Page 18
SAWU BIYU
BY
Khadijah Sulaiman
Young Talented Writers Association(YOTA)
Book 1
Page 18
Suna aiki gabaɗayan su da safe tare da Mami Aneesah ta shigo,sai da ta gaida Mami sannan ta gaida su Aunty Zeenah.
Ta tsaya kusa da Zarah tace"Hajja tace in kira ki".
Nan da nan ta ɓata rai,Allah ya gani ta tsani zuwa part ɗin Hajja,ta ajiye cup ɗin hannunta tace
"To me zan mata?"
Aneesah ta ɗaga kafaɗa tace"ya zan sani?ni dai cewa tayi in kira ki".
Mami dake juye ruwan zafi a flask tace"ki tsaya ki tafi mata da breakfast gabaɗaya tunda an gama".
Ba don ta so ba ta jira Mami ta shirya mata komai cikin basket ta dauka suka fito.
Tana zaune a kan gado as usual idonta kafe a kan TV hannunta riƙe da remote,Zarah ta ajiye basket ɗin hannunta kusa da ita tace"Ina kwana Hajja".
Hajja tace "da ban aika a kira ki ba ba zaki gaishe ni ba kenan?"
Zarah ta dauke kai ta zauna kan kujera Hajja ta bita da harara, ƙasa ƙasa tace"ni dai banyi wannan rashin kunyar ba wallahi,ban san me yasa aka sa mata sunana ba gaskiya".
Kamshin turaren da ya cika mata hanci yasa ta juyo ta kalli ƙofa,suna haɗa ido ta ɗauke kai da sauri ta maida kan kallon da take.
Ya ƙarasa gaban Hajja ya karɓi remote ɗin hannunta ya canza channel zuwa ƙwallo,a fusace Hajja ta buɗe baki zata fara masifa yayi saurin cewa"zan koma Canada gobe".
Ta ƙanƙance ido tace"yaushe ma muka zo har zaka wani ce mu koma gobe?"
Ya juyo ya kalleta yace"cewa nayi zan koma,bance Hajja ki shirya mu koma ba,ai ke kin dawo kenan".
"Da wannan bala'in zafin da ake fama a Nigeria zaka ce in zauna,ga rashin tsaro kota ina salon in fita a ƙwamushe ni,gara in koma garin ƴanci babu ruwan wani da wani,nan tsab yunwa zai iya halaka ni kana gani dai sai yanzu Hafsah ta aiko da brekpast,to akan wani dalili zan zauna?"
Ya ajiye remote ya koma ya zauna kusa da ita yace"ke dai kika sani".
A hankali Zarah tace"ina kwana".
Ya ɗago ya watsa mata wani kallo ya ɗauke kai.
Hajja tace"ke kuwa tun ɗazu ya shigo ba ki gaishe shi ba sai yanzu, ko ni ne ba lallai in amsa ba gaskiya".
Ta taɓe baki ta miƙe tsaye tace"ni zan wuce Hajja".
Abdallah ya buɗe baki ba tare da ya kalleta ba yace"zo ki haɗa min tea".
Tayi tamkar ba da ita yake ba ta juya zata fita, Hajja ta sake baki ta bita da kallo.
Da mugun mamaki ya ajiye remote ɗin hannun shi ya bita da kallo.
Hajja tace"ke dan ubanki dawo nan".
Ta juyo ta nuna kanta tace"ni?"
Hajja ta nuna kanta tace"a'a ni,baki ji abinda yace ba?"
Ta girgiza kai kamar gaske tace"ban ji komai ba Hajja".
Abdallah ya ɗauke kai daga kallonta ya cigaba da kallon da yake, Hajja tace"zo ki haɗa mishi tea".
Bata ce komai ba ta ƙarasa ta ɗauki cup ta tsiyaya ruwan zafin da tazo dashi ta haɗa tea ta ajiye kusa dashi,tana ƙoƙarin barin wurin yace"take it away kafin ki sha mari".
Zarah ta tsaya tana kallon shi da mamaki, Hajja tace"ji jaraba,zara'u wuce ki rabu dashi wannan ya cika fitina gaskiya".
Ya tashi daga kwancen da yake ya daka mata tsawa yace"da kin ci mugun duka wallahi,take this thing away and gerrout".
Hajja ta cire glass ɗin idonta tace"ban gane gerrout ba,yarinya da gidan ubanta za ka wani ce mata gerrout,to taje gidan ubanwa?"
Ya mata banza ya koma ya kwanta, Zarah ta ɗauki cup ɗin ta wuce kitchen ta dangwarar a wurin ta fita,tana fita ta fashe da kuka.
Sadauki dake fitowa daga part ɗin Daddy ya bita da kallo har ta wuce.
Sai da ta share hawayen fuskarta sannan ta shiga ciki sanin halin Mami.
Washegari kamar yadda yace ya bar Nigeria,sai Oum da zata ɗan ƙara kwana biyu kafin ta koma.
Hajja dama ta dawo kenan don tun wani aikin ido data tafi tace taga wuri babu abinda zai dawo da ita Nigeria.
Cikin satin Sadauki ya gama haɗa takardun shi da duk wani abu da za'a buƙata,ranar lahadi da sassafe yayi sallama da Daddy da Mami driver ya ɗauke shi zuwa Kaduna,sai da ya kai shi har hotel ya sauke mishi kaya sannan ya juyo.
Ya ɗauki kayan shi ya shiga ciki yayi booking ɗaki,bai bi ta kan abinci ba har zuwa dare sannan aka kawo mishi ruwan shayi ya sha ya kwanta.
Da safe ƙarfe bakwai da rabi ya isa Nigeria Defence Academy (NDA) Kaduna.
Dandazon mutanen da ya gani daga mata har maza yasa shi jinjina kai ya shiga layi.
Layi na zuwa kanshi wanda ke tsaye sanye da uniform yace"Candidate?"
Sadauki yace"Yes, Sir".
"Your Documents".
Ya miƙa mishi takardun hannun shi tun daga kan admission form har WAEC da JAMB result sai sauran credentials,bayan ya gama dubawa ya miƙawa na kusa dashi yace"check his name".
Sadauki ya koma kusa da wannan ya gama duba komai ya ɗago ya kalle shi yace "Get in".
Yana shiga ya tarar da wani sabon layi na medical screening,basu suka gama ba sai sha biyu da rabi.
Daga nan aka bada break zuwa ƙarfe ɗaya da rabi,suna dawowa aka cigaba da physical screening test.
Ƙarfe huɗu aka tafi Sallah,bayan an dawo aka raba musu uniforms sannan aka nuna musu ɗakunan su,zuwa sannan ba ƙaramin gajiya Sadauki yayi ba don ko sau ɗaya basu zauna ba.
Kana tsaye za'a kira sunanka da number ɗakin ka.
"Cadet Umar Muhammad Sadauki".
Sadauki ya amsa da "Yes Sir".
"Room 14 Block B,bed no 2".
Sadauki ya ɗauki kayan shi ya shiga,babban ɗaki ne mai ɗauke da ƙananun gadaje guda huɗu da drawer.
Sauran roommates dinshi suka shigo kowanne ya nemi number gadon shi ya ajiye kayan shi.
Da wuri yayi bacci saboda gajiyar dake jikin shi, ƙarfe biyar na safe ya miƙe ya shiga toilet ya dauro alwala.
Har ƙarfe biyar da rabi yana zaune kan darduma har wani daga cikin roommates din ya sauko ya shiga toilet.
Kusa da Sadauki ya tsaya ya tada sallah,bayan ya idar ya miƙa mishi hannu yace"sunana Bilal Usman Moddibo".
Sadauki ya miƙa mishi hannu yace"Umar Sadauki".
Da ƙarfi suka ji ance "Reveille".
Bilal ya juya ya kalli Sadauki,jin an taɓa kofar ɗakin su yasa Bilal miƙewa da sauri.
"Cadets ! Move !".
Sauran dake kwance kan gado suka tashi da sauri, Sadauki ya miƙe a nutse ya naɗe darduman hannun shi ya maida cikin kaya ya canza kayan jikin shi ya fita,zuwa sannan shi kaɗai ya rage a ɗakin.
Yana fita ya tarar da kusan kowa a waje sai Senior Cadets dake kai komo a wurin.
"Mogadishu Battalion! Fall in!"
Sadauki da sauran dake cikin unit ɗin suka matso kusa.
Senior Cadets dake riƙe da attendance list yace"Stand at ease !"
"Cadet Musa Aliyu".
"Present Sir !"
"Cadet Umar Muhammad Sadauki!"
"Present Sir ".
"Cadet Bilal Usman".
"Present Sir".
Sai da ya kai har ƙarshen sunayen su sannan wani military instructor ya nufo wurin fuska daure babu ko ɗigon rahma ya fara takawa a nutse yana binsu da kallo.
Sai da ya kai har ƙarshen roll ɗin sannan ya dawo gaba yace"Good morning,Cadets !"
"Good morning ,Sir!"
"Are you ready?"
Da ƙarfi suka ce"Yes,Sir!"
"I can't hear you".
Da ƙarfi duk suka sake cewa"Yes,Sir !!".
Ya jinjina kai alamar gamsuwa yace"Fall out!".
Lokaci ɗaya ko wannensu ya nufi training ground,Sadauki na kokarin juyawa ya sauke idon shi a kan wanda ko a mafarki bai yi tunanin ganin shi a wurin ba.
Da sauri ya ƙarasa inda yake tsaye ya juyo da fuskar shi yace"Ɗahiru!"
Wanda ya kira da Ɗahiru ya sauke hannun Sadauki dake dafe da kafaɗar shi yace"ka san ni ne?"
Da mamaki Sadauki ya zuba mishi ido,ganin yana ƙoƙarin barin wurin yasa shi cewa"Ɗahiru ni ne Sadauki,Ina Sani?"
Da ƙarfi ya buge Sadauki wanda hakan yasa saura kaɗan ya faɗi saboda yadda hakan yazo mishi unexpected yace"kar ka sake taɓa ni,ban san ka ba".
Lokaci ɗaya idon shi ya kaɗa jikin shi har rawa yake ya riƙe Ɗahiru yace"ƙarya kake kace baka san ni ba Ɗahiru,ina Sani?"
"Nace ban san ka ba,yau na fara ganin ka".
Bai yi wata wata ba ya ture Sadauki yayi kokarin barin wurin, Sadauki ya kai hannu zai riƙo shi suka ji ance"that's enough,stand back".
Babu wanda yayi motsi a cikin su,ya daka musu tsawa yace"I said stand back !".
Sadauki ya matsa baya yana wani irin huci.
Senior Cadet ya matso kusa dasu ya kalli Sadauki yace"what exactly is going on here?"
Sadauki ya sunkuyar da kai ya sanar dashi abinda ya faru,ya maida kanshi kan Ɗahiru yace"I have never met him before today Sir".
Sadauki yace"that's a lie".
Da ƙarfi mutumin yace"that's enough Cadet !"
Sadauki yayi shiru yana huci,mutumin yace"duk kuna jin Hausa ko?".
A tare suka amsa da eh,ya gyaɗa kai tace"ku biyo ni".
Gaban wani office da aka rubuta Senior Military Instructor suka tsaya,mutumin yayi knocking aka basu izinin shiga.
Yana zaune sanye da uniform yana rubutu Senior Cadet ɗin ya sara mishi,ya ajiye pen ɗin hannun shi yace"what is the problem?"
"Sir,sababbin Cadets ne,kaman sun sami misunderstanding ne tsakanin su,saura kaɗan suyi dambe".
Mutumin yace"Names".
Sadauki yace"Umar Muhammad Sadauki".
Ɗayan yace"Ɗahiru Sa'idu".
"Wa zai yi bayani a cikin ku?"
Yayi tambayar yana binsu da kallo.
Sadauki ya matso gaba yace"Sir,ni na fara tunkarar shi saboda shine mutum na karshe dana gani tare da ɗan uwana ranar daya ɓace".
Mutumin ya juya ya kalli Ɗahiru yace"ka san ɗan uwan shi?"
"Ban san shi ba Sir,hasalima shi kanshi yau na fara ganin shi".
Rai ɓace Sadauki yace"ƙarya yake Sir".
"Cadet ! do not interrupt me".
Sadauki ya koma baya trying hard to control his temper.
"Waye ya fara taɓa wani a cikin ku?"
Ɗahiru yace"nine amma ɓacin rai ne Sir,saboda yayi accusing ɗina da abinda ban san dashi ba".
"Koma meke tsakanin ku baka da right ɗin ɗora hannunka a jikin kowanne Cadet".
Ɗahiru yace"Yes Sir".
Ya juya wurin Sadauki yace"kai kuma,you cannot turn an allegation into an excuse for confrontation,idan kana tunanin ya san wani abu a kan ɗan uwanka sai kayi reporting immediately ba wai kayi approaching din shi kai tsaye ba".
A hankali Sadauki yace"Yes Sir".
Officern ya juya ya kalli Senior Cadet yace"until further notice,koda wasa kar na sake jin wani issue tsakanin su, sannan on no account za'a haɗa su wuri ɗaya ko ayi assigning ɗinsu tare on formation sai dai idan hakan yazo daga sama ne".
Yace"Yes Sir".
Ya juya wurin su Sadauki yace "dukkan ku kun zo nan ne don zama officers,officer baya taɓa yarda fushi ya rinjayi aikinsa,idan kuna da problem da juna report immediately ba wai ku ɗauki hukunci da hannun ku ba,za ku iya tafiya".
A tare su kace"thank you Sir".
Senior Cadet ya sa su a gaba har waje,Sadauki na ɗaga ido suka haɗa ido da Ɗahiru ya ɗauke kai da sauri.
Koda suka isa training ground har anyi nisa, Senior Cadet dake zagaye da sauran yace"hey Cadet !why are you standing?Fall in!".
Da ƙarfi suka ce "Yes Sir".
Da wani irin ɓacin rai Sadauki ya shiga cikin ƴan uwan shi dake push up,kafin ayi nisa jikin wasu ya fara rawa banda Sadauki da gabaɗaya hankalin shi baya tare dashi don da wani irin zafin dake sukar zuciyar shi yake hakan,zufa kawai ke gangaro mishi tun daga suman kanshi.
Ji yayi ance"fall out!"
Wasu suka zube a wurin suna sauke numfashi tsabar Jigata.
Wani Senior Cadet yace"Cadets,fall in on a straight line!"
A galabaice duk suka miƙe tsaye.
"Are you ready?"
"Yes, sir!"
"Cadets, prepare to run,when I give the command, move!"
Da ƙarfi suka ce"Yes Sir".
"Go! Go! Go!"
Da gudu suka fara gudun,in banda karan manyan takalman su babu abinda kake ji,tun suna gudun na marmari har wasu suka fara zubewa a ƙasa.
"Cadets, look at me".
Duk suka dakata suna kallon shi.
Ya shiga zagaye tsakanin su yace"I know you're tired. I know your legs are burning and your body is telling you to stop."
"But listen to me carefully. Training is not designed to show you what you can do when everything is easy. It is designed to show you what you can do when everything tells you to quit."
Ya dafa wani dake kusa dashi ganin sai tangal tangal yake yace"You came here because you said you wanted to become officers. An officer must learn to remain disciplined under pressure."
Ya sake shi ya koma kusa da Bilal yayi tapping bayan shi yace"You may be tired. That's understandable,but don't confuse being tired with being finished."
Da ƙarfi suka ce"Yes Sir".
"Cadets, you wanted the uniform. This is part of what comes with it,take a breath, regain yourself,then keep moving."
Da ƙarfi suka sake cewa"Yes,Sir".
"You will run five rounds. Maintain your pace and stay together."
Yana tsaye yana kallon su har su kayi round na hudu,zuwa sannan wasu jan kafa kawai suke saboda girman filin.
Da ƙarfi yace"Recover for five minutes."
Bilal ya dafa Sadauki ganin kaman bai san zafin jikin shi ba in banda zufan dake fita a jikin shi yace"sannu da ƙoƙari,ku ne sojoji".
Sadauki yayi murmushi kawai bai ce komai ba.
Can su kaji ance "Cadets,continue!"
Da gudu suka shiga fili a gajiye.
Bayan kusan mintuna biyar ya duba agogon hannun shi ganin karfe bakwai da rabi yace"Cadets, you are dismissed. Return, shower, dress and prepare for the next activity."
Sadauki ya ciro wani ƙaramin towel daga aljihun wandon shi ya shiga goge fuskar shi, ya ɗauke towel ɗin jin yayi karo da mutum,da sauri ta koma da baya tace"I'm sorry".
Bai ce komai ba ya wuceta ya bar wurin.
Yana shiga ɗaki ya tarar da sauran roommates dinshi guda biyu zaune suna share zufa.
Ɗayan yace"morning bro,nice meeting you I'm Emmanuel Okafor from Anambra".
Sadauki ya miƙa mishi hannu yace"I'm Umar,you can call me Sadauki from Bauchi State".
Ɗayan ya miƙa mishi hannu yace"Adewale Adebayo from Osun State".
Daga bakin kofa Bilal yace"Bilal Moddibo from Gombe State".
Duk suka fashe da dariya banda Sadauki da yayi guntun murmushi,ya ƙaraso ya haɗa hannun shi da nasu.
Emmanuel yace"Now I can see where the Fulani side of you comes from."
Bilal ya gyaɗa kai yana murmushi yace "Exactly,and I can hear the Igbo in your accent too."
Oum Rijalain
***