Zaren Rayuwar Mu

BABI NA ASHIRIN DA BIYU

by @zainabb

Zaren Rayuwar Mu 

WASHEGARI DA SAFE ranar hutu ne. Dama ina da niyyar zubar da juna biyun da nake ɗauke dashi. Bana buƙatar wannan cikin ganin abinda Zaid yayi harda familyn shi. Da safen ban fito ba kuma nasan Zaid ba ze taho ya duba ni ba. Pills na abortion na haɗiya ban tsaya wani tunani ko nayi ko kar nayi ba. Ina nan zaune ina jiran na fara bleeding se gashi ya taho da ƙarfin gaske wanda yafi wancan sosai ba kaɗan ba. Kaina ne naji yana juyawa sosai nasan naji wayata notification ya shigo ciki amma ban samu karantawa ba saboda ban san inda kaina yake kuma ba. 

Ahankali nake buɗe idanuna ina kallon surrounding ɗina. Farin fenti nake gani ta ko ina. Labulen dake ciki ma fari ga drip a gefe na na jini da fluid, hannuna ansa min duka biyun. Ƙafafuwana naji sun min nauyi sosai bana iya motsa su. 

I just look across me with my heavy eyes naga Zaid zaune a wurin ƙafafuwana. Rufe idanuna nayi na buɗe. Hawaye sun cika min idanu. Nasan ba Zaid ba, duk wanda yasan ankawoni asibiti yasan abinda yake faruwa dani, yasan abinda nayi. 
  “Kin tashi, Hadiza” Zaid ya faɗa min with his eyes that looks so distant. Nasan be san abinda ze yi ba. Be san abinda ze min ba, be san abinda ze ce min ba. 
Tashi yayi ya fita daga cikin ɗakin ba tare da yace min wani abu ba. Dawowa yayi tare da nurse da doctor. 
Duba vitals ɗina nurse tayi, doctorn kuma, yana kallo na yace “Wankin mara zamu miki, Hadiza. Dama muna so ayi stabilizing naki first ne. Kina zubar da jini sosai shiyasa kuma cikin be zube duka ba”
Blinking nayi ina kallon shi hawayen da suke cikin idanuna suka zubo. 
Shirya ni suka yi aka wuce dani OT. Zafin komai ban ji ba saboda anesthesia da aka min har aka gama wankin maran aka dawo dani a ɗaki. 

Ina jin gajiya da dizziness harda cramping a lower abdomen nawa saboda irin matalsar dana samu wurin zubar da juna biyun da na samu. 

Ina nan kwance ban san lokacin da bacci ya ɗauke ni ba. 
Tashin da na ƙara yi ne naga Zaid tare da Yaya Hauwa. Nurse dake nan ta chanja min pad dake jikina tace naci abinci domin na sha magani. 
Kayan tean da Yaya Hauwa tazo dashi ta haɗa min tea. Bayan ta haɗa tean ba tace komai ba ta fita. Zaid da kanshi ya taso ya fara bani tean. Ban wani sha dayawa ba na nuna mishi ya ishe ni. Bayan mun gama ne Nurse ta shigo ta bani magani. 

Ina nan kwance Zaid na zaune a wurin ƙafafuwana muka ji an buɗe kofa tare da yin sallama. Rufe idanuna nayi na buɗe. Mummy ce da Shahida da Muhammad da Zainab harda Abbansu. Ya jiki suka min nayi nodding kaina. 
   "Zaid kai ke jinya ko? To Allah ya bada lada yasa albarka”
         “Amin Abba”
Rufe idanuna na sake yi ban buɗe ba har se da naji an rage a cikin ɗakin. Koda na buɗe Shahida ce tsaye daura dani. 
      “Rahama fa?” na tambaya ahankali murya ta bata fitowa sosai
       “Rahama? Ta koma garinsu jiya dama lokacin auren ta ya matso”
Daɗi naji a cikin raina. 
   “Yaya wannan ƴar yarinya za'a yiwa aure. Ina ita ina aure fisabilillah?”
Murmushi nayi ban ce komai ba. Daga gani kuma wataƙila ba wanda yasan juna biyu na zubar. 
Dawowa suka yi zasu wuce. Nan suke addu'ar Allah ya kawo wani rayayye. Amma bayan sun ce haka Mummy tana kallo na ta kalla Yaya Hauwa da itama ta dawo cikin ɗakin tace “Nima juna biyu na ya taɓa zubewa kuma an min wankin mara amma ban wahala irin haka ba. Naga ita ko motsi bata so tayi bale magana”
    “Mummy kin san kowa da jikin shi” Shahida tayi saurin faɗa. Yaya Hauwa dai ba tace komai ba saboda ba zata taɓa iya faɗin wata magana da zata kare Hadiza ba. 
   "Allah ya bada lafiya Hadiza”
Murmushi na yiwa Abba tare da gyaɗa mishi kaina. 

Ba ciwon da nake ji bane yasa bana iya magana ba. Emotional shock da nake ciki ne ya hana min magana da kunyar abinda na aikata har Zaid ya sani. 

Da dare ma Shahida da Abba suka ƙara dawowa. Da zasu tafi ya bar Shahida ta tsaya ta kwana a wurina ita kuma Yaya Hauwa ta wuce gida. 
Da daren Zaid ya dawo min da wayata daga gida. Anan ne naga saƙon shi wanda shine last notification da naji ya shigo wayata kafin na suma. Saƙon nashi haƙuri yake bani for not standing up for Rahama rather he was protecting his brother. Be faɗa min dalili ba amma nasan be wuce alaƙar dake tsakanin shi da ɗan uwan shi ba. Nasan yana da wahala mutum ya tafi against his own for someone that doesn't belong to him. And that too, a maid. But what's justice if you can't go against your own for justice to prevail? 
Ganin saƙon shi kuma nayi dana sanin zubar mana da juna biyun da nayi. Me yasa ban duba irin soyayyar da nake mishi ba na bar baby na? Me yasa ban duba shi kanshi ba da duk alhairan shi da kuma haƙurin da yayi dani na bar mana babyn mu? Kenan se shine ze yi haƙuri da dabi'una ni ba zan iya haƙura inda ya kuskure ba?

A kwana na biyu ana monitoring nawa a asibiti saboda jinin da na zubar. Zaid baya min magana nima bana mishi amma yana nan asibitin a kodayaushe. 
Ina zaune akan gado yana tsaye a drawer yana haɗa min tea nace “I read your text, Zaid”
Be ce min komai ba amma nasan yana saurare na. 
    “Didn't you know of a verse that says whenever you speak, speak justly even if a near relative is concerned?”
Ban san lokacin da aka buɗe kofar ɗakin asibitin ba se muryar Yaya Hauwa da naji tana cewa “Wacce ta zubarwa mijinta juna biyu har sau biyu take magana akan duk kayi magana, kayi magana wacce ke cike da adalci koda ta shafe makusancin ka” Yaya Hauwa ta faɗa ta min wani irin kallo ta sake ce “Don't you know you're mocking your own self? What disgust!”
Abinda Zaid ke yi ya dena ya juyo ya rasa abin faɗa. 
  “Wallahi idan nine kai Zaid, wannan matar ba zata koma gidana ba. Dama na faɗa maka ban yarda da ita ba. She looks quiet and peaceful but she's not. Zuciyar wannan matar taka bata da haske taci amanar ka kuma taci amanar dukan mu”
  “Dan Allah Yaya kiyi haƙuri kiyi shiru dan Allah”
  “Shut up my friend!” Yaya Hauwa ta yiwa Zaid tsawa “Kai baka san ciwon kanka ba ko? Wane irin soyayya ne kake mata har haka da baka so a faɗa maka laifin ta? Tunda naje gidanku tana amarya muna magana akan menene favourite abincin ka ta min shiru nasan auren ku yana da matsala. Yanzu kuma ta ƙara nunawa ta zubar maka da ciki biyu ba ɗaya ba. And you're here saying ayi haƙuri. Ni ce zanyi haƙuri da halayen ta? Kaine zaka cigaba da zama cikin baƙin ciki idan baka sallame ta ba. Kuma wallahi ni ba zan sa idanu ta maida ka shashasha ba”
  “Akan dalilin me zata zubar maka da ciki? A waje ta same shi ne da zata zubar? Ko kai ke bata magani ta zubar baku so? Idan kaine se kayi magana na dena ɗaura mata laifi. Amma haka kawai saboda wani ra'ayi nata daban zata dinga zubar maka da ciki, akan dalilin me? Ciki biyu ba ɗaya ba. Inada tabbacin idan ta samu wani zata ƙara zubarwa ne. Kuma bata son cikin take yadda ku kasance tare. Wai wace irin mace ce kaje ka auro, Zaid? Does she even love you? This is the question you should ask yourself, does she even love you because I believe if she loves you, she won't abort your two pregnancies kuma waya sani ko ba biyu ta fara zubarwa ba? Who knows?"
Juyowa tayi daidai ni tana kallona tace “Wallahi kina ganina nan ne kawai saboda wannan yaron Zaid. Da ba saboda shi ba, se kowa yaji a familyn mu ba ɓari kika yi ba, ciki kika zubar har sau biyu kuma ba zaki ga kowa ba se shi kaɗai da yaje Kaduna ya kwaso ki kuma shi da yaji ze iya da mugayen dabi'un ki. Zaid is a good man menene makusar shi da zaki mishi irin wannan azabar? Ko kyawun banza be fi ki ba? Dame kika fi shi? Ba saboda ina Yayar shi ba, amma ban san wani abu na Zaid ba face alhairan shi. Nasan baya miki zalunci a zamantakewar ku, ina ma ya iya zalunci bale ya miki? Amma gaba-ɗaya ke hankalin ki baya kan auren ku and because he's very stupid he keeps on tolerating your stupidity and rubbish attitudes. To wallahi idan ba'a dena wannan ba, I'll go and tell Abba everything shi idan yace ka rabu da ita kar ka rabu da ita tunda rayuwar ka tana hannunta”
Shigowar Doctor a ciki ne yasa Yaya Hauwa ta fita daga ɗakin. Hadiza kuwa idanunta sun fara zubar da hawaye tana danasanin duk wani abu na rashin kyautuwa da ta yiwa Zaid saboda tasan babu ƙarya a cikin zancen Yaya Hauwa. 
   “Ku yi haƙuri. Rayuwar auren se ana haƙuri”
Murmushi me ciwo Zaid yayi ya gyaɗa wa Doctor kai. “You're getting discharged today. Nasan Hadiza ta gaji. Allah ya bata lafiya”
   “Amin doctor mun gode”
Dama kayan su a haɗe suke suna tsammanin sallamar a yau Doctor ya ƙara duba ta ya musu sallama. 

A cikin mota babu me magana a cikinmu har muka isa gida. 
Bayan mun isa ne na wuce banɗaki nayi wanka da yake da safe ne nasa doguwar riga na lace na zauna a ɗakina. Maganganun Yaya Hauwa na dawo min a cikin kaina. Maganar abortion da nayi kuma har sau biyu yana zama wani irin forbidden talk tsakanina da Zaid domin har yanzu be min maganar shi ba. Kaina naji yana min wani irin ciwo amma ya kamata naje wurin Zaid muyi maganar da zamu yi. Bana so yayi bottling komai a cikin ran shi. I want him to vent if needs be. I want him to yell at me. I'll accept everything he sends my way. 

Tashi nayi na wuce ɗakin shi na ɗaura hannuna akan gefen kaina. Nasan ba ciwo ne nake ji physical ba se de emotional one. 
Tsaye nayi ina kallon shi ya juya baya. Yana juyowa ganina tsaye yace “Hadiza, lafiya? Zo ki zauna”
Zama nayi ahankali. “Jikin har yanzu?” yace yana kallona da tausayin da ba ze iya ɓoyewa ba. 
“A'a, naji sauƙi, alhamdulillah”
Shiru yayi be sake cewa komai ba se gani nayi yana so ya bar min ɗakin. Da sauri na tashi tsaye nace “Dan Allah kayi haƙuri Zaid”
Tsayawa yayi jin abinda nace. “Wani irin haƙuri, Hadiza?”
“Nasan na maka laifi. Inaso ka bani wani chance, Zaid. It'll be the last chance, Zaid. I promise”
Juyowa yayi gaba-ɗaya jikin shi na duba na ya dawo kusa dani. “Me na miki, Hadiza? Why do you want to break me? What have I done wrong to you? Is my only fault loving you, Hadiza?”
Hawaye suka zubo min a fuska ina jin ƙaunar shi na ruruwa a cikin zuciya ta kuma ina jin tsoron kar ace ya dena sona ze turani gida. 
     “Wannan ba abun kuka bane ba. It's so frustrating when you cry while you're not supposed to. It's frustrating when you cry while you're not the victim, Hadiza. Just stop those crocodile tears”
   “Dan Allah kayi haƙuri Zaid. Dan Allah”
          “Why?”
       “I'm sorry”
Fuskar shi neutral ko motsawa be yi ba yace “Why, Hadiza? You have a reason. Why?”