
Maryam ta tsaya tana kallonsa.
Wannan ne karo na farko da ta ga ya yi dariya sosai haka a gabanta, dariya na mishi kyau shine kawai bayason yi, tana kallonshi tana tunani, ji kawai tayi ya daga ta sama ya nufi hanyar part dinsu, jikinta gabadaya ya saki Tana jin qamshin turaren shi yana shiga har cikin kanta, be ajiyeta ko’ina be se dakin shi, ya zaunar da ita kan dressing mirror dinshi ya qura mata ido, ta dauke nata idon a hnkali tana dan turo baki, ita dai Batason irin wannan kallon duk se taji kamar ana mata shocking, shi kuma yadda ta turo baki ta sauke ido duk ya tafi da imanin shi, hannunshi ya daga ya chire mata hijab, sannan ya zare mata hulla, gashinta ya sauko da qarfi don hadda ribbon din ya jawo tareda hullar, yasa hannu yana kwashe mata wanda ke fuskar ta, sannan ya daura hannu cikin gashin yana murzawa, ya dauketa se kan gadon shi, ya kwantar da ita kan kafar shi yana tattaro gashin da hannun shi, maryam dai jin take kamar suma zatayi idan aka qara minti daya saboda irin vibration din da takeji, tayi qoqarin ta miqe se jin bakin shi tayi kan kunnenta “shshshhh, massage zan yimiki a Kai har kiyi baccee” maryam gabadaya dauke wuta tayi kamar wata sumamma, zaid kuma yanata wasa da Gashin kanta har baccee ya dauketa, seda tayi mafarkin Zaid yana gaya mata wai Nadia tanada kirki kuma tasan kan aikinta Shiyasa take burge shi, seda zaid ya tabbatar da maryam Tayi baccee sannan ya gyara mata kwanciyar ta ya rufeta da duvet yayi kissing dinta a goshi sannan ya kashe wuta ya fita dakin ya sauka zuwa study office dinshi, yanaso ya kammala projects din Abuja kafin ya wuche, ya zauna kan kujera Laptop ɗinsa a gabansa, Amma ya gagara aiki
Ya tuna da yadda Maryam take tambayarsa game da Nadia dazu
Sai ya yi murmushi hankali yana fadin
“Kishi take?”
Ya fara tunani, shima dai ynzu ya gane ba wai kawai kokarin kula da maryam yake ba..ko ya fara sonta ne? Anya kuwa? but she’s so small, ko sonta din yakeyi Anya ze iya furta mata yana son ta? Amma ai yarinyar anty Ruqaiya warinta che gashi kuma tache mishi ma tanada ciki, “ko dai in qyaleta se ta dan qara girma?” Ya faɗa a hankali.
Sake sake yakeyi shi kadai babu me bashi ansa
Se ga wani email yayi popping a laptop dinshi, ya buɗe.
Subject ɗin ya sa ya tsaya yana sake karantawa
CONFIDENTIAL — NORTHERN CREST HOLDINGS
Fuskarsa ta canza, me ya hadashi da confidentian email din northern crest? Kodai Fahad za’a tura ma akayi mistake aka turo mishi? Ya buɗe email ɗin, Akwai wani attachment, Ya danna.
Ya fara karantawa…Bayan ƴa seconds…ya tsaya.
Akwai wani old document.
Northern Crest Holdings — Land Acquisition Records
Sai wani suna ya bayyana a ƙarƙashin document ɗin, sunan baban shi Rahman Balarabe, tareda wani suna Bashir me salati, ya maimaita sunan, sunan baban maryam kenan ai
Zaid ya ɗan shiga tunani
“Meyasa aka aiko min wannan? Me ya hada babana da baban maryam?”
Ya sake karantawa, Sai ya ga wani tsohon date kan takardar
Zaid ya jingina da kujerar shi
Wani abu ya fara zama suspicious.
Ba wai saboda sunan mahaifinsa da mahafin maryam ba kawai, Sai saboda document ɗin ya shigo masa daga wani email address da bai taɓa gani ba, Ya duba sender, Unknown.
Ya sake buɗe attachment ɗin.
A ƙasan page ɗin akwai wani rubutu
“In kanason kasan gaskiyar abudna ya faru shekaru uku zuwa biyar da suka wuche, ka nemo original records”
Zaid ya daskare, Ya kalli screen, original records kuma? Sai ya ɗaga kai.
Maryam.
Ya tuna tambayarta game da Northern Crest.
Ya tuna yadda take kallon abubuwa.
Ya tuna tambayar da ta yi masa:
“Akwai wani abu da ka boye a wannan dakin ne?”
A wannan karon…shi ne yake tambayar kanshi
Me Maryam ta sani?
Kuma…
me ya sa wannan file ɗin ya zo masa yanzu?
Zaid ya rufe laptop ɗin.
Amma bai iya cire tunanin daga kan shi ba.
A daren nan…
ba Maryam kaɗai ce take neman gaskiya ba.
Zaid ma ya fara tunanin tono ta.
Follow this link to join my WhatsApp group