Riya Chap 2
Riya …..
Kafin karfe 9 na dare nagama duk abinda zanyi , girki wanke wanke da sharen tsakar gida, lokacin yaran duk suna karatu ah tsakar gidan .
ina zawne a cikin dakina ina ta aikin tunanin dana saba wayana dake ajiye a gefena, kiran iPhone Xr ta fara ringing .
kauna ne , na kuma kwallon screen din wayar ah kwaro na biyu ina kwarewa sunan dake rubuce akai kwallo KAUNA ❤️ ….. Ban daga wayar bah nakuma zurfafa wa a cikin tunanin da nake ….
WAYWAYE…. WACECE Riya ?….
ASALI…..
Alhadji Saidu Idi wato baba Alo Alo shine ciken ken sunan Mahifin su banban Riya, Asalin dan kasar Niger Republic ne a garin Maradi cikin karamar hukumar dakoro.
A lokacin zaman boko sai wane da wane kasancewar ah ahalinsu sunada dukiya kuma sunada yar karamar sarawtar su sai ya kasance baba Sa’idu yayi karatun boko, kuma yanada gonaki sosai ah kyauwan .
baba sa’idu mutun ne mai son arme arman mata
dan bayan ya auri matar sa ta lalle wato zeynabu saida ya auri mata sama da 6 ….
Zeynabu yar kwayensu ce itama
mace fara irin farin nan mai dawkar ido sosai tanada tsage irin na fulani ah gefe da gefen bakinta.
Bayan samun aiki da yayi a garin Arlit nan cikin Niger , wani garin da ake hakar ma’adanan kasa irin su uraniums petrol da sawran .
ya dawki matarsa zeynabu suka koma garin da zama, lokacin bah mutaneh sosai ah garin dan
har ah lokacin mutaneh basuda yawa..
Rayuwa nata tafiya daga kwanaki zuwa satittika
zuwa shekaru masu dama
a kwalla yaran baba sa’idu zasukai 29 tsif …
Abdul Aziz shine da na 5 a cikin yayan baba sa’idu duk da cewa sawran idan ya rabu da mahaifiyarsu, to matan natafiya da yayan suneh..
Abdul Aziz ya kasance da mafi soyuwa a zuciyar mahaifin shi…
dan komaii nashi tare sukeyi, sufita yawo tare su zawna fira tare da yama a kofar gidan su , yayi karutu iya degree so samun aiki sai yazamo
mishi yuwa…
yana tafiya gareji koyan aiki garen motocin da daii sawransu
har i zuwa lokacin da Allah ya hadashi da
Djamila wato matarshi ta yanzu itace
mahaifiyar su Riya …
kafin auren djamila da Aziz ansha tsakwakiya mai zafi daga bangaren iyayen su musan man, Mahaifiyar Aziz , Dan a cewarta dan ta yayi karanta da aure kuma gah yayun shinan mazan har 2 busuyi aure bah
Djamila asalin yar Nigeria ce dan mahaifinta cikenkan da katsina ne hafaifiyar tace yar niger buzuwar garin Tahoua
Bayan Rabuwar iyayen ta sai suka koma cikin garin « Arlit » da zama , Haduwar Azuz da Djamila cikin kankanin lokaci suka shaku da juna
soyeya mai karfi ta shiga tsakanin su !!!
ah cikin kankanin lokaci aka dawra musu aure duk da cewa, Mahaifiyar Aziz bataso !!!
Rayuwa taci gaba da tafiya kuma a haka Djamila take ta hakuri da surikarta dan , ita mace ce mai matukar hakuri urin sosai dinnan,
Batan auren su ta dawku yar yayar ta ta 3 tana rikonta shekarar ta 8 sunanta Rumana
bayan wasu yan watannin Djamila ta samu, cikinta na farko kuma har zuwa wanan lokacin…. Tana fuskantar yulakanci daga mahaifiyar aziz dan kusan kullin tana zuwa gidansu aziz din, taya mama shi aiki koda kuwa bah ranar girkin ta bace …
duk da cewa akoy mace autar su aziz din ,
lokacin matan baba Sa’idu 3 ne dan yayi ta aure aure ah baya…. Ga tarin yara !!!!
Lokaci nata tafiya ….. Wata ranar Laraba da yama Djamila ta fara nakuda gadan gadan !!!!
har ta yuni ta kwana bata haihu bah hankalin kowa ya tashin dan harda na mamar su Aziz tana ganin zata rasa jika na fari ah gunta …
duk da cewa ta aurar da mata kuma sun haihu !!!! Amma wanan jikane nafari daga yayan ta maza kuma jika nafari agun dan mijinta mafi, soyuwa ah zuciyar sa !!!!
duk abinda ake ciki sai a lokacin baba Sa’idu yasan matar Aziz na asibiti sanan ta nemin
takarda aka medasu baban asibitin garin….
Aziz duk ya cucuce hankalinshi ya tashi baba sa’idu sai hakuri yake bashi…. Cikin ikon Allah ana zuwa asibi tin nan Djamila ta haihu… !!!
Ta haifi yarinya mace kyakyawa mai kawan gaske duk da cewa jaririya ce hakan be boye kyanta bah …
yan matan da samarin gidansu aziz sukayi ta zuwa dubiya wannan jaririyar dan yarinyar ta shiga zuciyar mutaneh sosai, duba da yadda baba Sa’idu ke nunamata soyeya karara , sawran matan baba sa’idu biyu ma duk sun zo …. sai kuma ah ranar mamar Djamila ta karaso garin dan batanan tana Algeria 🇩🇿 zama cen take kasuwancin ta , akoy yayar djamila agun dama tun euwansu asibitin…
Washe gari aka sallamusu daga asibiti
idan baba Sa’idu ya nemi da Aziz yayiwa diyar huduba ya saka mata suna !!! Nanfa aka fara maganga nu dan kamin aziz kowace nasu ace ita ta sakawa yarinyar suna … Akayi ta kananan maganganu har Aljanu yan matan gidan suka tashi dan sunadashi su !!!! Aysha babar yar matar baba Sa’idu ta biyu a lokacin itace tafi kowa zakewa dan saida akan ta abubuwa tsenfe tsenfe kafin , tadawo dede kuma anyiwa Aljanun nata alkawarin duk sunan da Aysha take so shi za’a saka !!!
Aka sawa jinjirar suna “ Lariyatu ” wanda sunan mamar sa’idu ne me rasuwa za’a rinka kiranta da ummy koh !!! « uwar masu giya»
Har akayi wanan tashin hankalin aka gama dangin, Djamila busuce komai dan ah cewar su
baruwansu da duk abinda zasuce !! Tunda dama sunada labarin takurawar da Mamar su Aziz kewa Djamila !!!!!
anyi suna ladiya ankare , Rago manta biyu Aziz ya yankawa yar sa …
Djamila nayin jegon ta cikin koshin lafiya dan bata tafi kida mamar ta takoma Algeria akoy tsohuwar da take kula da ita kuma , makwabciyar suce ah gefe yar yayarta na tayata wasu yan aikace aikace
bayan wasu shekaru……….
to be continued