Page 19
SAWU BIYU
BY
Khadijah Sulaiman
Young Talented Writers Association (YOTA)
Book 1
Page 19
Sadauki ya ƙarasa bakin gado ya ajiye towel ɗin hannun shi ya shige toilet,sai da yayi wanka sannan ya fito ya hau shiryawa cikin uniform.
Bilal da shima ke tsaye kusa dashi bayan ya fito daga wanka yace"me ya haɗa ka da wancan Cadet ɗin ne?"
Sadauki ya ɗan juyo ya kalle shi yace"nothing serious,nayi mistaking ɗin shi da wani ne,ashe bashi bane".
Bilal ya gyaɗa kai alamar gamsuwa ya cigaba da shirin shi.
Daga nan suka wuce breakfast, bayan sun gama kowannen su ya tafi class.
A hanyar su ta dawowa suna tafe suna hira su huɗu idan ka cire Sadauki dake duba wani ƙaramin handbook.
Jin yayi karo da mutum yasa ya ɗago da sauri,ta watsa mishi harara tace"ba kada ido ne?"
Sadauki ya kalleta daga sama har ƙasa yace"dani kike?"
"Akwai wanda ya bige ni ne bayan kai?"
Ta zagaye su ta bar wurin ya bita da kallo.
Emmanuel ya fashe da dariya yace"my guy dey vex".
Bilal ya taya shi dariyar yace"who see wetin I see? beauty dey cry".
Emmanuel ya bashi hannu suka tafa yace"na true my guy you get eye".
Adewale dai na gefe bai sa musu baki ba, Sadauki ya watsa musu wani kallo cike da takaici ya bar wurin.
Washegari kamar dai jiya haka suka fita da sassafe.
"Cadets ! Warm up".
"Twenty push up".
"Yes,Sir".
Bayan sun gama suka fara jogging,sai da su kayi kaman five rounds sannan aka sallame su.
Ya kai hannu zai ɗauki goran ruwan shi dake gefe ta kai nata hannun.
Ya ɗago a hankali ya kalleta,ya ɗaga mata gira alamar lafiya ta nuna mishi goran da ido tace"nawa ne".
Sadauki ya ɗauke kai daga kanta ya maida kan goran sai yaga ashe ba nashi bane,a hankali ya sake mata goran ya bar wurin.
Bilal yayi dariya ya ba Emmanuel hannu suka tafa yace"just watch".
Ya ƙarasa wurinta yace"hey beauty,I'm Bilal".
Ta ɗan kalle shi ta basar har zata gifta sai kuma tace"Adeyemi Idayat".
Emmanuel ya ƙaraso ya bige shi a ƙeya yace"hey Cadet,focus".
Bilal yayi dariya yace"yeah,sure".
A haka suka cigaba da rayuwa,da sassafe zasu tafi training,idan sun dawo suyi wanka su wuce suyi breakfast daga nan su tafi classes.
Cikin ƴan watanni jikinsu ya fara canzawa saboda irin training da su keyi kullum.
A ƴan kwanakin suka fara Obstacle course,duk su huɗun na tsaye sun zubawa dogon bangon ido mai ɗauke da tayoyi.
Emmanuel ya haɗiye wani abu daya tokare mishi maƙoshi yace"Bilal,tell me were just here to watch".
Bilal bai san sanda ya fashe da dariya ba yace"Yes definitely".
Sadauki ya juyo ya musu kallo ɗaya ya ɗauke kai ya cigaba da kallon Obstacles ɗin.
Instructor dake bayansu yace“Cadets! Prepare for the obstacle!”
"On my command!".
“Go! Over the wall!”
Bilal ya matso dai dai kunnen Sadauki yace"idan ban sauko da rai ba ka gayawa mahafiyata ta yafe min".
Sadauki ya watsa mishi wani kallo yace"You should be serious for once Bilal".
"Keep moving!"muryar instructor ta ƙara karaɗe wurin.
Zufa kawai suke haɗawa,wasu tun kafin su kai koina jikinsu ya fara rawa.
Idayat dake biye dasu Sadauki ta miƙawa Sadauki hannunta ganin tana neman zamewa ya ɗauke kai tamkar bai ganta ba.
Bilal ya miƙa mata nashi hannun yace"here Adeyemi".
Ta ɗago ta kalle shi ya gyaɗa mata kai,tasa hannunta cikin nashi ya taimaka mata ta haura.
Bayan sun sauko suna tsaye ta ƙaraso wurin tace"thank you Bilal,kana da good heart ba kaman wasu ba".
Sadauki yayi kaman bai jita ba,Emmanuel da Bilal suka yi dariya Ademola yayi murmushi don shima ta bashi dariya.
Bayan sati ɗaya aka bada wani guntun assignment, Instructor ɗinsu yayi dividing ɗinsu into various groups yace suyi analyzing in a case that suna filin yaƙi su nuna hanyar da yafi dacewa da zasu sami kansu a wurin da suke hari ba tare da an sami matsala ba.
Bilal da Sadauki da Idayat da wasu guda biyar sun kasance group ɗaya, kowanensu yayi shiru yana kallon map ɗin cike da nazari.
Can Aisha ta ɗora hannunta a wani wuri tace"ga hanyar da ya kamata mu bi,shi yafi kowanne hanya sauƙi".
Ba tare da Sadauki ya kalleta ba yace"hanyar da yafi kowanne sauri dai ba dai sauƙi ba".
Bilal ya kalle shi yace"saboda me?"
Ya dora ɗan yatsan shi kan wurin yace"wurin yayi ƙasa sosai, idan anyi ruwa mai ƙarfi zai bada wahalar bi, sannan kalli nan".
Ya sake kai hannun shi wani wuri yace"akwai ciyayi da yawa zai hana mu ganin gabanmu sosai".
Bilal ya gyaɗa kai alamar gamsuwa,Aisha ta kalle shi tare da cewa"amma wannan hanyar zai iya sa mu kara kusan awa ɗaya ba tare da mun isa ba".
"Is better mu isa late da mu sami matsala a hanya".yayi maganar tare da kallonta cikin ido.
Ta mishi wani kallo ta ɗauke kai,bai ƙara cewa komai ba ya ɗauke ido daga kanta.
Ranar da za'a yi presentation aka ce mutum ɗaya zai fito daga kowanne group as a group leader.
Duk yadda Sadauki yaso ya doje sai da suka fi ƙarfin shi.
Shine kusan ƙarshe,ya fito bayan an haɗa map reading ɗinsu da projector.
Tunda ya fara bayani hall ɗin yayi tsit baka jin karar komai sai muryar shi dake tashi cike da natsuwa.
Officers dake zaune kallon shi kawai suke cike da birgewa ganin yadda yake bayani dalla dalla tamkar wani babban soji.
Yana kai ƙarshen maganar shi hall ɗin ya ɗauki tafi, Colonel Musa Garba dake zaune a wurin ya karɓi mic yace"Your name?"
"Umar Muhammad Sadauki Sir".
"Your presentation was wonderful Cadet Sadauki I love it,you really access the map excellently try to keep it up,for that I'll call you Falcon".
Sadauki yayi murmushi yace"thank you Sir".
Tun daga ranar Sadauki yayi suna a Academy,daga kan Senior Cadet,officers da Cadets kowa ya san shi.
Idan ka kira Umar ba lallai a gane ba amma kana cewa Cadet Sadauki ko Falcon za'a nuna maka shi.
Officers musamman Colonel Musa Garba na ji dashi sosai saboda hazaƙar shi da jajircewar shi.
Suna tsaye bayan sun gama training kowannen su na share zufa Bilal ya hango Idayat,da ƙarfi ya ƙwala mata kira.
Sadauki ya watsa mishi harara yace"me yasa kake son gayyatar mara kunyar yarinyar nan ne Bilal?"
"Rashin kunyar me ta maka saboda Allah,kai dai ka cika fitina Sadauki".
Ademola ya share zufan dake gangaro mishi yace"ka san yaren mu basa ɗaukan nonsense,I think dalilin shi kenan na tunanin rashin kunya take mishi."
Emmanuel yace"ai hakan shi yafi,shi yasa take burge ni honestly,very brave lady".
Bilal ya ƙara da cewa"kuma gata soja,how will you expect soja ya ɗauki rainin wayo".
Dai dai nan ta ƙaraso wurin, Sadauki ya juya ya wuce block ɗinsu.
Bilal ya mata murmushi yace"kiyi hakuri da halin Falcon,you know how he behaves".
Tayi guntun murmushi bata ce komai ba.
Tsakanin Sadauki da Ɗahiru sai dai kallo daga nesa tun ranar da suka fara haɗuwa,koda wasa idan ya hango Sadauki yake canza hanya da saurin gaske,duk Sadauki na lura dashi amma ya fita hanyar sa.
Zamansa a cikin wurin ya ƙara mishi wani irin natsuwa wanda hakan ke burge mutane da dama,wasu ko kallon mai girman kai kawai suke mishi saboda rashin son maganarsa da hayaniya.
Yawancin lokuta Bilal da Emmanuel ke takura rayuwar shi da surutu don Ademola bai cika magana ba shima.
Sun zama zaratan samari masu jini a jika da ƙarfin samartaka da kuma yanayin training da ɗaga ƙarfuna ya ƙara huda ilahirin jikin su.
Da wani irin ƙwarjini mai girman gaske Sadauki ke gudanar da rayuwar shi,za ku iya yin wuni guda tare dashi ba tare da kaji sautin muryar shi ba.
Sanye yake da singlet navy green daya bayyana damatsen hannun shi sai three quarter iya gwuiwa shima navy green,jikin shi ya jike gabaɗaya da gumi hannun shi riƙe da ƙarfen da ya kai kusan mintuna arbain yana ɗagawa.
Ya zama cikakken saurayi dake cikin ganiyar shekarun samartaka.
Bilal ya sake ɗagowa ya kalle shi yace"dan Allah ka ajiye ƙarfen nan na gaji wallahi".
Emmanuel ya taɓe baki yace"You know that won't work, wannan abokin naka kamar bai san zafin jikin ba".
Bilal ya gyaɗa kai yace"nima na fara tunanin hakan gaskiya".
Idayat ta karaso wurin idonta kafe a kan Sadauki,ya ajiye ƙarfen hannun shi ya ɗauki towel dake kusa dashi ya hau goge jikin shi.
"Bani ruwan nan Bilal".
Idayat ta ɗauki goran ruwan kasancewar tafi Bilal kusa da goran ta karasa ta miƙa mishi.
Ba tare da ya kalleta ba ya wuce ta ya bar wurin,duk suka bishi da kallo.
Bilal ya ɗauke idon shi daga kan Sadauki ya kalleta,harga Allah ba ƙaramin tausayi take basu ba ganin ta ɗauki dala ba gammo.
Ganin hawayen dake cike a idonta yasa shi zuwa kusa da ita yace"kar kiyi kuka Idayat,have patient,this is a matter of time".
Ademola da tun ɗazu bai ce komai ba yace"Adeyemi,forget about that guy and focus on what brought you here".
Emmanuel yace"idan baya so ni ina so".
Idayat ta juya ta bar wurin duk suka bita da kallo.
A ɗaki suka tarar da Sadauki ya kwanta yana kallon rufin ɗakin bayan ya fito daga wanka.
Bilal ya zauna kusa dashi yace"me yasa kake haka ne Sadauki?"
Bai buɗe ido ba yace"me nayi?"
Da wani irin takaici yake kallon shi jin tambayar rainin wayon da yake mishi.
Ya dai daure yace"bana jin ɗadin abinda kake yiwa Idayat ko kaɗan,menene laifin yarinyar nan dan Allah?ruwa ta baka ɗazu kayi tamkar baka ganta ba"
Ya tashi zaune cike da ɓacin rai yace"ban gane wani irin tambaya kake min ba Bilal,na aiketa ta bani ruwan ne?ban aike ta ba,da kake cewa meye laifinta bari in baka amsa,rashin kamun kai,na tsani macen da bata san darajar da Allah ya mata ba."
Baki buɗe yake bin shi da kallo,ya ɗauke kai daga kallon shi kafin a hankali tace"amma baka mata adalci ba Sadauki,wani rashin kamun kai kake magana a kai,ka taɓa kamata da wani namiji ne ko me?
Idayat bata shiga harkar maza a Academy ɗin nan kaima ka sani idan ba mu ba,kuma tana da addini dai dai gwargwado".
Sadauki ya miƙe tsaye ya nufi wurin kayan shi yace"ai kaji irinta,ku ɗin maharramanta ne?"
Bilal ya miƙe tsaye yana kallon shi rai ɓace,Ademola da Emmanuel suka riƙe shi da sauri ganin yadda ran shi ya ɓaci.
Sadauki yayi guntun murmushi da ba kasafai yake yi ba ya fita.
Sadauki bai cika komawa gida ba ko da sun sami hutu,ya gwammace ya zauna cikin Academy har wasu suje su dawo tunda hutun da suke samu ba wani mai yawa bane.
Wani hutu da ya tafi ya sami labarin an kai Zarah Boarding School a Abuja,hakan yasa tun zuwan shi Academy basu sake haɗuwa ba saboda bai cika komawa gida ba.
Bayan Shekaru Biyar
Ranar ta kasance ranar farin ciki ga mutane da dama,su Sadauki da suka shigo wurin a matsayin Cadets amma a yau zasu amsa sunan Lieutenants.
Wurin ya cika maƙil da jama'a,kowannen su na tsaye sanye da Uniform.
Bayan an kawo ƙarshen program ɗinne aka fara miƙa award ga waɗanda suka cancanta.
Sadauki na tsaye yaji an kira sunan shi,bai taɓa kawo hakan a ranshi ba.
Ya rintse ido jin ance“Cadet Sadauki…”
“…is hereby awarded the distinction of Best Graduating Cadet in Military Science for outstanding performance throughout his training.”
Wurin ya ɗauki sowa da busan trumpet ,ya kasa motsawa daga inda yake tsaye har sai da Bilal dake tsaye kusa dashi yayi tapping bayan shi yace"go friend,you deserve it".
Da kyar ya iya ɗaga kafafuwan shi ya nufi wurin,yana fita suka haɗa ido da Mami,ya kafe ta da ido yana kallonta da wani irin expression.
Tana isa kusa dashi tayi murmushi ta riko hannun shi suka isa wurin.
Ta tsaya kusa dashi aka mika mishi award ɗin aka ɗaukesu hoto.
Ganin kaman ƙyallin hawaye a idon shi yasa ta ɗan duke shi tace"come on,baka san ka girma ba?"
Yayi guntun murmushi ya ɗauke kai,a duniya bayan Umma da Baba da ɗan uwan shi Sani baya jin akwai wani halitta da yake ganin kima da darajarsa kamar Mami.
Ta rungume shi tamkar ɗan data haifa,a dai dai lokacin da wani ya wulakanta shi mutane da yawa ke kyamatarsu da hantararsu saboda suna almajirai a lokacin ne ta kira shi ta rungume shi ba tare data duba ƙazanatar jikin shi ba.
A cikin set ɗinsu aka kira sunan mutane biyar ciki har da Sadauki inda military tayi sponsoring ɗinsu abroad for postgraduates training in Intelligence and Security.
Rasa wani irin farin ciki zai yi a wannan lokacin,ya juya ya fuskanci gabas yayi Sujūd ash-shukr saboda a dai dai wannan lokacin godiya kawai ya kamata ya yiwa mahaliccinsa.
Bayan taro ya watse ya karasa inda ya hango Mami,a nan ya ƙara tarar da wani abin mamakin,ƴan gida ne cike a wurin tun daga kan Hajja su Zeenah sai Umma da bai taɓa tunanin ganinta a wurin ba.
Yayi murmushin daya baiwa kowa mamaki ya ƙarasa ya rungumeta.
Umma ta ture shi tace"meye haka?"
Mami tayi dariya tace"daga abin arziki?"
Umma tace"A'a na yafe".
Ya ɗago daga jikinta still fuskar shi ɗauke da murmushi ya dora idon shi kan Zarah.
Ƙasa ɗauke idon shi a kanta yayi,mamakin ganinta a wurin yake ko mamakin irin girman da tayi,rabon shi da ita tun ana gobe zai zo Kaduna.
Maganar Hajja yasa ya ɗauke kai daga kanta ya ƙarasa kusa da ita ya ɗurkusa yace"Barka da zuwa Hajiya".
Hajja ta gyara tsadadden mayafinta tace"ai na zata baka ganni bane,babu ruwana don ka zama soja ba tsoranka zan ji ba yawwa".
Mami ta ɗauke kai ta zuba mishi jollof rice da pepperd chicken dake tashin kamshi ta matsa can gaba ta shinfiɗa lallausan darduma ta dawo inda suke tace"Faruq ga shinfiɗa can ka zauna za'a kawo maka abinci".
Ya miƙe tsaye a ladabce yace"to Mami".
Mami ta mikawa Zarah abincin ganin sai danna wayar hannunta take tamkar bata wurin tace"wuce ki kai masa abinci Zarah".
A nutse ta ajiye wayar kusa da Zeenah ta gyara mayafin kanta ta karɓi abincin.
Yana zaune tare dasu Bilal da suka iso wurin ta nufi inda suke da sallama.
Duk su kayi tsit tare da kafeta da ido musamman Bilal,Ademola da bai cika shiga harkar mata ba kasa daina kallonta yayi.
Ta cire baƙaƙen sneakers dake kafarta ta ɗora farin kafarta kan carpet ta ajiye plate ɗin hannunta.
Bata kalli kowannen su ba tace"ga abinci".
Bilal ya haɗiye abinda ya tsaya mishi a throat yabi kafarta da kallo.
Bata jira cewar su ba ta maida takalmanta ta bar wurin.
Ta koma zata zauna Mami da ta hango su Bilal tace"zo Zarah,na ga ba shi kaɗai ba ne,zo ki ƙara musu abincin".
Emmanuel yace"what ! who is she please Sadauki?"
Bilal ya harare shi yace"duk maitar ka wannan tawa ce".
Oum Rijalain
***