THE CONNECTION
SOKOTO
A chan Sokoto aikin da Zaid yasa ayi a makarantar Islamiyyah har ya fara nisa, Mlm yazo wurin mama tareda matar shi, yayi godiya sosai yayi farin ciki kuma yayita addua ga maryam da mahaifinta margayi, Yayi musu adduar zaman lfya da mijinta da kuma zuria me albarka, haka ma sauran malaman seda suka yita zuwa godiyar qarin albashi da suka samu, sannan kuma da gyaran da ake yima makaranta, Anayin sabon gini sannan an kawo littafan addini dayawa da za’a raba ma yara, sunata farin ciki sosai, ita mama batasan ma me zatache ba, se “Alhamdulillah Allah ya bada lada da take chewa”
A bangaren Imran kuma yanata zuwa wurin aiki, sannan kuma ya jajirce sosai yana yin aikinshi da kyau yadda ya kamata, baya wasa kuma yana jin daadin yadda yake aikin shi, gashi ynzu basuda matsalar abinci tun lokacin da zaid ya aiko musu da abnci tareda mama, duk da dai seda zuciyar shi ta motsa lokacin da inna ke gaya mishi wai mijin maryam ya aiko musu da abnci me yawan gaske kuma babu abunda ba’asa na kayan abnci ba, yaji kishi matuqa amma yayi qoqari ya danne saboda yasan ba wai ya aiko bane saboda yachi mishi fuska
A Amsterdam kuwa, tun da sukayi sallar Asuba basu koma baccee ba, bayan adhkar da karatun da zaid yasa maryan tayi mishi, se ya tashi ze shiga wanka yayi shirin zuwa office
“ki koma baccee ki huta, zan fita aiki kuma inaga bazan dawo da wuri ba saboda aiki ya taran min” maryam ta gyada kai amma bazata iya komawa baccin ba, ta riga ta saba da baccee tare dashi, yana shiga wanka se ta sauka ta nufi kitchen, su Samantha basu shigo ba da alama saboda ko’ina shiru, tunani ta fara me zata bashi yayi breakfast, Irish ta gani a cikin wani stand da aka jera tareda wasu abubuwa, debo shi ta ta fere sannan Tayi dicing dinshi into cubes, se ta bude fridge ta dauko broccoli, cauliflower, carrots da peas, duka ta gyara su se Tayi steaming din vegetables din sannan Tayi boiling potatoes dinta se Tayi mashing tareda butter, daga nan ta dauko chicken breast Tayi dicing shima into cubes se ta fara hada sauce dashi, tana cikin hada sauce din zaid ya shigo kitchen a shirye, hugging dinta yayi ta baya yana chewa “haya, dame dame kike hadawa haka gida ya cika da qamshi?”
Daqyar ta iya bude baki ta ansa mishi saboda yadda ya shigar da kanshi cikin wuyan ta yana kissing dinta
“Dame dame kakeso ka chi?”
“Ke nikeso in chi amma kina min rowa”
Kunya Che ke neman nutsar da maryam amma shi da yayi zanchen ko a jikin shi
Sulalewa tayi ta dauko plate ta zuba sauce din akai, sannan ta dauko mashed potatoes dinta da vegetables suma ta zuba se ta juyo tana miqa mishi ba tareda ta yadda sun hada ido ba
Dariya ta bashi sosai yadda taketa noqewa amma beyi dariyar ba se chewa yayi
“Ni ba chewa nayi zanchi wannan ba ai”
Kanta a qasa bata kalleshi ba ta amsa
“Kachi abnci kafin ka fita office”
“Ai wani abnci daban nikeso amma ana min rowa”
Kuka maryam ke neman fashewa dashi se yayi murmushi ya riqo hannunta tareda plate din suka nufi kitchen island din da ke zagaye da kujeru suka zauna, ya kalleta yaga yadda haryanzu kanta yake a qasa
“Mammi tache ki kula dani kuma kinche zakiyi amma baki chika alqawari ba, zan kirata in gaya mata”
“Toh ba gashinan ina kula da kai ba ina baka abnci”
“Ki bani abnda nache inaso ba wannan ba”
Tayi shuru bata amsa ba
“Kinji Mijn kleintje?” Yache cikin wata irin murya
Se kawai ta gyada kai
“Yaushe?”
Tayi shiru bata amsa ba
“Okay bari in dawo office zamu ida maganr ynzu na kusa yin latti”
Yachi abncin da dan sauri sannan yasa hannunshi ya tallabo fuskarta ta kalleshi, yayi mata smiling sanann yayi mata light kiss a lips dinta yache “thank you”, se ya juya ya fita
Tashi tayi itama ta hau sama Tayi wanka ta fito ta shirya sannan ta zauna a kan gado
Har yanzu ganin take kamar mafarki takeyi, tunani biyu ke mata yawo a Kai, record din da ta gani da sunan babanta, se kuma message din da aka turo mata, Ta ɗauki wayarta, Ta sake buɗe message ɗin, Ta karanta shi sau biyu kamar tana qoqarin gane wani abu, me ya sa duk lokacin da na kusanci wani abu game da bincike na, sai a fara turo min messages?
Ta ajiye wayar tana tsananin kewar mama, tayi waya da mammi so biyu ta WhatsApp call amma batayi waya da mama ba tun da tazo saboda mama bata WhatsApp, Ta sauko downstairs, Samantha da Rachel suna jin motsin ta suka fito suna tambayar ko tanason wani abu ne, suka nuna mata abnci a dining, zaunawa tayi su suka zuba mata tachi sannan ta dawo parlor ta zauna shuru har akayi zuhr ta shiga dakinta da ke qasa tayi sallah ta fito se ta kunna tv, batasan ma abnda akeyi ba don hnkalinta yana Chan tana tunani, a nan dakin qasa tayi sallar la’asar da magrib duka, tayi sallar isha tana zaune taji su Samantha suna gaida zaid, da sauri ta miqe ta fito har cikin ranta tanajin daadin dawowar da yayi don ta gaji da zaman shuru, jin daadin da ya gani a fuskar ta sanda ta ganshi yasa shima yaaji daadin har cikin ran shi, ya taka har wurinta yana jawota jikin shi ya dago ta sama kamar wata yar baby yayi kissing din goshinta “I’ve missed you so much my haya”
Tayi murmushi
“I’ve missed you too rouhi” ta fadi a shagwabe kuma kamar zatayi kuka
kallon Idonta yayi yaga hawayen da ke kwanche a ciki “ya akayi? Wa ya taba min hayatee?”
“Inaso inyi magana da mama, tun da mukazo banyi waya da ita ba”
“Meyasa? Ki kirata manah”
“Banida line din nan da zan kirata dashi”
“Ba naji kinyi magana da mammi da qawayenki ta WhatsApp ba? Itama ki kirata ta WhatsApp kafin muje a saye line din”
Maryam ta girgiza kai
“Mama ba ta WhatsApp ai”
Zaid ya tsaya.
“Da gaske? Yi sauri je ki shirya muje mu saye layi ynzun nan”
Ya fadi yana sauketa qasa
Da gudu ta haura stairs yana kallon yanda take gudu yana sake ganin yarinyarta a fili, ya girgiza kan shi kawai yana murmushi
Nan da Nan ta sauko a shirye cikin wando da Riga black se kuma doguwar jacket brown da takai mata gwiwa, yanata kallonta ta iso har gaban shi, bazaka kalleta kache yar Nigeria bache zaka dauka ko idan ta bude baki da Dutch zatayi magana, yayi nisa a tunani yaji muryar ta
“Amma ynzu ka dawo daga office bazaka huta ba?”
Ya ajiye laptop bag ɗinsa a console table din da ke wurin
“But you’re my wife, you come first”
Maryam ta yi murmushi
“Zo muje” ya fadi yana riqo hannunta
Bayan kusan mintuna arba’in suna tafiya a mota yana riqe da hannunta cikin nashi yana driving da hannu daya
Se ya tsaya a gaban wani babban telecom registration centre, ya sauka ze zagayo ya bude mata qofa amma ta bude ta fito da kanta, ya riqe hannunta suka shiga ciki, mutane cike sosai kamar ba dare ba
Wani staff yazo ya tarbe su, zaid yayi mishi bayanin abin da suke so da yaren Dutch, se mutumin ya juyo yana tambayar Maryam ta ba da passport dinta da sauran documents da yaren Dutch, tayi shuru tana kallon mutumin, zaid yayi dariya ya gaya mata abnda yache se ta chiro ta bashi
Bayan an yi registration aka bata sabon Dutch SIM, Zaid ya ɗauki wayarta ya dan duba, se suka matsa daga gefen masu registration zuwa wani side da aka jera wayoyi, nan ma dai da Dutch Zaid ke yima mutumin magana se ya tashi ya dauko sabuwar iPhone wadda take jin su safiya suna chewa Itache sabuwar da aka fitar wannan shekarar, mutumin ya bude ya karbi sim din hannun Zaid yasa a ciki sannan ya bashi wayar da kwalin da komai, ya karbi wayar yasa number dinshi ta Amsterdam ya miqa mata
“Kira ni in ga number dinki”
Tayi dialing.
Wayarsa ta yi ringing.
Yayi saving da My haya❤️
Maryam ta kalle shi.
“Me ka rubuta?”
“Mayramu.”
“Mayramu?” Ta maimaita don bata taba jin ya kirata haka ba
“Me kike so in rubuta?”
Ta yi shiru.
Zaid ya yi murmushi.
“In rubuta Mrs. Balarabe?”
Ta dan turo baki
Ya maida wayar shi aljihu, “haya ki dena turo min baki haka idan muna cikin mutane, zan iya yin abnda zakiji kunya”
Itakam batasan ma tanayi ba don abun ya zama dabi’a
Ta sake turo bakin “toh ai banyi ba”
Ya girgiza kan shi yana chije lips dinshi na qasa
“kira Mama ynzu tun kafin mu bar nan”
Ta kira mama bata daga ba, tanata bata fuska kamar zatayi kuka
“Qila bata kusa da waya ne, zata kira ki daga baya” ya fadi a qoqarin shi na ganin bata shiga bad mood ba amma ina, Duk yanayinta ba daadi haka dai suka isa wurin mota ya bude mata ta shiga shima ya zagaya ya shiga, Seda ya shigo ta fara yimishi godiya
“Nagode Allah ya saka da alheri Allah ya biya maka buqatun ka na alheri”
“Ameen haya, alhamdulillah Allah ya karba min Adduar samun mata ta gari, sora yara masu albarka ki bani”
Ta sunkuyar da kanta kawai tanata kallon wayar
Yanata tunanin me ze yimata ta dawo cikin good mood dinta, don tun da ta kira mama bata daga ba yaga duk batada walwala, se ya dauki wata hanya wanda ba hanyar gidansu ba, sunyi tafiyar kusan 1hr sanann sukayi parking wani wuri da zata iya chewa tun da tazo garin bata taba ganin qasa ba se a nan, ko a hanya bata taba ganin qasa ba daga titi se interlock, ta daga kai se taga an rubuta Amsterdam Canal Belt (Grachtengordel)
Suna shiga ciki taga wani security da ke wurin da sauri ya taso sunata magana da zaid da yaren Dutch, da alama dai gaisawa sukeyi, ta duba gefe taga layi inda Mutane ke bi idan sun shigo, tana tunanin idan sun qare gaisawa zasu bi Layin ne amma se taga sun bi wata hanya da aka rubuta privé aanlegsteiger (private cruise dock), suka dan zauna a wurin na mintina kadan sadda mutumin ya shiga daga ciki, be dade ba ya fito yana magana da Dutch yana musu nuni da babban hanyar da ke kare da glass koina, zayd ya riqo hannunta suka shiga ta hanyar, abnda maryam bata sani ba shine wannan hanyar Itache direct take zuwa private aanlegsteiger ɗin zaid, inda babban jirgin ruwan shi yake wanda ake kira da cruise ship, seda suka kai qarshen qofar ta tsaya cak tana kallon wasu irin ruwa da suke gabanta, bata ga farkon su ba balle qarshen su, ta kalla iyakar ganinta, daga chan nesa dasu sosai Mutane ne a layi suna nuna ticket dinsu suna shiga cikin wani jirgi wanda da alama commercial ne da yake yawatawa da Mutane, amma wanda take gani gabansu, babu kowa a wurin se wannan security din da ya shigo dasu, Babba ne me girman gaske fari ne tass da dan brown a jikinshi, se manyan windows da take gani na glass, a jikin jirgin an rubuta “ZAID RAHMAN, MERIDIAN AXIS” gabadaya mamaki ya hanata magana, dare ne wuraren qarfe 8:30 amma wasu irin manyan fitilu da ke haska wurin zakache da rana ne, tana nan tsaye tana kallo se taji hannun zayd cikin nata “zo muje”
Ya ja hannunta suka nufi jirgin a hnkali suka taka steps har suke haye ciki, se a lokacin ta lura jirgin ma hawa uku ne, sannan iya ganinta babu abnda bata gani ba a wurin, manyan luxury bedrooms, da parlours kusan uku, kitchen da dining area, hadda cooks guda uku suna abnci a kitchen din, seda ya zagaya da ita ko’ina sannan suka haye sama gabadaya, wani irin babban outdoor deck ne, ga kujeru a jere, har da irin kujerun nan masu kamar katifa, taje bakin railing din ta tsaya tana kallon yadda jirgin ke tafiya dasu a cikin ruwa, wani irin daadi na ratsa ta, dd nan wayar zaid tayi ringing, assistant dinshi na office ne, nan suka fara magana, maryam bata fahimtar komai saboda duk Zanchen office ne, sun dan dauki lokaci kafin suka qare wayar se kuma ya bude fara duba abubuwa a wayar da alama aikin ne yaketa yi, maryam ta dan fara jin haushi ganin yadda gabadaya attention dinshi ya koma kan waya, idan ta tambayeshi abu se ya bata very short answer ko kuma Yayi shuru ga alama gabadaya hnkalin shi baya wurinta, zaunawa tayi akan dayar kujerar da ke wurin tayi shuru, jin da yayi shuru na tsawon lokaci yasa ya dago kai Se ya ganta zaune kan kujera ta bata fuska
“Me ya faru haya?”
“Ba komai” ta ansa tana turo baki
Kashe wayar Yayi yasa a aljihun wandon shi yazo kusa da ita ya zauna yana riqo hannuwanta
“Ai nasan irin wannan ba komai din naki”
Ta juya fuska gefe “je ka qare aikin ka tukunna”
Yasa hannu ya juyo da fuskarta “I have a meeting with my wife, everything else can wait”
Qoqari take kar tayi murmushi amma ta kasa seda tayi, ya kalleta shima yana murmushi
A dd nan cooks din suka fara haurowa suna jera musu abnci a wani table da ke wurin, seda suka jera duka sannan babban chef din ya fara yimusu bayanin menu din da abubuwan da aka hada a abncin, da Dutch yake magana zaid kuma yana fassara ma maryam, seda ya qare bayanin shi sannan suka wuche su kuma suka fara chin abnci a natse, sun kai 1hr a wurin bayan sun qare chin abnci tanata yimishi tambayoyi
“ynzu wannan naka ne?”
“Eh”
“Toh da yaushe kake zuwa nan din?”
“Sometimes nan muke zuwa muyi business meetings da wasu abubuwa, wani lokaci kuma idan banajin mood dina dd ina zuwa ni kadai in kashe wayoyina se na gama hutawa tukunna”
Maryam ta gyada kai tana mamaki
“Zaki fara school gobe, idan kunyi hutu zamu zo muyi kamar 1 week”
Maryam taji wani irin daadi tana tunanin yadda zataji daadin zaman se taji yana chewa
“Tashi muje, gobe zaki fara zuwa lecture ya kamata ki kwanta da wuri”
Ai ko maryam ta bata fuska kamar zatayi kuka idonta duk sun ciko da hawaye tana turo baki, zaid yana lura da ita amma beson yayi magana kar ta fara yimishi kuka, hakanan ya riqe hannunta har suka sauko daga chan saman da suke sannan suka nufi ta inda suka shigo jirgin, seda suka tsaya jirgin ya gama daidaituwa ya tsaya dakyau sannan suka sauko, wannan security din da ya rakkosu yana nan qasa yana jiran su, shi ya rakkosu har suka fito suka nufi mota yana magana da zaid da yaren Dutch, koda suka isa wurin mota akwai wani mutum tsaye a wurin yana sanye da uniform din wurin, zaid ya miqa mishi mukullan Motar ya karba sannan ya bude musu kofar baya yana dan rusunar da kanshi kadan, seda maryam ta shiga sannan zaid ya shigo wannan security din yana daga musu hannu har drivern wurin yaja Motar suka fita daga wurin, maryam na kwanche jikin zaid tana ta zumburo baki wai ita a dole an bata mata rai, zaid ya duqo dd fuskar ta “nache fah in kin samu hutun school zamuje muyi kwanaki ma”
Batache Komi ba se baki da ta qara zumburo mishi, bata Ankara ba se jin tayi ya fara kissing dinta, jikinta ya dauki rawa tana qoqarin ture shi amma a kwanche take jikinshi yana qoqarin sakar mata nauyin shi, hannunta tayi qoqarin kaiwa fuskar shi daqyar ta dan tura fuskar, ya jaye kadan yana kallonta cikin ido “please ka Bari a mota muke fah, idan mutumin nan ya gan mu fah”
hannu yasa ya jawota ya kwantar da ita ya lumshe idon shi
Koda suka isa gida zaid ya fito dauke da maryam hannunshi, driver din kuma ya fito ya miqa ma security din gidan makullin motar sannan ya fita daga gidan, zayd direct ya bude qofar parlor ya haye sama da ita, seda ya shiga bathroom sannan ya ajeta, hannu yasa ya dago fuskar ta ya kalleta na dan lokaci se kawai ya kai bakin shi a kan nata ya fara kissing dinta, duk da yanayin shock din da maryam ta saba ji besa tayi qoqarin turw zaid ba, se ma kawai jin tayi ta kai hannunta ta bayan kanshi zuwa cikin gashin shi, jin hannun maryam a jikinshi yasa yaji gabadaya notikan kanshi suna kwanchewa daya bayan daya, sake riqeta yayi dakyau yana chigaba da kissing da kissing dinta, daukar ta Yayi ya ajiyeta zaune akan marble na mirror din da ke cikin bathroom din, wani irin abu maryam ke ji yana shiga cikin kanta Wanda bata taba ji ba, bata tashi dawowa hankalinta ba seda taji zaid na neman rabata da rigar jikinta, riqe rigar tayi da sauri tana sauke kanta qasa, se a lokacin shima ya lura da abnda yakeyi, juyawa yayi ya fito ya rufe mata qofa, a kasale Tayi brush tayi wanka ta fito sanye da bathrobe a jikinta ta nufi closet, shi kuma ya miqe daga zaunen da yake ya shige bathroom din. Seda ta duba time tayi calculating da lokacin Nigeria sannan ta sake danna ma mama kira, seda ta kusa katsewa mama ta daga
“Assalamu alaikum Mama.” Maryam ta fadi kamar zatayi kuka
“Wa alaiki salam.”
Mama ta ɗan yi shiru tana sauraren maryam da ta fara sheshekar hawaye
“Maryam?”
“Naam”
“Kukan kuma na minene wai bakisan kin girma ba?”
“Mama na kiraki dazu baki daga ba, se yau nasa layi”
“Naga missed call amma ban gane kan lambar ba shiyasa ban kira ba, Lambar chan che ko?”
Maryam ta yi dariya.
“Eh mama”
“Kuna lafiya ko?”
“Eh Mama, alhamdulillah”
“Yaya garin?”
“Lfya qalau mama alhamdulillah”
“Yaya gidan?”
“Gidan ma Lfya qalau mama”
Mama ta yi dariya.
“Toh ma shaa Allah haka akaso ai”
Suka fara fira mama na bata labarin abubuwan da zaid yayi a islamiyyar su, maryam tanata mamaki don Tasan yache zeyi amma be ma gayamata Yaushe ba, tana tunani taji mama na chewa “malaminku ma ya wuche umrah jiya da mata tai, ya anshi lambar ki amma yache yanata kira bata shiga, na hwada mai kunyi tahiya qila shiyasa be sameki ba”
Maryam ta yi shiru.
“Allah yasa Suyi karbabbar ibadah ya dawo dasu lfya, shi kuma Allah ya saka mai da alheri”
“Allahumma ameen ya Allah”
“Gobe ma zan fara zuwa makaranta in shaa Allah”
“Da gaske? Ma shaa Allahu”
“Eh. Mun riga mun gama registration ma
Mama ta yi farin ciki sosai
“Allah Ya sa ma karatunki albarka, shi kuma Allah ya biyashi da jannatul firdaus”
“Ameen.”
Suka ci gaba da magana na ɗan lokaci sannan sukayi sallama a dd lokacin da zaid ke fitowa daga bathroom
“Allah Ya tsare min ke.”
“Ameen mama, se anjima”
Maryam ta ajiye wayar.
Ta yi shiru.
Zaid ya kalleta.
“Autar mama kinji daadi ko?”
Ta gyada kai tana murmushi
“Sosai.”
Shima yayi murmushi
Seda sukayi shafa’i da witr sukayi addua, Zaid ya miqe yana qoqarin chire jallabiyar jikinshi maryam tayi sauri ya haye gado tana rufe idonta, Yayi murmushi ya chire sannan ya kashe wuta ya hau ya kwanta, Seda ya jawota jikinshi yana shafa gashinta har Tayi baccee sannan shima Yayi.
Washegari da wuri suka fita, Seda suka ajiyeta school shi da driver dinshi sannan suka tafi, ya gaya mata da ta qare lecture ta Kira shi, haka akayi, ta kirashi suka dawo suka maida ta gida sannan suka koma aiki.
Aiki yayi ma zaid yawa a office, duk ayukkan da suka taru yanata qoqarin yin su, kullun idan suka aje maryam school da safe shikenan se dare, idan ta qare lecture ta kirashi sedai ya aiko driver ya dauketa, sanda yake dawowa da dare tayi baccee ita kuma saboda gajiyar school, tanata qoqarin sabawa da yanayin makarantar saboda ba kamar wadda ta fito take ba, akwai banbanci sosai, duk da ma course mates dinsu sunada kirki har ta saba da wata Susan kullun tare suke komi a school har cafeteria tare suke zuwa, tare kuma suke zuwa library suyi karatu
Kusan sati biyu kenan maryam da zaid basu wata doguwar fira se da safe da yake sa tayi mishi karatu da kuma mota idan ze kaita school
Maryam ta fara gane kan rayuwar Amsterdam da taimakon Susan, ta koya mata yadda ake online, Shopping, tana sayen abubuwa da black card din zaid da ya bata ana kawo mata abubuwan da ta saye har gida, wani lokaci idan sun qare lectures tana gaya mishi zata fita da Susan se ya aiko driver ya kaisu duk inda zasuje sannan su kai Susan gida idan suka qare, ta sake da Susan sosai kuma tana jin daadin zama da ita, idan ka ga maryamar mama ynzu bazaka banbanche ta da yan Amsterdam ba don har Yaren Dutch Susan na koya mata kuma tana ganewa
A gefe daya kuma mystery ɗin Aisha bai fita daga ranta ba.
Yau sun qare lecture da wuri ta dawo gida se shiga study din zaid don tayi karatu…ta zauna a kujerar shi, zata fara karatu se ta fara tunanin yar uwar ta, ta dauki wayarta Ta buɗe old records ɗin da tayi screenshot.
European Trade Partnership — NCH
Ta fara searching names.
Aisha.
Northern Crest.
Rahman Balarabe.
Sai ta samu wani tsohon business article.
Northern Crest Holdings announces European partnership.
Ta danna.
Page ɗin bai buɗe sosai ba.
Se aka rubuta:
This article is no longer available.
Maryam ta yamutse fuska.
“Why?”
Ta sake searching title ɗin.
A wannan karon ta samu wani archived copy.
Ta fara karantawa.
Northern Crest Holdings had expanded its European business relationships with Bashir me salati and Rahman Balarabe as co-signatories, ta miqe tsaye, babanta? Tasan yayi aiki da northern crest amma ya akayi ya zama co-signatory?
Ta tsaya, Ta ɗauki notebook, Ta rubuta:
NCH Amsterdam Office — 5 years ago.
Sai ta rubuta:
Aisha — missing 3 years ago.
Ta haɗa su da line.
Ta tsaya tana kallon abin.
“Coincidence?”
Da yamma…Zaid ya dawo daga office, yau kam ya dawo da wuri
Ya shiga parlour ya same ta zaune da laptop.
“Karatu ake?”
Maryam ta ɗago kai Tana mishi Sannu da zuwa
“School dinnan akwai wahala”
Zaid ya kalli screen ɗin.
“International Relations din?”
“Eh manah.”
Ya zauna kusa da ita.
“Mu gani”
Maryam ta juya mishi laptop ɗin.
Zaid ya dan karanta.
“Sannu, Allah ya bada sa’a”
Ta kalle shi “Ameen”
Har ze miqe se ta tambayeshi
“Su Waye signatories na Northern Crest Holdings?”
Zaid ya tsaya, Sai ya kalleta.
“Again?”
Maryam ta ɗan yi shiru.
“Me yasa kache again?”
“Because kin taba tambayana gameda Kampanin”
“Ohh da gaske? Na manta”
Zaid ya kalle ta na ɗan lokaci.
“Mahreeyam…”
“Naam”
“Meyasa kike interested da Kampanin nan?”
Maryam ta yi shiru.
Ba ta san abin da za ta ce ba.
“Ba komi, inason jin ne kawai.”
Zaid bai amince da amsar ba, Amma bai matsa mata ba
“Okay.”
Ya tashi, Ya fara tafiya.
Maryam ta kalle shi.
Ta san ya lura tana boye wani abu
Amma abin da ba ta sani ba…
shi ma kanshi yana ɓoye wani abu
Da dare bayan sun chi abnci
Zaid yana cikin study dinshi, Laptop ɗinsa a gabansa.
Ya buɗe file ɗinnan da ya samo.
NORTHERN CREST HOLDINGS — ORIGINAL RECORDS
Ya fara karantawa.
Page ɗaya.
Biyu.
Uku.
Har ya kai page ɗin da ke ɗauke da sunan Aisha.
Ya tsaya.
Sai ya ga reference ɗin:
NCH Amsterdam Contact Office.
Zaid ya jingina da kujerarsa.
“Aisha? Meyasa tayi bincike har nan?”
Ya ci gaba da karantawa
Sai wani document ya bayyana.
Aisha ta taba yin request for access to original land records.
Date: Three years ago.
Zaid ya rufe idanunsa na ɗan lokaci.
Sai ya tuna Maryam.
Duk tambayoyinta.
Northern Crest.
Aisha yayarta
Rahman balarabe
Amsterdam.
Komai yana haɗuwa.
Amma har yanzu akwai wani abu da bai fahimta ba, shin Maryam neman Aisha take? Meyasa? Shin ba anche ta rasu ba?
Kuma me ya sa ba ta taɓa gaya masa komai ba?
A ɗayan ɓangaren gidan…
Maryam na kwance a kan gado se Ta buɗe sabuwar wayar da zaid ya siya mata, Ta duba contact ɗin Mama, Sai ta yi murmushi.
Aƙalla yanzu…ba ta jin ta yi nisa da Mama sosai kamar yadda takeji da.
Ta ajiye wayar Ta kalli sama
Sai tunanin Aisha ya dawo mata, Tana kewar yar uwar ta
“Me yasa kikayi binciken Kampanin nan sosai Aisha?
A dd wannan lokacin…
wayarta ta yi vibrating
Unknown number.
Maryam ta ɗauka.
Wani message ne.
Ki dena binciken abnda ya faru a Amsterdam
Zuciyarta ta buga.
Ta sake karantawa.
Sai wani message ya shigo.
Yayarki ma tayi wannan binciken amma binciken ba a chan yake ba
Maryam ta mike zaune.
Numfashinta ya tsaya na ɗan lokaci.
Yayata Aisha?
Ta fara typing.
Waye kai?
Ta aika.
Anyi viewing
Typing…
Sai ya tsaya.
Babu amsa.
Maryam ta sake kallon screen.
Ta tashi daga kan gadon , Ta buɗe ƙofar bedroom, Ta fito da sauri
A dd wannan lokacin kuma Zaid ya fito daga study yana haurowa Suka haɗu.
Ya kalleta yaga kamar tana firgice
“Mahreeyam?”
Ta tsaya.
“Me ya faru?”
Ta kalle shi, Ta kusan faɗa masa, Ta kusa cewa
“Wani ya ce min Aisha ta taba binciken abnda akayi signing a Amsterdam
Amma sai ta tuna duk abubuwanda ta ɓoye.
Sai tayi murmushin yaqe
“Ba komi.”
Zaid ya kalleta sosai.
“Kin tabbata?”
“Eh.”
Ya ɗan matso kusa.
“Haya”
“Naam?”
“In wani abu yana damun ki you can tell me..”
Ya tsaya.
“…tell me please”
Ta kalle shi.
A wannan karon…
ta ji kalmar ta shiga zuciyarta.
“Okay.”
Zaid ya gyada kai, Ya juya ze koma study don ya ma manta da abinda ya fito yayi
Maryam ta tsaya tana kallonshi, Ta san ya lura da wani abu, ya san ba ta faɗi komai ba.
Amma kafin ta koma ɗakinta…
ta sake kallon wayarta, Wani sabon message ya shigo.
Mijinki Yana kusa da gaskiyar fiye da yadda kike zato.
Maryam ta daskare, Ta kalli ƙofar study, Zaid yana ciki.
Sai ta sake kallon message ɗin.
A hankali ta furta:
“Wai waye wannan”
A wannan dare…
su biyun sun kwanta a gida ɗaya, gado daya, yana rungume da ita jikin shi
Amma kowannensu yana riƙe da wani sirri.
Maryam ta san wani yana bibiyar bincikenta.
Zaid kuma ya fara gano cewa Aisha ba ta rasu ko ta ɓace haka kawai ba, Tabbas Ta bar wani abu a baya.
Wani abu da ya haɗa ta da Northern Crest.
Da kuma Balarabe family.
Kuma wannan karon…
In shaa Allah ze gano gaskiyar da yake da tabbacin ba ta yi nisa da su ba.
Follow this link to join my WhatsApp group