FreeArewaPen original
KADDARAR ZUCIYA
- 1views
- 1chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
A passionate Hausa fiction writer, storyteller, and lover of beautifully complicated stories. I write about love, family, emotions, and the realities hidden behind every heart.💕🌚✍️
Sample · GIMBIYAR GIDAN ALHAJI KABEERU
*A NOTE FROM THE AUTHOR 🥹❤️*I'm not making empty promises when I say Kaddarar Zuciya is more than just a story to me, I wrote it from the deepest part of my heart, there were moments I cried while writing it, and moments I smiled like someone experiencing the scenes herself, every emotion, every pain, every little happiness… I felt them while writing this book, and if there's one story I'll always hold close to my heart, it will be Kaddarar Zuciya, it will forever be my favorite story I've ever written, so, dear readers, as you turn these pages, just know that you're not only reading a story; you're reading a piece of my heart.🥹*BISMILLAHIRRAHMAN ARRAHIM**KADDARAR ZUCIYA**CHAPTER ONE (1)**GIMBIYAR GIDAN ALHAJI KABEERU**JIDDAAH BARKUM*———"Inteeessarrr!" Muryar Khalil ta cika gidan da ƙarfi, har sai da na ji kamar bangon falon ma yana amsa kiransa, na ɗan haɗe fuska, ina zaune cikin kasala a kan kujera mai laushi, idanuwana a kan talabijin, duk da cewa hankalina bai kai ga abin da ake nunawa ba, na san Khalil yana nemana, amma saboda na san me zai biyo baya, sai na yi kamar ban ji shi ba, "Ban ji ba!" na amsa a hankali, ina ɗan ɗaga murya kaɗan kamar mai gaskiya, sai na ɗan ciji leɓena don kada dariyar da ke neman subuce mini ta bayyana, ban gama rufe bakina ba sai na ji takunsa yana tahowa da sauri, "Inteesar! Wallahi yau idan na kama ki, kin ga taki!" Wannan karon na kasa riƙe dariyata, na zabura daga kan kujerar, na yi hanyar kitchen da gudu, ina dariya kamar wata yarinya da aka kama da laifi, "Mommyyy! Ki ce masa ya bar ni mana!" Na shige kitchen ɗin da sauri, na buya a bayan Mommy Haleema, ina riƙe da gefen rigarta da hannuwana biyu, na leƙo da kai kaɗan, ina kallon ƙofar kitchen ɗin don ganin ko Khalil ya shigo, Mommy Haleema ta juya a hankali, ta sauke kallonta a kaina, fuskarta ɗauke da murmushi, yayin da ta ɗaga gira ɗaya, "Ke kuma, what have you done this time?" Na buɗe baki zan yi magana, amma ban samu damar yin hakan ba saboda Khalil ya shigo kitchen ɗin a fusace, ya tsaya yana nuna ni da yatsa, fuskarsa cike da alamar rashin yarda, "Mommy, please! Ki tambaye ta abin da ta yi, ta ɗauki key ɗin motata ta fita da ita, bayan kin san sau nawa na gaya mata kada ta sake taɓa motar nan ba tare da izinina ba!" Na zaro idanuwa, na fito daga bayan Mommy kaɗan, "Excuse me! Ni fa ban sace maka mota ba!" Khalil ya haɗe hannayensa a ƙirji, yana kallona da wani irin kallo na really? "Really, Inteesar? So what do you call taking my car without permission?" Na turo baki, na kau da kai gefe kamar ni ce aka zalunta, "Na ga ka yi barci ne, I only took it for a short drive, na dawo lafiya fa!" Ya buɗe baki, ya sake rufewa, kamar maganganun da nake yi suna ƙara masa hauka, "Short drive?!" ya maimaita, yana nuna kansa, "Ke kin san nawa na kashe wajen motar nan ...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.