41
💕 NUFIN ALLAH 💕
By
Anisa Muhammad yahaya
YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION YOTA
Page 4️⃣1️⃣
Ba ita ta tashi da safe ba sai after 10 dan bata saba wuce 3 bata kwanta ba
Amman jiya tun 2 bata koma ba kuma sai after 5 shiyasa ta kasa tashi
Toilet ta nufa, brush tayi, tayi wanka sannan ta fito, kaya ta nema mara nauyi ta saka, ta fesa turaren ta na lúne de éte me daɗin kamshi
Wayar ta ta dauko ta duba time, zaro ido tayi ganin 12 ta kusa, cikin ta ta ɗan taɓa tace
"Allah sarki no wonder nike jin yunwa"
Fitowa tayi bayan ta gyara ɗakin, ɗakin Ammi ta nufa, tana shiga taga su Batul na gyaran ɗakin
Sam ta manta suna gidan gaba ɗaya, duk wannan fitinar tasu bayi suke ba bare ka gane suna nan, sun koma zaman daki saboda Ya Umar
"Adda ina kwana"
"Lafiya klau ya kuke"
"Alhamdulillah kin sha bacci yau" faɗin Batul
"Hmm kedai bari, me kuka dafa da safe"
"Tea and bread ne" fadin Khadijah
"Bread!! Tabb yunwa ɗa nike ji yafi ƙarfin in ci wani breadi yanzu"
Fitowa tayi daga ɗakin
Ammi tagani a parlour ta juya ta koma inda take
"Ammi ashe kina nan,wai baku yi breakfast bane Ammi??"
"Maisa baza muyi breakfast ba, munyi mana"
"Breadi fah, nifa ban daukan bread a matsayin abin ci"
"Yoo daman ina zaki ɗauka,ci kamar gara Amman ba ƙiba, kamar a hure ki ki faɗi"
"Kai Ammi ni din, to nidai bara inje in nemi abinda zanci"
"Ki gama kuma kizo ki koma gidan Antyn ku ba kin baro cikin ƴanuwan ki"
"Amman Ammi tare zamu je koh"
"Saboda me yasa fah"
"Sai ki faɗawa Abba kin jiii"
"Wai saboda ni nafi kowa rashin hankali da kunya da rashin ta ido, nafi kowa son ɗiya shine zanje dan nice ma bakin naki koh??"
"A'a ba haka bane ai,to nidai in ba zaki je ba Nima ina nan ba inda zan koma"
"Ke dai kika sani dan indai Abban kune me iya biyo ki har nan ne kin san halin shi, kuma kika mai shirme ya baki kashe ba ruwan sa"
Baki ta tura gaba ta tashi tace"nidai na tafi nemar wa ciki na food"
"Allah dai ya kyauta miki da wannan cin naki, ace wai breadi ne mutum zai ce bazai ƙosar dashi ba"
Ahmad ne ya shigo parlourn yana waya, ya zauna kusa da Ammi yana murmushi, yace
"Ammi na gaida ki, sai anjima" sannan ya kashe wayar
"Ina wuni Ammi na"
Kallon shi tayi tace"lapiya kalau Babana kai da waye haka"
"Nabila ce fah, itama tace tana gaida ke"
"Uhmm su Ya Ahmad ƴan soyayya, ina jin rank ɗin Romeo ya kamata a dawo dashi kanka" fadin Anisa tana wajen kofar kitchen
"Ai ni in gaya miki nafi Romeo, bare Majnun"
"To dai Allah kyauta muku, iyayen soyayya baku barin kunnen mu ya huta da surutan junan ku kullum" ta faɗa tana shigewa
"Abinci zaki dafa mana"
"Kaima yunwa kake ji??"
"Eh wallahi Ammi ji nayi har ciki na ya rarike kamar ba ɗazu naci abinci ba"
"A gaishe ku wannan dai idan ba tsutsotsin ciki ke damun kuba se shegen ci a cikin kunnan, har gwara ma dai kai Baba ana gani a jikin ka, amma waccen taliyar da kamar a karya ta a riƙo ɗaya tafi kowa bani mamaki, gaskiya kuyi deworming"
''Ammi fa ba wani tsutsar ciki duka duka yaushe mukayi deworming ko kin manta ne''
'' to Allah ya kyauta ya yaye muku''
Abinda kawai tace kenan dan yau bama suyi breakfast da wuri ba,saboda duk bada wuri suka tashi ba har gwara ma su Batul Amman su kam har ita sai kusan 11 sukayi yanzu ko 1 beyi ba
Tashi yayi yabi bayanta yana faɗin
"Sister me zaki dafa mana"
"Zan dafa ma kaina dai"
"A'a gaskiya ki dafa dani in ba haka ba wallahi kika dafa iya naki to ki tabbatar daukewa zanyi saidai ki dafa wani"
"Gaskiya ya Ahmad budget zaka ɓata mun, nida nike son yi sharp Sharp, to mema zanyi"
"Kawai ki saka mana ɗanwake"
"Ɗanwake fah yah kawai in kama cin mai da yaji kayan ulcer daga tashi na tabb"
"Ai ya ma fi daɗi a matsayin breakfast Zan ma ɗibo miki flourn"
"Ya Ahmad ka iya dadin baki in kana son abu, Nabila zatayi fama, dan ina ji har sai ta tsani taga ɗanwake"
"Hmm ke ai ɗanwaken ne duniya ba zaki gane ba"
"Aikam dai indai ɗanwake ne kam ba ganewa zanyi ba"
Zama yayi a kitchen ɗin yana mata surutu, dan Ahmad indai ana ɗanwake kullum yana bakin gurin har agama dan a duniyar nan ba abinda yake so sama da shi, be ƙi ba ace kullum ayi ta yi safe rana dare, a cewar sa ko na kwano ɗaya akayi aka kawo mai seya cinye
Tana gamawa ta saka musu kowa a plate suka fito sai labarin Nabila yake mata dan a rayuwar nan indai fa zai zauna a guri karya ne ya tashi beyi zancen nabila ba sai dai ko idan suna tare da Ammah shima kuma dan kunyarta da yake jine
Dan ita Amma duk da faɗan ta da sakewar ta tanada kunyar ɗan fari ita kam Ammi bata da wannan, Amma ce ta gado shi yasa yafi sabawa da Ammi
Dining suka zauna har sun fara ci sai ga Ya Faruq ya shigo parlourn, Ammi ya gaisar ya nufo inda suke, zama yayi kan kujerar dake gefen ta yana kallon su
Dan taɓe baki yayi sai ya kalla plate ɗin sai kuma yace
"Ni ina nawa"
Ɗagowa tayi ta kalle shi, Ahmad ne yace
"Iya mu biyu ne ba naka"
Hararar shi yayi ya tashi ya nufi kitchen, Bai jima ba ya dawo ɗauke da fork, komawa yayi ya zauna inda ya tashi
Fork ɗin ya saka a abincin ta be ce mata komai ba,motsawa yayi ya dauka guda ɗaya yakai baki
Ɗagowa tayi ta kalle shi ta kalli abincin tana kwabe fuska, ƙin kallon ta yayi, saida ya kai kusan spoon uku sannan ya kalle ta ganin bata fara ci ba
"Baza kici bane"
Kai ta kawar gefe tana ƙunƙuni a ƙasan ranta
"In gama dafawa amman a ringa tambayar ko zanci ma hmm"
Ganin haka ya ja plate ɗin gaban shi ya cigaba da cin abun shi ko a jikin sa, da sauri ta juyo tana kallon shi,ta kalle shi ta kalli abincin tace
"Yahh banfa ci komai ba"
Shima kallon ta yayi sai ya matso da plate ɗin tsakiyar su yace
"Eat"
Hannu takai zata ja plate ɗin gaban ta yayi saurin riƙewa, to wai taya yake expecting suci abinci a kwano ɗayane ma,
Kallon tayi ya ƙara ɗaga mata gira yana nuni da plate ɗin alamar taci
''Is he for reals'' ta faɗa a ranta, taya ma zata fara suci abinci a plate ɗaya, ɗagowa tayi suka haɗa ido ta kwabe fuska, shikam ya haɗe rai ba alamar ma wasa a fuskarsa
Follow and like my account on arewapen ba dan halin wannan marubuciyar ba dan Allah 🥹 🙏 🙏 🙏 🙏 🙏 🙏 🙏
______________________
By
Anisa Muhammad yahaya 🌺