Chapter 3
╔══════════════════════╗
🌺🌺 *KOWA DA RABONSA* 🌺🌺
╚══════════════════════╝
🌺 A Story Filled With Lessons, Destiny and Love🌺
✍️
> BY MARYAM USMAN MAMYY WRITER (FULANIN JAJIRTATTU)
━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━
🏆 JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION
✨ FIVE STAR WRITERS✨
📞 ***
📚 BOOK 1
📖 Page 3
━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━
بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
Bismillahir Rahmanir Rahim.
> Wane lokacin kaddara ce take zaɓa maka rabonka, wani kuma rabon nasa ne kaddara. Duk abin da ya zama rabonka dole ne ka yi haƙuri da shi.
~NOTE: Ban yarda da wani ko wata su yi amfani da littafina ba. Ban yi littafin nan da wata ko wani ba. Duk abin da kuka gani mallakina ne, bana so wani ya yi min copy ba tare da sanina ba.~
> Kallonsu Innayi take tana jijiga kai, A.Maina ne ya gyara zama tare da fuskantar su yana cewa.
> "Innayi Daada ku yi haƙura amma Ummina na mallak..."
> "No! Bana so Innayi ki dauketa! Whatever Rahmah ta haifa a wannan cikin, she is mine har abada."
Da kallo suka bi M.Madawaki har ya shiga ɓangarensa, Daada ce ta bawa Innayi Nadiya tare da haɗa mata kayanta duk abin da suke Rahmah bata ce komai ba amma ta so Innayi ta yi haƙuri M.Madawaki ya ɗauki Nadiya kamar yadda A.Maina ya sanar da ita kuma ta amince.
A ɓangaren M.Madawaki kuwa Ruƙayyah ce ta nuna ita Nadiya take so, shi kuma ya yanke hukunci, haƙuri ya bata tare da nuna mata muhimmanci yin haka duba da soyayyar da Innayi take nuna wa Nadiya, wacce take a bayyana.
Zulaihah ce ta haifi yarinya mace ranar suna aka saka mata Fatimah (Inayaa,) duk abubuwan buƙata M.Madawaki ne ya yi, kuma Zulaihah ta ji daɗi amma hassada ta hanata nuna wa, daga ƙarshe ma cewa ta yi M. Madawaki ya fi yaran Rahmah.
Matar ƙanin A.Maina ce ta zugata ta yi musu rashin arziki, har sai M.Madawaki ya yi mata duk abin da ya yi a haihuwar Nadiya da Muhammad, sosai ta zuba musu rashin arziki har Innayi ta gaji ta kira Daada a waya tana sanar da ita abin da yake faruwa.
Ana kiran Daada ta shigo gidan cike da masifa faɗa ta fara yi sosai tana faɗa wa Zulaihah da daginta baƙaƙen maganganu, daga ƙarshe sai da suka kira A.Maina ya zu ya bawa Daada haƙuri sannan ta yi shiru tana komawa kan Innayi da bata iya shiga lamarin tashin hankali.
A haka dai aka yi sunan Inayaa zuciyoyinsu babu daɗi, Rahmah kuwa bata san abin da yake faruwa sai da Daada ta dawo tana masifa sannan gidan Madawaki family's suka sannan rashin arzikin da Zulaihah ta yi.
Watanni Inayaa biyu Rahmah ta fara nakuɗa, suka tashi asibiti amma bata haihuwa ba.
________________________________
Sati guda tsakanin Rahmah ta haifi yarinya mace mai kyau sosai har ta fi Nadiya kyau da haske, tun da suka shiga room ɗin A.Maina ya nuna wa M.Madawaki yarinyar da ido tare da cewa.
"Wai kai rowar yarinyar zaka yi min ka ɗauketa ka bani mana kamar ba barka na zo maka ba."
Murmushi duk mutanan da suke cikin room ɗin suka yi Daada ta yi saurin ɗaukar yarinya tana kallon fuskar M Madawaki ta ce.
"Yau dai Allah ya nuna min yarinyar Muhammad..."
Maganar ta tsaya ne sakamakon karɓar yarinyar da M.Madawaki ya yi yana rungumeta fuskarsa cike da farinciki, Baba Malam ne ya goge hawayen fuskarsa yana haɗa A.Maina da M.Madawaki ya rungume yana yi musu addu'a.
A lokacin M.Madawaki ya raɗawa yarinya suna Aishatu, Daada ta yi farinciki sosai ganin M.Madawaki ya yi mata mai suna, Rahmah ma ta yi farinciki duk da ba haka ta so sunan yarinyar ya kasance ba, ta so a sakawa yarinyar Ruƙayyah amma babu yadda za ta yi mahaifinta ya sakata mata sunan da yake ganin ya dace da ita.
Koda suka dawo gida Daada cewa ta yi dole Rahmah ta dawo gidansu da zama har sai yarinya ta yi ƙwari, A.Maina bai ce komai haka Innayi, ko da dangin Rahmah suka zo su ma babu wanda ya nuna wata damuwar har aka yi suna kowa ya koma inda ya fito.
Bayan suna M.Madawaki ya fara karɓar yarinya suna kwana da ita shi da Ruƙayyah da take ganin kamar in bata kwana da yarinyar ba, wani abu zai sameta.
Daada bata san sun karɓe yarinya ba sai cikin dare da Baba Malam ya rakota ganin yarinya domin tun da aka yi haihuwar Madawaki Dynasty suka rasa nutsuwa kowa so yake ya nunawa yarinya ƙauna, ba wai da basu da yara mata ba, sai dan nunawa M.Madawaki ƙauna akan abin da yake mallakinsa ne, Rahmah ta samu tana bacci cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, ihu ta yi tare da cewa an sace yarinya.
Ihun Daada ne ya saka kowa fitowa har M.Madawaki da ya fita tare da Shatu da take bacci a jikinsa, tana ganin Shatu a hannunsa ta karɓata tana komawa ɓangaren Baba Malam, da kallo duk suka bita, shi ma girgiza kansa kawai ya yi tare da kama hannun Ruƙayyah suka koma.
Tun daga ranar Daada da M.Madawaki suke ɗauke Shatu, kuma duk wanda ya ɗauka baya buɗe ƙofa har sai gari ya waye, inda Allah ya rufa musu asiri Shatu bata kukan dare sai na safe gari na waye in ta fara kuka har sai kowa ya gajiya.
Rahmah tana arba'in ta koma gidan A.Maina, a ranar Daada sai da ta yi zazzaɓi na rashin Shatu, washegari kuwa da sassafe ta shiga gidan tana ɗauko Shatu da ta gama rigima.
_____________________
A haka rayuwa taita tafi har Shatu ta isa shekara guda, da kanta ta daina shan nono, domin tana iya yi kwana uku ba'a kaita gidan A.Maina ba, gajiya Rahmah ta yi ta ce ta daina bata nono.
A Madawaki Dynasty ba su ban da hakan ba sai da Rahmah ta kawowa Ruƙayyah kayan Shatu tare da cewa su riƙe 'yarsu ta gaji, murmushi kawai Ruƙayyah ta yi tare da kallon gefen da M.Madawaki yake zaune da Shatu a kafaɗarsa.
Rayuwar Shatu a Madawaki Dynasty rayuwa ce ta gata da sangarta, komai ta yi daidai ne bata laifi duk abin da ta yi maka sai dai ka yi haƙuri, saboda masifar Daada, akwai yara a gidan sa'annuta da wanda suka fita shekaru su shida Meerah, Rima, Safa, Maira, Naya, Hala ga Inayaa da kusan kullum tana gidan, amma duk babu wanda Daada take gani sai Shatu.
Ita kuma Shatu, Allah ya jarabceta da masifar rigima. Komai na kuka ne a wajenta, shi yasa Daada take ganin laifin sauran jikokinta.
Ko ɗaya daga cikin yaran gidan ta ga kusa da M.Madawaki, sai ta fara kuka ita bata so yana ɗaukar wasu, tun Ruƙayyah na mamaki har ta fara dariya domin shi ma M.Madawaki baya ɗaukar sauran yaran kamar yadda Shatu bata so.
Ƙaramar magana ta isa ta fara zubar da hawaye ko wasa suke idan Meerah ta karɓi abin wasanta, sai ta yi kuka, dole sai Meerah ta bata, idan Rima ta ce ba za ta ba ta abin da take so ba, wannan ma na kuka ne, ko zama Maira ta yi a kan kujerar da take so sai ta buɗe baki da kiran.
"Daadaaa!"
Da zarar an ji wannan kira, kowa a gidan ya san an taɓa Shatu, a lokacin kuma Dadaa za ta fara masifa duk wanda ta samu a falon ya shiga uku.
Wata rana da yamma yaran gidan suna zaune a babban falo suna wasa. Shatu tana riƙe da wani ƙaramin abin wasa da M.Madawaki ya kawo mata daga tafiyar da ya yi.
Meerah ce ta kalle abun tana cewa,
"Shatu, bani in gani."
Ɓuye abun ta yi tana sake matsa shi a kirjinta tare da kallon inda M.Madawaki yake zaune ta ce.
"Ba zan ba ki ba."
Hala ce ta fara ƙoƙarin karɓa abun Shatu ta fara ihu.
"Daadaaa!"
Kafin ta ƙarasa kiran nata, Daada ta fito daga ɗakinta.
"Waye ya taɓa Shatu? M.Madawaki da yake falon Daada take tambaya shiru ya yi tare da karɓe abun ya bawa Meerah.
Ihu Shatu ta fara wanda yasa duk Madawaki Dynasty fitowa, kallon fuskar M.Madawaki suke da ya riƙe da hannayen Shatu da take miƙawa za ta karɓe abun wasanta, Ruƙayyah ce ta kamo Shatu tana tambayarta abin da yake faruwa.
Daada ce ta fara masifa akan me zai bawa Meerah abin wasan Shatu, cikin sanyin jiki Meerah ta miƙa mata abin wasan tare da cewa.
"Na gani kuma ni ma sai Abbana ya siya min irinsa."
Karɓa Daada ta yi tana bawa Shatu da take jikin Ruƙayyah girgiza kai Baba Malam ya yi tare da cewa.
"Daada, kina lalata yarinyar nan."
Juyowa Daada ta yi tana kalle shi.
"Haba Malam! Ita ce yarinyar da Muhammad yake so. Me ya sa zan bar wani ya dame ta?"
Murmushi Baba Malam ya yi yana kallon gefen M.Madawaki.
" Wata rana za ta girma, za ki sha mamakin halinta."
Dariya Daada ta yi.
"Shatu ba za ta taɓa girma a idona ba."
M.Madawaki kuwa yana tsaye ya yi shiru yana sauraron duk maganarsu a hankali ya ɗaga idanuwansa ya kalli Shatu da take dariya tana kallon abin wasan da aka ba ta.
Karɓe abun ya yi yana bawa Meerah sannan ya ɗauki Shatu suka fita daga falon, murmushi Baba Malam ya yi yana nunawa Daada abin da M.Madawaki ya yi, Abubakar Madawaki ne ya yi dariya tare da kallon fuskar Daada.
___________________________________________________
Shekaru sun fara tafiya yau shekarar Shatu biyar ta girma amma har yanzu da rigimar, har lokacin bata san M.Madawaki da Ruƙayyah ba su ne iyayenta ba, ta san dai A.Maina shi ne babban amininsa wanda take gani a uba shi ma kamar M.Madawaki, tsakaninta da Rahmah kuwa babu wata shaƙuwa domin Rahmah na yi mata faɗa akan rigimar da take yi.
Shi yasa bata fiya shiga gidan A.Maina ba sai dai Muhammad da Nadiya da suke tsananin ƙaunarta su zo wajenta, amma duk da haka sai sun yi faɗa domin Shatu ba ta da hali.
Tun tana shekara uku M.Madawaki ya sakata a school kullum shi yake kaita sannan ya koma ya ɗauko ta, ba school ɗaya suke da yaran gidan ba, ranar da ta ji a school ɗin su Meerah za'a yi wani program na wasan yara ta fara kuka ita ma sai an sauya mata school.
A ranar M.Madawaki ya yi magana da shugaban makarantar aka sauya mata, tun da ta koma school ɗin suke faɗa da Inayaa kullum sai Nadiya ta raba su.
Yawancin lokuta Inayaa ce bata da gaskiya amma da yake Shatu an santa da rigima sai ake ganin ita ce bata da gaskiya, tun Ruƙayyah na haƙuri da abin da ake yi wa Shatu har ta shirya ta je gidan A Maina ta samu Zaliha akan ta jawa Inayaa kunne.
A hankali shekaru suke tafiya abubuwa suna sake faruwa masu daɗi da a kasin su, shekarar Shatu bakwai jinyar ajali ta samu Ruƙayyah zazzaɓi kwana uku kacal ta yi Allah ya yi mata rasuwa.
Rasuwar Ruƙayyah ta girgiza Madawaki Dynasty Rahmah da Shatu kuwa ƙaramin hauka ne ya kama su, har aka yi sadakar bakwai Shatu bata dawo nutsuwarta ba, a ɓangaren M.Madawaki ma A.Maina ya yi fama da shi sosai domin shi ɗaya ne ya san halin da ya shiga.