Page 17
SAWU BIYU
Khadijah Sulaiman
YOTA
Book 1
Page 17
Follow the KHADIJAH SULAIMAN LIBRARY channel on WhatsApp: ***
*INA MASU SON SU RAGE TUMBI*?
*INA MASU SON SUYI KWALLIYA AMMA TUMBI YA HANA SU?*
*INA MASU JIN KUNYAN FITA CIKIN JAMA'A SABODA TUMBI*?
*INA MASU SON RAGE NAUYIN JIKIN SU*?
*INA WANDA SUKA HAIHU DAGA BAYA TUMBI YA HANA SU WALWALA DA KWALLIYA*?
*SHIN KINA SON NIMAN
MAGANIN RAGE TUMBI AMMA KINA TSORON YA MIKI ILLAH*?
*TOH ALBISHIRIN KU*👌
*KU MATSO NISA TAZO KUSA*💃💃💃💃💃💃💃
*Nazo muku da challange of 1 month flat tummy tea don samun saukin wannan tumbin da kike Jin kunya da son yin ado Babu dama
*
*ZAMU FARA SECOND BATCH*🗣️
*ZAMU FARA WANNAN CHALLENGE DAGA ON 25TH OF OCTOBER ZUWA 25th OF NOVEMBER IN SHA ALLAHU*
*Don samun damar shiga wannan challenge din akwai kudin biya 1k kachal👌*
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
PAY INTO THIS ACC
HABIBA SULAIMAN
OPAY
8133475029
VENUE:WHATAPP GROUP
*KAR KI BARI WANNAN DAMAR TA WUCE KI*🧚♂️🧚♂️🧚♂️🧚♂️🧚♂️🧚♂️
Ya ɗauke kai daga kallon Hajja ya miƙe ya shiga ɗakin Oum, Hajja ta gyaɗa kai tace"ji wani gulma,to duk za ku ji dashi".
Zarah tace"zan tafi Hajja".
"To dama akwai aikin da kike min ne zaki wani ce zaki tafi,bana son iyayi da feleqe,ki zo ki buɗe abinda kika taho dashi,Hafsah da sanyin jiki ace sai yanzu zaki aiko da abin kalaci har rana ta fito kuma wai a haka likita ce,inda Ramlah ta fita kenan gaskiya ba dai zafin nama ba,sai dai ko karen hauka ya cije ni ba zan yarda inci abincinta ba,an sha ni na warke,ahto".
Zarah ta ƙaraso ta shiga fito da warmers din,na farkon ta fara buɗewa dake cike da manyan masa,ta buɗe na biyun da aka yi pepper chicken sai na ƙarshen miyan masan ne cike da cow leg,sai tea flask.
Hajja tace"to ai dole ma ta ɗauki lokaci,irin wannan aiki haka,ko da wannan dole ta kwace miji ta bar Ramlah da kallo mata sai jaraba".
Zarah ta taɓe baki ta miƙe tsaye tace"zan tafi".
Hajja ta watsa mata harara a fusace tace"cizon ki ake a nan ne ko me,ko ita Hafsah ce tace idan kin kawo kar ki zauna kar in cinye ki,da ina cin mutane da bata ga ubanki ta aura ba,wuce kitchen ki ɗauko min plate ni kar ki ɓata min lokaci nansense".
Zarah ta turo baki ta wuce kitchen,tana dawowa Firdausi ta shigo parlourn ta gaida Hajja.
"Mami ta ce kije tana kiran ki".
Hajja tayi tagumi tace"oh ni Fatima yau ina ganin ikon Allah,daga shigowar yarinya yanzu yanzu ko minti ɗaya bata cika ba shine za'a sani gaba da zarya?to ki wuce kice mata nace ba yanzu ba".
Firdausi tace"magani za ta sha Hajja".
Hajja tace"Shi maganin ba za'a iya kawo shi nan bane dole sai a ɗakin ku za'a sha,kuji jaraba".
Dai dai nan Daddy ya shigo,ya ƙarasa ya zauna gefen Hajja,bayan ya gaisheta yace"me ke faruwa Hajja?"
"Babu komai,kawai dai Hafsah ce ke min abinda bana jin daɗi,akan me daga aiko yarinya za ki wani turo ki ce zata sha magani,shi maganin ba za'a iya kawo shi nan ba ne?"
Daddy ya kalli Firdausi yace"ki wuce ki kawo maganin nan,kafin ki shiga ciki ki kiramin Sadauki ya same ni a nan".
Firdausi ta amsa da toh ta juya ta fita, Zarah dai na zaune ta rasa abinda ke mata ɗaɗi.
Hajja ta kalleta tace"ki wuce ki gyaramin ɗaki,kuna mata dole sai ana saku aiki,ki gyara min gado da kyau,ba zan zuba ido ina kallon ku a sangarce ba".
Ta miƙe kamar za ta fashe da kuka ta shiga ciki.
A nutse Sadauki yayi sallama a bakin kofa aka amsa mishi ya shigo,Hajja ta gyara glass ɗin idonta ta bishi da kallo har ya zauna can nesa dasu.
A hankali yace"sannu da zuwa, kin zo lafiya,ya hanya?"
Tace"lafiya kalau,ya wajen iyayen ka?"
Kanshi a ƙasa yace"lafiya Alhamdulilah".
Abdallah ya turo kofa ya fito Oum biye dashi,ya ɗurkusa ya gaida Daddy.
Cike da kulawa Daddy ya amsa,ya miƙe zai bar wurin suka haɗa ido da Sadauki.
Lokaci ɗaya duk suka ɗauke kai.
Oum ta zauna kusa da Daddy tace"Good morning Yaya".
Daddy yace"morning Khadijah,ya gajiyan hanya?"
Tayi dariya tace"gajiya yabi lafiya Yaya,mun same ku lafiya?"
Yace"lafiya Alhamdulilah".
Sadauki ya gaida Oum,ta amsa cike da fara'a.
Ya juya ya kalli Sadauki yace"za ka iya tafiya Umar,ka same ni around eleven".
Sadauki ya miƙe yace"in sha Allah".
Bayan ya fita Oum tace"waye wannan Yaya?"
Ya kalli Hajja da ta zura mishi ido ya shiga mata bayani yadda zata gane har ya kai karshe, Hajja sai wiƙi wiƙi take da ido don hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba.
Da sauri tace"amma wani bahagon tunani ne haka,a wannan rayuwar da akeyi a Nigeria ta rashin tsaro shine zaka ɗauko almajiri daga titi kai da matar ka kace zaku taimaka masa?,ni dai gaskiya ban yarda ba,naga sai wani sunne kai yake da gani bai da gaskiya don kama yake da munafukai".
Daddy ya girgiza kai yace"na san da haka Hajja,ba haka kawai na ɗauki yaron nan ba sai da nayi kyakkyawar bincike,kar ki manta ni soja ne,yaron bai da matsala in sha Allah,yanzu haka ya samu admission a makarantar sojoji zuwa next week zai tafi".
Oum ta sauke numfashi tace"i trust you Yaya,duk da ba sanin komai nayi ba but I'm sure haka kawai ba zaka ɗauko shi without proper investigation ba,Allah ya taya ka riƙo yasa hakan shine mafi alkhairi".
Yayi murmushi tace"thank you Khadijah".
A can ɗakin Hajja Zarah na kokarin gyara gadon Hajja dake bata wahala Abdallah ya shigo,yana ganinta ya watsa mata harara yace"ki daina kallo na da wannan manyan idon naki kaman na owl suna firgita ni,mara kunya kawai".
Ya ƙarasa ya ɗauki wayar shi dake saman mirror ya juya ya fita,da wani mugun harara Zarah tabi bayan shi ta ja tsaki tace"mugu kawai,I hate you".
Da yamma Mama ta shigo wurin Hajja,bayan sun gaisa Hajja da dama neman wanda zata fitar da abinda ke ranta take tace"wai ke kuwa Ramlah kina gidan nan wannan almajirin yayi baƙe baƙe cikin gidan jama'a baki hana mijin ki ba?,ai yanzu duniyar ba yarda,ka yiwa mutum alkhairi ya rama da sharri shi yasa ko sadaka na daina basu saboda mugaye ne wallahi".
Mama ta gyara zama ranta fari ƙal kamar ta tashi ta taka rawa ta sauke murya tace"ai wallahi babu yadda banyi ba Hajja amma kaman wadda ake zugawa har faɗa sai da mu kayi a kan hakan".
Hajja tace"ai ba cewa za kiyi kamar wadda ake zugawa ba,zugan ne mana,don lamarin babu taknology sam a ciki,dole ma yaron ya bar gidan nan don hankali na bai kwanta dashi ba gaskiya".
Hajiya Mama tace"hakan shine mafita Hajja,yaron bai da hali kwata kwata,akwai ranar da na nemi wani dubu biyar na rasa kuma tabbas na ganshi kusa da inda na zauna ta wurin garden,na san shi ya ɗauka kawai fitina ce bana so shi yasa banyi magana ba kin san halin Hafsah".
Hajja ta gyaɗa kai tace"ni ko na san halin Hafsah ciki da bai,sai dai in ba wani labarinta".
Shigowar kiran aminiyarta Zainab ya sa ta miƙe da sauri tace"Hajja nayi bakuwa,zan dawo zuwa anjima".
Hajja tace"to shikenan sai anjima".
Tana fita Hajja ta cire hulan kanta ta ajiye saman gado farin gashinta ya bayyana tace"wai,daga baƙin munafiki sai Ramlah,mata sai mugun hali,yanzu zuga ni take in sa yaron nan a gaba ya kori almajiri ko me?tunda gani ƴar banza,to Allah ya fiki muguwa kawai,bakin cikin lada take mana,tunda na san har ni sai na sami lada tunda ni na haifi mai gidan".
Bayan an idar da sallar magriba Zarah ta fito daga part ɗinsu riƙe da basket ɗin abincin Hajja,harta gifta sai ta hango Sadauki dake kokarin shiga part ɗinsu shi da Sudais,ta kwala mishi kira da ƙarfi tace"Yaya F".
Ya juya da sauri don harga Allah ya ɗauka faduwa tayi,ganinta tsaye tana dariya yasa ya tamke fuska,ta ƙaraso gaban shi tace"Yaya F".
Wani harara ya galla mata yace"ni sa'an kine zaki kira sunana da ƙarfi haka da wannan daren?"
Ta langwabe kai tace"kayi hakuri,dama Mami ce tace idan na ganka in sanar da kai tuwo tayi amma ta dafa maka indomie ka shiga ka karɓa".
Ya kalleta tun daga sama ganinta da siririn veil yace"Ina za ki je haka?"
Ta nuna mishi basket ɗin hannunta tace"abinci zan kaiwa Hajja".
"Shine aka ce kar ki sa hijab?"
Za tayi magana ta hango Abdallah dake tafe yana danna waya,hasken solar daya karaɗe gidan ya haska farin fatar shi,tana ganin shi ta ɗauke kai da sauri don ko haɗa ido bata son su yi.
Har zai wuceta sai kuma ya juyo ya mata kallon up and down yace"kina jira in gaishe ki ne?"
Da sauri ta sunkuyar da kai tace"ina wuni".
Ya galla mata harara ya bar wurin Sadauki ya bishi da kallo.
Sai da yayi nisa ya ɗauke kai daga kallon shi ya juyo ya kalli Zarah yace"waye shi?"
Zarah tayi shiru tana ƙoƙarin maida hawayen da ya cika mata ido.
A hankali yace"Mimie".
Ta ɗago a hankali tace"na'am".
Ya watsa mata harara yace"menene abin kuka anan,kuka bai da wahala a wurin ki ko,maza ki share hawayen nan bana son gani".
Ta sa ƙasan mayafinta ta share idonta ta ɗago tana kallon shi.
"Ɗan uwan ku ne?"yayi tambayar yana kallonta.
Ta gyaɗa kai tace"yaron Oum ne".
Sadauki yace"ita Oum itace wata fara haka dana gani?"
Tace"eh,kanwar Daddy ce,su biyu kawai Hajja ta haifa,ita wannan masifaffiyar daka gani itace Hajja,sunanta aka sa min,ni wallahi da ba'a sa min ba ta cika masifa".
Sadauki ya waro ido da mamaki yace"really,to kuma naga har kama kuke da ita".
Zarah ta fashe da kuka tace"ni dai banyi kama da ita ba da Mami nayi kama".
Sadauki ya koma baya yace"lafiyar ki kuwa Mimie?ɗauki basket ɗin nan ki bar nan kafin in mare ki".
Da sauri ta ɗauki basket ta juya ta bar wurin tana turo baki.
Hajja dake zaune kan gado riƙe da Ipad ta gyara zama ta ajiye Ipad ɗin hannunta tana kallon Zarah tace"kukan uban me kike?"
Abdallah dake zaune kan kujerar ɗakin yana kallon ball hannun shi riƙe da Apple ya mata kallo ɗaya ya ɗauke kai.
Zarah ta turo baki tace"babu komai".
Hajja ta ɗauki Ipad dinta tace"ki ci kanki,sai yanzu Hafsah ta gama abincin dare kenan,ko dai tsabar wulakanci yasa sai yanzu za'a kawo min tunda ta san ba kowanne abinci nake ci ba sai nata,ita wancar hamshakiyar tun ɗazu ta kawo abin ka da ƴar zaman kashe wando,duk da mai aiki ke mata girki ba kamar Hafsah da ke yi da kanta ba".
Abdallah ya juyo yace"kina distracting ɗina,bana gane komai a nan".
A fusace tace"sai ka tashi ka fita tunda ɗaki dai nawa ne,kana da naka ɗakin akan me zaka takurawa rayuwata,salin alin nake kallon pim ɗin Hausa daga shigowarka ka canza zuwa ƙwallo nayi shiru bance komai ba shine zaka hana ni magana ni ba kurma ba,to da sake wallahi,ina Khadijah ta zo ta shiga tsakani na da kai don ba zan iya ba gaskiya".
Zarah tace"ni zan wuce Hajja".
Hajja ta juyo kanta a masife tace"ki fi ruwa gudu ke kuma,yara duk sun bi sun sa ka a gaba sun hana ka sukuni,dubi girman ɗakin nan amma haka zai shigo yayi baƙe baƙe tamkar nashi ya addabi rayuwata numfashi mai kyau gagarata yake,idan kayi magana ya hau turance ka kamar shi kaɗai yayi boko a duniya".
Zarah ta juya ta bar musu ɗakin su ci kansu.
Washegari Sudais ya dawo don dama baya nan ya tafi Katsina wurin mahaifinsa.
Ƙaton jaka ya kawowa Zarah cike da kaya don mahaifinsa babban attajiri ne.
Ta rungume sa cike da farin ciki tace"nagode Ya Sudais".
Sadauki dake zaune a dining ɗin Mami yana cin abinci ya ɗauke kai.
Sudais ya riƙe hannunta suka zauna kan kujera yace"don't mention my Zarah,kin wuce haka a wuri na".
Mami ta sauko riƙe da handbag da alama fita za tayi, Zarah na ganinta ta miƙe da sauri don ta san zata sha faɗa,Mami tayi tamkar bata ganta ba ta ƙarasa wurin Sadauki tace"Faruq ka gama?"
Ya shafa kai tatce"na gama Mami".
Ta miƙa mishi key ɗin hannunta tace"tashi ka kaini wurin aiki,ina da theater nan da awa ɗaya".
Ya miƙe yasa hannu ya karɓi key ɗin ya fita,Sudais ya gaida Mami ta amsa da fara'a ya juya ya bar parlourn.
Ta watsawa Zarah wani harara tace"wuce ki ɗauko hijabi ki same ni a waje".
Ta wuce ɗaki jiki a sanyaye,duk sonta da yawo wannan kam bai faranta mata rai ba.
Tana shiga ɗaki ta wuce gaban wardrobe ta buɗe ta ciro dogon hijab ta sa,tana ƙoƙarin fita Naima tace"ina zuwa?"
Ta mata banza ta buɗe kofa ta fita.
Naima ta gyaɗa kai cike da masifa tace"za ki dawo ki same ni".
Zeenah tace"ba zai wuce ita da Mami ba tun da yanzu ta sauka kuma kin san tun ɗazu take parlourn".
A cikin mota ta tarar da Mami sai Sadauki zaune a driver seat,tana shiga kamar Mami jira take ta wanke fuskarta da mari.
Da sauri Sadauki ya juyo, ganin tana ƙoƙarin ƙara mata yace "ki yi hakuri Mami".
A fusace ta kai mata wani marin tana cewa"ka barni in ɓalla yarinyar nan Faruq tun da har yanzu ba tayi hankali ba,ban hana ki shigewa maza ba,ban hana ki rungume Sudais ba ko an gaya miki har yanzu ke yarinya ce?"
Ƙasa ƙasa take kuka in banda rawa babu abinda jikinta yake.
Sadauki ya sunkuyar da kai yace"ki yi hakuri Mami,za ta kiyaye".
"Kar ta kiyaye ta cigaba,uwar shi ta hana shi mu'amala dani amma sai makale masa take,ba zan hana ki magana dashi ba amma karki sake rungume shi,ko hannun ki karya sake taɓawa,ba shi kaɗai ba that applies to duk maza".
Zarah ta gyaɗa kai da sauri don ba ƙaramin rikicewa tayi ba,a duniya ba ƙaramin tsoron duka take yi ba.
Har bakin asibitin Mami Sadauki yayi parking,ta juyo ta kalle shi tace"Nagode Faruq, Daddy ya maka maganan School ko?"
Yace"ya min magana jiya,yace ranar Monday za muyi reporting".
Mami tayi shiru kamar mai tunani,can tace"ba zai yiwu ka tafi ranar Monday ɗin ba ai sai dai ko Saturday ko Sunday,za kayi lodging a hotel kenan,ka tafi gida nagode,idan na dawo zamu ƙarasa".
Ta juya ta kalli Zarah yace"ko saina fito dake?"
Da sauri ta fito daga motar tana share hawayen fuskarta, Sadauki ya bi fuskarta da kallo ganin yadda yayi jawur tsabar kuka.
Mami ta nufi cikin asibitin ta bita a baya,sai da ya ga shigar su sannan ya ta da mota ya bar wurin.
Ƙarfe tara na dare suka dawo gida,Zarah na shiga ɗaki ta cire kayan jikinta ta shiga wanka,bayan ta fito ta shirya cikin kayan bacci riga da wando ta hau gado ta kwanta don bata jin yunwa.
Oum Rijalain
***