GIMBIYAR GIDAN ALHAJI KABEERU
*A NOTE FROM THE AUTHOR 🥹❤️*
I'm not making empty promises when I say Kaddarar Zuciya is more than just a story to me, I wrote it from the deepest part of my heart, there were moments I cried while writing it, and moments I smiled like someone experiencing the scenes herself, every emotion, every pain, every little happiness… I felt them while writing this book, and if there's one story I'll always hold close to my heart, it will be Kaddarar Zuciya, it will forever be my favorite story I've ever written, so, dear readers, as you turn these pages, just know that you're not only reading a story; you're reading a piece of my heart.🥹
*BISMILLAHIRRAHMAN ARRAHIM*
*KADDARAR ZUCIYA*
*CHAPTER ONE (1)*
*GIMBIYAR GIDAN ALHAJI KABEERU*
*JIDDAAH BARKUM*
———
"Inteeessarrr!" Muryar Khalil ta cika gidan da ƙarfi, har sai da na ji kamar bangon falon ma yana amsa kiransa, na ɗan haɗe fuska, ina zaune cikin kasala a kan kujera mai laushi, idanuwana a kan talabijin, duk da cewa hankalina bai kai ga abin da ake nunawa ba, na san Khalil yana nemana, amma saboda na san me zai biyo baya, sai na yi kamar ban ji shi ba, "Ban ji ba!" na amsa a hankali, ina ɗan ɗaga murya kaɗan kamar mai gaskiya, sai na ɗan ciji leɓena don kada dariyar da ke neman subuce mini ta bayyana, ban gama rufe bakina ba sai na ji takunsa yana tahowa da sauri, "Inteesar! Wallahi yau idan na kama ki, kin ga taki!" Wannan karon na kasa riƙe dariyata, na zabura daga kan kujerar, na yi hanyar kitchen da gudu, ina dariya kamar wata yarinya da aka kama da laifi, "Mommyyy! Ki ce masa ya bar ni mana!" Na shige kitchen ɗin da sauri, na buya a bayan Mommy Haleema, ina riƙe da gefen rigarta da hannuwana biyu, na leƙo da kai kaɗan, ina kallon ƙofar kitchen ɗin don ganin ko Khalil ya shigo, Mommy Haleema ta juya a hankali, ta sauke kallonta a kaina, fuskarta ɗauke da murmushi, yayin da ta ɗaga gira ɗaya, "Ke kuma, what have you done this time?" Na buɗe baki zan yi magana, amma ban samu damar yin hakan ba saboda Khalil ya shigo kitchen ɗin a fusace, ya tsaya yana nuna ni da yatsa, fuskarsa cike da alamar rashin yarda, "Mommy, please! Ki tambaye ta abin da ta yi, ta ɗauki key ɗin motata ta fita da ita, bayan kin san sau nawa na gaya mata kada ta sake taɓa motar nan ba tare da izinina ba!" Na zaro idanuwa, na fito daga bayan Mommy kaɗan, "Excuse me! Ni fa ban sace maka mota ba!" Khalil ya haɗe hannayensa a ƙirji, yana kallona da wani irin kallo na really? "Really, Inteesar? So what do you call taking my car without permission?" Na turo baki, na kau da kai gefe kamar ni ce aka zalunta, "Na ga ka yi barci ne, I only took it for a short drive, na dawo lafiya fa!" Ya buɗe baki, ya sake rufewa, kamar maganganun da nake yi suna ƙara masa hauka, "Short drive?!" ya maimaita, yana nuna kansa, "Ke kin san nawa na kashe wajen motar nan kuwa? What if something had happened to it?" Na ɗan yi shiru, sai na lumshe ido, na sake buɗewa, kafin in ce cikin ƙaramin murya, "But nothing happened…" Khalil ya ɗaga hannuwansa sama, "Ya Allah, give me patience!" Mommy Haleema ta fashe da dariya, har sai da ta riƙe gefen teburin kitchen ɗin, "Wallahi ku biyun kun fi yara ƙanana rikici! Khalil, ka daina bi ta kamar za ka ci ta, ke kuma, Inteesar, ki daina ɗaukar kayan mutane ba tare da izininsu ba," na ɗan sunkuyar da kai, ina wasa da yatsuna, "Okay, Mommy," sai na ɗaga kaina a hankali, na kalli Khalil da murmushin yaudara, "Happy now?" Ya zaro ido, "INTEE!" Na yi saurin komawa bayan Mommy, kitchen ɗin ya cika da dariya, dariya mai daɗi, dariya mai cike da natsuwa da soyayya, wannan shi ne gidanmu, gidan da ko ana faɗa, dariya ba ta rasa wurin zama, gidan da kowa yake da halinsa, amma babu wanda ake bari ya ji shi kaɗai, gidan da na taso cikin kulawa, ƙauna da gata har ban taɓa zama na tambayi kaina ko akwai wani abu da ya rage mini a rayuwa ba, bayan ɗan lokaci, na fito daga kitchen ɗin ina riƙe da cup ɗin tea, ina tafiya a hankali cikin corridor ɗin da ya ɗan yi shiru, na ɗan tsaya a tsakiyar corridor, ina kallon hotunan iyalinmu da aka jera a bango, hotunan da ke ɗauke da murmushi, farin ciki da wasu lokuta na musamman da muka yi tare, na yi murmushi a hankali, this is my home, my safe place, a nan nake jin kaina, a nan nake jin cewa komai yana daidai, ni ce Inteesar Kabeeru, yarinyar da kowa yake kira Princess, yarinyar da ake yi wa gata fiye da yadda take buƙata, yarinyar da ko ta yi shiru na ɗan lokaci, sai an tambaye ta ko lafiya, yarinyar da ba ta taɓa sanin yadda rashin kulawa yake ji ba, amma duk da haka… a wani ɓangare na zuciyata, akwai wani ƙaramin tunani da nake ta kawar da shi duk lokacin da ya taso, wani tunani da yake nuna mini cewa rayuwa ba za ta kasance haka har abada ba, na girgiza kai kaɗan, na ɗauki cup ɗin tea ɗin da kyau, na ci gaba da tafiya, "Inteesar…" Na tsaya cak, muryar da na fi so a duniya, muryar da idan na ji ta, nakan ji wani irin kwanciyar hankali yana sauka a zuciyata, Daddy, Alhaji Kabeeru, na juya a hankali, yana tsaye a tsakiyar falon cikin nutsuwa, sanye da farar kaftan mai kyau, agogonsa a wuyan hannunsa, fuskarsa cike da kamala, yayin da idanunsa suka sauka a kaina, kamar yadda ya saba, kallonsa yana ɗauke da wani irin taushin da yake sa ni jin kamar ni ce mutum ɗaya tilo da yake gani a duniya, na ajiye cup ɗin tea ɗin a kan ƙaramin teburin gefe, na nufi inda yake da sauri, "Daddy!" Na rungume shi a hankali, ina jingina kaina a ƙirjinsa, ya yi murmushi, ya ɗora hannunsa a bayana, yana shafa ni a hankali, "My princess," na ɗaga kai, ina kallonsa da murmushi, "Daddy, you called me?" Ya ɗan matsa daga gare ni, ya gyara min wani ɗan yatsin gashin da ya fito daga inda na daure shi, "Kin ci abinci?" Na girgiza kai a hankali, "Not yet," ya ɗan matse gira, "Why?" Na turo baki, na kau da kai gefe, "Khalil ne fa yake damuna tun safe," Daddy ya ɗaga gira, ya kalli inda Khalil yake tsaye yana ƙoƙarin ɓoye murmushinsa, "Khalil?" Khalil ya ɗaga hannayensa, "Daddy, please don’t tell me you’re taking her side again, this girl took my car without permission!" Na juya masa da sauri, "Daddy, don’t listen to him! He’s exaggerating!" Daddy ya girgiza kai yana murmushi, kafin ya ɗaga hannu ya dakatar da mu, "Enough, both of you," sai ya sake kallona, wannan karon fuskarsa ta ɗan canza zuwa ta uba mai son a kula da abin da yake faɗa, "Inteesar, ki daina wasa da abinci, it’s not good for your health, princess," na sauke kaina kaɗan, ina kallon yatsuna, "Okay, Daddy," ya shafa kaina a hankali, wannan shafawar… wannan kalmar princess… wannan irin kulawar da yake nuna mini ba tare da ya gajiya ba… duk suna da wani matsayi na musamman a zuciyata, saboda Daddy ba uba ne kawai a gare ni ba, shi ne ginshiƙin rayuwata, shi ne mutumin da idan na yi kuka, nakan fara nemansa kafin kowa, shi ne mutumin da nake jin kamar komai zai daidaita muddin yana kusa da ni, shi ne mutumin da ban taɓa iya tunanin rayuwa ba tare da shi ba, na rungume hannunsa, na ɗan matse shi, "Daddy, you know I love you, right?" Ya yi murmushi, yana kallona cikin wani irin taushi, "I know, my princess, and I love you more than you can ever imagine," na yi dariya, na sake rungume shi, "More than everyone?" Ya yi kamar yana tunani, ya ɗan ɗaga kai sama, "Hmm… let me think," na zaro ido nan take, "Daddy!" Ya fashe da dariya, ya ɗora hannu a kaina, "Of course, princess, you have a special place in my heart," na yi murmushi mai faɗi, a wannan lokacin, babu abin da nake buƙata daga rayuwa, ba kuɗi, ba kayan alatu, ba wani abu da duniya za ta iya bayarwa, ina buƙatar wannan mutumin kawai, ina buƙatar jin muryarsa, ina buƙatar ganin murmushinsa, ina buƙatar sanin cewa yana nan, ban taɓa sanin cewa mutum zai iya zama wani ɓangare na zuciyarka har ka kasa tunanin rayuwa ba tare da shi ba, sai da na fahimci irin matsayin da Daddy yake da shi a rayuwata, amma ban san cewa wasu abubuwan da muke ganin za su dawwama… ba su da tabbas a wannan duniyar, ban san cewa wani lokaci, soyayyar da ta fi kowace soyayya ƙarfi… ita ce take iya barin raunin da babu wanda zai iya warkarwa, "Daddy!" Muryar Mommy Haleema ta fito daga kitchen, "Breakfast yana nan fa! Ku zo kafin abincin ya huce!" Daddy ya kalli inda muryarta ta fito, sannan ya sake kallona, "Come on, princess, let’s eat," na ɗaga kai da sauri, na kama hannunsa, "Race you to the dining room!" Na saki hannunsa na yi gudu, ina dariya, "Hey! Inteesar!" Muryarsa ta biyo ni, cike da mamaki da dariya, na juya ina tafiya da baya, ina dariya, "Too late, Daddy! I’ve already won!" Ya girgiza kai, yana dariya, "Wannan yarinyar…" Na sake juyawa da sauri, na nufi dining room ɗin, a lokacin, gidan ya cika da hayaniya, Yaya Faruq yana zaune a falon yana dariya, har sai da ya jingina da bayan kujera saboda abin da Yaya Jaafar ya faɗa masa, Yaya Salim kuwa yana zaune cikin nutsuwa, yana shan tea ɗinsa, kamar yadda ya saba, shi ba ya yawan shiga hayaniyar gidanmu, amma idan ya yi magana, yawanci kowa yana sauraro, Yaya Abubakar yana zaune a gefe, yana kallonmu cikin nutsuwa, fuskarshi ɗauke da wannan kamilalliyar natsuwar da ta bambanta shi da sauran ’yan uwanmu, shi ne irin mutumin da ba sai ya yi magana da yawa ba kafin ka fahimci cewa yana lura da duk abin da ke faruwa a kusa da shi, Yaya Adam, babban yayana, yana tsaye a kusa da dining table, yana taimaka wa Mommy wajen shirya sauran abubuwan breakfast, shi ne wanda ya ɗauki nauyinmu kamar uba a wasu lokuta, musamman idan Daddy ba ya nan, Yaya Jaafar da Yaya Alamin kuwa har yanzu suna gardama a kan wani abu da ban san me yake ba, "Wallahi kai ne ka fara!" Jaafar ya ce, yana nuna Alamin, "Me? Me? You started it!" Alamin ya mayar masa da martani, na tsaya a bakin ƙofar dining room, ina kallonsu, kafin in fashe da dariya, "Can you guys ever have breakfast in peace?" Faruq ya juya ya kalle ni, "Look who’s talking! The same girl who stole Khalil’s car?" Na buɗe baki, na ɗora hannu a ƙirji kamar an yi mini babban cin mutunci, "Excuse me?!" Sai duk suka fashe da dariya, Khalil ya shigo daga baya, yana nuna ni, "Thank you! At least someone understands my pain," na juya masa da sauri, "Keep quiet, Khalil!" "Make me!" Na yi masa wani irin kallo, na juya masa baya, na nufi kujerata, "Children," Salim ya faɗa a hankali, ba tare da ya ɗaga kansa daga cup ɗinsa ba, nan take Faruq ya sake dariya, "See? Even Salim knows you’re all children," "Shut up, Faruq!" muka faɗa a tare, ni da Khalil, dariya ta sake mamaye dining room ɗin, gidanmu kenan, gidan da babu ƙarancin murya, gidan da babu ƙarancin dariya, gidan da kowa yake da matsayinsa a zuciyar kowa, kuma a tsakiyar duk wannan soyayyar, ni ce ƙaramar gimbiya da kowa yake ƙoƙarin karewa daga duk wani abu da zai iya cutar da ita, na ja kujera na zauna kusa da Daddy, Yaya Abubakar ya turo min plate a hankali, "Ki ci," na ɗaga ido na kalle shi, na yi masa murmushi, "Thank you, Yaya," ya ɗan gyada kai, sannan ya koma ga abincinsa, shi ba ya yawan magana da ni kamar sauran ’yan uwanmu, amma kulawarsa tana da nata salon, wani lokaci yana lura da abin da nake buƙata tun kafin in furta shi, na fara cin abincina a hankali, yayin da sauran suke ci gaba da hira, sai na lura Daddy ya yi shiru, na ɗaga kai, na kalle shi, yana kallona, amma ba irin kallon da ya saba yi mini ba, fuskarsa ta ɗan sauya, murmushin da yake yi tun da farko ya yi rauni kaɗan, na tsaya da cokalin da nake riƙe da shi a hannuna, "Daddy?" Ya ɗan girgiza kai, kamar yana ƙoƙarin kawar da wani tunani, "Hmm?" Na karkatar da kai, "Are you okay?" Ya yi murmushi, amma a wannan karon murmushin bai kai idanunsa ba, "I’m fine, princess," na ɗan zuba masa ido, "Are you sure?" Ya ɗan yi shiru, kafin ya miƙa hannu ya gyara min wani ɗan yatsin gashin da ya fito daga inda na daure shi, "Inteesar…" "Na’am, Daddy?" Ya ɗauki lokaci kafin ya sake magana, "Ki daina fita ke kaɗai, Banaso," na lumshe ido, na ɗan yi murmushi, "Why, Daddy? I’m not a little girl anymore," ya ɗan matse gira, yana kallona cikin wani irin natsuwa, "I know you’re growing up, princess, but that doesn’t mean I won’t worry about you," na turo baki, "Daddy, you worry too much," ya yi murmushi kaɗan, amma sai ya sake kallona da idanu masu ɗauke da wani abu da ban iya fassarawa ba, "Saboda duniya ba kullum take da kyau kamar yadda wannan gidan yake ba," maganarsa ta sa na ɗan yi shiru, na kalli fuskarsa, ina ƙoƙarin fahimtar abin da yake nufi, "Daddy… what do you mean?" Bai amsa nan take ba, ya sauke cokalin da yake riƙe da shi, ya ɗan jingina da bayan kujerarsa, sai ya ce a hankali, "Ki yi hankali da mutanen da za ki haɗu da su a rayuwa, Inteesar, ba kowa ne yake yi miki murmushi saboda yana son alherinki ba," na lumshe ido a hankali, ban saba jin Daddy yana magana da irin wannan yanayin ba, ya kasance mutum mai nutsuwa, mai son mu yi farin ciki, kuma ba ya yawan saka damuwarsa a gabanmu, na ɗan matsa kusa da shi, "Daddy, you’re scaring me," ya yi murmushi, wannan karon ya ɗan fi na baya, sannan ya kama hannuna, "There’s nothing to be scared of, princess, just be careful, okay?" Na gyada kai a hankali, "Okay, Daddy," ya matse hannuna kaɗan kafin ya sake shi, na koma cin abincina, amma a zuciyata akwai wani abu da ya fara motsawa, wani irin tunani da ban san daga ina ya fito ba, me ya sa Daddy yake faɗin waɗannan maganganun? Me ya sa fuskarsa ta canza lokacin da yake kallona? Me ya sa yake magana kamar akwai wani abu da yake tsoro zai faru? Na ɗan kalli fuskarsa a ɓoye, yana ci gaba da cin abincinsa, yana sauraron hirar sauran ’yan uwana kamar komai yana daidai, na girgiza kai a hankali, na kawar da tunanin, maybe I’m just overthinking, na sake murmushi, na koma shiga hirar da sauran suke yi, a wannan lokacin, ban san komai ba, ban san abin da rayuwa ta tanadar mini ba, ban san cewa duniyar da nake ganin babu abin da zai iya girgiza ta za ta iya sauyawa a cikin ɗan lokaci ba, ban san cewa wata rana zan tuna waɗannan kalmomin Daddy, in ji zuciyata ta tsage saboda na fahimci ma’anarsu a lokacin da ya riga ya yi latti, domin a lokacin… ni ce kawai Inteesar Kabeeru, gimɓiyar gidan Alhaji Kabeeru, yarinyar da ta yi imani cewa muddin Daddy yana kusa da ita, babu wani abu a duniya da zai iya cutar da ita, amma rayuwa tana da nata tsarin, kuma wani lokaci, kaddara tana fara rubuta labarinta ne tun kafin mu san cewa muna cikin labari.
JUNE 2026