Chapter 2
*Tudu Biyu!*š
*Aysha Shafi'ee.*
*#WomenOfWords*
*****
*2*
~~
KHALID SULAIMAN BARUWA.
07:40am
Karar knocking din kofar dake tahowa daga can nesa kadan yasa Khalid bude idanunsa daga baccin da yake yi, hasken da ya tafi kai tsaye cikin idanuwasa ya sa shi saurin maida sunya runtse kafin ya zuro da kafafunsa ya suko daga gadon, gajeren wando ne da ya wuce gwiwa kalar sea green a jikinsa sai kuma farar singiletin dake fito da faÉin kafadunsa duk da cewa kuwa kana kallonsa ne zaka jera shi cikin layin sirara.
Bayan ya bude kofar dakin ya fita, ya mike cikin falon dake manne a jikin dakin ya karasa kofarsa shima. Kuma abinda ya riga ya sani ne ya faru, yana bude kofar yarinyar dake tsaye tayi tsalle ta fada jikinsa tana fadin.
"Daddy! Daddy!"
Ya nade ta a cikin hannayensa tare da ya zura fuskarsa a cikin kafadarta ta dama sannan muryarsa ta fito.
"Kin tashi lafiya ʓanmata?"
Maimakon ta amsa sai ta kyalkyale da dariya sanin abinda zai biyo baya shima dariyar yayi sannan ya fara yi mata cakulkulin da ta shiga juyi tana cigaba da kyalkyala dariyar a cikin jikinsa.
"A'a... Wallahi baku isa ba, don't even start Khalid, saki yarinyar nan kafin ka cukurkuda mata uniform, baza ku sani canja kaya ba."
Muryar Aunty Nafisa ta fada lokacin da take karasowa rike da jaka da kuma lunchbox din Safiyyan.
Khalid ya dago ya kalle ta yana dariya yayin da ya mike tsaye yana daga Safiyan dake cigaba da dariya sama ya dora ta a saman kafadunsa.
" Ga School bus can fa har tazo ka sauke ta idan ba so kake kuma sutafi su barta ba."
Sai ya gyada kansa yana kallon Aunty Nafisan
" Ba komai, idan sun tafi zan kaita da kaina."
Daga saman kafadun nasa, Safiyya ta daga hannayenta cikin murna tana fadin.
"Yeeeehh."
Aunty Nafisa ta girgiza kanta.
" Wallahi ba zai yiwu ba, the last time da na kyale ku ai bata je makarantar ba kace wai kun makara."
Khalid yayi dariya sannan ya sauke ta kasan, ya sunkuya yana kallon fuskarta da ta dan hade rai yace.
" Kar ki damu, ni zanzo in dauke ki yau idan an tashi da kaina kinji?"
"Daga nan sai muje mu siyo kayan makeup din?"
Ta bashi dariya, jin bata manta alkawarin da yayi mata na siyo kayan kwalliyar da tace masa tana so ba.
"Insha Allah... I promise."
Ya fada yana miko mata tafin hannunsa, tasa nata dan hannun ta tafa da iya karfinta sannan ta nuna shi da dan yatsanta daya.
"Kazo da wuri.ā
Ya gyada kansa yana murmushi.
"As early as possible Babygirl."
Itama ta gyada kanta tana dariyar sannan ta juya ta karbi jakarta daga hannun Aunty Nafisan, ta goya sannan ta sake juyowa tayi masa bye-bye daidai lokacin da horn din schoolbus din daga can waje ya shigo har nan, sai ta juya ta ruga da gudu, Aunty Nafisa tayi dariya tana bin bayanta rike da lunch box din amma kafin tayi nisa ta juyo ta kalle shi ta nuna shi da yatsa.
"Kaje ka saka kaya Malam, ka san Abba ya kusa saukowa."
Da haka tayi kwanar koridon da Safiyya ta bi suka bace daga ganinsa bakiÉaya.
Sai kawai yayi dariya yana shafo bayan keyarsa kafin ya bude kofar ya koma ciki. Kuma cikin mintuna kadan kamar yadda ya saba, ya shirya cikin shigarsa ta zuwa aiki.
Dogwayen kaya ne kaftaan kalar sky blue da hula da ta ciza kalar kayan ( dark blue) da kuma bakin takalmin dake kyalli kamar sabo. Lokacin da ya sauko kasan benen daga cikin makeken falon gidan, yana hango can wajen dining inda al'umnar gidan bakidaya ke zaune suna kalacin safe kamar yadda yake kaida a kowacce rana mai sunan monday ta gidan, Safiyyarsa ce kawai bata nan kasancewar ita makarantarsu karfe bakwai ake shiga a kowacce safiya, hakan yasa take missing wannan lokacin, iya haduwar cin abincin weekend kawai take samu wanda shi ake yinsa da dare.
Idonsa ya tsaya akan dattijon mahaifinsa Proffessor Sulaiman Baruwa, cikakken dan bokon da har a yanzu shekaru basu sa ya rissana daga akidunsa da kuma tsarinsa ba, a gefensa matarsa ce Hajiya Nadiya da kowa ke kira da Amma, taci kwalliyarta kamar kodayaushe tana gyada kai cikin hirar da suke yi da mijin nata.
A tsallakensu Amira ce zaune a gefen Sadiq da idanunsa manne cikin wayarsa kamar kodayaushe ba tare da ya taba abincin dake gabansa ba. Daga bayansa matarsa Aunty Nafisa ta taho ita da daya daga cikin masu aikin gidan rike da wasu farantan abincin, bayan ta ajiye na hannunta, ta shammaci mijin nata ta zare wayar dake rike a hannunsa.
"Ya salam!" Ya fada yana daga hannayensa sama.
ā Dan Allah ki bani wallahi abu nake karantawa.ā
Ta girgiza kanta.ā
"Ai ko waye sai da kace masa ya yi hakuri... This is family time."
Ta soke wayar a jikin skirt dinta.
Ya sake bude baki zaiyi magana Amma ta girgiza kanta.
ā Nima ka san ba son danne-dannen wayar nan nake yi ba.ā
Amma ta fada itama cikin dariya, sai kawai ya girgiza kansa, yana watsa hannayensa sama.
"Ya zanyi? I gave up."
Wannan karon har Proffesor Sulaiman sai da yayi dariya.
Aunty Nafisa ta juya ta karbi flask din hannun yar aikin da suka taho tare wadda ke tsaye a bayanta, yar aikin ta juya ta ta fi.
Ta bude flask din ta shiga debo soyayyen dankalin ciki tana zubawa a plate din mijin nata.
" Kuma yau sai ka cinye wannan tsaf zaka fita office, I can't recall the last time da ka cinye abincinka."
Wannan karon Proffessor Sulaiman din ne yayi magana yana gyada kansa.
" Na yarda dake anan nima..."
Sadiq din ya kalle shi baki a bude, sai kuma ya girgiza kansa.
"Ai shikenan tunda yau naga alama duk taron dangi za'a min."
Dukkaninsu suka sake kyalkyalewa da dariya, wata dariya da ta zama tamkar mashi a kirjin Khalid, don a lokaci guda yaji wannan yanayin da rayuwarsa ta taso a ciki ya mamaye shi, cewa kamar kar ya karasa gare su. Kamar ya tsaya daga inda yake kawai ya cigaba da hangen dariyarsu, dariyar da har yau rayuwa bata bashi damar mallakar irinta ba, bata kuma bashi gurbin zama a cikin tasu ba. Don haka ya cigaba da tsaiwa a inda yake kawai yana cigaba da kallonsu har zuwa lokacin da mahaifin nasa Professor Sulaiman ya juyo da kansa ya kalle shi.
Ba shiri sai ya cire takalmansa sannan yabi ta kan lallausan carpet din dake shimfide a tsakiyar falon ya ratsa ya nufi dining din.
Tun kafin ya karasa Aunty Nafisa mutum ta biyu mai maāana a rayuwarsa bayan mahaifin nasa ta juyo ta kalle shi fuskarta da murmushi.
"Ina son wannan punctuality din naka Khalid, 10- minute har ka shirya ba kamar wasu ba."
Sadiq mijin nata ya sake daga hannayensa sama alamun ya san da shi take lokacin da Khalid din da ya ja kujerarsa ya zauna bayan ya karaso.
"Abba Barka da asuba."
Ya fara gaishe da mahaifin nasa bayan ya zauna.
Ya gyada masa kai yana tauna abinda ke bakinsa kafin ya amsa.
"Mun tashi lafiya? Ya gajiyar aikin naku."
" Alhmdlilah." Ya amsa sannan ya gaishe da Amma wadda ta amsa masa fuskarta babu yabo ba fallasa kamar yadda ta saba a kowanne zamani na rayuwarsa.
Da ya juya ya gaishe da Yayan nasa, shima ya amsa masa ne tare gyada kai kawai ba tare da ya kalle shi ba.
Babu abinda yaji a ransa game da hakan don haka yanayin gaisuwarsu take tun kafin wannan zamanin balle kuma a yanzu da wasu abubuwa suka faru, don haka ya juya ya kalli Amira da tayi masa murmushi suka gaisa. Amira ʼyar Ęanwar Amma ce da ta dade da dawowa gidan don taya Amman zama tun lokacin daAunty Nana babbar yarta tayi aure, kain Sadiq shi ma yayi nasa auren, don haka ta dade da zama kamar yar gida tare da ita ake komai.
Aunty Nafisa da ta zauna kusa da mijinta, ta miko masa plate din wainar kwai daga tsallakenta, ya karba ya ajiye a gefensa kafin ya shiga kokarin zuba tea. Kuma duk da ba kallon Amma yake ba, yana jin nauyin idanunta akansa kamar kodayaushe, kamar kowanne lokaci idan har Aunty Nafisan zata yi wani abu na kyautatawa gare shi.
Lokacin da ya kai wainar kwan da ta miko masa bakinsa, sai yake laluba salatin da ya saba wajen mika godiyarsa ga Allah da ya halicci Aunty Nafisa a doron duniya kuma ya kawo ta cikin rayuwarsu har tayi gwagwarmayar daidaita tarin alamuran da bai san iyakarsu ba a gidan.
Don tun daga ranar da garin Allah ya waye da ita a matsayin surukar gidan, ta tunkari fafutukar alāamarin rayuwarsu zuwa wani sabon alāamari da ya kasance daban a wajensu, don a wannan safiyar ta ja ragamar hada breakfast daga hannun yan aikin gidan ba, breakfast din da kowa sai dai ya shaida cewa an auro mace gidan don a tarihin gidan tun da suka taso Amma bata taba damuwa da harkar kitchen a rayuwarta ba, duk abinda yan aiki suka ga dama suka dafa a wajenta daidai ne kawai.
Bayan hakan kuma sai tayi bajintar tattaro kowannensu zuwa kan teburin cin abincin da ya zama na ado kawai a sannan, a wannan lokacin ya tabbata kowa yayi mata kara ne wajen fitowar saboda kasancewarta amarya a lokacin, haka suka zo suka zauna kowa na zare ido da gyara zama tunda haduwa waje guda wani abu ne da babu shi a tarihin rayuwarsu, banda Proffesor Sulaiman da ya cika da mutukar farin ciki hakan tare da yabawa Aunty Nafisan.
Wani abu da ya fara bakanta ran Amma akan Aunty Nafisan kenan a wancan lokacin, duk da cewar itace da kanta ta zabowa Safiq din ita daga cikin yayan kawayenta da taje ji dasu, amma duk da haka da ta fahimci yadda Aunty Nafisan ta fara yin kane-kanen a rayuwar kowa na gidan wajen kulawa da faran-faran musamman da Proffesor Sulaiman ke yaba mata tare da fadin yadda kokarinta ke tuna masa da na marigayiyar matarsa...Safiyya, mahaifiyar Khalid.
Sai abun ya shiga bata mata rai, don haka ba sau daya ba sau biyu ba ansha samun matsala tsakanin Amman da Aunty Nafisan, amma da yake Aunty Nafisan mace ce da ta iya zama da kowa cikin salama da kwantar da kai sai yau da gobe ta tafiyar da duk wani sabani a tsakaninsu. Amman ta saki duk fushinta da fadanta ta hakura tunda ko Professor Sulaiman din ta lura Aunty Nafisan ta gama siye shi da kirkinta.
Abu daya ne kadai Khalid ya san har yau Amman bata gama karba akan Aunty Nafisan ba tsawon wadannan shekarun shine yadda take nuna kulawarta akansa da kuma yarsa. Don duk lokacin da ta yi wani abu da ya dangance shi, ko bata yi magana ba a fuskarta kadai zaka fahimci bata so, to amma baya jin ko sau daya bacin ran Amman ya taba sawa Aunty Nafisa ta kalle shi a matsayin baren da su suke daukansa.
Kalmar baren da aka makala masa karfi da yaji shi kuma yasa hannu ya karba tunda kasa ta dade da rufe idon wadda zata kange shi da hakan⦠mahaifiyarsa, mahaifiyarsa da ta dade da barin duniyar, ta tafi ta bar tarihin da shine umulāabaisin duk wani hali da taso tana tsintar kansa a ciki a gidan.
Don a sanin kowa ne Proff. Sulaiman bai taba son wani abu a duniya irin yadda yaso Safiyya ba. Aurensa da Amma hadin gida ne irin tun wanda iyaye keyi idan yaro ya kammala karatu, lokacin daya kammala karatun degree dinsa zai tafi kasar waje (London) masters da Phd aka hada shi aure da Amman wadda take itama ʓaruwa ce a family din Kaitan.
A rayuwar da suka yi acan ne ta haifi yayanta mata biyu Fatima da Nana Asma'u. Bayan da suka dawo Nigeria, a lokacin Fatima tana da shekaru biyar sai Allah yayi mata rasuwa. Kuma tun daga kan Nana Asma'un sai bata kara haihuwa ba tsawon shekaru kusan shida.
A lokacin har ʓanuwa sun fara yiwa Proff din tayin yaransu kasancewar Allah ya buda masa yana da arziki sosai, sai dai duk wannan bai sa Proff ya karo aure ba sai bayan shekara guda da Amman ta sake samun haihuwa kuma ta haifi Namiji Sadiq, a lokacin da take ganin ta rufe bakin dangin nasu tunda ta sami namijin da ake kafawa Proff din hujjar ya kamata ya samu.
A lokacin ne wani binciken harkar research din bishiyu da tsirrai da yake yi na kokarin kaiwa matakin Proffessor ya kaishi wani kauye a can Gombe, inda ya zauna har na sati guda, anan ya hadu da iyayen Safiyya da kuma ita kanta Safiyyan, fulanin tashi ne su a baya masu yawo waje- waje kafin su sami kauye guda daya suyi mazauni. Don haka ya sami ilimi mai yawa daga bakin mahaifinta wanda ya karbe shi hannu biyu, kuma a lokacin ne soyayya mai karfi ta shiga tsakaninsa da kyakkyawar ʓar mutumin Safiyya.
Wata irin soyayya mai tsananin zurfi da shakuwa da Sulaiman bai taba saninta a rayuwarsa ba tunda ko a lokacin yarintarsa karatu kawai yasa a gaba bai taba kula wata mace da sunan so ba har sanda aka bashi Amma matsayin matarsa.
Don haka yana daya daga cikin abinda ke yiwa Amman ciwo har a yanzu na yadda bayan ya samo auren Safiyyan baya iya boye son da yake mata a gaban kowa, kusan maida ita gefe yayi ya ajiye ita da ʓaʓanta hankalinsa ya koma kan bafulatanar da banda kyau babu abinda zata nuna mata a bangaren wayewa da kuma ilimi, don itama a wannan lokacin har matakin masters ta kai yayin da Safiyya ko karatun sakandirenta bata kammala ba akayi mata auren.
Sai dai Safiyyan tana da hankali da nutsuwar da ko ita da take kishiyarta ba zata ce ga wani aibunta ba ta harkar zamantakewa da ma mu'amala da mutane, wannan ne yasa duk da yadda ta kai ga jin tashin hankali da firirita akan son da Sulaiman ke mata hakan bai taba sawa sun samu wata matsala ba don Safiyya ta girmama ta, tayi mata biyayya sannan tayi hakuri mai yawa da ita a tsawon zaman da suka yi na shekaru goma cif! Kafin Allah yayi mata rasuwa.
Khalid, Éanta guda daya da ta haifa bayan shekaru biyu a gidan yana da shekara shida lokacin da ta rasun, wata rasuwa da ta girgiza daukacin al'ummar duk da suka santa, fon tana dauke da ciki wata bakwai a lokacin, mahaifinta ne ya rasu don haka dole tafiya ta kamata can garinsu, tafiyar da ta zama ta ajali don akan hanyar suka yi wani hatsari tayi mai muni da ita da direban da zai kaita a mota duk suka mutu, Khalid yana gida bata tafi dashi ba a lokacin saboda makaranta. Yadda aka kawo gawarta kaca-kaca wani abu ne da ya daga hankalin daukacin al'umma.
Don haka ba Proffessor Sulaiman kadai ba, kowa ya kadu da mutuwar nan, anyi alhini mai yawa kafin rayuwa ta dawo daidai. A haka Khalid ya taso a rayuwarsa ba tare da sanin dumin uwa ko dawainiyarta da kaunarta ba, don iyakacinsa da Amma a gidan nan kawai kallo ne da kuma gaisuwa wadda yake ganin itama tana amsawa ne albarkacin maraicin da yake tare dashi, kuma tun Professor Sulaiman na yi mata magiyar ta dinga kula dashi har ya hakura ya watsar.
Don haka tun Khalid bai gama gane inda duniya ta dosa ba ya iya kula da kansa, don yan aikin da Professor Sulaiman ya dora alhakin kulawarsa akansu ba kodayaushe suke damuwa dashi ba musamman wajen shirin makaranta da safe, ba sau daya ba sau biyu ba an sha tafiya dasu Sadiq a barshi sakamakon bai gama shiri da wuri ba. Haka zai je majarantar washegari ya lodo tarin nes din da akayi aka wuce shi, islamiyya kuwa ba zai kirga shekara nawa aka dauka ana masa dukan makara ko fashi ba.
Babu lokacin da rayuwa tayi masa wahala kamar lokacin da maāaikatan gidan kaf suka fahimci cewar matar gidan Amma bata dauke shi da muhimmanci ba, shikenan sai ya zama kamar bora duk wani abu da ya hada sai da su zai samu, to kuwa sai yasha mutukar wuya kafin su waiwaye shi.
Haka kayansa zasu taru suyi datti wani lokacin har ya rasa na sakawa kafin ya samu da kyar mai wankin gidan ya karba yayi masa, don kullum zaice masa wankin Hajiya ko nasu Sadiq yake yi, wannan yasa a dole ya koyi wankin kayansa da kansa, tun yana yi basa fita har ya kware.
Ya zamana ba iya wankin kadai ba, a hankali a hankali ya fara koyon duk wani abu da ya zamana sai ya hada da wani zai samu, kuma da yake zuciyarsa na dauke da ciwo da zafin hakan, sai ya zamana duk abinda yasa a gaba cikin kankanin lokaci yake iya shi. Don haka a kananun shekaru Khalid ya iya tarin abubuwan da ba zai iya lissafawa ba, ya koma bayan abinci babu wani abu da yake bukata daga kowa a gidan. Shi kadai ne zai jira sai anyi sannan ya zo ya diba kamar kowa.
Ranar da Professor Sulaiman ya fara ganinsa yana wankin kayansa haka yayi ta fada a gidan kamar zai ari baki, ya samu malam Abdullahi mai wankin ya dinga fada da barazanar zai iya korarsa, sai da ya samu ya bashi hakuri da kyar ya sauko.
To amma maimakon hakan ya zama sauki sai ma alāamarin ya kara cakudewa, don tsanar duniya ita malam Abdullahi ya dauko ya dora masa, ya zamana idan ya karbi wankin nasa ma to ba zai taba ganin daidai ba haka zai dawo masa da kayan kamar ba āa wanke ba duk datti sannan idan ya dauki iron ya dora musu sai dattin ya kara samun matsugunni yaki fita, haka zai je makaranta ana kallon kayansa duk datti. A dole ya tattara gabadaya ya daina bashi wankin ya kuma daina yi a inda zaāa ganshi balle har wani ma ya lura sai ya shige bandaki ya wanke kayansa tas! Yawanci ma sai dare yadda idan ya shanya su zuwa asuba sun bushe sai ya kwashe abinsa kafin kowa ya gani.
Haka shekaru suka mikar da rayuwarsa har zuwa girma a gidan nan, ya fahimci cewa kwanciyar hankalinsa shine kar ya shiga shirgin Amma da kuma yaranta, musamman Sadiq, da Amman ta kafa ta tsare kan cewar bata bukatar duk wata alaka da zata hada su, musamman da suna yara idan Sadiq din yayi kokarin jawo shi cikin alāamarinsa yanzun nan zata bata rai ta rufe ahi da fada ko a gaban Proffessor ne kuwa, don shi kansa tun yana iya magana akan cewar baya kaunar raba kansu da take yi har ya gaji ya daina.
Hakan yasa shi da kansa Khalid din ya koyi janye jikinsa daga cikinsu, dama Sadiq din ne kawai da yake namiji zasu iya abubuwa tare,, amma ita Aunty Nana baya jin idan zaāa shake ta ma ace ta lissafo mutanen da ta sani a rayuwarta zata fado sunansa, sai ta ganshi ne kawai take tunawa dashi.
Bayan mahaifinsa, a waje guda ya san maāanar soyayya da kulawa shine idan yaje Gombe wajen kakaninsa da kuma yanuwan mahaifiyarsa⦠anan ne kadai yake ganin tsantsar kulawa da kauna⦠don gida-gida ake yawo dashi a cikin yanuwa ana bayanin ga dan gidan Safiyya yazo. Gata kuwa ba irin wanda baya gani duk da cewar mutane ne masu raunin karfi amma Khalid baya damuwa, har Allah-Allah yake lokutan hutu su zo don a kaishi can.
A lissafin Khalid zai iya cewa daya daga cikin abinda ya kara masa samun kwanciyar hankali a gidan shine yadda abinda kowa ya dinga tunani bayan mutuwar Mahaifiyarsa bai faru ba, cewar mahaifin nasu zai daukaka shi fiye da Amman da ʓaʓan ta saboda tarihin son da yake yiwa Mahaifiyar tasa, to amma sai kowa yaga akasin hakan, sai aka ga babu banbanci da yadda yake nunawa Sadiq din da kuma shi, sau da yawa ma har ya fi jan Sadiq din akansa tunda shi ne babba.
Musamman bayan da Sadiq ya gama karatu kuma Professor Sulaiman din ya dora shi a matsayin General manager babban kamfaninsa na sarrafa magunguna. Shi kuma Khalid din bayan ya gama nasa karatun sai kawai ya bashi gurbin aiki a kamfanin kuma ba wani matsayi babba ba.
A shekaru shida baya, Khalid yayi aure tare da wata abokiyar karatunsa a jamiāa Farida, shi da ita sun hadu ne a can kasar London inda yayi karatun jamiāar, kasancewar daga shi har Sadiq duk mahaifinsu can ya tura su can jamiāar da yayi nasa karatun ne. Kuma har yau Khalid zai rantse cewar bai san ya akayi aurensa da Farida ya tabbata ba.
Don Farida kyakkyawar matashiya ce, mai aji, jin kai kwalliya gayu da kuma tsari, iyayenta suna da tsananin kudin da kusan duk wani abu da take so tana samunsa,saboda ko da ta nace akan aurensa din bayan soyayar da suka sha a london suka dawo, iyayen nata musamman mahaifinta bai so aurenta dashi ba, watakila ya saka ransa a cewar a yadda yar tasa take da kyau kuma gejin kudinsa sai dan shugaban kasa ko kuna wanda ya tada kai da wata darajar.
zai iya cewa wannan yana daga cikij dalilin da yasa auren nasu bai je koina ba ma, don shi dai ya san har ranar da ya rubuta mata takardar saki babu wani kwakwaran laifi da zsi ce ya haddasa rabuwar tasu, kawai wasu kananun abubuwa ne da bai ma san ta yadda zai kissafa su ba suka taru suka dimga haifar da matsala a tsakaninsu.
Watan Safiyya goma sha biyu a lokacin kuma tana kaiwa watanni goma Faridan ta yaye ta daga nonon da dama tunda ba wani bata take yi sosai ba suka dawo masa da ita da cewar aure zata yi.
Wani lokaci da alāamarin gidan ya kusa sake cakudewa. Don babu wani tunani Aunty Nafisa tace zata dauki yarinyar ta shayar da ita, tunda tana tsaka da maraicin rashin haihuwar da basu samu ba ita da Safiq har a lokacin, sai dai babu kara Amma kuma ta buga tsalle tace hakan ba zai yiwu ba, dole ta saka Sadiq mijin nata ya hana ta akan wasu dalilai da suka kawo marasa karfi. Khalid baiyi magana ba bai ce komai ba har zuwa lokacin da Professor Sulaiman ya tara su tare da yanke hukunci da kuma bada hakurin cewa a karbi tsarin Amman.
Sai dai kuma hakan bai hana Safiyya samun cikakkiyar kulawar da kowanne yaro a irin shekaru ta ke bukata ha. Don bayan aljihunsa da yayi kuka wajen neman dukkan abinda zai inganta lafiyarta, Aunty Nafisa ta cike duka sauran gurbin da kokarinsa ba zai iya ba da kulawa irin ta uwa a wajen yarinyar.
Ko kadan hukuncin da Amman ta yanke baisa ta gaza da yarinyar ba, haka Amman tana ji tana gani itama ta kalli abinda ba zata iya hanawa ba yadda Aunty Nafisan ta maida Safoyya kamar yarta ya zamana shayawar da aka hana ta ce kawai katangar dake tsakaninsu. Kuma bayan ita Safiyya ta samu kukawa daga kusan kowa a gidan nan banda Amman kawai, Don har a yanzu babu ruwanta da yarinyar, gurbin da ta ajiye mahaifinta na ko in kula nan itama nan ta jefa ta tun da dadewa.
A yanzu shekaru hudu kenan, kuma tun daga wannan lokacin sai Khalid babu abinda yake yi a rayuwarsa banda aikinsa da kuma rainon yarsa, cikin kokarin ganin ya tsaya ya bata irin kulawar da rayuwarta ba zata zama irin tasa ba mai cike da gibi kala kala.
Kuma a cikin wadannan shekarun Professor Sulaiman babu irin yadda baiyi dashi ba akan batun sake aure amma baya kulawa, don daga kalmar auren har duka abubuwan da ta kunsa ya tattara su ne ya kulle a zuciyarsa tun daga lokacin da hannayensa suka rubuta takardar saki guda ga Fareeda.
A cikin haka ne har aka gangaro gabar da watarana guda daya jal! ta canja akalar rayuwarsa bakidaya, ta barar da duk wani tsari da yake hangen rayuwarsa zata cigaba da tafiya akai⦠ta rusge dukkan yadda yake hango kansa a gaba⦠Ranar da Sadik ya tabbatar masa da abinda ya dade yana zargi a kansa.
Bai ko shirya tunkararsa a wannan ranar ba. Kawai zuciyarsa ta ja shi ne ya shiga office din nasa bayan da yaci kari da abinda ya hautsina tunaninsa, yana waya a lokacin da ya shiga kuma da ya dago ya kalle shi sai bai nuna mamakin ganin nasa ko wani abu ba.
Ya cigaba da wayarsa ne yayin da ya tsaya a gaban teburin nasa.
āEh ka gaya musu su gyara invoice dinā¦ā
Ya fada sannan ya cigaba da maganar cikin harshen turanci.
āNo, I said just adjust it. Weāll sort the rest later.ā
Khalid yana tsaye yana kallonsa, zaman da yayi da ma yadda muryarsa ke fita hankalinsa a kwance kamar ba shine ya aikata abinda yazo tunkararsa akai ba.
Ganin yana cigaba da tsaiwa yasa ya sake kallonsa, kuma da idanunsu suka hadu, a cikin sakan guda sai wani abu ya haska a cikin nasa idon alamar ya fahimci cewa zuwan nasa ba irin na koyaushe bane. don haka yace a cikin wayar da yake yi.
āIna zuwa zan kira ka.ā
Sannan ya katse kiran ba wai don ya gama abinda yake yi ba.
Ya ajiye wayar akan teburin sannan ya sake kalle shi kai tsaye.
ā Ya akayi?ā Ya tambaya.
Kuma Khalid bai bata wani lokaci ba ya kara taku biyu ya matsa gaban teburin nasa sannan ya ajiye takardar dake hannunsa. Idanun Sadiq suka bi takardar da kallo yana karant abinda ke jiki.
Transfer kudi ne na naira miliyan talatin wadda yayi da kansa a satin da ya gabata. Watakila bai gama karantawa ba lokacin da Khalid din yace.
āWannan transfer da kayi zuwa sunan suppliers din dake rubuce akai, na duba babu suppliers din, babu wasu mutane ko kamfani mai wannan sunan.ā
Sakanni suka wuce bayan fadin haka, office dinya dauka da wani irin shiru mai nauyi kafin ga mamakinsa Sadiq din ya kyakyale da dariya.
Wata dariya mai tsayi kamar babu abinda zai daina ba. Ya koma da baya a cikin kujerarsa yana girgiza kai, sannan yace.
āAbinda kazo har cikin office dina ka gaya min kenan?ā
Khalid bai amsa ba, ya cigaba da kallonsa kawai.
Sai ya dago ya kalle shi.
āBincike kake akaina da kuma abinda nake yi?ā
Khalid ya girgiza kansa.
āSo nake na gane me kake yi da dukiyar mahaifinmu.ā
Ba shiri ya sake wata dariyar yana kallonsa.
āDukiyar mahaifinmu ko kuma tamu? Har yanzu kana tunanin arzikinsa nasa ne?ā
āKar ka canja zancen da muke yi Ya Sadiq, wannan abin da kayi sata sunansa.ā
A lokaci guda sai yanayinsa ta canja, ba zuwa fushi ba, ko bacin rai. Wani abu a tsakanin hakan.
āMe yasaka fada to a hankali? Ka daga muryarka mana ka fada da karfi, ko ka fita kaje ka gaya masa cewa na saci kudinsa, sai mu ga idan zai yarda da kai.ā
Khalid ya cije lebbensa sannan yace.
āBa yau ka fara wannan abin ba Ya Sadiq.ā
Sai kawai ya taso, ya fito daga teburin sa ya shiga zagaye a cikin office din kamar mai lissafin yadda zai rike kansa daga rufe shi da duka kafin ya dawo ya tsaya a gabansa. Khalid ya juyo shima ya kalle shi.
āSai me?ā Ya tambaya.
ā Sai me khalid? Na dade ina diban kudi daga kamfanin nan me zaka iya? You think youāre better than me because you follow rules? To bari na gaya maka umarni a harkar kasuwanci ba abinda yake sai dakushe mutum.ā
Khalid ya sake girgiza kansa.
āBa zancen kasuwanci muke ba Ya Sadiq, zancen cin amana muke yi anan.ā
Ba shiri sai ya sake wata dariyar sannan yace kalli gefe.
āKana tunanin dukkan maāaikatan Abba masu gaskiya ne kenan? Kana tunanin ni kadai nake wannan abin?ā
Sai kawai Khalid ya sake matsowa gabansa dab da shi.
āDuka wannan ba dama bace da zaka dinga satar kudade masu yawa haka.ā
Idanun Sadiq suka kankance yana kallonsa.
āKa iya bakinka Khalid. Kar ka sake danganta mi da kalmar sata a gabana haka.ā
A lokacin ne wani abu ya kwance a zuciyar Khalid yaji shi ya tarwatse a cikin kirjinsa bakidaya. Don haka sai kawai ya girgiza kansa yana kallonsa yace.
ā Idan kuma ba haka ba fa?ā
Yana rufe bakinsa kuwa naushin yazo. Sadiq yasa duka karfinsa wajen naushinsa a fuska, yayi baya kamar zai fadi, kuma a lokaci guda mamakin dukan da ya kamashi ya juye zuwa fushi, zuciyarsa ta harzuko shima don haka ya dawo da sauri tare da kawo masa nasa naushin shima.
Sadiq ya tafi da baya ya daki gaban teburinsa, sai kawai ya sake kawowa Khalid wani naushin ya kare da hannunsa, ya wawuro kujerar dake gefe ya jefe shi da ita, Khalid ya kauce kujerar ta tafi ta daki bango, kara ta cika ofishin kuma daga nan sai komai ya hargitse⦠babu sauran magana komai ya kacame, dukkan abubuwan da zuciyoyinsu suka dade suna dannewa suka shiga fito da kansu.
Hakurin da aka dade ana yi tsawon shekaru ya tarwatse, Khalid bai san iya lokacin da suka dauka a wannan halin ba tare da saāar shigowar wani cikin ofishin ba, kowannensu bashi da niyyar tsayawa, Ofishin gabadaya ya hargitse.
Kuma a wannan halin Khalid abu daya yake tunani, ba kamfanin ba, ba kudin ba, ba mahaifinsu ba, sai cewar ba zai taba iya gyara alakar dake tsakaninsa da danuwan nasa ba, ba zai taba iya gyarawa ba.
Don haka har lokacin da wani mai suna Hassan ya yi nasarar shigowa ofishin tare da raba su, zuciyarsa kawai rawa take tare da kallon Sadiq din, yadda numfashinsa ke fita a sama, gabansa rigarsa a yage sannan idanunsa na haskawa da tsananin fushi da kuma bacin ran dake kara haska masa cewar watakila ko zasu rage iya su biyu a duniyar nan Sadiq ba zai tabasake kallonsa da rahama ba.
Sai kawai yaji cewar zucyarsa ta kai karshe shima, duk wani kokari da ta dade yana yi wajen bin Sadiq din tsawon shekaru ya kare, duk wani fatansa akansa ya tarwatse a iska, ya kalle shi sannan ya zaro ID Card din dake cikin aljihunsa, Id card din da ya bashi damar zama maāaikacin kamfanin da suke hargitsawa.
Allah ya sani tun da farko ya karbi wannan aikin ne saboda mahaifinsa, saboda ya sani cewar yana son ganin hadin kansu tare, ya tabbata ya hana shi yin kowanne aiki ne da fatan zamansu tare a waje guda zai taimaka wajen samun fahimta a tsakaninsu, abinda bai sani ba shine wadannan shekarun basu isa su samar da abinda na baya suka kasa ba.
Don haka yana kallon idanun Sadiq din ya cillar da ID card din a kasa, sannan ya juya da niyyar fita ba tare da tunanin muryar Sadiq din zata katse shi ba.
āSeriously?? Saboda wannan abin zaka bar kamfanin? To me zaka gaya masa? Me zaka gayawa Abba?ā
Tambaya ce mai sauki da yaji ta a cikin kunnensa a lokacin, abinda bai sani ba shine wannan layi guda daya na tambayar na dauke
da akalar canja rayuwarsa zuwa wani bigire da bai taba hasashen sa ba.
***