Chapter 34
https://www.arewapen.com/book?id=6ab251c3cb0cfb2373811a7f
https://www.arewapen.com/book?id=6ab251c3cb0cfb2373811a7f
🔐❤️🩹ƊAURIN ZUCI BOOK TWO.
34
Sai da ta yi tafiya me tsawo, har sai da rana ta ganjare ta dinga dukanta gaba da baya amma bata saurara ba, sai da lokacin sallah ya gabato, sannan ta tsaya a inda ta ke ta soma dube-duben inda zata samu ruwa.
Iya hangenta bata iya ganin kowa facen tsili-tsilin ababen hawa da ke wucewa akan titi.
Waigawa bayanta ta yi tana hangen mutanen da ke can nesa sosai da ita kasancewar titin me tsawo ne sosai daga Shinkafi ya miƙe har wajen Ƙofar sauri.
"Ya Subahanallah." ta faɗa tana dafe kanta da bai tsaya ko kaɗan ba daga sarawar da yake yi mata.
'Kada kiyi wasa da ibada a duk inda kike, wannan inabadar da zaki riƙe ita ce zata ci gaba da haska miki hanya komi tsananin duhun da za ki shiga.'
Kalaman Kakanta suka hasko ma ta, da azama ta miƙe tsaye tare da soma ɗagawa ababen hawan da ke wucewa hannu, wasu su tsaya wasu su wuce.
"Ya Hajiya ina muka yi ne?."
Wani ɗan acaɓa ya tambayeta lokacin da ta tsaida shi.
"Ruwa.. dan Allah, Sallah nike so inyi lokaci yana ƙurewa." ta bashi amsa tana share hawayen da ke zuba daga idanuwanta.
"Mtwsssss aikin banza da wofi kawai, to sannu Ta sallah ko ince Saalaha, wannan ai iskanci ne ina ce bada faranti ko kwando kika ganninba ina tallar ruwa ko?."
Ya faɗi yana buga mashin ɗinsa ya baɗe ta da hayaƙi ya murza shi da mugun gudu ya wuce ta.
Bayan shi kusan masu mashin biyar ta tsayar, wasu suce mata babu, wasu suyi mata masifa su wuce su barta.
Ya kamata ace ta haƙura hakanan, amma sarewa ba nata bane, hasalima imbanta tsananin tashi babu abin da hankalinta ke yi, tana ƙiyasta yanda lokacin ke shuɗewa yana gudu daga second zuwa mintuna, har ya zamana saura ƙiris lokacin sallar ya shige daga lokacin data saba yin tata sallar, a ɗimauce ta gangara tsakiyar titin tana tara dukanin hannayenta tana ƙoƙarin tsayar da motar cike da fatan samun nasara.
"Yah hayyu ya ƙayum ka azani kan bayinka su tallafe ni da ruwan da zan yi ibadarka, Allah ka ɗaure min zuciyar wannan me tuƙin ya taimaka min." ta faɗa a sarari tana ƙara shan gaban motar da ta yi kusa sosai da ita.
Da ace Maryam ta san addu'arta zata amsu a wannan lokacin, wataƙila data roƙi wani abin na daban, na daban kamar dai sauran buƙatunda ta.
Haɗuwa ta biyu.
Junaid.
Ƙoƙari ya ke yaga ya take burkin motar ta ƙarfin tsiya, dan gujewa bigeta, ba iya gangar jikin shi ba hatta da zuciyar shi sai da ta saka ƙarfinta sannan ya samu ƙarfin danne burki yaja ya tsaya da motar kan shi na dakuwa da jikin kujerar motar ta baya.
"Ya hayyu ya ƙayummm." ya faɗa yana yawata idanuwansa akanta, wannan hasken nata da ke yawan yu ma shi gizo tun sanda ya ganta, har yanzun akwai shi tattare da ita, can sama sosai ya tsinkayo muryar Uncle yana faɗin.
"Oh my god! wani sabon problem ɗin kuma, please je ka duba ka gani dan wallahi idan na fita zamh iya samun matsala tsaf zan daddalawa wannan ƙoɗaɗiyar farar fuskar tata mari akan rainin wayo da tai mana, dan ina kyautata zaton ba makauniya bace sarai tana gani."
"Mari?." Junaid ya faɗa yana kamar me tambaya, domin kuwa ita kaɗai ce kalmar daya iya tsinta daga kalaman Uncle ɗin.
A fusace ya ɗago da zumar yin magana, amma sai wani abu, wani abu me nauyi ya danne ƙirjin shi, ya kuma ɗago da zuciyar shi ta harba da tsananin ƙarfi kamar zata fito waje, wani sanyi ya ratsa tundaga kan shi har ƙarƙashin tafin ƙafar shi ya saukar ma shi da wata iriyar kasala tattare da nutsuwa ta musamman, a hankali, a hankali sosai ya soma juyar da kan shi kamar me fama da lalurar ciwon wuya.
Cak ya tsaida ganinsa da gaba ɗaya hankalinsa, bakinta wannan ɗan ƙaramin, me ɗaukar hankali da ɗaukar ido wanda yasaka Junaid mantawa da muhimmin abin da ke gabansa, ya tattara nutsuwarsa yana kallon yanda ta ke buɗe shi kuma take rufewa ba ƙaramin jan imaninsa ta yi ba.
Nutsuwa ya yi sosai kamar bai da wani abin yi bayan kallon bakin nata.
Maryam
Yanayin ƙarar tsayuwar motar, da kuma kusan kaɗetan da motar ta yi bai ɗaga hankalinta ba kamar yanda kowace daƙiƙa da ke wucewa da ƙuracewar lokacin ibada.
Jikinta na kakkarwa ta zagaya bayan wajen sit ɗin driver data samu glashin a sake, tasan dai tana kallon cikin motar amma takamaimai bata san wanda take kallo ba kai tsaye, cikin sanyin murya ta soma faɗin.
"Bawan Allah dan Allah ku taimakamin da ruwa zan yi sallah lokaci yana shigewa."
Ta faɗa da duka gaskiyarta, ganin kamar babu wanda ya jita saita sake faɗin.
"Kai ne mutum na shida dana tsayar na tambaya, bana so inyiwa jinsin mutane jam'i wacen cewa baku da kirki, please ka kaimaka min da ruwan iya su kaɗai." ta sake maimatawa kanta tsaye tana kuma fatan ya fahimceta.
Da farko Uncle bai yi niyyar kulata ba amma jin ta ce jinsin mutane sai ya matso kusa sosai bayan ya yunƙura yana ƙare mata kallo ta kusa da Junaid, a ɗage ya ce da ita.
"Au ashe ke ba daga jinsin mutane kike ba, kinga ko ba lallai mu mutane mu iya taimakawa wanda ba jinsinmu ba gudun cutarwa.
Malama maza ƙara gaba baki samu matsugini a nan..." Bai idasa ba Junaida da hucin maganar shi ya dawo da shi duniyar zahiri ya katse shi da faɗin.
"Muhammad." murya a kausashe.
Sai kuma ya buɗe murfin motar ya fito har yana ɗan bangajeta kaɗan, gaba ɗaya hankalinsa ya tatara gare ta, cikin danne abin da ke fizgar shi a game da ita ya bule bakin shi tare da faɗin.
"Mi kike buƙata?."
"Maƙwat". ta haɗiyi yawu jin abin da ya ce, a gajiye sosai ta buɗe bakinta zata sake maimaita ma shi, amma sai wani irin ƙaƙƙarfan kuka ya kubce mata, kukanta da yasa birkin Junaid ƙwacewa har baisan sanda ya matsa kusa da ita ba, ya kama hannuwanta a cikin na shi ya riƙe da ƙarfi yana rasa abin yi.
Bayan Ummy, Ummie ɗin shi sai sauran yan uwan shi mata suma ƙalilan wanda ke can ƙasar Dubai su kaɗai, su kaɗai yatama sanin ya runguma a jikin shi, side hug al'adar larabawa ce amma zai iya cewa banda shi, wataƙila dan ya kasance shi ɗin half caste ne shi yasa.
Amma a yau kuma a yanzu nan take, ba zaice ga dalilin shi ba sai ji yayi hannayensa na janyo naya hannayen da ɗan ƙarfi ya soma kusanta kan shi da ita har bai san lokacin daya sakata gaba daya a jikin shi ba ya rungume ta tsaf, a tsakiyar hanya ba tare da yasan asalin abin da ya aikata ɗin ba.
A idon shi ya kalleta ne a matsayi wata, wata ta daban me cike da rauni, kuma tayi ma shi kama da wacce ke cikin wani yanayi, yanayin da a baya ya tsinci kan shi, baya son sam baya son sake ganin koda kwatankwacin wannan yanayin ne a kan fuskar wani ko wata bare kuma ita wannan ɗin wacce ya ke ji ita ɗin kamar ta fita daban.
Maryam sake ƙanƙame shi ta yi, tare da zagaye hannayenta a ƙugunta tana sake fashewa da wani sabon kuka.
"Ba kaifina bane Kaka bani da laifi, tun ɗazu nike neman ruwa amma ban samu ba, babu wanda ya kulani babu wanda ya banu ruwa bansan inda zan samu ba." ta faɗa cikin kuka.
Lumshe idon shi ya yi gam tare da yaƙar zuciyar shi ya samu da kar ya cireta daga jikin shi tare da ja baya kaɗan cikin son ƙarewa fuskarta kallo, amma kuma hannuwanta sun hana shi damar hakan.
Sakin baki halala Uncle ya yi yana kallon abin al'ajabi da ɗumbin mamakin da suka daskarar da shi a cikin motar.
Kallo yake yana ƙarawa wai yau Junaid ne Junaid dai na shi Junaid Abubakar Saminaka, yaron da zai iya rantsuwa ya kuma akan ba zai iya lissafo kamanin fuskokin matan da basu wuce a ƙirga da cikin yatsuba, idan aka cire ƴan gidansu Mommy da Angle sai kuma grandma ɗin shi dake Dubai, sai kuma ƙalilan daga abokan kasuwancinsa baya jin ya taɓa kasancewa da wata mace ta daban, bazai taɓa manta wata fira da suka taɓa yi ba shi da Fahad.
'Zaune suke kamar yanda suka saba, gaban su fresh fruit ne aka aje musu suna sha suna fira, Fahad ya kalle shi ya ce.
"Gaskiya Uncle ya kamata kai da Ya Jay kuyi aure hakanan wallahi, antashi kaina a bikin auren wannan friend ɗin nawa yaron Deputy Governor A,A Bashir." ya faɗa yana taunar Apple ɗin da ke ya gatsa."
Dariya Uncle ya kece da ita yana hasko yanayin da fuskar Junaid zata yi a sanda aka ce masa ga mata, matar da zai aura ko za'a aura ma shi, da dariya akan fuskar shi ya kalli Fahad sannan ya ce.
"Ai ina jin wannan yayan naka sai de muyi ma shi auren dole, domin kuwa bana jin yama taɓa yin wata aba wai ita budurwa, ina jin sai de Yaya ya yi ma shi auren dole nan gaba idan aka gaji da gwaurancinsa."
Ya faɗa yana hasko yanayin da Junaid zai kasance tare da wata mace da sunan mata da miji.
"See Uncle, ai ina jin harda kai Dad zai haɗa yayiwa auren dolen, saboda baka da banbanci kai da Big bro ɗin harma gara shi akan ka kainefa babba amma kaima baka yi aurenba har yanzu." Fahad ya faɗa.
"Zanci ubanka wallahi fahad ni sa'an wasanka ne." Uncle ya faɗa yana gallawa Fahad ɗin harara, amma acan ƙasan zuciyar shi yana wani fata, fatan ace yau ga ranar da Junaid zai dawo ƙasar shi ta haihuwa yayi aure, ya auri bahausa wacce soyayyarta zata rinjaye shi ta kakkaɓe du wani datti da ke zuciyar shi ya manta da komi, komi da ya taɓa faruwa ya fuskanci gaba.'
A yanzu kuma da yake iya ganin bagan Junaid ɗin da fararen hannayenta suka zagaye, wai wani abu ya taso ma shi, wani zallar farinciki da kuma al'ajabin yanda komi ya auku a gaggauce, bai saniba ko wata rahamace da Ubangiji yakan yi ga bayinsa masu tawakkali idan wata fitina ta same su, kamar yanda yake da tabbaci akan Junaid baya cikin walwala yana cikin tashin hankalin da bakin shi bazai iya furtawa ba, sai de zuciyar shi data cika fal da tarin abubuwa, abubuwan da suka kasance na baƙin ciki da damuwa wanda ke neman ɓalleta....✍🏻
To Alhamdulillahi yau dai Allah ya nufe ni da dawowa hutun kwana biyu da naje, kuma na ɗora a inda na tsaya, da fatan zakuci gaba da taya ni da share kamar yanda aka saba.
Nayi umarni gadu wacce ta karanta book ɗinan da tazo tayi like sannan ta yi comment, idan ba haka ba zan sake komawa wani sabon hutun😎 yanda kuka dama haka zamu sha 🤷♀️.
MARYAM STAR CE...