Zaren Rayuwar Mu

BABI NA ASHIRIN DA ƊAYA

by @zainabb

Zaren Rayuwar Mu 

SATI ƊAYA kenan kowace rana se na kasance tare da Zaid har nazo na gaji jikina duk ciwo yake min. Ranar sati ɗaya da kwana biyu nayi saurin rufe idanuna kamar me bacci. Yasan ba bacci nake ba ya fara kai hannun shi a jiki na wanda yasa dole na tashi. “Dan Allah mu ɗagawa wannan ƙafa. Duk na gaji jikina ciwo yake min”
   “Please Diza” yace yana kallona ashe bashi da kunya ko kaɗan 
   “Gaskiya ba zan iya ba, Zaid. Na gaji jikina fa yake min ciwo”
   “It is okay” yace tare da hugging ɗina a kwancen da yake. Hannuna nasa na riƙe gaban rigar shi na shige mishi sosai a jiki ina jin warmth da ƙamshin shi. Hannun shi na sumar kaina da yake bashi da kitso yana min massage ahankali. 
   “This is peace, Diza. Thank you for bringing it home”
Murmushi nayi ina ƙara shigewa a jikin shi. 
  “You are more beautiful when you are happy”
Wani murmushin na ƙara yi me ƙara. 
   “When will you take me to the court of law?”
  “You want to go to the court of law? To do what?”
   “i want to be convicted for loving you too much”
Murmushi nayi na buɗe idanuna ina son sa su a nashi “Is that a crime?”
     “Yes, a big one”
     “I'll draft a sheet then”
   “Yes, you should. I'd want to get my own sentence and you come and visit me everyday and I'll tell you how much I love you whenever you come”
Dariya nayi jin abinda Zaid ke faɗa. 
     “It will be great to have you tell me that every day”
         “Yes, it'll be”
  “it will be” na maimaita abinda yace 
   “Sleep. You have work tomorrow”
Rufe idanuna nayi jin abinda yace nace “Goodnight”
   “Goodnight, Diza”

Wata biyu yanzu kenan muna shiri sosai da Zaid. Duk wasu abubuwa da nake ji na cikin zuciya ta na cire su na cire duk damuwa da abinda ke iya faruwa of me liking him. Zaid has been clingy and kind and respectful. Abinci har yanzu ba koda yaushe nake yi ba saboda aikina. Shima wani lokaci baya nan tunda aikin shi ya haɗa da tafiya ƙasashen dake akwai mai a Nijeriya. 

Ina wurin aikina aka kira ni da wata number. Ɗauka nayi aka fara gaidani. Amsawa nayi se tace “Yaya baki gane wake magana ba?”
   “Kamar dai zan gane amma kiyi haƙuri ban gane ba”
       “Rahama ce”
Nan take gabana ya faɗi. “Rahama ta gidansu Shahida?”
     “Eh ni ce” ta faɗa murya ƙasa ƙasa 
  “Lafiya dai ko?”
  “Eh lafiya, Yaya. Dama ina so na faɗa miki wani abu ne” tace se ta fashe da kuka 
Zuciya ta ta cigaba da bugawa ina tunanin abinda be dace ba. “Ki dena kuka ki min magana Rahama”
Shiru tayi ina jin surpassing kukan da tayi da ƙarfi se kuma ta kashe waya. 
Inalillahi wa inna ilaihi rajiun na dinga maimaitawa ina roƙon Allah yasa ba abinda nake tunani bane ba. Ji nake kamar na buga mota naje gidan kuma Mummy na iya ganin mu tare muna magana tace me muke magana akai. 

Bayan na koma gida nake tambayar Zaid yaushe zamu tafi gida mu gaida su Abba kwana biyu bamu tafi ba. Kallona yayi da mamaki saboda yasan ban taɓa tambaya yaushe zamu tafi ba. 
  “Yanzu aiki nake” yace ya kalle ni ya maida idanun shi kan laptop. 
   “Ko gobe ne toh”
   “Okay, Allah ya kai mana rai”

Washegari da rana da wuri na dawo gida daga wurin aiki saboda zuwa gidansu naji abinda ke faruwa da Rahama. Zuciya ta tana bugawa ina roƙon Allah yasa ba abinda nake tunani bane ya faru. 
Lokacin da muka shiga gidan, lokacin Mummy ta fito zata je uniAbuja wurin lecture ɗin ta. Gaisawa muka yi da ita muka shiga ciki. Wurin Abba muka fara shiga gaida shi. Muna chan Zaid na magana da Abba na tashi na fito daga parlourn shi. 

Tsaye nayi a babban parlourn su ina duban inda zan ga Rahama. Kitchen na fara shiga ahankali na duba ban gan ta ba. Na kira sunan ta ba'a amsa ba. Ban san inda ɗakin ta yake ba yasa nayi tsaye ina tunani. Wani ɗaki na gani wanda nasan ba na Shahida bane. Murɗa kofa nayi na shiga ahankali. “Rahama” nace ina kallon ɗakin. Shiru ba'a ce komai ba yasa na rufe na fito. Ina nan tsaye se gata naga ta fito daga hanyar kitchen. “Rahama. Ke nake nema” nace ina kallon ta idanun ta sun yi jazir gata nan duk ta zama wani iri kamar wacce ke cikin firgici. Wurin ta na matso sosai nace “Menene ranar kin kira ni. Kina lafiya kuwa?”
Gyaɗa min kai tayi ta sunkuye kanta. 
“Ki faɗa min. Me ke damun ki? Wani abu akayi ne?”
Kuka ta fara yi nayi tsaye ina kallon ta zuciya ta bata dena bugawa ba. 
   “Gida nake so a maida ni. Na gaji da aiki anan gidan”
   “Me yasa Rahama? Ba ke ce kike musu aiki tun ba yanzu ba?”
Gyaɗa kai tayi tace “Khalifa ne” ɗago kai tayi tana kallo na tace “Kar ki faɗawa Mummy. Ni gida kawai nake so na koma”
     “Ina ne garin ku?”
“A Niger nake”
“Shine kika zo aiki har nan Abuja?”
Gyaɗa kai ta ƙara yi idanun ta sun cika da hawaye. 
   “Me Khalifa yayi?” nace tare da kai hannuna akan kafaɗar ta ina bata damar faɗa min abinda ya dame ta. 
Hanci ta ja ta fara “Sati biyu kenan bayan Mummy ta fita zuwa makaranta yace na biyo shi ɗakin shi na gyara mishi. Nace mishi Mummy ta hana tunda ba ni nake ɓatawa ba da ze ce na gyara. Shine yace ze sa a kore ni daga gidan idan ban mishi aiki ba kuma ze faɗawa Mummy na mishi rashin kunya har na zage ta. Bayan na tafi dakin shi shine ya rufe ɗakin yace na cire.......” Shiru Rahama tayi kuka na cin ƙarfin ta. 
Squeezing kafaɗar ta nayi softly ban ce komai ba. Idanuna da duk jikina sun yi sanyi ina jin burden a cikin zuciya ta. 
Rahama ta jima sosai tana kuka har na fara jin tsoro kar wani ɗan gidan ya taho. “Me ya faru? Ya miki wani abun ne? Zaki iya min magana”
  “Yace na cire kayan da nake sanye dasu yace na hau gadon shi shine ya fara taɓa min jiki”
Shiru nayi ina son samun wuri na ɗaura jikina akai amma haka na daƙe nace “Fyaɗe?”
Girgiza kai tayi tace “Ya dauko wuƙa yace ze cire min kai idan ban yi abinda yace ba daga baya yace wa mummy ni ce na kashe kaina”
     “Khalifa ya miki duk haka?”
Gyaɗa kai tayi nace “Babu ƙarya a cikin zancen ki?”
Girgiza min kai tayi. “Wallahi Yaya duk yayi min waɗannan ban mishi ƙarya ba. So nake a maidani gida ba zan iya wannan aikin ba. Dan Allah ki sa baki inaso na koma gida dan Allah”
     “Ya isa” nace tare da share mata hawayen ta “Komai ze dawo daidai. Zan sa bakina akan lamarin ki, kar ki damu” 
Kafin Rahama tayi magana se ga Zaid. Hannuna na sauke akan kafaɗar ta. Kallon mu yake da alamar tambaya yace “Idan kin gama mu tafi”
Hannun Rahama da na riƙe sosai na saki na bi bayan Zaid. A cikin mota babu wani me cewa wani abu har muka isa gida. 

Sallah Maghrib nayi ina nan zaune ina tunanin yadda zan yi magana akan Khalifa da Rahama. Loyalty na ya rabu biyu to an oppresor whom his dad helped me find a job and the oppressed, whom it's my job to protect. Kuma da nice na tura ƴa ta zuwa wani gari aiki daban domin samu, zan ji daɗi yaron gida ya mata irin wannan abun?
Sallah Isha ce ta riske ni a inda nake. Isha'in nayi ina nan zaune ina nazari har Zaid ya dawo ya same ni. 
  “Me kike tun ɗazu anan ana neman awa biyu”
Shiru nayi na kalle shi ban ce komai ba. 
“Lafiya dai ko Hadiza? Naga tun chan kin zama wani iri har dawowar mu gida”
     “Dan Allah ka zauna”
A gefen gado ya zauna yana kallo na. 
“Ban san ya zaka ɗauka wannan abun ba, Zaid. Amma kayi tunani, idan ƴar ka ce, zaka ji daɗi idan ta faɗa maka magana irin haka ko kuwa idan ta faɗa maka zaka zauna baka ɗauki kowane irin mataki ba”
 “Menene?” ya faɗa yana ƙara maida hankalin shi akaina jin abinda nake cewa
   “Maganar Rahama ce” nace tare da kallon cikin idanun shi na sauke idanuna a nashi “Rahama ce da Khalifa. Tace min yasa ta cire kayan ta kuma ya taɓa jikinta” na faɗi mishi ina jin nauyin faɗa. Ko ba komai, duk abinda Khalifa yayi, ɗan uwan shi ne. 
Girgiza kai yayi ya tashi “Shi Khalifan?”
“Tace ba ƙarya take mishi ba, Zaid”
     “Ban yarda ba”
    “Wallahi idan ka duba ta zaka san yarinyar nan na cikin firgici, Zaid”
Ƙara girgiza kai yayi yace “Dama ina mamaki da kika ce kwana biyu bamu tafi mun gaida su Abba ba. Dama abinda kike so ki je kiji kenan, Hadiza? Me yasa bata faɗawa Shahida ba se ke? Kuma me yasa ba'a gane cikin yanayin da take ba se ke zaki gane, Hadiza? Dan Allah ki dena wannan maganar saboda ba gaskiya ce ba”
   “I'm a Barrister, Zaid, in case you forgot”
“Okay. What do you mean?” 
Nan take ɓacin rai ya bayyana akan fuska ta. Shima Zaid ran shi ya ɓaci saboda kawai na faɗa mishi abinda ƙanin shi yayi wa ƴar aikin su. Shikenan idan mutum bashi da galihu ba za'a yarda da maganar shi ba? Duk tsawon lokacin da suka yi da ita ta taɓa kawo musu irin wannan maganar ba se yanzu ba? Me yasa ba zasu duba ba to? 
   “Saboda tana ƴar aiki ba za'a yarda da ita ba? Ko ka mance ranar da muka tafi gidanku muka ji Mummy na mishi faɗa akan ya dena sa ta aiki a cikin ɗakin shi?”
   “Da wannan kika dogara, Hadiza? Dan Allah ki dena wannan maganar kar ki tarwatsa mana gida”
Tashi tsaye nayi “Ban yi tunanin wannan daga wurin ka ba. Kayi tunani idan ƴar ka ce zaka faɗi haka ba tare da kayi bincike ba”
   “Let's drop this and I want you to stop talking about it, please Hadiza”
Ban san lokacin da na ɗaga murya ta ba, raina na ɓaci nace “I'm reporting sexual harassment of your housemaid by your brother to you and you're telling me to drop it, Zaid. Are you serious? I'm ashamed this is the family I'm married into”
Tsaye yayi yana kallon outburst ɗina. Ina faɗa mishi haka na wuce ɗakina. Rufe kofa nayi nasa jikina a jikin bango na idanuna. Hawaye masu zafi na fara ji suna bin kuncina.  
Hawayen dake bin kuncina na share da hannuna na dawo na zauna a bedside tunani kala-kala na yawo a cikin raina. Wayata dake kan table na bedside lamp nake kallo kamar zan ɗauka na kira Yaya Hauwa na faɗa mata amma kuma nayi tunanin against it saboda idan na faɗa mata tayi treating abun kamar yadda Zaid yayi, I'll be outraged and can draft a sheet of sexual harassment a cikin gidansu wanda zasu ga ban musu adalci ba kuma bani da wani evidence against it. Kuma drafting sheet be ma taso ba tunda ban sanar da wanda yake ɗauke da gidan ba yayi treating abun as untrue and nonsense. 

Matsalar irin waɗannan abubuwan, idan ba'a fara tackling nasu ba, sune ke zama abinda ba zaka iya controlling nan gaba ba. 

Kwana biyu akan zancen da na yiwa Zaid yasa bama shiri sosai dashi. Yayi keeping distance nashi and he hardly talk. Kuma naga alamar ba ze yi maganar abinda na faɗa mishi ba kuma na faɗa mishi ne dan ya jawa ƙanin shi kunne amma ba ze yi ba saboda be yarda ba, zan tarwatsa musu gida ne. 
Zama nayi a carpet na ɗakina ina tunanin kiran Mummy na faɗa mata tunda yaron ta ne ta mishi magana. Tunani nayi against it na fara rubuta saƙo ina faɗa mata abinda ke faruwa. Bayan na gama rubutu na tura mata da sanin komai ze iya faruwa. 
Ina gama rubutun naji zazzaɓin da nake fama dashi kwana biyu yana ƙoƙarin dawowa. Babu abinda nake tunani ina da se juna biyu. Kuma idan ya tabbata shine nasan yayi wata uku yanzu. A farkon sanin shigar cikin idan shine, na kudirtawa raina zan iya barin shi tunda na gama magance matsalar gidana amma yanzu saboda wannan maganar na sexual harassment da na faɗa wa Zaid kuma yaƙi komai akai yasa ina tunanin zan zubar dashi saboda fushin da nake dashi da kuma jin haushi. 
Tashi nayi na fita zuwa pharmacy na siyo pregnancy test strip. Ban fara dubawa ba se da na duba waya ta ban ga Mummy tace komai ba. Shiga bathroom nayi na duba ko da gaske akwai juna biyun. Layi biyu ya nuna min wanda ya tabbatar min da hasashen da nake akan juna biyu. Discarding pregnancy test strip ɗin nayi na fito daga banɗaki. Wayata na fara dubawa. Kiran Mummy na gani wanda ya nuna min ta karanta saƙo na. Zuciya ta ce ta fara bugawa saboda ban san abinda tazo dashi ba. 
Ban kira ta domin naji abinda zata faɗa ba. Zaunawa nayi se ga Zaid ya shigo ɗakina cikin fushi a fusace. “Ni nace kije ki faɗawa Mummy abinda Rahama tace miki Khalifa yayi mata? Ni na tura ki Hadiza?”
Blinking idanuna nayi sau ɗaya na tashi tsaye. “Ba kai bane ba”
   “Ko menene dai yanzu kin jawo min zagi hankalin ki ya kwanta ko?”
     “Wani irin zagi kake magana, Zaid? Daga faɗin gaskiya”
  “Kina da evidence akan gaskiyar da kike faɗa? Waya san gaskiya kike faɗa ko ta shirya miki ƙarya saboda kina Barrister kin yarda da ita”

“I hate that you're a coward, Zaid. You're a coward”
Tsaye yayi yana kallona kamar be ji abinda na faɗa ba. “Ki wuce mu tafi Mummy na neman ki”
Tsaye nayi bani da niyyar wucewa mu tafi. “Idan kuma baki tafi ba, me kike so tace?”
Fuska ta neutral na ɗauka mayafin abaya ta muka wuce gidansu. 

Gaida Mummy kawai nayi ta fara magana “Kina da evidence akan abinda kike zargin yaro na?”
Cikin girmamawa nace “Mummy.,...ki kalla Rahama kiga yadda duk ta koma cikin frigici”
   “Yaushe har kika zo gidannan da har zaki ce kinsan yadda kowa yake?”
Shiru nayi na sunkuyar da kaina domin girmamata a matsayin ta na mahaifiya gare su. 
“Ga Yaya Hauwa ga Shahida, mun zauna da ita shekara da shekaru amma ta rasa wanda zata faɗawa damuwar ta se ke da kika taho shekaran jiya?”
Shiru nayi baƙin ciki na ƙara haɗe min a cikin zuciya ta. 
“Kuma dake za'a haɗa a yiwa yaro na ƙazafi?” Mummy tace ta kalla Zaid “Ka faɗawa matar ka ta fita daga cikin harkokin gidana ta duba na gidanta. Bana son shishshigi”
Zaid be ce komai ba ta ɗaga murya ta kira Shahida. Bayan Shahida ta taho tace ta kira mata Rahama. Rahama aka kira jikinta duk tsoro idanunta sun chanja. 
   “Ke da yake kina munafuka kina son ki ɓatawa mutane suna shine zaki je kina faɗawa Hadiza magana? Me ya faru dani da Yaya Hauwa da Shahida da ba zaki faɗawa ba? Saboda kin san ƙazafi ne karya kike ko?”
  “Wallahi Mummy ba ƙarya nake mishi ba” Rahama na faɗin haka, Zaid ya fita daga ɗakin Mummy. 
“Khalifan ne ze ce ki cire kayan ki? To idan kika cire kayan ki me a cikin jikinki da ze gani? Zan wawwatsa miki mari se kin suma nan wurin” Mummy tace cikin faɗa muryar ta na ɗagawa bisa ga ɗazu. 
Kuka Rahama ta fara. Kukan ta yana shiga cikin zuciya ta. 
   “Cewa kika yi kina son ki tafi gida kina ji a jikinki mamar ki ba lafiya ba. Na kira wacce ta kawo ki ta kira number maman ki number baya shiga shine zaki muna ƙazafi ki lalatawa yaro na suna?”
Girgiza kai Rahama ta fara yi kuka ya hana mata magana. Bani da evidence na abinda Rahama tace banyi tsammanin wannan abun ya kai haka ba. Me ze hana ta zama alert ga abinda yake faruwa gidan ta? Kuma tasan yarinyar nan tun ba yanzu ba. Tasan idan ƙazafi take ko ba ƙazafi ba. 
   “Mummy kin ce kinsan yarinyar nan tun ba yanzu ba. Idan da gaske kin san ta, zaki san abinda zata iya yi da wanda ba zata iya ba. Kin san yadda yanayin ta yake. Ta taɓa cewa tana so taje gida kuma duk ta firgice haka? Ya kuke so ku danne gaskiya ba tare da bincike ba saboda kawai yazo akan naku kuma kuna ganin naku yafi ƙarfin wacce ke zargin shi?” Raina ya ɓaci sosai na ƙara da “Maganar sexual harassment muke anan fa. Da Shahida ce ta kawo miki wannan ƙarar zaki tsaya ki ce ƙazafi ake yiwa wanda ta kawo ƙarar shi? Okay wannan saboda ba taki bace?”
   “Ni kike faɗawa maganganu irin haka, Hadiza? Zaid ne ya baki dama?”
  “Maganganu fa Mummy? Me yasa kowane abu da kike gani kamar laifi se ki ce Zaid? Zaid ne ze sa min magana a cikin baki na? I'm an adult. I don't operate base on his ideas. Kuma maganar Rahama, idan da gaske adalci ake so ayi ba share magana ba. A kira Khalifa a haɗa su su biyu suyi rantsuwa da Alkur'ani akan abinda yake faruwa in har dai suna tsoron Allah, ba aba mutum ɗaya gaskiya ba aba wacce ta kawo ƙara rashin gaskiya. Wallahi Mummy idan har dai baku yi adalci a tsakaninsu ba, ina ji miki tsoron abinda ze faruwa nan gaba. Ba wannan abun ze tarwatsa muku family ba, abinda ze faruwa nan gaba shine ze tarwatsa muku family ya tarwatsa miki yaron ki”
Tashi tsaye nayi na fita daga ɗakin ta na wuce compound a parking lot. A chan na samu Zaid a cikin motar shi. Shiga nayi muka wuce gida ba tare da kowa yayi magana ba.