Chapter 2
╔══════════════════════╗
🌺🌺 *KOWA DA RABONSA* 🌺🌺
╚══════════════════════╝
🌺 A Story Filled With Lessons, Destiny and Love🌺
✍️
> BY MARYAM USMAN MAMYY WRITER (FULANIN JAJIRTATTU)
━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━
🏆 JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION
✨ FIVE STAR WRITERS✨
📞 ***
📚 BOOK 1
📖 Page 2
━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━
بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
Bismillahir Rahmanir Rahim.
~Wane lokacin kaddara ce take zaɓa maka rabonka, wani kuma rabon nasa ne kaddara. Duk abin da ya zama rabonka dole ne ka yi haƙuri da shi.~
> NOTE: Ban yarda da wani ko wata su yi amfani da littafina ba. Ban yi littafin nan da wata ko wani ba. Duk abin da kuka gani mallakina ne, bana so wani ya yi min copy ba tare da sanina ba.
> Baba Malam ne ya jinjina kai alamar ya gamsu da abin da ya faru. Abubakar Madawaki ne ya kalli Shamsudeen da sauran yaran da ke zaune a gefen Daada, ya ce su koma dakunansu.
> Magana suka yi iya manyan Madawaki Dynasty sai matansu, waɗanda ke mamakin abin da M. Madawaki ya yi wa Hajarah na aure da ya sauke.
━━━━━༺🌺༻━━━━━
*TUBALI!!*
Mafarin komai.
*MAMUB.*
MAMUB shine cikakken sunan da duniya ke kiran su da shi, wato Abubakar Muhammad Maina da Muhammad Aliyu Madawaki.
Aminci mai karfi ne a tsakaninsu, wanda ya daure su fiye da jinin da ke yawo a jikinsu, haka ma zukatansu suka ɗaure da kaunar juna.
Sun taso tamkar uwa ɗaya ce ta haife su, suna matukar kaunar juna. Kowannensu yana ganin amanar ɗan uwansa tana hannunsa ne. Tun daga makarantar firamare suke tare, babu wanda bai san irin kaunar da suke yi wa juna ba.
Sun girma tare, har abotarsu ta kai matsayin da babu wanda zai iya cewa akwai banbancin jini a tsakaninsu. Sun kasance kamar inuwa da mai ita, inda ɗaya yake, ɗayan yana nan.
Idan ɗaya ya yi farinciki, ɗayan ma farinciki yake yi. Idan daya ya shiga damuwa, ɗayan baya samun kwanciyar hankali har sai sun warware komai.
Irin wannan kakkarfan abota ce ta sa gidajen Maina da Madawaki suka zama tamkar gida daya. 'Ya'yansu suka taso suna kiran juna 'yan uwa, iyaye kuma suka zama tamkar iyali daya.
Kasancewar gidajensu suna kallon juna ne ya kara karfafa wannan kusanci. Ba a taba samun ranar da ba a ga ɗaya daga cikinsu a gidan ɗayan ba.
A wajen mutane, MAMUB ba kawai sunan abota ba ne, tarihi ne na aminci, amana da kaunar da ta girma tare da su tun suna yara.
Bayan sun kammala karatunsu ne suka fara aikin MADAWAKI DYNASTY HOLDINGS.
Madawaki Dynasty kamfani ne da aka kafa shekaru da dama da suka gabata daga dangin Madawaki. Daga karamin kasuwanci ya bunkasa har ya zama daya daga cikin manyan rukunin kamfanoni masu zaman kansu.
Babban sirrin karfinsa shi ne, ba mutum daya ne ke mallakar komai ba. Kasuwancin yana da alaka da kowa na Madawaki Dynasty.
Founder & Chairman: Alhaji Aliyu Madawaki, wato Baba Malam. Mutum mai shekaru, natsuwa da kwarewar kasuwanci.
CEO: Abubakar Aliyu Madawaki. Babban mutum mai kamala, mai tsauri wajen aiki, amma mai zurfin tunani. Shine ke jagorantar manyan harkokin kamfanin.
Executive Director: Sayyid Aliyu Madawaki, wanda yake taka muhimmiyar rawa wajen tafiyar da kamfanin.
Manyan matsayi aka basu tare da bawa kowannensu office ɗinsa, kusa da juna. Sannan suna da private executive office a saman bene na Madawaki Dynasty Tower, wanda yake da babban tagar gilashi da ke kallon tsakiyar kamfanin. Duk abin da yake faruwa a kasa suna gani.
Tun fara aikinsu kamfanin ya sauya. Domin M. Madawaki har ya fi Abubakar Madawaki tsanani, kowa tsoronsa yake ji. Idan ma'aikata suka ga motocinsa sun shigo harabar kamfanin, kowa ya san cewa "Boss ya iso." Duk abin da suke yi ba daidai ba, za su yi saurin gyarawa kafin ya karaso.
Shekaru uku da fara aikinsu, suka fara neman aure. A lokacin Allah ya hada su da wasu abokai da suke matukar kaunar juna, wato Rahmah da Ruƙayyah. Wasu kawaye ne da suka taso da tsananin son juna.
M.Madawaki ne ya nuna yana son Rahmah, A. Maina kuwa yana son Ruƙayyah. Sai da soyayya ta yi nisa ne Rahmah ta fahimci cewa Ruƙayyah M.Madawaki take so.Sai Rahmah ta yanke hukuncin cewa bata son M.Madawaki, ita A. Maina take so.
Rigingimu suka fara, har takai iyayensu sun shiga lamarin. A lokacin kowa ya san dalilin da Rahmah ta ce bata son M. Madawaki. Kuma ta sake tabbatar musu da cewa in M. Madawaki ba zai auri Ruƙayyah ba, sai dai duk su haƙura.
Baba Malam ne, wanda yake mahaifin Muhammad Madawaki, shi ne ya tara su, yana nuna wa kowannensu su yi haƙuri su karbi juna a yadda kaddararsu ta nuna. A bangaren matan sun amince, domin su bakinsu ɗaya, duk abin da ɗaya take so za ta iya hakura ta barwa 'yar uwarta, kamar yadda Rahmah ta yi yanzu.
Baba Malam ya san M.Madawaki bakin A. Maina ne, shi ya sa ya tsare A. Maina da idanunsa tare da cewa,
"Abubakar, na san duk abin da ka fada, shi Muhammad zai fada. Ina so ka san KAWO DA RABONSA, ba kowa ke zabar rabonsa ba, wasu rabonsu ne ke zabar su."
"Gashi dai wacce ka zaɓa ba rabonka ba ce, amma shi Muhammad rabonsa ne ya zabe shi. Don haka nake so kowa ya karɓi abin da yake rabonsa ne. Allah ya rubuta Rahmah ita ce matarka, shi kuma Ruƙayyah."
Murmushi A. Maina ya yi tare da kallon fuskar M. Madawaki wanda ya yi shiru kamar baya wajen.
"Babu komai Baba Malam, na san M. Madawaki ya karɓi Ruƙayyah a matsayin mata, ni ma kuma zan karɓi Rahmah."
A satin aka daura auren tsakaninsu, kowa ya karɓi abin da Allah ya zaba masa. Wani aminci mai ƙarfi ya ƙara shiga tsakaninsu, matansu kansu a haɗe, suma haka babu wanda ya taba jin wata matsala a tsakaninsu.
Shekara ɗaya da aure, Allah ya azurta A.Maina da Rahmah da haihuwar yaro namiji. Ranar suna ya ci sunan mahaifinsa, Muhammad Madawaki.
Haihuwa kacal Rahmah ta yi, Ruƙayyah ce take yi masa komai. Ita ce mai kula da shi, sai ya yi kuka take kaiwa Rahmah shi. Shekara na zagayowa, Rahmah ta sake haihuwar yariya mace wacce ta ci sunan mahaifiyar A. Maina, wato Nadiya.
Haihuwa Nadiya ne Ruƙayyah ta ɗaga hankalinta akan rashin haihuwar da basu samu ba. Daada ma, mahaifiyar M. Madawaki, ta shiga damuwa ganin matan ƙannansa sai haihuwa suke, amma shi shiru babu labari. Takurawa M. Madawaki aka yi zuwa ganin likita ko da wata matsala.
Domin Madawaki Dynasty sun yi tunanin Ruqayyah ce mai matsala. Asibiti na farko da suka je, sakamakon ya nuna dukkansu kalau suke, babu wata matsala, Allah ne bai kawo ba.
Daada ce ta nuna bata yarda ba, dole sai ta kai Ruƙayyah asibitin da kanta. M. Madawaki bai fiya yawan magana ba, shi ya sa bai yi mata musu ba. A. Maina ne ma ya nuna wa Daada yin hakan ga Ruqayyah bai dace ba.
Idanuwan Daada sun rufe, bata gane komai ba. Burinta shi ne ta ga jinin M. Madawaki kafin ta koma ga Allah. Zagaye asibitoci suka fara da Ruƙayyah, amma duk inda suka je sakamakon ɗaya ne, lafiya Ruƙayyah take.
Kwanakin Rahmah arba'in da haihuwar Nadiya, A. Maina ya sake aure da wata mai suna Zulaihah, wacce Rahmah ta dauka 'yar uwa. Ruƙayyah ce ma take kishi da Zulaihah kamar A. Maina ne mijinta.
Watanni Zulaihah uku ta samu ciki, wanda take taƙama da shi.
Shekarar Nadiya ɗaya ciki ya bayyana a jikin Rahmah wanda yake bata wahala kamar za ta mutu, duk sun tsorata Innayi mahaifiyar A.Maina ce ta bada shawarar a zubar da ciki tun bai girma ba, duba da yadda Nadiya ta fara shiga matsala sakamakon nonon da take sha ya fara taɓa ta.
M.Madawaki ne ya nuna bai amince da wannan shawarar ba, duk yadda A.Maina ya so a zubar da cikin M. Madawaki bai bashi goyan baya ba, dole sai haƙura Innayi ta yi saboda masifar Daada da ta sakata a gaba.
Domin Daada akwai masifa sosai, Innayi kuwa bata cika magana ba, shi yasa wasu suke cewa ita ce ta haifi M. Madawaki, duba da irin shirunsa ba kamar A.Maina da yake da sakakkiyar fuska ba.
Daga ƙarshe Rahmah gidansu M.Madawaki ta dawo Daada da Ruƙayyah suke kula da ita da Nadiya, har cikin ya shiga wata haihuwa sannan aka cire Nadiya daga nono, a ranar Innayi ta ce a bata ita.
Shiru A.Maina ya yi yana ƙoƙarin tashi daga falon M.Madawaki ya dawo da shi sannan ya kalle Innayi ya ce.
"Innayi wannan Ruƙayyah A.Maina ya bawa ki yi haƙuri bayan haihuwar Rahmah sai a baki....."
"Wacce Ruƙayyah kuma Muhammad bana son munafurci kin ga Hajiya Nadiya wannan yarinyar Muhammad, Abubakar ya bawa ita ina jinsu suna magana shi ne suka fake da Ruƙayyah.."
Kallonsu Innayi take tana jijiga kai, A.Maina ne ya gyara zama tare da fuskantar su yana cewa.
"Innayi Daada ku yi haƙura amma Ummina na mallak..."
"No! Bana so Innayi ki dauketa! Whatever Rahmah ta haifa a wannan cikin, she is mine har abada."