FreeThe story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · Chapter 1
*Tudu Biyu!*💞*Aysha Shafi'ee.**#WomenOfWords*******1*~~FANNE MUHAMMAD NASIR.05:30pmKowa ya sani cewa babban burin Fanne shine ta koma gidan mijinta Hadi, amma duk da haka a cikin lissafin Aunty Halmu bata taba kawo cewar zata iya kallonta kai tsaye ta fadi wannan maganar ba, don haka bata san lokacin da ta juyo ta nemo salati a cikin bakinta ba.“Inalillahi wainna ilaihir raji'un... Fanne? Me kike nufi? Auren kisan wuta zaki yi?"Matashiyar da ta kira da Fannen ta bata rai sannan ta girgiza kanta."Ni fa ba haka nake nufi ba, kawai cewa nayi da ace akwai wata hanyar da zan iya komawa gidan Hadi wallahi sai na bi ta."Aunty Halmu ta girgiza kanta, ta ja tsaki sannan cikin yarensu na shuwa arab tace."_Ma'arfa shunu no'a al-junuun fihaa..._ Ban san wace irin mahaukaciyar yarinya ce ke ba wallahi Fanne, bana jin a rayuwata kaf na taba haduwa da mace irinki mai taurin kai da kuma banzan ra'ayi..."Aunty Zainab dake can zaune gaban mudubi tana fente bakinta da wani jan jambaki ta juyo ta katse ta."Dan Allah Halmu ki ja bakinki kiyi shiru akan al'amarin yarinyar nan, wallahi don dai a musulunce auren ya kare tsakaninta da Hadin nan ne da wallahi ni kaina sai na san yadda zanyi na komar da ita gidan nasa taje can ta cigaba da cin uw*r da take ci."Ta juya a fusace ta cigaba da dadira jambakinta kamar tana ganin har yanzu tasirinsa bai kamo kalar jan kayan da take sanye dasu ba.Fanne ta sake bata rai tana taune gefen bakinta kamar tana son hana kanta fito da maganar da take son furtawa.Aunty Halmu ta tabe baki ta dauki wani turare tana fesawa duk a cikin shirin fita bikin da suke yi sannan ta cigaba."To ba gashi nan ba, duka mata sa'anninta sun tafi wajen kwalliya amma ita an barta damu tsofaffi, muna gyara tsufan namu ma amma ita tana zaune ta kima daurin kai kamar Ladi Kwali."Ba shiri Fanne ta saki lebben bakinta da ta cije don a yanzu maganar da take dannewa ta kai gejin da ba zata iya cigaba da dannewar ba."Ni fa ba son kwalliya nake ba kun sani, ko da bikina ma ai banyi ba, kuma ko ita Safar na gaya mata ba wata kwalliya da zanyi don za'ayi bikinta. Zancen da kuke yi kuma ai naga gwara ni, tunda daga ni har mijina muna son komawa auren namu, ku duk da aka sako ku ai ko biko mazajenku basu taba zuwa ba..."Kwalbar turaren dake hannun Aunty Halmu ce ta fadi daga hannunta har kasa ta tarwatse yayin da Aunty Zainab ta debo salati tun daga farkonsa har karshe ta dire." Inalillahi wainna ilaihir rajiun.... Na shiga uku ni Zainab _shunu ana amla kida?_ mu kike gayawa haka Fanne?"Fanne ta sake hade ranta."Kuyi hakuri idan ranku ya baci amma ai gaskiya na fada, kawai sai ku sani a gaba kuyi ta fada don nace ina san in koma gidan mijina? Bani da uwa bani da uba, da inyi ta rabe- rabe a gidan yanuwa ba gwara na koma inda nake da gata ba?"Aunty Halmu t...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.