MIJIN AMAL

Chapter 16

by @reza12


*Chapter 16*
Ganin yadda ya rikice ne likitar ta ce "Kaga Yasir, ka kwantar da hankalinka, ba lailai ne kaima kana ɗauke da wannan ciwon ba, kuma bana tunanin itama tasan tana da cutar, da ta sani zata faɗa maka. Ka natsu muyi magana dan Allah, ka fahimci abun da yake damun matarka ba wai tuhuma ba". Ta ƙarasa tana share hawayen fuskarta domin dai tasan irin son da yake wa matarsa, dole wannan abun ya taɓa shi. Yasir ya dafe kai sai kawai ya saki wani siririn kuka mai ciwo yana cukuikuye takardar result ɗin da ke hannunsa. Ta sake faɗin "Ka natsu kai namiji ne, kuma kai ne ya dace ka san asalin gaskiya ta sigar kwantar da hankali ba wannan fishin ba. Ita gaddara bata taɓa sauyawa daga yadda Ubangiji ya turota, yarda da hakan shine cikar imani". Ya ɗago da jajayen idanunsa yai mata wani irin kallo. Sai ya tashi yayi waje a fusace bai ce mata komai ba. Likitan ta biyo bayansa da sauri tana kiran sunansa. Tana buɗe ƙofar ta same shi a durƙushe yana kuka. Sai ta tsinci kanta da karasawa kusa da shi tana kallonsa, ta kasa ce masa komai sai kallo. Ya kai minti biyu a haka kafin ya miƙe. Ya ce "Likita kin tabbatar wannan result ɗin ta ne ba na wata Amal ɗin bane?" Ta ce "Sai da na gwada sau uku yana bani abu ɗaya, tun safe nake so na faɗa maka amma na kasa, saboda abun babu dad'i". Ya kama hanyar gida yana tafiya a hankali.

Tun da ya fita hankalinta ya kasa kwanciya da tafiyar Nana. Ko ina taje oho, gashi number ta bata shiga. Gashi yau ma ta tashi jikinta ba ƙwari, da ta daɗe a tsaye wani irin jiri ne ke kamata. Amma a haka ta lallaɓa tayi aikin gidan ta gaba ɗaya tana yi tana hutawa. Girki ne dai ta kasa yi, tana so ma ta kira Mama taji ko Nana ta dawo amma ta fasa. Kamar daga sama taji an banko ƙofar gidan an shigo ba ko sallama. Lokacin tana falo kanta ya mata wani gingirin. Ita kanta ta san akwai sauyi a jikinta, sai ta bar hakan a matsayin ɓarin da tayi ne. Mama ce tare da Nana suka shigo gidan tana faɗin "Ɗauki waya ki kira mana Mijinki yanzu, wallahi bai isa ba yau sai naga waye ubansa a garin nan, har ni za'a wulaƙantawa yarinya". Amal ta kalli Mama ta kasa gane dawa take faɗa. Sai ta ce "Wai wa za'a kira mijin Nana ko na Amal?" Ta faɗa da ƙarfin hali tana kokarin tashi amma ta kasa. Cike da zagi da ɓacin rai tace "Mijin ki zaki kira min dan ubanki". Sai ta sake kalli Nana tana tauna kalmar mijin nata ta ce "Mai ya haɗa ki da Yasir da zan kira shi?" Kafin Nana tayi magana Mama ta ce "Ubanki ne ya haɗa su, ko ba zaki kira min shi bane?" Duk da tana cikin ciwo amma tayi ƙarfin halin faɗin "To wai Mama mai Yasir ɗin yayi, ban gane ba, ya ga mijinta ba za'a kira ba sai nawa, kuma ma yanzu ya tafi gurin aiki, ki ma menene a fara faɗa min mana naji" Mama ta ce "Innalillahi wa innalillahi, yanzu Amal ni Kike fadawa haka akan nace a kira min Mijinki, Amal akan ɗa namiji ko?" Nana ta ce "To kema Mama fisablilillahi meye na cewa a nemo shi ne, bafa abun da zai iya wallahi". "To idan ba shi ba waye muke da shi, shine zai tsaya a ƙwato mana yancin mu, shi wancen ɗin ba dan yana da kuɗi bane zai mana wannan wulaƙancim". Sai yanzu Amal ta fahimta. Ta ɗauki waya ta kira shi. Amma ba'a ɗagawa. Ta sake kira nan ma. Ta ce "Mama ba'a ɗagawa yana gurin aiki". Ta faɗa tana sake zama jin kamar zata fadi. "Ina ne gurin aikin nasa?" Mama ta faɗa. "Nima ban sani ba". Ta bata amsa. Sai ta ce "To ina number wannan abokin nasa, mai motar nan da ya taɓa bani dubu goma?" Nana ta ce "Haba Mama, kawai mu bari Yasir ɗin ya dawo". Amal na son yin magana amma jikinta ya hana ta, taso daga Mama har Nana ta faɗa masu maganganun da zasu gane kuskuren da suka yi. Amma ita burninta ma su tafi ta ɗan mike. Daga haka suka bar gidan Mama na sake faɗa mata ta sanar masa da ya dawo. Suna fita kuwa ta miƙe a kan kujera, sai ta sake jin jirin na san kamata a kwancen ma. Sai ta tashi ta nufi ɗaki. Tana shiga ta kwanta tana faɗin "Ya Allah!". Kamar daga sama ta jiyo karar wayarta. Amma ta kasa tashi. Tana kwance har karfe ɗaya, ita ba barci ba kuma ba komai ba. Sai lokacin ta ɗan ji daidai. Ta tashi ta shiga toilet ta dauro alaulau tana jin wata bahaguwar yunwa na bijiro mata. Bayan ta fito ta same shi zaune a ɗakin wnada sai da ta tsorata. Ta tsaya daga bakin toilet ɗin ta ce "Beb wallahi ka bani tsoro, sai kace wani aljani, ban fa ji shigowarka ba". Ta faɗa tana ƙarasowa kusa da shi ta zauna. Sai ya kalleta. Ya ɗan matasa kaɗan. Ta ce "Tun safe jikina ba dad'i, jiri, ga gajiya". Ya ce "Sannu, shi yasa na baro gurin aiki na duba ki, kuma naga kiran ki, ina ce ma jikin ne". Ta ce "Yauwa ka amso result ɗin nan a gurin likitan, wata ƙilla a result ɗin zamu ga abun da yake damu na, duk jikina ba dad'i". Ya ɗan kawar da kai kaɗan ya ce "Da yamma zamu je tare, na manta ne". Ta kalleshe ganin kamar dai yana cikin damuwa ganin yana amsa mata a daƙile. ta ce "Kaman fa kana cikin damuwa, mai ya faru?" Ta faɗa tana Kama hanunusa. Ya kalli hannun da sauri. Sai ya zame nasa hannun ya tashi tsaye ya ce "Damuwar halin da kike ciki ne Amal, bana son ganinki a damuwa". Ta ce "Nima haka, amma ko ma menene ai yanzu zamu sani, ba ma zai wuce maleriya ba fa, kawai naje asibiti a bani gado na kwana biyu a min aiki mai kyau, saboda fa Allah jikina gaba ɗaya ya sauya daga wannan barin". Tun da take maganar yake ta kallonta har ta gama. Hakan ya sake tabbatar masa da cewar bata sani ba. Ta sake faɗin"Yauwa ɗazu Mama tazo tace wai na kira ka, na kira baka ɗaga ba, so zan iya kiranta yanzu?" Yasir ya ɗan yi jim yana tunano abun da ya faru ɗazu. 

Lokacin da ya baro asibiti ya nufo gida ne akan ya ji shin dama tasan tana da wannan ciwon bata faɗa masa ba, mai yasa za tai masa wannan zaluncin. Har ya kama ƙofar gidan zai buɗe ya ji shi a buɗe. Yana jin duk maganganun da su kayi ɗazu. Hakan yasa ya fasa shiga ya koma asibiti. Ya na shiga ya ce da likitan. "Wata Alfarma ɗaya nake so ki min". Ta ce "Tana jin sa". Nan take yasa aka masa gwajin nasa ciwon. Daga shi har likitan a tsorace suke, shi kam ya ma san yana da ita, kawai dai yana so ya tabbatar ne. Cikin ikon Allah aka tabbatar masa da cewar shi bashi da ciwon kwata-kwata. Abun ya bashi mamaki, ta yaya za'a ce shi ba shi da ita, kuma matarsa tana da ita. Daga nan ya tafi shago ya zauna shi ɗaya yana ta tunani. Kuma a bayanin likitan ana iya samun cutar ne ta hanyar kusanta, ko amfani da abun bukata ga mai cutar na yau da kullum, ko yawan kasancewa a guri ɗaya da mai cutar. Babban hanyar da za'a fi ɗauka kuma taraiya. Zumbur ya miƙe tsaye yana hasaso tun farkon haduwarsu da yadda har suka fara soyayya har aure da bayan auren. Innalillahi wa innalillahi rajiun kawai yake furtawa. A fili ya ce "Ta yaya ta yaya ta yaya, Amal kuma a garin yaya, Allah mun tuba, Allah kai kasan abun da kake nufi, Allah ga matata na yarda da ita, Allah kar ka tabbatar da abun da ba shi bane. Har sai sha biyu da rabi ya tashi yayi alaulau ya je masallaci yayi Sallah. Ya daɗe yana addu'a harda kuka Kafin ya fito ya nufi gidan jikinsa a mace. A hanya ya sake kiran likitan ya faɗa mata alfarmar da yake so tai masa.

Bayan ya dawo daga tunanin ya ce "Zan je gidan yanzu ba sai kin kirata ba". Yana faɗa yayi waje. Da karfi ta ce "Beb ban fa ci abinci ba, kuma ina jin yunwa, ban iya dafa komai ba wallahi". Jin bai amsa bane ta biyo shi palon. Ta samu ya ba ƙofa baya yayi shiru. Ta rungume shi ta baya tana faɗin "Ina jin yunwa, idan kana dawowa daga gidan Mama ka zo min da abinci please". Ta faɗa tana kwantar da kanta a bayansa. Yasir ya ja jiki da sauri har yana ɗan tureta. Ta kalleshi. Yayi saurin faɗin "Am am ba alaulau kikayi bane, so kike na karya miki ita ko". Tayi dariya tana faɗin "To shine zaka karya ni, ko ka manta banda lafiya ne". Ya ce "Mai zaki ci nazo miki da shi?" Ta sa hannu a baki alamar tunani. Shi kuma yana ta kallonta har ma ya ɗan faɗa tunani bai san tana magana ba. Ta ce "Farfesu mai yaji, da kuma ƙwai dafffe da moltina mai sanyi". Ta maimaita Kafin ya ce "Ok ok Tom!" Yayi hanyar fita ta ce "Ka dawo da wuri please kar na mutu". Yana fita ya zauna a cikin mota ya saki satali yana ɗora kai a kan gaban motar. Yanzu dawa zaiyi wannan maganar. Wacce irin gaddara ce wannan mai wahalar cinye wa. Ta ina zai fara, mai zai ce. 

Bayan ya isa gidan suka gaisa da Mama ta fara zaiyano abun da take so ayi. Shi bai ma ji gaba ɗaya ba. Sai kawai ya ce tom za'ayi. Ta ce "So nake a kai min wannan tsinannan mutumin ƙara kotu. Ya auri ƴartawa, bai tare ba, yayi mata ciki, yanzu kuma ya sakar min ita, abun haushin ma bamu san ina zamu same shi ba. Dan Allah Yasir ka taimakawa ƙanwarka, ka ƙwato mata hakkinta dan Allah Alhaji Yasir". Shi kansa kalmar karshen ta so bashi dariya. Bayan ya miƙe Ta ce "Daga nan koton zaka je ko?" Yasir ya ce "Sai ranar Monday sai muji yadda za'ayi". Nana ta fito daga ɗakin tana faɗin "Ni yaya ko ganinsa ne ma dan Allah ina so nayi?" Yasir ya bisu da kallo yana aiyana wa ransa da ace zasu fahimce shi ai da yayi maganar abun da yake damun Amal da su, ko su ɗin zasu san gaskiya. Ya musu alkawarin zaiyi duk mai yiwuwa in sha Allah.

Har sai da yazo ƙofar gida ya tuna da cewar ta bashi sako. Sai dai bai ma san me zai sayo mata ba. Hakan yasa ya ɗauki waya ya tura mata text message. Kafin ta ba shi amsa ya ɗauki hanya. Har yayi nisa yaga wayarsa na ƙara. Yana dubawa yaga CEO ce. Ya sauke hajiyar zuciya domin gaba ɗaya ya manta da ofis ma. Kuma ba wanda ya san da cewar ya fita. Yayi ƙarfin halin ɗagwa da sallama. Ta cikin wayar Suhailait ta ce "Na baka minti goma ka tabbatar min da takardar yarjejeniyar nan a cikin ofis dina kuma a cike". Ya ce "Please Madam ban ma yi aikin ba, kuma dan Allah ki..." Ƙit! Yaji ta kashe wayar. Daga saman wayar yaga message ɗin Amal ya shigo. Bayan ya karanta ya ɗauki hanya. Yana ta kokarin kiran abokin aikinsa ya taimaka masa. Yana ɗagawa ya ce "Please ofis na zaka je..." Tun kafin ya karasa ma ya ce "Gaba ɗaya kamfani ba wanda bai san da wannan maganar ba. Yanzu haka ma ta tara mu a filin miting" Yasir ya sauke ajiyar zuciya. Yana jin abokin na tambayar sa ko dai ya taɓa mata wani laifi ne a baya, ganin yadda kowa yasan irin wulaƙancin da take masa.

Bayan ya sayi abincin. Sai ya fara tunanin ya je ofis ɗin ne ko ya kaiwa Amal abincin. Ya tuno da kalmar ta ta karshe da tace "Kayi sauri kar na mutu. Ya kuma tuno da abun da zai faru idan bai je ofis ɗin nan ba. Sai kawai ya shiga Mota ya nufi shagonsa. Yana zuwa ya bawa yaron shagon kuɗin mashin yace ya kai wa Amal yanzu". Shi kuma ya nufi kamfani. Yana shiga ya nufi ofis ɗin sa ya ɗauki takardar. Dama ya fara aikin kafin ya tafi. Ya zauna ya cike komai ya nufi ofis ɗin ta. Sai ya samu a rufe. Hakan yasa ya nufi gurin da ake miting ɗin. Yana shiga ya samu kowa na zaune ana tattaunawa. Sai idon kowa ya dawo kansa. Ya ƙaraso kujerar da take kusa da ita dama tasa ce. Ya sunkuya zai zauna ta daka masa tsawa!. Ya fasa zama yana kallon yadda kowa yake kallonsu. Ta ce "An baka aiki ka barshi ka tafi yawon banza. An haɗa minti tun ɗazu baka zo ba, sai yanzu. Kuma kana kokarin zuwa ka zauna babu neman afuwa ko?" Ya ce "I'm sorry, uzuri ne ya taso min mai muhimmanci". Ta ce "Uzurin yafi aikin ne? Idan haka ne ka ajiye akin mana sai ka ji gaji da uzurin naka ko?" "I'm sorry Madam". Ya faɗa yana risinawa. "Sorry for your self ba dai ni ba". Ya miƙa mata takardar ta ce "Wannan ai mun gama da ita, mun sa an gama mana. Yanzu ga aikin da zakayi replacement ɗin wanda aka yi maka. Nan aka tara masa aikin da sai ya kai awa goma ma yana yi. Ta kalleshe ta ce "Zuwa safiya ka tabbatar da ka kawo min su ofis na kafin na iso". Daga haka miting ya watse. Haka ya dinga fama da aiki har lokacin tashi. Haka ya tafi da wasu gida dan ya rage. Yana shiga gidan gabansa na faduwa da ya tuno da abun da yake faruwa. Ya zauna a palo yana dafe kai. Minti ɗaya sai gata ta fito tana waya. Ganinsa yasa ta tsayar da wayar ta ce "Wai beb yanzu ka daina sallama ne, kuma ma waye yake buɗe maka gidan ne?" Ta faɗa tana jin kamar fa ya sauya. Ya ce "Kin shirya muje asibitin?" Ta ce "Kai nake jira dama. Amma mai yasa ka daina yin sallama"? "Ba dainawa nayi ba, nayi ne baki ji ba". Ya faɗa yana tashi yayi waje ya ce "Ki same ni a Mota, dan Allah banda bata lokaci". Yana faɗa yayi waje. Ta koma ciki ta sa hijabi. Bata sa nigab ba. Ta fito ta shiga gidan gaba. Tana jira yayi mata magana amma taji shiru. Ya tada motar. Ta ce "Yasir!" Ta faɗa da muryar da yaji tsakar jikinsa ya tashi. Ya kalleta yaga shi take kallo. Ta ce "Ina sonka". Ta faɗa tana murmushi. Domin dai ta tabbatar abu na damunsa, kuma dole idan sun dawo ta san menene wannan. Ya ce "Kinyi kyau". Ya faɗa kamar baya so. Daga haka har suka ƙaraso asibitin da ya fadawa likitan gasu nan. Bayan sun zauna ne likitan ta ɗauko result ɗin ta mika masa. Ya amsa ya fara karantawa, suka haɗa ido da litlkitar sai tari ya sarketa ta, hakan yasa ta ce musu minti ɗaya ta tashi ta shiga toilet. Amal ta ce "Mu gani menene ya ke damun baiwar Allah". Ta fara karantawa daga farko har ta gama. Daidai lokacin likitar ta fito. Ta ce "Amma likita ina yawan jin jiri haka da kuma ciwon kai, duk maleriyar ce take kawo hakan?" Ta ce "Eh ya haɗu ne da yanayin da kike ciki na ɓarin ciki na farko a matsayin ki ta budurwa da bata taɓa aihuwa ba, shi yasa kike jin haka, amma zamu ɗora ki a kan magani, sannan akwai abubuwan da dole zaki daina su wanda zasu taimaka miki. Wannan wani yanayi ne mai wahala da mace ke iya samun kanta a ciki idan cikinta ya wuce wata biyar kuma ta rasa shi, cutar tana da wahalar sha'ani, dole sai kin kiyaye, yawancin matan da basu taɓa aihuwa bane suke kamuwa da ita a karon farko, amma idan suna shan magani ba wata matsala. Ta ce "Likita ina tsoro, amma dai ba zata hana ni komai ba ko?" "no ba abun da zata hana ki". Amal ta ce "Tom likita, mun gode sosai. Ta kalli Yasir ta ce "To kaji ma inji likita ashe ba wani ciwo bane". Ya ɗago suka haɗa ido da likitan ta kawar da kai. Ya ce "Mun gode likita". Daga nan aka kafa mata sharuda, harda kalan abincin da zata dinga ci, har zasu tafi tace "Yauwa likita, wannan ƙurajen fa da suke fito min a goshi, ga wasu ma yau na gani a wuya na". Ta faɗa tana nuna mata. Take likitan ta rikice ta fara kame-kame. Ta ce "Eh duk dai wannan ciwon, kuma idan kina  shan magani duk zasu tafi". Ta ce "Likita babu wani sabulu da xan yi amfani da shi?" Yasir ya ce "Ga magani nan duk zamu saya". Haka suka bar asibitin nan bayan ya amsa musu maganin da aka cire su a cikin gidan su. Suna shiga Mota ta ce "Beb wallahi haka kawai naji gabana na faduwa. Kamar likitan nan ta ɓoye mana wani abu?" Ya taka burki da karfi yana kallonta...📝


Hamm