FreeArewaPen original
KOWA DA RABONSA
- 1views
- 1chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
I'm proud to be a Muslimah, I love reciting holy Qur'an, reading novels, watching and listening news. I may do all my best to pleasing my followers, thank you all.
Sample · Chapter 1
╔══════════════════════╗ 🌺🌺 *KOWA DA RABONSA* 🌺🌺╚══════════════════════╝ 🌺 A Story Filled With Lessons, Destiny and Love🌺 ✍️> BY MARYAM USMAN MAMYY WRITER (FULANIN JAJIRTATTU)━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━🏆 JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION✨ FIVE STAR WRITERS✨📞 ***📚 BOOK 1📖 Page 1 ━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِBismillahir Rahmanir Rahim.~Wane lokacin kaddara ce take zaɓa maka rabonka, wani kuma rabon nasa ne kaddara. Duk abin da ya zama rabonka dole ne ka yi haƙuri da shi.~> NOTE: Ban yarda da wani ko wata su yi amfani da littafina ba. Ban yi littafin nan da wata ko wani ba. Duk abin da kuka gani mallakina ne, bana so wani ya yi min copy ba tare da sanina ba.━━━━━༺🌺༻━━━━━"Inna Lillahi Wa'inna Ilaihir Raji'un!"Shi ne sautin da ya fito daga bakinta tare da zabura. Tana kallon fuskarsa da yake murmushi cikin farinciki marar misali.Rawa jikinta ya fara, hawaye na zuba daga kyakkyawar fuskarta. Tana kokarin fahimtar abin da Abbansu Nadiya yake fada.Cikin kamala da kame fuska yake sake jaddada mata auren da aka daura mata jiya da MAMUB. Wanda yake tamkar uba a gare ta, ko ta kira shi da uba ma gabadaya.Cikin tashin hankali da firgici take kallonsa. Abin da yake fada a bakinsa tana ganin masifa ce babba a rayuwarta. Domin ta san ta gama rayuwa daga yau din nan.Tsayawa zuciyarta ta yi da aiki. A lokaci daya tana ganin sama da kasa na juyawa, idanunta na rufe wa, numfashinta na kokarin tsayawa.A lokaci guda hankalinta ya fita daga jikinta. Tunanin makomarta ne ya saka ta fashewa da kuka. Hakika tana cikin wani hali da bata san waye zai fitar da ita ciki ba.Amma duk halin da take ciki, Abbansu Nadiya farinciki ne kwance a kan fuskarsa. Har wani tattausan murmushi yake yi yana sake kallonta.Suna cikin wannan yanayin ne suka ji ihun Mummy ta na cewa,"Inna Lillahi Wa'inna Ilaihir Raji'un! Na shiga uku! Me kake fada min haka M. Madawaki? Me ya sa za ka yanke wannan danyen hukuncin?"Ba ta ƙarasa maganar ba, ta yanke jiki ta faɗi.Da gudu duk suka fita zuwa inda suke jiyo ihun Mummy. Kwance a kasa suka ganta a sume, M. Madawaki na tsaye a kanta. Jiri ne ya ɗebeta ko taku ɗaya bata yi ba ita ma ta faɗi a sume, masu aikin gidan ya kira, suka saka masa Mummy a mota. Shi kuma ya dauki Shatu a kafadarsa. Yana fitowa, Security guards ɗinsa suka yi saurin bude mota.Da mugun gudu suka fita daga Madawaki Dynasty. Mintinan kaɗan ne suka kaisu Madawaki Special Hospital.Security na Hospital ɗin na ganin motocin M. Madawaki suka bude Gate tare da zagaye motar suna jiran fitowarsa.A. Maina ne ya fara fitowa yana kiran nurse. Kafin ya rufe baki, nurses ɗin asibitin suka fito da gadon daukar marasa lafiya.Mummy aka fara shiga da ita, sannan M. Madawaki ya fito da Shatu a jikinsa wacce take sume.Taimako...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.