BA NI DA MADOGARA

Chapter 3

by @narrnarhhbukar00

*_The Amazing Pen_ ✍️..........*










*Bani da Madogara*
  (Sai Allah...)




 


003

Hujayrah dai tana a kwance ba ta yi bacci ba tana saƙa da warwarar yadda za ta ɓullowa wannan bala'in da ya ke shirin tunkarota.Sama-sama take d'an jin kamar ana maganganu,sai a hankula ta mik'e zuwa k'ofar bedroom d'in Allah yasa a lokacin da za su fita basu kulle k'ofar ba sai ta fito zuwa inda take jin kamar ana magana, wani bedroom ne wanda yake kallon nata bedroom sai ta je kusa da ƙofar bedroom ɗin  tare da kai kunnanta daidai inda za ta ji maganar  da kyau,ai kuwa rad'au take jin magaganunsu, natsuwa tayi da kyau don sauraron mai suke tattaunawa a kai, ai da wani irin ƙarfi k'irjinta ya bada Ras! Ras! Rarassssss! ,lokaci guda ƙwaƙwalwarta ta tafi wucin gadi na ɗan wasu sakanni, komai na duniyar ya koma mata bibbiyu, waro dara-daran idanunta tayi waje tare da rufe bakinta kar tayi ihu su jiyota, a zuciyarta tana cewa' Ni Hujayrah na shiga uku na lalace daman Baba Zakari sai da ni yayi ga wa'innan azzalumin, Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un!' sosai jikinta ya fara rawa kamar ɗan mazari, domin kuwa hirarsu ta yi mugun tayar mata da hankali tare da rikirkita mata lissafi. 

Alhaji Sambo Dala da abokinsa ne suke tattaunawa a game da batun Hujayrah wanda basu san da wanzuwanta a ƙofarsu ba, abokin Alhaji Sambo Dala ne ya gyara zamansa yana cewa

"Mutumina a gaskiya kai namijin duniya ne,kayi matuƙar ƙoƙari wurin binciko wannan yarinyar, dole Demon king ya ƙara maka matsayi" 

Dariya sosai Alhaji Sambo Dala yayi sannan ya ce


"Yoo Senata wa ya ke wasa da ɗaukaka, ai bari ka ji duk inda nasan ɗaukaka ta ke to ina wurin, wai ka manta shekaru kusan ashirin da suka wuce mai girma Demon king ya ce an haiho yarinyar da ɗaukakarmu ke ƙarƙashinta, idanunta da zuciyarta su ne mahaɗar da  ta rage mana mu ɗaukaka har mu wuce tunanin mai tunani" 

Jinjina kai Senata yayi tare da cewa
"Tabbas haka ya faɗa Demon king, kenan tun daga ranar ga bazama nemanta " 

"Eh tun daga ranar na baza idanuna a duk faɗin Nijeriya nan, birni da ƙauye, lungu da saƙo har da kusufa-kusufa na bi,na baza yarana a duk faɗin Nijeriya har da wajenta,duk da mun daɗe muna neman yarinyar nan kasan sai a wani ƙauye a jihar Kaduna mai suna *KWANAR KWARA ƘWAI* a nan wani yarona da na sakashi aiki a ta ɓangaren ya nemota, ni da kaina na je garin don tabbatarwa, sai kuwa ilai ita ce, mai kalar idanun da Demon king ya suffanta haka idanunta suke exactly, ita a lokacin batafi shekara 12 a duniya ba, sai na haɗa baki da yayan babanta mai shegen son kuɗi, kasan shegiya Nairi, ai baiyi wata-wata ba ya yarda da ƙudirina akan yarinyar,idan baka manta ba Demon king ya ce sai yarinyar takai shekera 23 sannan Za a cire idanunta da zuciyarta don ƙarashe aikin da muka ɗauko na shekaru aru-aru"

Jinjina kai Senata yayi yana sauraransa don ba zai iya cewa komai ba, don yaga ubansa a wurin hatsabibanci, tabbas Alhaji Sambo Dala hatsabibi ne na ƙin ƙarawa,duk da a wancan lokacin shi da sauran members ɗin ƙungiyar har da ma members na ƙasashen waje sun yi iya ƙoƙarin binciko wannan yarinyar amma sun gaza,duk da ba fasawa su ka yi ba, amma Alhaji Sambo Dala ya taka su a naci, gashi ya samota. Katse mishi tunani Alhaji Sambo Dala yayi da cewa

"To a nan ne Yayan mahaifin nata ya ce kar na damu shi zai ji da ta ɓangaren in dai akwai Naira, ya sanarmin da cewa zai hana ta samari wanda bansan yadda zai hana hakan ba,kuɗi sosai na ba yayan mahaifin nata sannan duk wata ina tura mai da kuɗi wanda a ƙalla #200, 000, kai in taƙaice maka bayan case ɗin yarinyar nan har da taimaka mana ya ke da shi da mai unguwan garin wurin samo mana yara ƙananu wa'inda muke amfani da sassan jikinsu kai har da wasu ƙauyakun duk yana mana hanyar yadda zamu samu yara cikin sauƙi,abin farin ciki ya cika alƙawarinsa tunda yanzu haka yarinyar tana gidan nan, na umarci Eze ya haɗa mata abinci da maganin da Demon king ya bani, sosai maganin yayi aiki don yanzu haka tana can shegiya tana bacci"

Tafi Senata yayi ji kake Raf!!! Raf!!! Raf!!! Tare da yi masa jinjina da babbar yatsarsa yana cewa


"An gaishe ka jarumin jarumai,ka ce zuwa Next year za muyi blur a duniya bana Nijeriya ba, shi kenan  faɗuwa tazo daidai da zama daman Next year za a yi general  election, sai na fito takarar Gwamna hankali kwance raina fes! Babu hayaniya balle tashin hankalin zaɓe" 

"Tunani mai kyau, amma ni nawa tunanina yafi naka  faɗaɗa don takarar shugaban ƙasa zan fito, tun da mun samu mahaɗar ɗaukakarmu a hannun mu, ai dole mu ɗaukaka duniya ta samu kowa yasan da labarin mu " 

Ɗaukar glass cup Senata yayi ya kai bakinsa  ya kurɓa lemun sannan ya ajiye ya ce

"Kai mutumin wato ka bi ta Hausawa da su ke cewa *idan zaka yi roƙo to ka roƙa da babban masaki* yanzu ya za ka yi da iyayan yarinya nan idan suka ganka a TV, kar su tona maka asiri fa" 

Wata bazawarar dariya Alhaji Sambo Dala yayi har da dafe tumbinsa,da kallo Senata ya ke binsa da shi na alamar lafiya, sai da Alhaji Sambo Dala yayi dariya ma'ishinsa sannan ya tsagaita yana duban Senate wanda ido ya zuba masa, wani ƙasaitacce kuma munafikin murmushi Alhaji Sambo Dala yayi, kamar ba zai ce komai ba sai kuma can ya fara magana cike da izza da jiji da kai

"Karka manta da Alhaji Ayyub Abdulfatah Gaɗau kake tare, nafi hatsabibi iya hatsabibanci,ƙwaƙwalwata tana aikin da computer bata yi, a duk al'amarina ina yinsa da taka-tsantsan ne da  kuma matuƙar kula,ban yarda asan ainihin wane ne ni a duk inda na shiga ba,ɓadda kama nayi domin zan iya rantsewa iyayenta har da yayan mahaifinta bazasu taɓa gane ni a asalina ba,don takanas-ta-Kano daga India na saka aka kawomin suffar da zan yi amfani dashi a duk lokacin da zanyi ɓadda kama na je ƙauyen,in fact ina da siffofi mabanbanta da nake amfani dasu a wurare mababbanta,bara ka ji ko yayan babanta bai san asalin daga inda na fito ba,na ce mishi ni mazaunin Katsina ne balle a ce wata rana su zo nemana"


Sosai hatsabibanci Alhaji Sambo Dala ya ke ba Senata mamaki,daga Demon king Sai Shi a hatsabibanci, ai dole Demon king ya ƙara masa matsayi. Haka suka ci gaba da hirarsu wanda duk hirar nan da su ke yi Hujayrah na kusa da ƙofa a zube kamar kayan wanki tana sauraransu, gefe guda ruhinta ya daɗe da barin gangan jikinta, a zuciyarta tana cewa 'Ya Rahman! Ka dubeni da idon rahma, ka kawo mini ɗauki daga hannun wa' innan azzaluman bayin naka, na shiga uku na lalace, daman Baba Zakari kuɗin da yayi lokaci guda ba na Allah na annabi ba ne, Ashe sai dani yayi sannan duk ɓatan da yara suke yi a garinmu da saka hannunsa da na mai unguwa, Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un dole nabar gidan nan a yau ɗin nan, dole asirinsu Babu Zakari ya tonu a idon duniya' tana a haka ta ji alamar motsin mutum yana tahowa ai da sauri ta lallaɓa saɗaf-saɗaf tabar ƙofar zuwa bedroom ɗin da ta ke  ta kwanta kamar wata mai bacci, ba a yi mintuna goma da kwanciyarta ba ta ji shigowar Eze wanda bai yi mintuna biyar a ɗakin ba ya fita daman ya zo ya tabbatar bacci ta ke sai ya fita ba tare da ya kulle ƙofar ba,kamar wacca aka umurta ta kalli bangon ɗakin inda ta saka kanta, karaf! Idanunta su ka yi arba da frame na hoton Alhaji Sambo Dala wanda idan da bata ji ya ce ɓadda kama ya ke ba ta bazata taɓa yarda shi ne Alhaji Sambo Dala ba, fari ne a hoton ba kamar a zahiri ba, yana da dogon fuska mai ɗauke da saje mai haɗe furfura ta tsufa, yasha hula mai ƙube ɗinkin Maiduguri, a ƙasan hoton a saka *Alhaji Ayyub Abdulfatah Gaɗau* ai da sauri ta miƙe ta ciro hoton saboda ta kafa hujja sai a hankali ta buɗe jakarta ta saka ta kulle sannan ta koma gadon, bacci yaƙi zuwa mata tana tunanin yadda zata bar gidan nan a yau ba sai gobe ba...✍️


                  🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎

*Kwanar kwara ƙwai, Kaduna State, Nigeria.*

Bayan motarsu Hujayrah ta bar layin sai Hannatu ta dubi Murja sai kawai suka saki murmushi,Fatsima na kula dasu a zuciyarta tana cewa 'idan ma wani mugun abun kuke shirin ƙullawa to Allah ya fiku matsiyata baku da aiki sai sharri'  Mammi tana  a daskare a wurin tun bayan motarsu Hujayrah tabar layin, sauke nauyayyar ajiyar zuciya tayi tare da kai hannunta a saman idanunta tana goge hawayen da suka zubo mata, zuciyarta na suya,Allah kenan saboda rashin galihunsu yasa aka ma ƴarsu auran wulaƙanci,aka aura mata wanda ba a san asalinsa ba kuma tsoho, ba komai Ubangiji na tare dake Hujayrah, wani sabon hawayen ne ya ke kwaranyo mata tana ƙara gogeshi. Hannatu ce ta  cillara kuɗa tare da cewa

"Ayyiriri nanaye! Ayyiriri nanaye! Maman Balki" 

Murja ce ta amsa mata da 

"Na'am Maman Harira" 

Idanunta Hannatu akan Mammin Hujayrah ta ce

"kinga abun mamaki, wai ɗiyar fari ake ma kuka don tayi aure, yau naga salalan tsiya ni Hannatu" 

Itama Murja duban Mammin Hujayrah tayi sai ta taɓe baki tana cewa

"Ummm iyayi ne kawai sai ka ce Hujayrah ce ɗiyar fari, Allah dai mun gode maka da ka rabamu da mai ido mujiya, ta je can ta ƙarata da tsoho, mu dai yaranmu sabon jini suke aura ba tsoho ba wanda ya kusa tafiya lahira" 

Murmushin takaici Mammi ta saki tana kallonsu, da alama suna gab da kai ta bango,basu san halinta ba amma su juri zuwa rafi wataran tulunsu zai fashe. Riƙo hannun Haroon Mammi tayi kamar baza ta ce musu komai ba sai kuma ta ce

"Kubar ganin kun aurar da yaranku ga samari a tunaninku shikenan baku da matsala,Kubar ganin Hujayrah ta auri tsoho a tunaninku rayuwarta za ta shiga wahala, Kubar ganin kuna iskancinku mazajenku na ɗaure muku gindi kuyi tunanin ku ne da nasara, ku ne a sama damu,Hmmmm kusani *a ruwa kaɗai ne ake daɗewa ba a wuta ba* rayuwa takan canja a kowani lokaci, ni tausayi ma kuke bani wallahi domin ƙarya dai fure take ba ƴaƴa, kowa ya ɗibo da zafi ya kai bakinsa,ba haihuwar ba kajin ƙaurin sannan bakun aurar da ƴaƴanku ba, zaman auran shi ne abin magana, in shaa Allah Hujayrah sai ta ɗaukaka sama da ƴaƴan..."

"Wannan kuma ƙarya ne wallahi,ƴaƴanmu ne za su ɗaukaka ba Hujayrah ba, baƙin ciki ki ke kuma sai dai ki mutu, don kinga yaransu suna auran masu gwaɓi ba tsoho ba"  cewar Hannatu a zafafe wacca kamar kibiya Mammi ke soka mata a ƙahon zuciyarta, tabbas sai ta gyara mata zama da Hannatu take. 

Fatsima ce ta ce ma Mammi ta wuce gida karta biyema haukansu, ilai ita da Haroon suka wuce cikin gida, Kakulle ma ta biyosu cikin gidan har sashensu aka bar Fatsima dasu Hannatu da Murja muryarsu kawai ake ji suna ta kumfar baki, matan garin da yara sunyi cirko-cirko suna kallonsu, masu goyon bayan su sai tofa abarkacin bakinsu suke. 

Fatsima da dubi su Hannatu ta ce

"Ku ɗin nan Hmmmm ku jira ƙarshenku, wallahi bazai taɓa kyau  idan baku canja hali ba, jibeku kowaccanku tayi jika amma kuna sai da hali a layi, mtsw! Allah ya wadaran naka ya lalace" 

Fuuu! Tabar wurin ba tare da ta saurari me za su ce  ba, ai kamar ta ƙara man fetur ne a wuta, sosai suke masifa suna cewa, sai sunyi maganinsu, duk jijiyoyin wuyan sun tashi saboda masifa, ga kumfan  da ke fita daga bakunansu suna ta faman masifa babu ji babu gani. Su Baraka da sauran yaran ne suke ta basu haƙuri tare da zanyosu zuwa cikin gidan saboda mutane ƙara ƙaruwa suke, daman halin ƴan garin kenan kamar jira su ke a fara fada ko kuma wani bala'i ya sauka su kwashi jiki ƙwansu da ƙwarkwatansu su je kallon ƙwaƙwaf tare da ƙara Maggi da gishiri a yayi bada labari. 

Da sallama Mammi ita da Haroon suka shiga ɗakin lokacin Abbu na zaune tare da Salim a tabarmar kaba,amsa mata sallama su Abbu su ka yi sai ta samu wuri ta zauna ita da Haroon, ko ƙarasa zama Mammi bata yi ba ta ji sallamar Kakulle, a tare suka amsa mata ta shigo cikin ɗakin. 

Kamar masu zaman makoki haka su ka yi shiru babu mai cewa komai, kowa na karanta wasiƙar jaki a zuciyarsa,da shiru yayi yawa sai Kakulle ta fara magana cike da damuwa

"Duk abinda ubangiji ya tsarawa bawa to babu makawa sai ya sameshi,ba tsarin mu ba ne tsarin Allah ne ko munƙi ko kun so tunda Ubangiji ya tsara akan Hujayrah sai ta auri wannan mutumin babu yadda muka iya,wallahi sai bayan tafiyarsu Hujayrayh sai na ji dama ba a yi auran ba,akwai ruɗu a game da auran Hujayrah da wannan mutumin,taya za a ce shi kaɗai ne zai zo ɗaurin auransa ba tare da ɗan uwa ko aboki ba,mai amsar mishi auran ma nemoshi  Ɗan inna ya yi, anya babu wata a ƙasa kuwa, a ce ko ƴan uwanta ya hana a je dasu balle zuga wuri sai ita kaɗai ƙwallin-ƙwal,a gaskiya akwai alamar tambaya ɓaro-ɓaro a wannan auran, ni mutumin ma sai yau na ƙare masa kallo tsaf! Sai naga suffarsa wata kalar har da fatar jiki sa wata iriya da ita" (Oh su Kakulle da kallon ƙurilla 😂😂😂) 

"Nima Ina tantama a kai Inna ƙaddarar rashin idanuna ne ya sa haka amma Allah ya fisu, Allah yana tare da masu haƙuri da juriya,Inna in shaa Allah alkhairi auran nan zai zamantowa Hujayrah, idan ma da wata manufa Zakari yasa Hujayrah auran mutumin Allah ba zai taɓa barinsa ba kodan zumunci mai ƙarfi da ke tsakanina dashi,domin tsakani da Allah na ke tare dasu, bazan taɓa zaɓama yaransu mutanen banza ba, na ɗaukesu kamar yarana ne wa'inda na haifa a cikina ba bare ba,duk abinda mutum ya shuka shi zai girba,zan ci gaba da bin Hujayrah da addu'a a duk inda take Allah ya yi mata tsari  daga abin cutarwa" cewar Abbu wanda cikin ƙonar zuciya ya ke maganar. 

Mammi dai bata ce komai ba sannan bata da niyyar tofa albarkacin bakinta,sai jajantawa Kakulle da Abbu suke suna a haka da su ka ji sallamar Fatsima, amsa mata sallamar su ka yi sai ta shigo cikin ɗakin tare da samun wuri ta zauna tana cewa

"Ashe Inna kina nan" 

"Eh wallahi,lokacin da Zaytuna ta taho gida nima na biyosu don ban ga abinda zan tsaya a kai ba, aure ne an riga da an ɗaura sai dai muyi fatan Allah ya basu zaman lafiya tare da haƙuri da juna" cewar Kakulle tana ƙara gyara zamanta 

"Ai Inna baki ji yadda na ke ji a cikin zuciyata ba, ban san meke damun Innar Balki da Innar  Harira ba  a ce suna abu sai ka ce yara, Allah shi kyauta" 

"Ameen ya Allah" cewar Mammi tana ƙoƙarin gyara kwanciyar Haroon a saman cinyarta kasancewar ya yi bacci. 

Haka suka ci gaba da jajantawa wanda hirar daga Abbu, Kakulle sai Fatsima ita Mammi sai dai ta bi bakunansu da kallo, shi kuma Salim ya rakuɓe gefe kamar wani maraya, idanuna cike da ƙwalla...✍️


              🌎🌎🌎🌎🌎🌎


A ɓangarensu Hannatu da Murja tunda suka shigo gidan sai suka wuce ɗakin Hannatu, acan suka baje suna ƙulle-ƙullansa na yadda za su magance Mammi da Fatsima duk da suna shakkar Fatsima da mijinta saboda ba ƙyalesu suke ba musamman ma Baba Musa shi sha yanzu ne magani yanzu kamar Hujayrah ya ke, shi yasa ake cewa halinsa ta biyo bana mahaifanta ba.Hannatu da Murja suna zaune a bisa kujerar mutum biyu, suna maida zancen abinda ya faru ɗazu , cike da ɓacin rai Hannatu ta dubi Murja ta ce

"Innar Balki da alama saina saita Zaytuna don naga wani sabon iskanci da ɓullo dashi a yau,macen da a da ko yatsa ka saka mata a bakinta bata iya cizawa amma yau mu take mayar ma martani da zafafan kalamai masu ƙuna gangan jiki da ruhi,dani ta ke wallahi zabta san ruwa ba sa'ar kwando bane, duk wanda yaci tuwo dani miya yasha"

Taɓe baki Murja tayi tana cewa

"kadai bari nima abinda tayi a yau ɗin nan ya bani mamaki, a tunanina tunda Hujayrah mai idon mujiya tabar garin, zata yi sanyi ta ƙara shiga matsananciyar damuwa amma sai wani sabon wulaƙanci da ta ɓullo dashi da rana tsaka, Mtsw!" 


"Barta kawai idan ta san wata ai bata san wata ba, Innar Balki matso da kunnanki kiji wani shiri da nake akansu" 

Matsowa Murja tayi da kunnanta, raɗa tayi mata a kunne lokaci guda ta saki dariya tare da juyowa ta kalle ta da cewa

"Da gaske Hannatu kike?" 

"To na taɓa miki ƙarya ne Murja kin jiki da wani batu" 

Fuska a ɗaure tayi maganar, da sauri Murja ta ce mata tayi haƙuri mamaki ne kawai ya cika ta amma a zuciyarta tana cewa 'Shegiya ina binki ne don tawa manufar, sai shege isa da ƙasaita ita ga mijinta mai ƙudi, zaki ci ubanki je, na fiki iya iskan in, muje dai zuwa mtws! 

Ci gaba da hirarsu su ka a yi wanda mafi yawanci hirar tasu akan Mammi ne da Fatsima tare da ƙudiri akansu tunda mai tona musu asiri tabar garin...✍️


Washe gari  wurin 10:35am na safe Baba Musa ya iso garin bayan jiya da daddare Fatsima taci sa a wayar tashi ta shiga,bata ɓata lokaci ba wurin nasar masa abinda ke faruwa a gidan,bata cire komai ba. Sosai ya ke faɗa kamar ya ari baki har faɗan ma yaso ya shafeta akan mai yasa bata aiko har Zarian a kirashi ba tunda tasan wurin da ya ke sana'a, duk da ba lokacin dawowarshi ba ne amma a daran ya shirya komai na tafiyarsa, da sassafe ya taho tasha ya hau mota matsalar da aka samu rashin passenger ne da zuwa 9:00am na safe ya iso garin kasancewar babu nisa sosai tsakanin garinsu da Zaria. Ko sashenshi bai shiga ba ya aiki yaro ya je ya ce ana sallama da Zakari, haka ya aiki wani yaron daga gidan ya ce ana kiran Zubairu, halinsa kenan tun yarinta baya girmamasu tunda ya gane ba mutanan arziƙi bane, kansu kaɗai suka sani da iyalansu. Kakulle ta fito zata je sashensu Mammi saita ci karo da Baba Musa sai faman huci ya ke shi kaɗai kamar wani kumurcin maciji,russunawa ya yi ya gaisheta, idanunta akan ta amsa masa cike da kulawa tana cewa

"Musa dawowan safe haka" 

"Inna dole ce tasa haka ashe Hujayrah aure Zakari ya yi mata da baƙon mutum wanda ba a san daga ina ya ke ba" 

"Bari Musa sunfi ƙarfina akan maganar, na nuna ƙin amincewata amma dukkaninsu sun goyi baya tunda ta rasa mai auranta a cewar su" 

"Eh da ya ke ba yaransu ba ne shi yasa,don sun ga Audu baya gani shiyasa suka aikata haka..." 

Bai ƙarasa maganar ba sai ga Zakari da Zubairu sun fito a tare kamar sun haɗa baki, direct wurin Kakulle suka nufa sai suka gaisheta wanda rabonsu da hakan an daɗe,basa zuwa ɗakinta gaisheta balle matansu, Mammi ce da Fatsima kullum suke zuwa gaisheta,Abbu ma lokacin da yake gani kullum sai ya shigo ya gaisheta kamar Musa. Gyara tsayuwa Baba Musa ya yi yana kallonsu, kasancewar yaran basu ce musu ga wanda ya ke kiransu ba yasa suka fito da sun san Musa ne ke kiransu bazasu fito ba. Ganin suna da niyyar fita waje sai Baba Musa yayi saurin cewa

"Nina aika a kiraku ganin da safe ne" 

Wata wawuyar harara Alhaji Zakari ya cillama Baba Musa tare da yin ƙwafa, a zuciyarsa yana cewa 'Zanyi maganinka, karan bana ne ke maganin zoman bana' cike da takaicin wannan raini hankali Alhaji Zakari ya ce

"Wani Sabon wulaƙanci da rana tsaka, a ce muna sama da kai shi ne kake sa wa a kiramu, ai wannan rainin hankali ne" 

Taɓe baki Baba Zubairu ya yi,muskili ne na ƙarshe wanda sai ya gadama ya ke magana,yanzu ma bai ce komai sai dai ya zuba ma Baba Musa idanu. Shi ko Baba Musa ko a jikinshi ya fara magana da ɗan faɗa-faɗa daidai lokacin Abbu ya fito shida Salim ya ɗan dafa kafaɗar Salim za su fita wa je don Abbu yasha iska sai ya ce ma Salim ya kaishi gun ƴan uwansa ya ji kamar da murya Musa a ciki. Babu musu Salim ya karkata akalar tafiyarsu zuwa wurinsu Baba Musa.

"Audu ka fito ne" cewar Kakulle 

"Eh Inna na fito shan iska ne har zamu wuce sai na ji kamar muryar Musa, shi ne nace ya kaini inda kuke" 

"Audu barka da Safiya" cewar Baba Musa yana sakin murmushi wanda tun shigowarsa gidan sai yanzu ya saki murmushi 

"Musa kai ne a garin namu da safe" shima murmushin ya ke

"Dole ce tasa haka, Audu mai yasa ka aminta a ɗaurama ƴarka aure da tsoho wanda ba a san inda ya ke ba" 

Murmushin takaici yayi yana cewa

"Yarda da amintuwar da nayi dasu Zakari a matsayinsu na ƴan uwana yasa na amince Hujayrah ta auri mutumin, kasan ba gani nake ba balle na tantance mai kyau da marar kyau, naga ƴan uwana ne baza su zabar ma jinina tumun dare ba" 

Gyara tsayuwa Baba Musa yayi da cewa

"Ashe ko tumun dare suka zaɓarma Hujayrah domin a yadda Fatsima ta sanar min bai da asali hasalima shi kaɗai yazo ɗaurin auransa ba tare da kowa nasa ba, sannan a nan aka nemo  mai amsar masa auran, abin ban takaici da haushi shi ne kuka bari mutumin da baku sanshi ba ya ɗauki Hujayrah ita kaɗai ba tare da ƴar rakiyar amarya kamar yadda ake yi a aladan ce ya tafi da ita haba! Haba! "

" Kai Musa bar ganin nayi shiru na ƙyaleka kana sakin maganganu yadda kake so nasan dani kake aure ne an ɗaura sannan da kake cewa bashi da asali, abokina ne na ƙut-da-ƙut, ɗan Katsina  ne acan ya ke da zama da iyalansa"

"Au Allah shikenan saika shirya muje gidansa gobe tun da ka ce abokinka ne" 

A nan ta kai gumi ya fara tsattsagoma Alhaji Zakari, Ina ya sanshi garin da ya ke kaɗai ne ya ce masa, amma wani abu akanshi bai sani ba, ko aikin ɓoyen da yake masa da yaran sa ya ke, shi akan Hujayrah ne kaɗai ya sansa, Tab! Akwai ƙura kenan idan Musa ya nace akan sai ya kaishi wurin Alhaji Sambo dala, dole ne yayi wani abu a yau ɗin nan ba sai gobe ba, idan ba haka ba to asirinsa na gab da tonuwa kuma Baba Musa ne zai tona masa don bashi da kirki.Sosai ya Lula cikin duniyar tunani sai Baba Musa ya katse mishi tunani da cewa

"Zakari da kai nake fa kayi shiru ka ƙyaleni ina ta magana" 

Firgigit ya dawo hankalinsa yana haɗa magana da cewa

"To to to Aaallah ya kaimu ɗin" 

Baba Musa ya lura da yanayinsa tabbas bai da gaskiya,don Hausawa sunce shi mara gaskiya ko a ruwa gumi ya ke.Wucewa Alhaji Zakari ya yi sashensa shi kuma Baba Zubairu ya fi cewar shi   shi daman ba magana mai tsayi ya ke ba sai in ta kama dole. Su Baba Musa sai suka ci gaba da hirarsu wanda kusanci akan auran Hujayrah ne suke hirar a kai...✍️


                  🌎🌎🌎🌎🌎🌎


Da wani irin ƙarfi Alhaji Zakari ya buɗe ƙofar ɗakinsu lokacin Hannatu ta kammala wanka har ta saka kaya tana zaune a falo tana kallo,jin an banko ƙofa yasa da sauri ta ɗago  kanta daga kallon TV tare da cewa

"Lafiya Alhajina naga Ka shigo cikin irin wannan yanayi kai da Ka fita cike da farin ciki yanzu ka dawo fuskarka shimfiɗe da damuwa tare da tashin hankali" 

Bai tanka mata ba sai ma Safa da marar da ya fara a ɗakin ya goya hannayansa a baya ga gumi sai ƙara tsattsago masa ya ke a duk ilahirin jikinsa, ganin bai amsa mata ba saima jeka-ka-dawo yake a falon sai ta miƙe zuwa inda ya ke tana cewa

"Alhajina wai lafiya?" 

Sai da ya sauke nauyayyan ajiyar zuciya sannan ya dubeta yana cewa cikin sanyin murya mai nuna gazawar mutum a fili

"Hannatu akwai matsala" 

Duk da bata san wani irin matsala ba ce sai da gabanta ya faɗi,da sauri ta ce 

"Matsala matsala Alhaji,wani irin matsala kuma da rana tsaka" 

Samun kujerar mutum biyu ya yi  ya zauna, ita ma sai ta zauna a kujerar tana kallonsa alamun tana neman ƙarin bayani, sai da ya ɗan nisa sannan ya fara magana cike da damuwa

"Wai ni Musa ya ke son tonama a asiri,yaushe aka haifeshi da zai nunamin zafin kai" 

"Alhajina ban gane zai tona maka asiri a fito fili kayi min bayani ta yadda zan gane" 

Sai da ya saki dogon tsaki sannan ya ce

"Ashe shi ya aiki yara su kiramu ni da Zubairu,maganar Hujayrah ya taso dashi akan mai yasa ba a kira anji ta bakinsa ba a matsayinsa na uba a gareta" 

Taɓe baki Hannatu ta yi sannan ta ce

"Yanzu wannan ne abun ɗaga hankali akai Alhaji?" 

"A'a Hannatu ba a nan gizo ke saƙar ba, ya ce tunda mijin Hujayrah ta hannuna ya zo kuma na sanshi, na shirya gobe mu tafi tare ya je yaga gidan ta" 

"Tofa wannan shi ne  tashin hankali wanda ba a saka mai rana, naga garinsu kaɗai ya faɗa maka bayan haka akwai wani abu daya sanar maka dangane dashi" 

"Ko kusa Hannatu, ko harƙallar da muke yi ni dashi da mai unguwa duk yawanci da yaronsa muke, auran Hujayrah ne kawai yasa shi ne dalilin da na sanshi, ya ce min shi mutumin Katsina ne" 

Sosai Hannatu ta shiga tashin hankali saboda tasan ɓoyayyar harƙallar da mijinta ya ke,ita ma tana bashi goyon baya saboda yana samun maƙudan kuɗi a wannan harƙallar,shiyasa ta ke bashasha da kuɗi yadda take so, ta baza mulkinta iya son ranta.Lallai zama bai gansu ba dole suyi wani abu a yau ɗin nan kafin gobe,ɗan daidaita zamanta tayi sannan ta ce

"To kai Alhaji wace mafita ka samowa kanka kafin goben" 

Jingina kansa yayi a saman kujerar tare da lumshe idanunsa kaɗan, bai amsa mata ba sai can ya ce

"Kwarin ɗan dodo zani a yau ɗin nan ba sai gobe ba, Kinsan acan ne na samo asirin da Hujayrah taƙi auruwa to Kinga zan iya samo asirin da zai kulle bakinsa" 

Dariya Hannatu ta saki tana cewa

"Alhajina hatsabibin kansa ne wallahi, kasan kan duniya tabbas za ka yi maganin ɗan banza, kenan wurin Malam Tani mai Allon ƙarfe zaka je" 

Murmushi ya mata sannan ya ce

"Eh mana ai malamin aikinsa na yi kamar yankan wuƙa" 

"Haka ne kuwa" 

Ci gaba da hirarsu su ka yi sai can Alhaji Zakari ya miƙe zuwa uwar ɗaka don ya shirya tafiya zuwa ƙauyen kwarin ɗan dodo wurin hatsabibin bokansa mai aiki da hatsabiban aljanu... ✍️



*Ƙarin bayani*

Hujayrah bata iya gane anyi mata asiri sai dai idan anyi ma wani tana ta ke ganewa wannan ita ce baiwarta,asirin da Alhaji Zakari ya yi ma Hujayrah mai ƙarfi ne saboda a lokacin da Alhaji Zakari ya ce ma bokan nasa mai tsuffar malunta yana so Hujayrah karta auri domin akwai shirin da ya ke a kanta idan ta kai shekara 22 a duniya, bayan Malamin ya yi ƴan surkullensa sai can ya ce masa,

"Aiki akan yarinya nan ba ƙarami bane domin jininta mai ƙarfi ne sannan akwai wata baiwa da yarinyar ta ke tattare da shi,ƙarin daɗi tana da aljanu akanta wanda ta gadesu daga wurin mahaifiyar Babanta, ita ma a wurin mahaifinta ta gadesu sannan su wa'innan aljanun suna da ƙarfi sosai ta fannin sanin magunguna da iya karya sihiri,wani jinsin aljani bai isa ya aikata wani abu a kansu ba"

Ɗan shiru Alhaji Zakari ya yi,wannan shi ake kira ga samu ga kuma rashi, idan aiki baiyi akan Hujayrah ba taya zai tatsi maƙudan kuɗaɗe a hannun Alhaji Sambo Dala, shi da ya ke son ya yi kuɗi lokaci guda yanzu Allah ya kawo masa dama amma tana niyyar suɓuce masa Ina bazata taɓa saɓuwa ba wai bindiga a ruwa, dole asiri yaci Hujayrah idan yanaso yayi kuɗi, a dinga kiransa da Alhaji.Cikin sanyi murya ya ce

"To malam yanzu baka da dubara wanda zai saka asiri yaci yarinyar, don a gaskiya ina muƙatar so asiri yaci yarinyar saboda idan taƙi aure hakan zaisa kowa yabi shawarata, Sannan zamantowa na mai arziƙi yana ƙarƙashinta,ka taimaka asirin nan ya yi" 

Ɗan shiru Malam Tani mai Allon ƙarfe yayi sai can ya dubi Alhaji Zakari ya ce

"Mafita ɗaya ce a garemu yanzu,amma fa zaka yi aiki tuƙuru tunda ka nuna kana buƙatar asirin yaci yarinyar, akwai wani aljani daga cikin jinsu wanda zan kirasa muyi aikin tare nasan aikin zai yi tunda ɗaya daga jinsu su ne,amma za a nemo abubuwan da zai sa ya zo"

Cikin zumuɗi Alhaji Zakari ya ce

"Yawwa Malam Tani mai Allon ƙarfe, mai aiki da hatsabiban aljanu ka cire tuta a duk faɗin Nigeria" 

Surkullensa ya ci gaba da yi yana duba wata baƙar randa wacca ta ke a gabansa, ya jima yanayi tsubbace-tsubbacensa sai can ya ɗago ya ce

"Zaka nemo kitsan jaɓa,gashin yarinyar na gefan hagu,sannan zaka nemo idanun mujiya har bakwai daga wa'innan ka barni da komai aikinka kamar anyi an gama" 

Duk da aikin mai shege wuya ne amma ya zai yi tunda yana son ya yi kuɗi, dole ya nemo abubuwan. Alhaji Zakari yasha baƙar wuya wurin neman abubuwan da bokansa ya umurcesa ya nema musamman kitsan jaɓa da idanun mujiya har bakwai.Tunda ya kawo abubuwan bokansa ya yi masa aiki akan Hujayrah wanda daga lokacin har girman Hujayrah ta gaza samun mai auranta a garin har ta kai shekarun da  Alhaji Zakari ya ke buƙatar wanda Alhaji Sambo Dala ne ya ke son hakan sannan ya je aka warware auran wanda a washe gari ya bijiro da auran Alhaji Sambo Dala ga ahalinsa. Wannan kenan


              🌎🌎🌎🌎🌎🌎


*Bauchi state, Nigeria*

A ɓangaren Hujayrah ta kasa runtsawa saboda tashin hankalin da ta ke ciki,bacci bai ga fuskar tunkararta ba a wannan yanayin,bini-bini idanunta akan agogon ɗakin, ta yi matuƙar kosawa tsakiyar dare ya yi ta nemi hanyar guduwa gashi an fara tsawa alamun ruwa na niyyar sakkowa ga walƙiya ta ko'ina. A daidai misalin ƙarfe 2:56am na dare Hujayrah ta miƙe daga kwanciyar da ta ke, jin babu motsin kowa sai ta miƙe a hankali ta ɗauki jakarta ta saɓa a hammatanta, kasancewar ɗakin a buɗe  Eze ya barshi hakan ya bata damar fita daga ɗakin ba tare da ƙofar ta yi motsi ba, saɗaf-saɗaf ta ke tafiya tana duba-duban hagunta da damanta, hanyar da suka shigo cikin gidan ta hanyar tabi,ta yi matuƙar sa a duka ƙofofin ɗakin a buɗe su ke daya ke Eze bai kullesu ba ganin ya bata magani a abinci kuma maganin ya yi aiki yasa kawai bai rufe ƙofofin ba,har babban falo Hujayrah ta zo ba tare da taci karo da mutum ba, tana shigowa falon sai tayi arba da Eze yana ta sharar baccinsa hankali kwance a gefansa kuma  kwalbar giya ce da plate wanda ya ke ɗauke da sigari, a hankali tabi ta gefansa ta wuce ba tare da tayi wani motsi ba. 

Har gate ta nufa inda gwaramar ta ke a kulle gate ɗin ya ke,sai ta  ɗan yi waige-waige ko zataga makullin gate ɗin ga walƙiya ta ake yi har yayyafi ya fara sauka, munshari ta ke ji yana fita daga wani ɗan ƙaramin ɗaki a kusa da gate ɗin, direct ta nufi ɗaki babu tsoro a tattare da ita, ƙofar ɗakin a buɗe ta ke, akwai hasken fitila a ɗakin kasancewar mai ɗakin bai kashe fitilar ɗakin ba, a gefansa akwai kwalbar giya iri ɗaya data wurin Eze sai key wanda ta ke da tabbacin na gate ɗin ne, a hankali ta saka kanta cikin ɗakin direct ta ɗauki key ɗin gate ɗin saita fito zuwa gate,with cautious ta ke buɗe ƙofar gate ɗin da key, tana buɗewa ƙofar tafi uban ƙara hakan yasa mai gadin da Eze suka tashi daga bacci duk da sunsha giya da ya ke giyar ba mai ƙarfi ba ce shiyasa da suka ji motsin gate sai suka farka, mai gadi ne ya yi saurin fitowa sai Eze shima ya fita amma ina tuni Hujayrah tabar gidan a sittin, suma bin bayanta suka yi da gudu ga shi har an fara ruwa mai ƙarfi, sosai ta ke gudu suna biye da ita,kasancewar Layin babu gidaje da yawa saboda sabon layi ne wanda ya ke a ƙarshen gari,cikin dajin Hujayrah ta nufa da gudunta suma suna biye ta ita suna ce mata ta tsaya ko su kasheta amma ina tayi kunnan uwar shegu da zantuttukansu. 

Sosai ruwan yayi ƙarfi suna biye da ita cikin dajin sai keta ciyayi da manya-manyan bishiyu ta ke, ganin ta yi musu nisa yasa ta ɓoye a wurin wata bishiya babba wacca take kewaye da ciyayi jakarta na maƙale a hammatanta. Ganin ta ɓace musu yasa suka tsaya suna haske-haske ko za su ganta ga kiranta ta suke suna tsorata da cewa idan bata fito ba kashe za su yi idan suka nemota. Tsoratarwa tasu ta banza ce domin zuciyar Hujayrah ta ƙeƙashe babu alamun tsoro ko firgici a tattare da ita.abinka da mutumin ƙauyen daman ta saba shiga daji shiyasa bata ji ɗar-ɗar na tsoro a cikin zuciyarta ba balle firgici.

Tana a maɓuyanta ne ta ji abu mai sanyi ya taɓa mata ƙafafu,daga ji abun mai girman gaske ne saboda sanyi da abun ya ke dashi da kuma nauyinsa, kamar daman jira ake sai ga walƙiya ta haskake ilahirin daji kamar rana, karaf! Hujayrah tayi arba da ƙasurgumin... ✍️






*Narrnarhh Bukar's Amazing pen✍️*
 ***