SAWU BIYUFree

ArewaPen original

ThrillersFreeOngoing

SAWU BIYU

  • 1views
  • 2chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

ongoing

No synopsis yet.

Sample · Page 12

SAWU BIYU BY Khadijah Sulaiman Young Talented Writers Association (YOTA)Book 1Page 12Cike da wani irin nutsuwa Sadauki ya koma makaranta,gabaɗaya ya nemi ɓacin ran abinda ya faru dashi ya rasa.Sadiq dake zaune a ɗaki tare da wasu yaran ya ɗan bi shi da kallo ganin yadda yake murmushi,ya ajiye allon hannun shi da mamaki don abu ne da ba kasafai ya ke yi ba yace"ikon Allah,wai wani labarin ka samo ne haka ka shigo kana wannan murmushin?"Da sauri ya juya suka haɗa ido,ya shafa kai ya nemi wuri ya zauna still yana murmushi yace"babu komai".Sadiq yace"ban yarda ba gaskiya,haka kawai ba za ka dinga wannan murmushin ba Sadauki".Ya miƙe ya bar ɗakin Sadiq ya bi shi da kallo.Gabaɗaya yinin ranar cikin farin ciki Sadauki ya yi ta,shi kan shi ba zai ce ga ƙwaƙwaran dalilin da yasa yake wannan farin cikin ba.Bayan an idar da sallar magrib ya kasa tafiya gidan kamar yadda ta umurce shi duk da yaso yin hakan,haka ya koma ya zauna yana kallon sauran dake cin tuwo.Washegari kamar yadda aka saba bayan an gama karatu aka fara barin makarantar.Bayan yayi wanka ya ciro riga daga jakarsa,duk da a koɗe rigar take amma bai da datti.Har ya sa rigar maganar yarinyar jiya ya faɗo mishi,yayi murmushi yana tuna yadda take bin shi da kallo cike da mamakin koɗewar kayansa.Tun da ya fita yake yawo ko Allah zai sa ya samu ɗan aikin da zai yi,tun ɓacewar Sani ya daina bara kuma gashi yanzu ya fara zama saurayi shi yasa yake kokarin neman aikin hannu da zai yi ya samu na cin abinci.Sai da yayi sallar azahar a wani masallaci sannan ya taka har ƙofar gidan,ya kai kusan minti biyar a tsaye yana tunanin yadda zai shiga gidan.Kamar haɗin baki sai ga motarta,suna isa dai dai inda yake ta sauke glass tana kallon shi tace"Sadauki ba ka shiga ba?"Ya sunkuyar da kai cike da kunya yace"ina wuni".Ba ta amsa ba tace"ka shigo ciki".Driver ya ja motar suka shiga Sadauki ya bi bayan su bayan ya gaisa da mai gadi,ta fito sanye da hijab sai labcoat da ke riƙe a hannunta tace"jiya da daddare na jira shiru,me yasa baka dawo ba?"Yayi shiru kanshi a ƙasa,Mami da ke lura dashi tace"ai ni nace ka dawo Umar,kar ka sake min haka,daga yau anan za ka dinga cin abinci daga na safe har na dare,idan dai ka zama mai gaskiya ba ka da matsala da ni,ka zauna zan aiko a kawo maka abinci".Ya sunkuyar da kai yace"to Hajiya".Sai kuma yayi saurin cewa "Mami".Mami tayi murmushi tace"gara da ka gyara tun wuri".Tana shiga parlour ta tarar da Zeenah riƙe da bulala sai Zarah kusa da ƙofa fuskar nan shaɓe shaɓe da hawaye.Mami ta bisu da kallo tace"lafiya?"Zarah ta rungume ta da sauri ta fashe da kuka,Zeenah ta taɓe baki don kukan da take ba cetonta zai yi a hannunta ba.Mami tace"me ya faru,kin ishi mutane da kukan banza?"Cikin kuka tace"Mami ! Aunty Zeenah want to flog me"Mami tace"ai gara ta zane min ke tunda kin...

Continue reading free chapter

Contents

Table of contents

Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.

chapters2
premium1
01

Page 12

Premium
Updated 2 hours agoAvailable now

Continue in the ArewaPen app

Unlock offline reading, audio mode, and sync your bookmarks instantly.

Download on the App StoreGet it on Google Play