THE NEW CITY
Sunyi tafiya ta kusan awa daya, Maryam ta dan fara gajiya da zama, tana zaune kusa da window, idonta a kan giragizai da ke ƙarƙashinsu.
Komai yana mata kamar a mafarki, a Jiya tana Abuja, Yau kuma tana kan hanyar zuwa Amsterdam.
Ta ɗan gyara veil ɗinta, ta jingina bayanta da seat, Zaid yana zaune kusa da ita, hannunsa riqe da laptop dinshi yanata dubawa, Maryam ta kalle shi da tunanin shidai baya gajiya da aiki, Sai kuma ta kalli window, ta bude idonta dakyau a ƙoƙarin ta na qin yin bacci amma ta kasa, Bayan wasu mintuna, ta fara jin idanunta suna qara nauyi.
Ta lumshe su a hankali, Ta buɗe, Ta sake lumshe su, Har a ƙarshe…ta kasa yaƙi da baccin, A hankali kanta ya fara karkacewa har Saida ya sauka a kan kafadar Zaid, ya tsaya da aikin da yake yi, Ya kalleta, tana baccinta peacefully, Fuskarta ta yi looking so calm, curls ɗinta sun fito kaɗan daga ƙarƙashin veil ɗinta sun sauka a face dinta Zaid dade yana kallonta a hankali ya furta "ya khaliq,” yarinyar nan tana neman ta haukata ni, komai nata kyau yake mishi, Ynzu ji yadda ta dan turo baki tana baccee, ba don yana tsoron ta tashi ba dan ya dan taba lips dinta, ya ɗan yi murmushi, Bai motsa kafadarsa ba, Sai ya chigaba da kallon laptop ɗinsa.
Bayan wasu mintuna, flight attendant ta zo da trolley.
“Sir, would you like...Zaid ya ɗaga yatsa a hankali.
“Shhh…”
Ta kalli Maryam.
Sai ta fahimci cewa bayason a Tashe ta, Ta yi murmushi kaɗan.
Zaid ya kalleta.
“leave, We'll have it when she wakes up.”
“Sure.”
Ta juya a hankali ta tafi
Maryam ta ɗan motsa ta daura hannunta a jikin shi yadda zataji daadin baccinta, Zaid ya tsaya yanata kallon ta, yaga yadda ta rungumo shi ta kwantar da kanta jikinshi ba ba tare da ta sani ba, A hankali ya rada mata
“Hayatee…” "ummmm.." tayi murmuring tana qoqarin bude ido
Ya yi murmushi.
“Shh..sleep.”
Sai ya koma da idonshi kan laptop ɗinsa amma se ya kasa aikin, wani button ya taba da ke tsakanin kujerun su, a take kujerun suka hade sukayi baya yadda maryam zataji daadin kwanciyar, blanket din da ke gefe ya janyo ya bude shi ya rufa musu a qafafun su sannan ya gyara ma maryam kwanciyar dakyau a jikinshi
Bayan kusan awa biyu…ta fara motsawa a hankali..Ta motsa kanta, ta buɗe idanunta, Da farko ba ta gane inda take ba, Sai ta ji kamar tana kan jikin mutum,Ta ɗago kai, Ta kalli Zaid, ya kwantar da seat din yadda ta samu damar kwantawa jikin dakyau, Shi ma kallonta yake,
“Good morning sleepy head"
Maryam ta ji kunya.
“I m I'm sorry…”
“For what?”
“Na yi bacci bansan na..naa..kwantaaa..ta kasa qarasawa tana kallon inda take kwanche ta miqe da sauri yayin da yake fadin
“gabadaya hannuna yayi ciwo .ouchchch"
Maryam ta rude
“kayi hakuri ban sani ba”
Zaid ya kalli kafadarsa.
“Na kasa motsawa dan danna min”
Da sauri maryam ta kai hannunta tana danna hannunshi
“Ouch akwai ciwo kiyi a hnkali”
Ta qara rudewa tana dan danna mishi a hnkali ta ranqwafo saboda yadda ya kwantar da kujerar, bata Ankara ba se jin tayi yayi kissing dinta wuya, tsoro da shock yasa ta jaye hannun da ta dafa dashi se gata ta fado kan shi gabadaya
Da sauri yasa hannuwanshi ya riqeta ya jawota jikinshi dakyau
Ta runtse Idonta da sauri saboda yadda fuskokin su suke dap har hancinsu na goguwa da na juna
Zaid ya yi murmushi yayi kissing kumatun ta
“Zaki Ki ci abinci.” Ya rada mata a kunne
Shuru ta kasa ansawa se zuciyar ya da ke tsalle a qirjin ta
Ya danna wani remote se ga flight attendant din ta dawo,
"Good morning ma" ta fadi tana smiling
Maryam na qoqarin tashi daga jikin zaid ya riqe ta yana fadin “ita wannan ba ruwanta dake kada ma kiji kunyar ta”
"Morning" maryam ta amsa a kunyache
Maryam ta kalli abincin da ta ajiye musu a tray
"Thank you"
"Please call us if you need anything else"
Maryam ta gyada kai
Zaid ya Kalli fuskar ta yaga yadda duk kunya ta mamaye ta "tundazu sukazo serving kinata baccee"
“Me yasa baka tashe ni ba?”
“Kinata baccee kinyi kyau kamar sleeping beauty, kuma nasan kinajin baccin sosai tunda jiya tsoro ya hanaki bacce”
Ta yi shiru
“Meyasa kikejin tsoro na?”
“Toh kaine ai se ka rinqa baccee ba riga kuma..”
Ya daga gira “kuma me?”
“Kuma se..” ta kasan qarasawa tana taba lips dinta
Yana kallon yadda ta turo lips din tana tabawa da hannunta seda wani iri a cikin kan shi da jikin shi gabadaya
“Toh ba ke kikache min kinason baby ba?”
“Eh inaso”
“Toh ya zaayi ki samu?”
“Allah ze bani ai inayin addua idan nayi sallah ina chewa rabbanaa hab lanaa min azwaajina wa zurriyaatina qurrata a’ayunin wa ja’alnaa lil muttaqeena imaama”
“Allahumma ameen ya Allah my haya, kin riga kin samu miji sora baby in shaa Allah”
Ta dago tana dariya “shima zan samu ai ko?”
“Eh amma se kin dena tsorona tukunna”
“Toh zan dena”
“Yawwa my haya” Yayi mata light kiss a baki ya dago dasu yana fadin “let’s eat”
“Okay.”
Suka fara cin abinci.
Ba su yi magana sosai ba.
Bayan sun gama cin abinci…
Zaid ya kalli babban screen da ke gaban su
“Mun kusa sauka.”
Maryam ta kalli inda yake kallo
“Da gaske?”
“Yeah.”
Ta fara kallon ƙasa daga window, seda ta dauki lokaci tana kallo sannan A hankali birnin Amsterdam fara bayyana, Gine-gine,Hanyoyi, Canals, Gidaje, green grasses.
Maryam ta yi shiru, chan ta furta
“Wow…”
Zaid ya kalleta.
“First time dinki a Europe?”
“Eh.”
“Then welcome.”
Ta yi murmushi.
“It’s beautiful.”
“zaki saba soon"
Bayan ɗan lokaci…
pilot ya sanar da su cewa suna shirin sauka.
Zaid ya ɗaure seat belt sannan ya daura mata nata, Jirgin ya fara sauka, Maryam ta kalli window, Zuciyarta ta fara bugawa.
A wannan lokacin ne ta tabbatar da gaske ta bar Nigeria, Komai yana baya, Ta sauke ajiyar zuciya.
“Ya Allah…”
Zaid ya kalleta.
“Harynzu tsoron ne Mijn kleintje?”
“A little.”
“Don’t worry, ina nan tare da ke”
Jirgin ya sauka lafiya bayan ya qare taxiing,
Bayan an gama parking ɗinsa a private aviation section, ƙofar jirgin ta buɗe, yamma yayi duhu ya fara sauka se hasken fitillu da ke wurin, Cold air ya shigo ciki, maryam ta qanqame jikinta don yadda sanyin ya shigo ya shallake sanyin Ac da ke kunne a jirgin, ta ja dogon numfashi
“akwai sanyi”
Zaid ya yi murmushi.
“Welcome to Amsterdam.” Ya fadi yana chire jacket din jikinshi ya saka mata a jikinta
Sun fito suna sauka tare a hankali yana riqe da hannunta
Tanata kallon airport ɗin, Ta kalli jirgin, Sai ta kalli Zaid taga shima ita yake kallo
A gefe guda, wata black luxury SUV tana jiran su, Drivern ya fito.
“Good evening, sir.”
“Good evening.”
Ya karɓi hand luggages dinsu daga hannun su, se gashi an kawo dayan akwatin na Maryam duka ya karba yasa mota
Zaid ya bude ma maryam m kofar motar ta shiga shima driver ya zagaya da sauri ya buɗe mishi dayan side ya shiga, Motar ta bar airport, suka kama hanyar cikin garin Amsterdam, maryam tanata kallon garin ta window se taji driver yayi magana da wani yare “Gaan we naar huis of naar kantoor?”
Tana mamakin wannan da wa yake magana se taji zaid yana magana “We gaan naar huis. Ik ben met mijn vrouw en ze is helemaal uitgeput”
Mamaki ke nemen kashe maryam daga zaune, zaid na kallonta kamar zeyi dariya se kuma ya gintse “yaren Mutanen garin nan kenan, Dutch language, ya tambayeni gida zamuje ko office, se nache mishi gida zamuje ina tare da hayatee kuma ta gaji tanaso ta huta”
Tayi murmushi tana gyada kai alamar ta gane
Ta maida hnkalinta wurin kallon garin, zaid na riqe da hnnunta cikin nashi yanata murzawa, shi dai besan meyasa yake samum wata irin natsuwa idan yana riqe da hannunta ba
Maryam kam se kallon mutane take ta window, wasu suna ta cycling kan bicycles suna wucewa, tana kallon Trams, Canals, Gine-ginen da suka bambanta da na Abuja, Komai sabo ne a gare ta.
Zaid yana kallonta lokaci-lokaci.
“You okay?”
“I’m okay.”
“Sure?”
“Eh.”
Ta ɗan yi shiru.
“Kawai..Ina kallon sabon wuri ne”
Zaid ya yi murmushi.
“Na gaya miki, zakiji dadin zuwa”
Tayi murmushi tana chigaba kallon waje
Bayan wani lokaci…
Motar ta shiga wani quiet residential area suka chi gaba da tafiya, tsarin gine ginen ma abun kallo ne, da ka kalli gidajen kasan a tsare akayi su amma kowane da style dinshi
Seda suka kai wani gate suka tsaya a gaban wani babban modern house, driver Yayi horn wani me gadi ya leqo, yana ganin motar ya danna wani remote da ke cikin dakin shi, a take gate ya wangale suka shiga, driver seda ya kai gaban kofar main parlor yayi parking, Maryam ta kalli gidan, Ta yi shiru tanata kallo, har Zaid ya sauka, ya zagayo Ya buɗe mata ƙofa.
“Muje”
Ta sauka.
Suka shiga gidan yana riqe da hannunta
Tana saka kafarta ta shiga…ta tsaya.
Gidan ya yi kyau sosai, ya hadu har batasan ma wane irin gida ne wannan ba, manyan windows, gini me tsayi, hadaddun English furnitures, fitilu masu hasken gaske, Akwai wuta a wani ɓangare na parlour tana chi a hnkali qarqashin wani gini me kamar chimney, ga stairs da suka haura sama, Kuma komai a tsabatace ko ma tache tass babu ko dugon datti
Maryam ta kalli Zaid.
“Wannan gidan zamu zauna?”
“Yeas"
“Wow.”
Zaid ya ɗan yi murmushi.
“Muje”
Ya nuna mata wasu ɓangarorin gidan.
Kitchen, Dining, dayan parlor din,Guest room, study Office dinshi, Sai garden, Maryam ta kalli garden ɗin ta window din parlor “wow Beautiful.”
“Qaramar garden dina che da nike shukka flowers din da nikeso”
Ta kalle shi.
“Small?”
Ya yi murmushi.
“Bazaki hada girmanta da na abj ba ai.”
Maryam ta yi murmushi kawai
Se drivern da ya daukosu ya shigo da luggages dinsu, kofar baya ta bude wasu yan mata biyu suka shigo suna yi musu welcome suka gaida maryam "welcome ma, my name is Samantha daya kuma tache and I'm rachel"
Maryam ta ansa musu, zaid ya kallesu “Breng haar bagage naar de grote slaapkamer beneden” waton (ku dauki akwatunanta ku kai babban dakin da ke qasa)
A take suka fara cika umarnin da aka basu
Ya riƙe hannun maryam suka haura sama suka shiga bedroom dinshi, Da suka shiga bedroom..Maryam ta sake tsayawa tana kallon ikon Allah, Ta ga an shirya mata abubuwa a ciki
Kayan sawa irin na yanayin sanyi da ake a garin, takalmi, jakunkuna, kayan Skincare, designer turaruka, Komai, tsaye tayi tana kallo se taji ya rungumota ta baya
Ta daga kai ta kalleshi
"Ba dakinka bane nan? meyasa aka shirya duk wannan a ciki?”
"Tare zamu zauna a nan, daki daya ne a sama kuma bazan iya barin ki kina kwana ke kadai a qasa ba, kuma bazan sauka qasa in bakki ke kadai a nan ba, wasu kayan da basu samu space a nan ba suna dakin ki a qasa an jera, kayan da mukazo dasu ma suna chan dakin”
Gaban maryam ya buga da karfi
“Tare zamu tsaya nan? har zuwa Yaushe?”
“Why?”
Zaid ya kalleta.
“Saboda mammi tanata nanata min in kula dake
Maryam ta yi murmushi
“Nagode, amma..”
“Shhshhh”
Ya ɗan tsaya.
“Ki shiga kiyi wanka ki fito mu chi abnci mu huta”
“Okay.”
“Gobe idan kin huta zamu shiga school”
Maryam ta gyada kai.
Se da ta dauko duk abubuwan da take buqata sannan ta shige toilet, tafi minti goma tana kalle kalle a ciki sannan tayi brush tayi wanka ta shafa moisturizer tasa bath robe, sannan ta saka wa’inda ta chire a laundry dama koda ta buɗe kofar toilet seda ta wuche laundry kafin ta kai bathroom din
Underwears ɗinta da ta wanke se ta rasa yadda zatayi dasu, haka dai ta daure ta shanya su a wurin da aka tanada na shanya kaya sannan ta fito.
Koda ta fito da tarar da zaid ya Debo abnci da fruits ya aje kan coffee table da ke cikin dakin, a hnkali tayi magana “ni bnga night wears ba”
Takawa yayi zuwa closet tana kallon shi ya nuna mata wurin da aka jera kayan baccee, ta kalleshi, ta kalli kayan, wai ita zatasa wa’innan? Ai dasu da babu duk daya, a fili kawai chewa tayi “okay thank you” ya gyada kai ya juya ya fita, ta dauko wata riga wadda take ganin tanada dama dama tasa, ta kalli madubi “kam Balai Wallahi ba dani zaayi wannan ba”, ta bude wurin da taga an jera hijabs ta dauki daya tasa sannan ta fito
takawa tayi taje wurin coffee table da yake zaune yana jiranta, a plate daya suka chi abnci sannan ta tashi ta fara sallah, zaid kuma ya shiga bathroom
Kafin ya fito har tayi baccee kan prayer mat
Ya dauketa a hankli ya kwantar da ita kan gado ya rufeta da quilt sanann yasa jallabiya ya fara sallah, bayan ya qare yayi addua ya hau yanajin irin rashin lfyar da yake fama da ita kowane dare tana sauko mishi, Amma kamar ta yau ma tafi ta sauran kwanakin, ya Kalli maryam ta cikin hasken dim lamp din da ke ajiye a bedside, a ranshi yana fadin “wai da hijabi zatayi baccee” ya kalleta se yaga tana riqe da hijab din gama kamar za’a chire mata, Yayi dariya ya fara zare mata shi a hnkali har ya chire mata, seda ya Kalli kayan jikinta sannan ya gane dalilin da yasa taqi chire hijabin, silk rigar baccee che pink color ta Victoria secret, tana kwanche a jikinta kamar fatar ta, ji yayi duniyar zata fara juya mishi Yayi sauri ya kashe lamp din ka gefen gadon yayi addua ya shafa mata a jiki, jin yadda hannunshi ya sauka akan skin dinta yasa shi ya sauke ajiyar zucciya a hnkali, itama a cikin baccin seda ta sauke nata, sannan ya jawo ta a jikinshi yana tura fuskar shi cikin wuyan ta yana shaqar qamshin jikinta har baccee ya daukeshi
Washegari da asuba…
Koda zaid ya bude ido yaga maryam ta shige cikin jikin shi tana qanqame dashi
Ya dade a haka yana jin daadin yanayin, seda yayi gudun kar lokacin sallah ya wuche sannan ya jaye ta a hankali ya kwantar da ita kan pillow ya tashi ya shiga bathroom yayi arwallah, Koda ya fito maryam ta tashi zaune kan gadon, ya kalleta da sauri ya dauke kai saboda yadda silk rigar baccin ta kwanta a jikinta, da sauri ta lalabo hijab dinta tasa tana mamakin cikin baccee ya chire ko shine ya chire mata
"Je kiyi arwallah muyi sallah"
Ta tashi ta shiga toilet tayi arwallah kafin ta fito har yayi raka'atanul Fajr, tana fitowa ta tsaya a baya yaja su sallar asuba suka qare se ya fara azkar da adduoin shi, kafin ya qare ya juyo maryam har tayi baccee kan prayer carpet. Yayi dariya ya dauketa ya kwantar da ita a gado ya chire mata hijab, take gashinta ya watse har kan face dinta, ya tsaya yana kallonta yasa hannu a hankali yana kwashe mata gashin da ke kan fuskar ta, ya dade yana abu ɗaya har yana taba wuyan ta yaji shi kamar da zafi, lullubeta Yayi daga baya ya koma kan coffee table da laptop din shi ya fara duba aiki
Safiya ta dan fara wayewa, Maryam ta tashi da wani irin ciwon ciki, dama tun Asuba take jin kamar mararta zata fara ciwo ta dauka abun ze kai gobe amma gashi ma ya tashe ta daga baccee, tun tana daurewa daga nan kwanche har ta fara kuka a hankali, zaid na zaune yana aiki yaji kamar sheshekar kuka da sauri ya tafi yana tambayar ta “me ya faru?” A gigice
cikinta ta rinqa nuna mishi se yayi tunanin ko don sunyi tafiya ne saboda wasu suna samun matsalar ciwon ciki idan sukayi tafiya irin haka, taso da ita yayi zaune ya rungumeta yaji jikinta da zafi sosai, a gigice ya saka mata hijab ya tallabeta ya sauka downstairs ya fita daga gidan a gaggauce, mota ya bude ya kwantar da ita sannan ya shiga yaja motar da sauri, kuka take ta yi shi kuma sautin kukan ke qara gigita shi, asibitin cikin estate din ya shiga, beyi parking ba ma tsayar da motar kawai yayi ya daukota ya nufi cikin da ita, da sauri nurses din da ke nan suka karbeta emergency suka shiga wani daki aka kira drs on duty, binsu yayi ciki shima suna examining dinta cikin qwarewa suka gane menstrual cramps ne kuma irin intense one dinnan, allura dr din tayi mata sannan ta daura mata drip, baa dauki lokaci ba baccin wahala ya kwashe ta
Bayani dr din tayi ma zaid sannan tache idan ta fara irin haka a rinqa yimata massage da hot water bottle, ta rubuta mata drugs din da za’a saye da yadda zaatsha drugs din, sannan ta tafi ta batta qarqashin kulawar nurses
Kallonta zaid yayi se yaga kamar ma ta dan rame dama ba jikin ne da ita ba, zaune yake tare da ita a dakin yana riqe da hannunta har ta tashi, da sauri sauri yake tambayarta ya jikin kuma me takeji? Ta ansa mishi da kai alamar da saukee, hawowa gadon yayi ya zauna ya kwantar ta kanta a kan chinyar shi yana shafa kanta, suna nan har drip din ya qare se yaje ya kira nurse din ta chire mata, tanaso ta tashi ta gyara jikinta don tanajin kamar ya bachi amma ta kasa miqewa gaban shi, nurse tayi ma magana ita kuma tache mishi ya dan jira su a waje, se ya fita ya tsaya a qofa har suka qare nurse din ta chnja mata bedsheet ta kwanta sannan ya dawo ciki
“Sannu haya, ya kikeji ynzu?”
“Naji saukee kadan kadan kawai yakeyi”
“Sorry, Allah ya sauwaka”
Nurse din che ta sake shigowa da allura tache za’a yimata allura se su tafi gida shikenan se ta chigaba da shan drugs din da aka bata, ai ko a nan maryam tache batasan zanchen ba, akayi akayi taqi tsayawa, fiye da minti sha biyar ana abu daya, qarshe zaid kawai daukar ta Yayi sama ya rungumeta sosai a jikinshi sannan yayi ma nurse din alama da ido, ta matso ta dan sauke wandon maryam din, ai ko ta zabura da qarfi tana qoqarin sauka ya kai bakin shi dd kunnenta “shhh, sorry hayatee bakison kiji saukee ne?”
Yana fadin haka yayi mata light kiss a wuya, shock din da maryam ta shiga yafi ma na allurar don har nurse din ta qare bata sani ba, gyara mata kayanta yayi sannan ya karbi ledar maganin ya nufi mota da ita riqe a hannun shi, kwantar da seat din gaba yayi ya ajeta a hnkali sannan ya rufe qofa ya zagaya ya shiga ya tayar suka wuche gida, koda suka isa ma shi ya fito ya dauketa ya wuche da ita sama ya kwantar da ita kan gado, seda ta fara baccee sannan ya dauki laptop dinshi ya chigaba da aiki, ya kamata yaje office ya duba abubuwa amma baze iya fita ya batta ba, duk motsin da zatayi idonshi na kanta, har lokacin shan maganinta yayi, ya tada ta ya bata tasha daqyar tanata lumshe ido ta koma baccee, da yamma yayi dakyar ya tada ita tachi abnci kadan tache ta qoshi baccee takeji, magungunan ya dauko ya duba yaga akwai me saka baccee a ciki, se kawai ya gyara mata kwanciyar ta
Har dare zaid na dakin sedai ya sauka ya debo abnci ya dawo sama, tashi Yayi yaje yayi wanka yayi nafilolinshi ya hau gadon ya kwanta tanata baccee, jawota jikinshi yayi yanata shafa gashin ta, yayi musu addua ya shafa amma ya kasa baccee, ya dade sosai kafin ya samu baccee ya dauke shi
Da Asuba maryam ta tashi, taji jikinta da saukee ba kamar jiya ba, zaid na kwance ya matse ta a jikinshi, baccin shi yayi nauyi sosai don jiya Zafin jikinta ya tada shi baccee bayan ya samu yayi daqyar, seda yayita goge mata jiki da towel da ruwa, ta dan saukar da hannun shi ta sauka daga gadon a hankali, Allah yasa koda ta shiga toilet taga ya jera mata sanitary pads, Tayi wanka da ruwan zafi taji jikinta ya qara saki sannan ta shirya ta fito se ta ganshi zaune, “haya, ya jikin ki?”
“Alhamdulillah naji saukee”
Zo kisha magani ya tashi ya dauko ledar da ruwa mara sanyi ya bata tasha ta kwanta sannan ya tashi Yayi arwallah ya fara sallah, kafin ya qare har ta koma baccee, shima kwantawa Yayi ya rungumeta a take baccin ya daukeshi. Basu tashi ba se 10:15am na safe, a gida zaid ya yini yau ma yanata kula da maryam, sedai ya sauka qasa ya karbi abnci hannun su Samantha ya koma sama, yan office sunsan oga ya dawo amma sunata mamaki basu ganshi ba, Nadia har kiran shi Tayi don ta dauka ko beda lfya ne, seda zaid yayi 4days a gida yana kula da maryam har ya lura ta samu saukee sosai har Tayi wanka ta fara sallah sannan yaji wani nauyi ya sauka daga kirjin shi,
Ranar da dare yake chemata ta shirya gobe zasuje school, washegari maryam da Murnar sabuwar school ta tashi ta shirya, Ta zaɓi simple but elegant outfit, Veil ɗinta ya rufe gashinta se curls din gaban kawai
Ta sauko downstairs.
Zaid yana zaune yana jiran ta.
Yana sanye da dark trousers da light shirt. kusa da shi Nadia Che zaune suna magana
Maryam ta gane ta nan take ba don tasan face dinta ba se don yadda suke maganr ta tabbatar babu wani daga office da zaid ke magana dashi irin haka
Zaid ya kalli Maryam
“Har kin shirya.”
"Umm” ta amsa a daqile
Nadia ta gaida ta
“Good morning, Mrs. Balarabe.”
Maryam ta amsa itama a daqile
“Good morning.”
Zaid ya kalli Nadia.
“Everything ready?”
“Yes, sir. The university confirmed the appointment.”
“Good.”
Maryam ta kalli Zaid.
“Yanzu za mu je?”
“Yes amma ki chi abnci tukunna"
"Na qoshi" ta amsa
Ya yi murmushi saboda ya gano fushin na miye ya miqe ya isa inda ta zauna "muje"
Yasa ta gaba har dining table ya debo mata oats yasa madara da caramel syrup sannan ya fara bata a baki, dama duk kwanakin nan da batada lfya a bakin yake bata abnci, seda yaga ta shanye wanda ya diba sannan ya goge mata baki da tissue Yayi mata light kiss a goshi yana chewa “toh muje”
Ya riqe hannunta har mota ya zaunar da ita sannan ya zagaya ya shiga, Nadia da driver ke gaba se mamaki suke wai zaid ne wannan kuwa?”
kai tsaye university din suka nufa, suka samu wuri sukayi parking
Maryam ta sauka.
Ta tsaya tana kallon campus ɗin.
Students suna ta wucewa.
Wasu suna riƙe da books.
Wasu laptops.
Wasu suna magana da abokansu.
Wata irin sabuwar duniya che gareta
Maryam ta ɗan gyara hand bag ɗinta.
Zaid ya matso ya tsaya kusa da ita.
“Ready?”
Ta kalle shi.
“In shaa Allah”
“Muje”
Suka shiga wani office
Nadia tana biye da su.
A admissions office suka zauna.
An duba documents din Maryam.
Passport.
Transcript.
Academic records.
Application.
Residence information.
International student documents.
An yi wasu gyare-gyare a records ɗin.
Nadia tana magana da wasu staff din
Zaid kuma yana zaune kusa da maryam yana tabbatar da komai ya tafi yadda ya kamata.
Maryam ma tanata saurare da yake da turanci suke magana
A ƙarshe staff member ɗin ta ce:
“Everything is in order. We can proceed with the registration.”
Maryam ta yi murmushi.
“Thank you.”
Zaid ya kalleta.
“Zaki fara lecture soon.”
Maryam ta yi murmushi.
“Alhamdulillah”
Shima ya maimaita “Alhamdulillah”
A wannan lokacin…
ta ji kamar ba ta zo Amsterdam ne kawai saboda mijinta yazo da ita ba.
Ta zo ne domin ita karan kanta
Domin karatunta.
Domin makomarta.
Bayan sun fita daga office…
Maryam ta tsaya a entrance.
Ta sake kallon campus din wani irin daadi yana ratsa ta, ita kam wache kalar godiya zata yima zaid?
Ta Kalle shi yana tsaye kusa da ita, ta kama hannunshi daya da hannayenta duka biyu, mamaki ke neman kayar da zaid daga tsayen da yake, wai maryam che ta riqe hannunshi da kanta, for the very first time bashi ya riqota ba ita ta riqo shi, be fito daga duniyar mamakin ba se jin muryar ta yayi
“Rouhi”
Ya qura mata ido yana jin daadin sunan da ta kirashi
“Jazakallah khairan, Allah ya saka maka da Jannatul firdaus”
Hannu kawai ya miqa ma driver din, driver a take ya gane abnda ogan shi ke nufi, yasa mishi key din mota ya juya ya wuche, sum sum Nadia ta bi bayan drivern tana dariya
Zaid kam besan ma sunayi ba ya kama hannun matanshi yana kallonta cikin ido
“Muje wani wuri mu chi abnci kafin muje gida”
Ta gyada kai, suka tafi mota
Sunyi tafiya me dan nisa a Motar hannunshi daya yana riqe da nata har suka isa wani wuri da taga an rubuta “Restaurant Flore”
Shiga sukayi suka wuche VIP room suka zauna, waiter ta shigo da tablet a hannunta don ta karbi order dinsu, gabadaya da yaren Dutch suke magana, zaid ya gayamata duk abnda zata kawo musu, kamar wasa maryam taga ana shigowa da abnci sun fi kala goma, yache ta debi kowane taji wanda zata iya chi, maryam ta chi iya wanda zata iya chi ta qoshi, kuma ta sha drink din pinna colada sosai, seda suka qare suka tashi suka fito taga basu biya kuddi ba
“Naga basu bada bill ba, sun sanka ne?”
“Ni keda highest share a restaurant din, zasu tura bill zuwa company daga chan za’a tura musu”
Maryam ta cika da mamaki amma bata nuna ba se kai kawai ta gyada
Daga nan suka wuche wani mall da aka rubuta “De Bijenkorf”, kaya zaid ya kwasar ma maryam kamar batada komi a gida, wasu abubuwan batasan amfanin su ba, kuma a nan suka tafi suka bar kayan wai Mutanen shagunan zasu kai kayan gida, daga nan gida suka wuche
maryam ta gaji sosai, tayi wanka ta sauko dakinta da ke qasa tabar zaid a sama ya shiga bathroom, tana shigowa taga su Samantha duk sun jera mata kayan da tazo dasu daga Abj har sun hada luggages sun kaisu gefe daya sun ajiye
Ta zauna a gefen gadon tana kewar mama
Ta fara tunanin yar uwar ta Aisha.
Ta ɗauki wayarta.
Ta buɗe notes.
Ta karanta abubuwan da ta rubuta
Wataƙila…za ta samu amsar da ta shafe shekaru tana nema.
Ta buɗe browser.
Ta rubuta:
Northern Crest Holdings Amsterdam
Search results suka bayyana.
Ta fara scrolling.
Sai wani old document ya bayyana.
European Trade Partnership — NCH
Maryam ta danna, Page ɗin ya buɗe, Ta fara karantawa, Sai ta ga sunan Rahman Balarabe, a hnkali ta furta "again"
Hannunta ya tsaya, Zuciyarta ta buga.
“Again…”
Ta ci gaba da scrolling, Sai wani line ya bayyana.
Land Acquisition — 5 years ago, transferred from Bashir me salati
Maryam ta daskare.
5 years ago, shekarar da baba ya rasu kenan
Me ya kawo sunan shi nan
Tayi screenshot.
A wannan lokacin…
wayarta ta yi vibrating
Unknown number.
Wani message guda ɗaya yayi popping
"Kin fara gano wani abu”
Maryam ta kalli screen din da kyau, jikinta ya yi sanyi.
Ta sake karanta message ɗin
Sai ta ji zuciyarta tana bugawa da ƙarfi.
A dd lokacin zaid ma ya sauko qasa yana study office dinshi yana duba abubuwa a laptop dinshi…
email ya shigo
A kan screen ɗinsa wani old file ne
NORTHERN CREST HOLDINGS — ORIGINAL RECORDS
Ya buɗe shi.
Page 17 ɗin da ya ɓace a Nigeria sadda yana karantawa, yana nan ynzu
Zaid ya fara karantawa, Sai ya sake ganin sunan Alh Bashir Misalati.
Ya ɗan shiga tunani
“Ya akayi sunan ke cikin nan again?”
Ya ci gaba.
A ƙasan page ɗin akwai wani reference number.
Northern crest Office — Confidential.
Zaid ya jingina da kujerarsa.
A hankali ya furta:
“Maryam…kinsan wani abu ne?”
A wannan lokacin…
su biyun suna cikin gida ɗaya.
Maryam tana neman amsar Aisha.
Zaid kuma yana riƙe da wani ɓangare na gaskiyar.
Amma babu wanda ya san…cewa gaskiyar da suke nema guda ɗaya ce.
Kuma lokaci ya fara ƙurewa.
Follow this link to join my WhatsApp group