MIJIN AMAL

Chapter 15

by @reza12


*Chapter 15*
A fili ta ce "Alhamdu Lillah! Allah mun gode maka da wannan kyautar" Shima ya furta kalmar yana riƙo hannunta ceke da tsntsar murna. Likitan ta ce "Saura goron albishir ɗina ko?" Ya ce "Zaki ga saƙo" Tun daga ranar ta fara rashin lafiya sama-sama. Ga yawan barci da ciwon kai. Gashi shi kuma baya samun lokaci sosai. Wani sa'in ma idan ya bar gidan sai biyar zai dawo. Ko waya baya samun damar kira sau ɗaya. Gaba ɗaya ta rame sosai ga cewar sa. Duk Laulayi ya tsotse mata jiki kamar ana sassaƙar ta. Sai yanzu ma ta sake tabbatar da cewar ashe wannan yawan kallon ma da suke yi duk rashin abun yi ne. Yanzu idan ba ranar Lahadi ba, baya ma samun lokacin yin kallon kwata-kwata. Ranar lahadin ma wani lokacin barci yake yi abun sa sai yace ya gaji. Sai da cikinta ya kai wata biyar kafin abubuwa suka dawo mata daidai. Har zuwa lokacin dai itace ke ɗauke da nauyin gidan su bangaren abinci. Domin ya na karewa Mama zata zo ta kwasa. Da yake duk wata idan an masa albashi yana bata wani abu daga ciki. Kuma kayan abinci baya yanke musu. Shi da kansa ma yana saya harda su Mama ɗin a cewar sa. Zuga ne dai har yanzu taƙi daukar ko ɗaya daga wanda uwar ke mata. Babu irin huɗubar tsiyar da bata mata ba, amma Amal ta ƙi yarda. Hakan yasa ita da kanta Mama ta fara haƙura da wasu abubuwan. Dama ita babban matslarta shine auran talaka, ace tazo da buƙata ace babu. Yanzu kuwa alhmadu Lillah, duk da ba yadda take so ne take samu ba. Kuma ga yaron akwai kyuta. Amma dai dole ta sake shiri. Bangaren Nana ma dai har yau babu batun tariyar. Sun dai yi tafiya na wata guda sun dawo. Taci gaba da zama a gida. Ita kanta Mama abun ya fara damunta. Hakan yasa tai masa magana ya ce a karshen watan nan za'a gama aikin. Da yake yana mata kyautar kuɗi yasa bata ƙara tada maganar ba. Yanzu babban burninta Allah ya sauki Amal lafiya, ita kuma Nana ta tare a gidan mijinta. Daga nan zata fara tatsar kowacce har itama ta bar wannan tsohon gidan tunda dai Allah ya sa ta haifi wanda suka auri masu shi. 

Tun daren jiya take jin gefen kanta na mata wani irin zillo kamar ana yankawa da wuƙa. Hakan yasa barci ma rabi da rabi tayi. Tana ta daurewa akan kar ta hana shi barci taga ya dawo a gajiye. Ta tashi cikin daren ta zauna a bakin gado ta rike kan. Kamar tayi ihu amma sai ta toshe baki tana kallonsa. Da yayi mata wani irin zugi bata san sanda ta kurma ihu ba tana riƙe hannunsa wanda shima ya farka da salati. Ganin halin da take ciki ne ya rungume ta yana tambayar ta. Sai kawai ta fashe da kuka tana nuna masa gefen kanta. Ya dafe gurin yana mata addu'a. Amma kamar kara tsurkulin gurin akeyi. Ya duba gurin da suke ajiye maganin gaggawa ya ɗauko mata boska ya bata ta sha. Sai zufa take yi tana sake kaman kan. Yana tai mata saunnu. Sai yayi kamar ya lafa sai ya ƙara tashi. Har zuwa asuba suna wannan yanayi. Haka yayi Sallah a gida yana ta mamakin wannan ciwon. Bata taɓa yin irinsa ba. Tana yin Sallah kuma barci ya ɗauke ta. Ya tashi ya shiga kichin ya soya musu ƙwai da shayi. Sai da ya fara ci tukunna. Ya shiga ya shirya. Kafin ya ɗauki waya ya kira likitan yace dan Allah ta biyo ta gidan sa yanzu kafin ta tafi asibiti. Nan ta sheda masa ai a cen ma ta kwana. Kawai ya zo da ita sai ta duba ta. Ya kalli agogo. Sai ya tuna da tafiyar da zasuyi karfe takwas zuwa Lagos. Yasan halin wannan matar, zata iya kawo masa matsala idan yayi laitti. Kuma baya son ya tafi bai san abun da yake damun matarsa ba. Yana shiga ɗakin ya sameta zaune ta riƙe kan nata. Ya ƙaraso yana kiran sunanta. Ta ce "Beb kai na". Ta faɗa da ƙyar. Ya ce "Tashi mu je asibiti". "Ba zan iya tashi ba, Please kama min kan irin na jiya". Ta faɗa tana lalubo hannunsa". Ya kamata yana addu'a. Ya ce "Wai dama kina yin irin wannan ciwon?" "Ban taɓa yi ba sai jiya". Tana rufe baki suka jiyo Muryar Nana a palon. Hakan yasa ya amsa yana cewa ta shigo cikin ɗakin. Dama yanzu yake tunanin wacce zai kira ta zauna da Ita. Ta turo ƙofar dakin ta shigo hannunta reƙe da wata ƙaramar kula. Tana ganinsu a haka ta ƙaraso tana tambayar lafiya mai ya same ta.

Haka ta taimaka mata ta shirya. Da ƙyar taci farfeson da ta kawo mata, wanda dama kusan kwana huɗu kenan Amal ɗin na sawa tai mata ta kawo mata. Tace idan tayi da kanta bata iya ci, tun kafin ya dafu yake fita kanta. Sai ta tura mata da kuɗi ta sayo kayan ciki ta dafa mata. Ko tazo gidan nata tayi ko ta haɗo daga cen gida. Taci kaɗan ta kamata suka tafi asibiti. Bayan ya sauke su shi kuma ya wuce gurin aiki. Yana isa kamfanin har sun fito zasu tafi. A cikin mutane ta fara ci masa mutunci da gargadin rasa aikinsa idan ya kara bata musu lokaci. Kaman yadda yayi tsammani haka har suka isa filin jirgin tana aibata shi. Bai samu yayi waya da su ba sai bayan laasar lokacin suna hanyar dawowa. Bayan ta tabbatar masa cewar suna gida kuma jikin da sauki. Ya sauke wayar yana sauke ajiyar zuciya. Haka kawai yaji son yaro ko yarinyar da za'a haifa ya shige shi. Sai sakin murmushi yake yi shi ɗaya idan ya ai yana cewar watarana shima za'a nuna wannan ace ɗan sa ko ƴarsa. Ya buɗe ido sai suka haɗa ido tana masa wani irin kallo. Ta kawar da kai tana tsaki. Daidai lokacin jirgin nasu ya ƙaraso. Yana fita daga jirgin wayarsa na ƙara, ya ɗaga yana cewa eh sun iso lafiya. Bayan ya kashe wayar yaga miss calls ɗin likitan har biyu. Yaso ya bita amma ya fasa akan sai ya sauka. 

Da marmarin ganinta ya shigo gidan ɗauke da sallama. Jin ba'a amsa bane ya sake ware baki yana kiran sunanta. Haka ya dinga kiranta yaji shiru har sai da ya shiga ɗakin. Ya sameta a duƙunƙune a cikin bargo tana rawan sanyi kuma ga fanka a kunne. Da sauri ya kashe fankar yana ƙarasowa gurin. Ya ce "Lafiya dai, ina Nanar take? Wai tafiya tayi ta barki a wannan halin?" Ta buɗe kanta ta ce "Ka dawo?" "Eh na dawo , ya jikin naki, wai wani irin ciwo ne wannan ne, ko dai za'a zubar da wannan cikin ne Amal, har yanzu kin kasa samun lafiya, ina tsoro". Ya taɓa jikinta yaji zafi zau. Ya sake faɗin kan ne dai har yanzu?" Ta ce "Eh, amma yanzu gaba ɗaya jikina ne, harda mara ta". Ta faɗa cikin kaɗuwar sanyi. Ya yayi bargon yana faɗin sannu. Ina maganin da aka baku?" Ta nuna masa da hannu tana sake rufe jikinta. Ya ɗauko yana dubawa. Ya ce "Kin sha kuwa?" Ta ɗaga masa kai daga cikin bargon. Ya ce "Kinci abinci kafin ki sha?" "Nan ma ta ɗaga masa kan. Ya tashi ya shiga kichin ya tarar da komai a gyrae. Harda abincin ma an gama an juye shi. Ga nasa nan a kula a zuba masa. Ya ɗora ruwan zafi. Sai da yayi zafi ya ɗauka ya kai toilet ya sirka. Ya ɗauke ta tana sake faɗa masa sanyi take ji. Ya shiga da ita. Tana rawan sanyi amma sai da yayi mata wanka yana mata sannu. Bayan sun fito ya haɗo mata shayi mai zafi. Ya ɗauko abincin nasa. Ya hau gadon yana bata hankali. Tana cikin ci kuma ta fara amai. Sai da ta dawo da gaba ɗaya wanda taci. Ya gyara gurin, ya sake goge mata jiki ya bata tii ɗin tasha kaɗan kafin ta kwanta. Shima ya shiga yayi wanka ya ci abincin. Ya hau gadon yana kiran sunanta. Sai yaji ta amsa. Ya ce "Wannan cikin idan yana baki wahala a zubar da shi kawai". Ta girgiza kai kawai. Domin ita kaɗai tasan halin da take ciki. Ya rugumeta yana karanta musu addu'ar kwanciya barci. 

Da safe ma dai ta sake tashi da ciwon ciki. Wanda har jini tagani yana bin cinyarta. Taso ta daure har ya tafi kar ta ɗaga masa hankali. Amma da kansa ya ankara da ita saboda tun da ya tashi hanlinsa na kanta. Nan ma asibiti suka fara zuwa. Suna zuwa yace a cire cikin gaba ɗaya basa bukata. Likitan tace ai kuma cikin lafiya lau yake, sannan ita kanta Amal ɗin ta ce ba cikin bane ke damunta. Yasir yace amma dai ai duk cikin ne ya jawo wannan ciwukan. Haka dai likitan ta lallaɓa shi aka haɗo musu magani. Bayan sun dawo gida ya kwantar da ita bayan ya tabbatar tasha maganin. Kaman wasa sai ga shi laulayin ya lafa har kwana uku bata sake yin ko ciwon kai ba. Ta dawo tana yin komai harda girki da kanta. A kwana na huɗun ne da yamma jini ya ɓalle mata tana shiga toilet. Lokacin ba kowa a gidan. Ko lokacin da ya dawo har ta suma. Bata ko motsi. Nan ma ya ɗauke ta suka tafi asibiti hankali a tashe. Da ƙyar aka fita da shi daga cikin ɗakin da za'a fara mata aiki. Yana faɗin su taimaka masa kar ta rasa rayuwata. Sosai yake kuka kamar karamin yaro. Ya tsaya a bakin ƙofar har sama da awa guda bai zauna ba. Likitan na fitowa ganin halin da yake ciki sai tayi saurin faɗa masa cewar matarsa na cikin koshin lafiya, ta farfaɗo. Amma sun rasa cikin jikinta. Bai ko bi ta kan cikin ba ya ce "Zan iya ganinta dan Allah likita?" "No tana buƙatar hutu sosai, yanzu ta samu barci. Sannan akwai jini da za'a kara mata idan ta farka". Ba shi ya samu ganinta ba sai cikin dare karfe goma. Har lokacin barci take yi. Ga ledar ruwan da aka saka mata ya kusa karewa. Ya kafe ta da ido yana jin wani irin tausayinta da soyayyar ta. Ta rame sosai kamar ba ita ba. Ya riƙe hannunta sai yaji kaman ta ɗan motsa. Ya kalli fuskarta yaga hawaye. Ya sa hannu ya share mata yana faɗin "Daga yanzu shikenan in sha Allah, muddin ciki ne zai saka ki wannan abun to mun hakura da shi kenan". Sai washegari yan gidan su suka samu zuwa. Harda Anty Maryam. Kwana uku aka sallame su. Mama tace wai zata wuce da ita gida ko kuma su zasu dawo gidan da zama. Amal ta ce ita babu ko ɗaya daga ciki, idan ma ya zama dole to kawai Nana ta dawo su zauna. Mama kuwa tace bata isa ba, ai bata da lafiya kuma ɓari tayi, dole a zauna da ita kafin ta warware. Haka dai dole Nana ce ta zauna da su. Kwana biyu da dawowa wasu irin ƙuraje suka fito mata a gefen wuya. Haka kawai ta fito daga wanka ta gansu ƙanana da su a guri ɗaya. Washegari ta sake ganin wasu a goshi. Abun ya bata tsoro tai masa magana ya ce zai fadawa likita sai a bata magani. Kwana ɗaya suka sake ƙaruwa. Hakan yasa da kansa ya kawo ta asibiti. Itama likitan tayi mamakin ganin ƙurajen. Har tana masu tsiyar cewar ko basa so kyawun ta ya ragu ne. Ta rubuta musu magani ta ce muddin ta sha zasu tafi. Sai dai Yasir yace kawai ai mata text domin aga abun da yake damunta. Haka dole a kai mata text ɗin. Ta rubuta musu maganin ƙurajen da rashin ƙarfin jikin. Tace zuwa gobe idan result ya fito sai yazo ya amsa. Amma dai ita ta faɗa masa ba abun da yake damun matarsa. Haka suka dawo gida a ranar yana ta tsokanrta cewar wai ta fara tsufa ne kawai. Sai kuwa ta fashe da kukan shagwaɓa akan wai bata tsufa ba, kawai wannan cikin ne yake son ya mayar da ita haka, kuma tunda yanzu babu ya bari yaga yadda zata dawo idan ta warke. Suna daga cikin ɗakin suna hira suka jiyo Muryar Nana na kuka tana surutai da karfi. Hakan yasa Amal ta tashi ta nufi ɗakin shima ya biyo bayanta. Tana shiga ta sameta tana ta kuka ta kifa wayar a bakin gado. Ta ƙarasa ta dafa ta tana tambayar mai ya faru. Sai kawai ta faɗa jikin yayayr tata tana sake rushewa da kuka. Ganin haka yasa ta barta tayi sosai, tana ta buga bayanta, tana tunanin mai zai sa Nana kuka har haka. Yasir na daga wajen ƙofar yana kallonsu. Amal ta ce "Mai ya faru?" Nana ta ce "Anty ciki ne dani, kuma ina faɗa masa ya ce wai ya sake Ni". Fa faɗa da muryar kuka. Chak Amal ta tsaya daga yunƙurin maganar ta kasa cewa komai tana kallon kanawar tata da ta ɗauki waya tana sake nuna mata shedar sakin ba ma iya ta fatar baki ba. Yasir kansa abun ya dake shi. Bai san lokacin da ya turo kai ya shigo dakin yana faɗin "Saki kuma Nana? Bani number sa, saboda me to?". Ya faɗa yana ciro wayarsa daga aljihu. Cikin kuka ta ce "Dama ya daɗe baya ɗaga kira na, tun ba yanzu ba, kaman yasan ina da cikin ne, kuma yace ba zai sake ɗaga min kira ba, wai ya bar min yaron da zan haifa naje ya sake ni". Ta ƙarasa tana fashewa da kuka" Amal bata san lokacin da ta saki wani irin zagi ba tana kallon Yasir. Ta ce "To saki a wani dalilin? Ko kin masa wani abun ne dan ubanki?" Nana ta girgiza kai da sauri. Amal ta mike tsaye ranta a mugun ɓace. Yasir ya riƙe ta yana faɗin ta natsu abi komai a hankali dan Allah. Haka Nana ta kwana tana kukan soyayya Amal kuma tana addu'ar kaiwa gobe domin aji daga bakin sa. Washegari kuwa da sassafe ta bar gidan ba tare da ta fadawa masu gidan ba, itama Amal ɗin tazo tashin ta ne ta samu bata nan. Bayan ya tafi aiki ne ta kira Mama ta faɗa mata abun dake faruwa, kuma tace gashi dai Nana bata gida yanzu haka. Tun daga cikin wayar ta fara zaginta akan in sha Allah wannan mugun fatan nata ba zai tabbata ba. 

Bangaren Yasir kuwa. Har ya manta ma da batun result ɗin gwajin Amal. Yana ofis yaga kiran likitan. Daga yanayin muryarta kaɗai ya tsorata. Ta ce masa kawai yanzu ya bar duk abun da yake yi yazo asibiti. Haka kuwa bai ƙara ko minti biyar ba ya iso asibitin a guje. Yana shiga ofis ɗin ya samu ta dafe kai tana ganinsa kuwa ta miƙe tsaye ta rasa ma mai zata fara ce masa. Ya ce "Likita mai yake damunta, wani irin ciwo ne da naga kin min irin wannan kiran? Dan Allah faɗa min?" Lokacin da yaga ruwa a cikin idanunta sai yaji jikinsa ya mutu. Ya kafe ta da ido, yana kuma kallon takardar dake hannunta. Da sauri yasa hannu ya ɗauka yana fara karantawa daga sama. Yana kawowa karshe bai san lokacin da ya kai ƙasa ba. Ya ɗago yana kallon likitan da kuka ya kufce mata. Ya kasa magana sai binta da kallo yake yi yana sake juya takardar. Abun da ya fara masa yawo akai shine "Ta yaya hakan zai faru, mai zai kawo wannan cutar jikin Amal, kuma Tun yaushe take da ita, kuma tasan tana da ita bata faɗa masa ba. kuma hakan na nufin shima yana ɗauke da wannan cutar kenan...?📝

Tambayoyi ne marasa adadi akansa, wanda bai san ta ina zai fara samun amsar ba. Shin wani irin ciwo ne haka? Kuma da gaske shima yana da ciwon? To ita Amal ta san tana da cutar? Mai zai biyo bayan hakan?